Ka Dauki Sabon Hali kuma Ka Ci gaba da Hakan
‘Ku yafa kuma sabon mutum.’—KOL. 3:10.
WAƘOƘI: 43, 106
1, 2. (a) Me ya sa za mu iya kasancewa da sabon hali? (b) Waɗanne irin halaye masu kyau ne aka ambata a littafin Kolosiyawa 3:10-14?
LITTAFI MAI TSARKI ya ambata “sabon mutum.” (Afis. 4:24; Kol. 3:10) Wannan furucin yana nufin wasu halaye ne da ake sabontawa “bisa ga Allah.” Kuma mutane za su iya koyan irin waɗannan halayen. Me ya sa? Don Jehobah ya halicce mu a cikin kamaninsa, saboda haka za mu iya nuna halayensa masu kyau.—Far. 1:26, 27; Afis. 5:1.
2 Da yake mun gāji zunubi daga iyayenmu na farko, muna iya yin sha’awar da ba ta dace ba. Wataƙila ma abubuwan da ake yi a yankinmu zai iya shafanmu. Duk da haka, za mu iya zama irin mutanen da yake so. Za mu bincika wasu halaye da aka hure manzo Bulus ya rubuta don mu iya yin hakan. (Karanta Kolosiyawa 3:10-14.) Ban da haka ma, za mu bincika yadda za mu nuna irin waɗannan halayen sa’ad da muke wa’azi.
DUKANKU ƊAYA NE
3. Wane hali mai kyau ne ya kamata mu kasance da shi?
3 Bayan da manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu ɗauki sabon hali, sai ya ce rashin son kai yana cikin irin waɗannan halaye masu kyau. Ya ce: “Ba shi yiwuwa a ce da Ba-helleni da Ba-yahudi, da kaciya da rashin kaciya, da baubawa, Sikitiyu, bawa, ɗa.” * Me ya sa bai kamata mutum ya riƙa nuna cewa ya fi wani don kabilarsu da ƙasarsu da kuma matsayinsa ba? Domin mu mabiyan Kristi na gaskiya “ɗaya ne.”—Kol. 3:11; Gal. 3:28.
4. (a) Yaya ya kamata Shaidun Jehobah su riƙa bi da mutane? (b) Me zai iya sa ya yi wa Kiristoci wuya su kasance da haɗin kai?
4 Idan muna da wannan sabon hali da aka ambata, za mu riƙa daraja mutane ko da daga wace irin kabila ko ƙasa suka fito. (Rom. 2:11) Amma hakan yana yin wuya a wasu ƙasashe. Alal misali, a dā a Afirka ta Kudu, hukuma ta ware wani wuri da mutanen wasu kabilu za su riƙa zama kuma har yanzu mutane suna zama a wurin har da Shaidu ma. Don haka, a watan Oktoba na shekara ta 2013, Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yi wani shiri na musamman don ’yan’uwa su yi tarayya da juna. (2 Kor. 6:13) Mene ne hakan ya ƙunsa?
5, 6. (a) Wane shiri aka yi don ’yan’uwa su kasance da haɗin kai? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.) (b) Wane sakamako ne aka samu?
5 ’Yan’uwan sun yi shiri cewa a kowane mako, ikilisiyoyi biyu da suke yare dabam-dabam za su taru don su shaƙata. ’Yan’uwa da suke waɗannan ikilisiyoyin sukan fita wa’azi tare su halarci taro kuma su ziyarci juna. Ikilisiyoyi da yawa sun yi hakan kuma ofishin Shaidun Jehobah a ƙasar sun sami rahoto masu kyau har daga mutanen da ba Shaidu ba. Alal misali, wani limami ya ce, “Ko da yake ni ba Mashaidi ba ne, amma kuna da tsari mai kyau na yin wa’azi kuma kuna da haɗin kai sosai.” Ta yaya wannan shirin da aka yi ya shafi Shaidu?
6 Da farko, wata ’yar’uwa da take yaren Xhosa mai suna Noma tana jin tsoron gayyatar turawa da suke ikilisiyar Turanci zuwa gidanta. Amma bayan da ta yi wa’azi tare da turawan kuma ta ji daɗin shaƙatawa da su, sai ta ce, “Su ma mutane ne kamar mu!” Kuma da lokaci ya yi don ikilisiyar da suke yaren Xhosa su gayyaci ’yan’uwa da suke Turanci, sai ta dafa abinci kuma ta gayyaci wasu ’yan’uwa har da wani dattijo, bature. Noma ta ce, “Na yi mamaki cewa wannan ɗan’uwan ya zauna a kan kiret na lemun kwalba da aka ajiye a ƙasa.” Kuma sakamakon da ake samuwa a yin haka shi ne ’yan’uwa suna ƙulla abokantaka da juna kuma sun ce za su ci gaba da cuɗanya da ’yan’uwa.
TAUSAYI DA ALHERI
7. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance masu tausayi?
7 Za mu ci gaba da fuskantar matsaloli har sai an kawo ƙarshen duniyar Shaiɗan. Muna fama da rashin aiki da cuta da tsanani da bala’i kuma muna asarar dukiyarmu. Don haka, muna bukatar mu zama masu tausayi idan muna son mu riƙa taimaka wa juna. Idan muna da tausayi za mu riƙa yi wa mutane alheri. (Afis. 4:32) Za mu iya yin koyi da Allah kuma mu taimaka ma wasu idan mu masu tausayi ne kuma muna alheri.—2 Kor. 1:3, 4.
8. Mene ne sakamakon nuna wa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya juyayi da kuma alheri? Ka ba da misali.
1 Kor. 12:22, 25) Alal misali, Dannykarl ya ƙaura daga Filifin zuwa ƙasar Jafan. Don shi baƙo ne, ba a bi da shi a wurin aikinsa kamar yadda ake bi da mutanen ƙasar ba. Sai ya halarci taron Shaidun Jehobah. Dannykarl ya ce: “Kusan kowa da ya halarci taron ɗan Jafan ne, amma sun marabce ni sosai kamar sun waye ni a dā.” Alherin da ’yan’uwa suka nuna masa ya sa ya ci gaba da kusantar Jehobah. Da shigewar lokaci, Dannykarl ya yi baftisma, kuma shi dattijo ne yanzu. Sauran dattawa a ikilisiyarsu suna farin ciki cewa Dannykarl da matarsa Jennifer suna tare da su, kuma sun ce: “Da yake su majagaba ne, sun sauƙaƙa rayuwarsu kuma sun kafa misali mai kyau na saka al’amuran Mulkin Allah a kan gaba.”—Luk. 12:31.
8 Ta yaya za mu nuna alheri ga waɗanda suka zo daga wasu ƙasashe da kuma matalauta da suke ikilisiyarmu? Ya kamata mu zama abokansu kuma mu sa su ji cewa suna da muhimmanci a ikilisiyar. (9, 10. Ka ba da misalin sakamako da ake samu idan muka ji tausayin mutane sa’ad da muke wa’azi.
9 Muna da zarafin yin “nagarta zuwa ga dukan mutane,” sa’ad da muka yi musu wa’azi game da Mulkin Allah. (Gal. 6:10) Shaidu da yawa suna jin tausayin baƙi, don haka suke ƙoƙarin su koyi yarensu. (1 Kor. 9:23) Wannan ya kawo sakamako masu kyau. Alal misali, wata ’yar’uwa majagaba a Ostareliya da sunanta Tiffany ne ta koyi yaren Swahili don ta taimaka wa wata ikilisiya da ake yaren Swahili a birnin Brisbane. Ko da yake yin hakan bai yi mata sauƙi ba, rayuwarta ta ƙara kasancewa da ma’ana. Ta ce: “Idan kana so ka ji daɗin hidimarka, ka yi hidima a ikilisiyar da ake wani yare. Yana kamar ka je wani wuri ba tare da ka fita daga inda kake ba. Za ka san game da ’yan’uwanmu da ke faɗin duniya kuma ka ga yadda suke da haɗin kai.”
10 Wata iyali a Jafan ma sun yi hakan. ’Yarsu Sakiko ta ce: “A shekara ta 1990 zuwa 1999, mukan haɗu da mutanen da suka fito daga Brazil a lokacin da muke wa’azi. Sa’ad da muka karanta musu nassosi kamar su Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 ko kuma Zabura 37:10, 11, 29 a yaren Portugal, suna saurarawa kuma wani lokaci su zub da hawaye. Amma iyalin suna son su taimaka musu. Sakiko ta ce: “Sa’ad da muka ga cewa suna so su koya game da Jehobah, sai dukanmu a iyali muka soma koya yaren Portugal.” Daga baya, iyalin suka taimaka don a kafa ikilisiya na yaren Portugal. Da shigewar shekaru, iyalin sun taimaki mutane da yawa da suka ƙauro daga Brazil su soma bauta wa Jehobah. Sakiko ta ƙara da cewa: “Sai da muka dage sosai kafin muka koyi yaren, amma albarka da muka samu ya fi fama da muka yi, muna godiya ga Jehobah sosai.”—Karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
KA ZAMA MAI TAWALI’U
11, 12. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da muradin da ya dace idan muna so mu ɗauki sabon hali? (b) Mene ne zai taimaka mana mu zama masu tawali’u?
11 Abin da ya sa muke ɗaukan sabon hali shi ne don mu ɗaukaka Jehobah ba don mutane su yabe mu ba. Ka tuna cewa wani mala’ika da a lokacin da aka halicce shi kamili ne ya zama mai fahariya kuma ya yi zunubi. (Gwada Ezekiyel 28:17.) Saboda haka, zai fi yi wa ’yan Adam wuya su guji fahariya da girman kai don su ajizai ne! Duk da haka, zai yiwu mu zama masu tawali’u. Mene ne zai taimaka mana mu yi hakan?
12 Muna bukatar mu keɓe lokaci don mu riƙa bimbini kullum a kan abin da muka karanta a Kalmar Allah. (K. Sha. 17:18-20) Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne yin bimbini a kan abin da Yesu ya koya mana da kuma misalin da ya kafa mana na zama masu tawali’u. (Mat. 20:28) Yesu ya wanke ƙafafun manzanninsa. (Yoh. 13:12-17) Don haka, muna bukatar mu riƙa addu’a a kai a kai don ruhun Allah ya taimaka mana mu guji halin ganin cewa mun fi wasu.—Gal. 6:3, 4; Filib. 2:3.
13. Mene ne amfanin zama masu tawali’u?
13 Karanta Misalai 22:4. Jehobah yana so mu zama masu tawali’u. Zama masu tawali’u zai sa ’yan’uwa a ikilisiya su zama masu salama da kuma haɗin kai. Ƙari ga haka, za mu samu alherin Allah. Manzo Bitrus ya ce: “Dukanku kuwa ku ɗaura kanku da tawali’u, da za ku bauta ma juna: Gama Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana ba da alheri ga masu-tawali’u.”—1 Bit. 5:5.
KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI DA HAƘURI
14. Wane ne ya fi kafa mana misali mai kyau na sauƙin kai da haƙuri?
14 A yau, mutane suna ɗaukan masu sauƙin kai da haƙuri kamar marasa ƙarfi ne. Amma, hakan ba gaskiya ba ne! Don Jehobah wanda ya fi kowa iko yana da waɗannan halaye masu ƙayatarwa. Jehobah ne ya kafa misali mafi kyau na kasancewa da sauƙin kai da haƙuri. (2 Bit. 3:9) Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya kasance da haƙuri a lokacin da ya tura mala’ikunsa zuwa wurin Ibrahim da Lutu kuma suka yi masa tambayoyi. (Far. 18:22-33; 19:18-21) Ƙari ga haka, fiye da shekaru 1,500, Jehobah ya yi haƙuri da al’ummar Isra’ila.—Ezek. 33:11.
15. Wane misali ne Yesu ya ƙafa mana na zama mai tawali’u da haƙuri?
15 Yesu “mai-tawali’u ne.” (Mat. 11:29) Ya yi haƙuri sosai da kasawar almajiransa. A lokacin da yake hidima a duniya, masu adawa da shi sun zage shi. Duk da haka, Yesu ya zama mai tawali’u da haƙuri har lokacin da aka kashe shi. Sa’ad da yake shan azaba a kan gungume, ya yi addu’a cewa Ubansa ya gafarta ma waɗanda suke gana masa azaba cewa “ba su san abin da suke yi ba.” (Luk. 23:34) Babu shakka, Yesu ya kafa mana misali mafi kyau na tawali’u da haƙuri a lokacin da yake shan wahala.—Karanta 1 Bitrus 2:21-23.
16. Ta yaya za mu zama masu sauƙin kai da haƙuri?
Kol. 3:13) Hakika, muna bukatar mu zama masu sauƙin kai da haƙuri kafin mu bi wannan umurnin. Amma, idan muna gafarta wa ’yan’uwa, hakan zai sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai.
16 Ta yaya za mu zama masu sauƙin kai da haƙuri? Bulus ya ambata hanya ɗaya sa’ad da ya rubuta wa ’yan’uwa cewa: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi.” (17. Me ya sa sauƙin kai da haƙuri suke da muhimmanci?
17 Jehobah yana bukatar mu zama masu sauƙin kai da haƙuri. Idan muna son mu sami ceto, wajibi ne mu kasance da waɗannan halayen. (Mat. 5:5; Yaƙ. 1:21) Abin da ya fi muhimmanci shi ne, idan muka nuna waɗannan halayen za mu ɗaukaka Jehobah kuma mu taimaka wa mutane su bi shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.—Gal. 6:1; 2 Tim. 2:24, 25.
KA RIƘA NUNA ƘAUNA
18. Wace alaƙa ce ke tsakanin ƙauna da rashin nuna bambanci?
18 Dukan halayen da muka bincika suna da alaƙa da ƙauna. Alal misali, almajiri Yaƙub ya gargaɗi ’yan’uwansa domin suna nuna cewa su masu arziki ne kuma sun fi talakawa muhimmanci. Ya gaya musu cewa hakan ya saɓa wa dokar Allah da ta ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” Sai ya daɗa cewa: “Idan kuna tara, zunubi kuke yi.” (Yaƙ. 2:8, 9) Idan muna ƙaunar mutane, ba za mu nuna musu bambanci domin ba su da ilimi ko don ƙabilarsu ko kuma matsayinsu ba. Ba zai dace mu nuna cewa ba ma nuna bambanci a baki kawai ba, ya kamata mu yi hakan da gaske.
19. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa nuna ƙauna?
19 Ƙauna kuma tana sa mutane su yi “haƙuri da kirki” kuma ba za su riƙa yin girman kai ba. (1 Kor. 13:4, Littafi Mai Tsarki) Muna bukatar mu zama masu haƙuri da kirki da kuma tawali’u domin mu ci gaba da yi wa mutane wa’azi. (Mat. 28:19) Ƙari ga haka, waɗannan halayen suna sa ya yi mana sauƙi mu riƙa cuɗanya da dukan ’yan’uwanmu a ikilisiya. Mene ne sakamakon yin hakan? Mutane za su ga cewa muna da haɗin kai kuma su soma bauta wa Jehobah. Shi ya sa ya dace da Littafi Mai Tsarki ya kammala wannan batun da cewa: “Gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.”—Kol. 3:14.
KA CI GABA SABONTA HALINKA
20. (a) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa? (b) Wane lokaci ne muke jira?
20 Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Mene ne zan ƙara yi don na canja halina kuma kada in koma gidan jiya?’ Muna bukatar mu yi addu’a don Jehobah ya taimaka mana, kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu shawo kan kowane hali da zai hana mu shiga Mulkin Allah. (Gal. 5:19-21) Ƙari ga haka, muna bukatar mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Shin ina ci gaba da sabonta ra’ayina don na faranta ran Jehobah?’ (Afis. 4:23, 24) Domin mu ajizai ne, muna bukatar mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu riƙa sabonta halinmu. Za mu ji daɗin rayuwa sa’ad da kowa ya sabonta halinsa kuma ya yi koyi da halayen Jehobah sosai!
^ sakin layi na 3 A zamanin dā ana raina Sikitiyu don ana ganinsu ’yan ƙauye ne.