Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Mu Kawar da Halin Banza

Yadda Za Mu Kawar da Halin Banza

Ku “tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa.”​—KOL. 3:9.

WAƘOƘI: 83, 129

1, 2. Mene ne aka lura game da Shaidun Jehobah?

MUTANE da yawa sun lura cewa halin Shaidun Jehobah ya bambanta da na sauran mutane. Alal misali, wani marubuci mai suna Anton Gill ya yabi Shaidun a lokacin da Nazi suke mulki a ƙasar Jamus, ya ce: “Yan Nazi sun tsani Shaidun Jehobah sosai.  . . A shekara ta 1939 an riƙe Shaidu 6,000 a [sansanin fursuna].” Duk da cewa sun sha wahala sosai, an lura cewa za a iya tabbata da su, sun natsu ko da yake ana matsa musu, sun kasance da aminci ga Allah da kuma haɗin kai.

2 A kwanan baya, mutane a Afirka ta Kudu sun lura da wani hali mai kyau game da Shaidun Jehobah. Akwai lokacin da Shaidu ba sa cuɗanya da juna a ƙasar domin launinsu ya bambanta da juna. Amma abin mamaki ne cewa a ranar Lahadi na 18 ga Disamba ta 2011, ’yan’uwanmu fiye da 78,000 daga wurare dabam-dabam daga Afirka ta Kudu da kuma wasu ƙasashe sun halarci taro a wani babban filin wasa da ke birnin Johannesburg don su ji jawaban Littafi Mai Tsarki. Wani manajan filin wasan ya ce: “Ban taɓa ganin mutane masu halin kirki kamar waɗannan mutanen ba. Dukansu sun yi ado da kyau. Kuma kun share wannan filin da kyau. Mafi muhimmanci ma, kuna son mutane da suka fito daga kowace ƙasa.”

3. Me ya sa muka bambanta da sauran addinai?

3 Da yake waɗanda ba Shaidun Jehobah ba sun yi wannan furuci, hakan ya nuna cewa da gaske halinmu ya yi dabam da na sauran mutane. (1 Bit. 5:9) Me ya sa muka bambanta da sauran addinai? Dalilin shi ne Kalmar Allah da ruhu mai tsarki suna taimaka mana mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kawar da halinmu na dā kuma mu ɗauki sabon hali.​—Kol. 3:​9, 10.

4. Me za a bincika a wannan talifin, kuma me ya sa?

4 Bayan mun kawar da halinmu na dā, muna bukatar mu ci gaba da yin hakan. A wannan talifin, za mu bincika yadda za mu kawar da halin banza da dalilin da ya sa yin hakan yake da muhimmanci yanzu. Kuma za mu ga cewa zai yiwu mutum ya canja salon rayuwarsa duk da cewa ya yi munanan ayyukan sosai a dā. Ƙari ga haka, za mu bincika abin da waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah za su iya yi don su kawar da halin banza. Me ya sa muke bukatar wannan tunasarwa? Domin wasu da suke bauta wa Jehobah a dā sun koma gidan jiya. Saboda haka, dukanmu muna bukatar mu tuna da wannan gargaɗin: “Wanda yake mai da kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.”​—1 Kor. 10:12.

KA “MATAR” DA KOWACE IRIN SHA’AWAR “FASIKANCI”

5. (a) Ka faɗi dalilin da ya sa yake da muhimmanci yanzu mu kawar da halin banza. (Ka duba hoton da ke shafi na 17.) (b) Waɗanne halayen banza ne aka ambata a Kolosiyawa 3:​5-9?

5 Me za ka yi idan kayanka ya yi datti, ko wataƙila ma yana wari? Babu shakka, za ka tuɓe kayan nan da nan. Hakazalika, muna bukatar mu yi wani abu da gaggawa don mu yi biyayya ga umurnin da aka ba mu na kawar da banzan hali da Jehobah ya tsana. Ya kamata mu bi umurnin da Bulus ya ba Kiristoci a zamaninsa: “Ku kawar da dukan waɗannan.” Bari mu bincika halayen banza guda biyu da Bulus ya ambata, wato fasikanci da ƙazanta.​—Karanta Kolosiyawa 3:​5-9.

6, 7. (a) Ta yaya furucin Bulus ya nuna cewa muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu kawar da halin banza? (b) Wace irin rayuwa ce Sakura ta yi, amma me ya taimaka mata ta canja salon rayuwarta?

6 Fasikanci. Kalmar Littafi Mai Tsarki na asali da aka fassara zuwa “fasikanci” ta ƙunshi mutane biyu da ba su yi aure ba amma suna yin jima’i har da luwaɗi. Bulus ya gaya wa Kiristoci su “matar” da ‘gaɓaɓuwansu,’ wato su kawar da dukan sha’awoyi da za su iya sa su yi “fasikanci.” Furucin da Bulus ya yi amfani da shi ya nuna cewa suna bukatar su ƙoƙarta don su kawar da sha’awoyin banza. Duk da haka, za su iya shawo kan waɗannan sha’awoyin.

7 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Sakura * ’yar Jafan. Ta yi fama da kaɗaici kuma tana baƙin ciki sa’ad da take girma. Sai ta soma fasikanci da mutane dabam-dabam tun daga lokacin da take ’yar shekara 15. A sakamakon haka, ta ce: “Na zubar da ciki sau uku.” Ta daɗa cewa: “Da farko na samu kwanciyar hankali sa’ad da nake lalata, ina ganin cewa mutanen suna so na. Amma da na ci gaba da yin fasikanci, sai na ga cewa ba ni da kwanciyar hankali.” Sakura ta ci gaba da irin wannan halin har sai da ta kai shekara 23. Sai ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma ta ji daɗin abin da take koya. Kuma Jehobah ya taimaka mata ta daina irin rayuwar da take yi da yake sa ta baƙin ciki da kuma kunya. Yanzu Sakura tana hidimar majagaba na kullum, ba ta jin kaɗaici kuma. Maimakon haka, kamar yadda ta ce, “Ina farin ciki matuƙa cewa Jehobah yana ƙauna ta sosai.”

YADDA ZA KA DAINA HALIN BANZA

8. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa mutum ya zama ƙazami a gaban Allah?

8 Ƙazanta. Kalmar Littafi Mai Tsarki na asali da aka fassara zuwa “ƙazanta” za ta iya yin nuni ga abubuwa da yawa da suka ƙunshi wasu halayen banza ba fasikanci kaɗai ba. Ban da haka ma, tana iya nufin halin shan taba ko kuma maganganun banza. (2 Kor. 7:1; Afis. 5:​3, 4) Ƙari ga haka, ta ƙunshi ayyukan ƙazanta da mutum yake yi a ɓoye, kamar karanta littattafai da ke ta da sha’awar yin jima’i ko kallon batsa, da za su iya sa mutum ya soma yin wasa da al’aurarsa.​—Kol. 3:5. *

9. Ta da ‘sha’awa’ zai iya jawo wane mummunan sakamako?

9 Mutane da suke kallon batsa a kai a kai suna ta da ‘sha’awar’ da za ta sa ba za su iya kame kansu ba kuma hakan zai sa su mai da yin jima’i kamar cin abinci. Masu bincike sun lura cewa masu kallon batsa a kai a kai suna nuna halaye irin na masu yin maye da masu shan ƙwaya. Shi ya sa halin kallon batsa yakan jawo mummunan sakamako. Hakan yakan sa mutanen su riƙa jin kunya kuma ba za su riƙa aiki da ƙwazo ba, ban da haka ma, iyalansu ba za su riƙa farin ciki ba. Ƙari ga haka, zai iya sa a kashe aure da kuma kisan kai. Bayan wani mutum ya yi shekara ɗaya da daina kallon batsa, sai ya ce: “Daga baya, na samu mutuncin kaina.”

10. Ta yaya Ribeiro ya daina halin kallon batsa?

10 Mutane da yawa suna fama sosai kafin su daina kallon batsa. Amma, za su iya shawo kan wannan halin kamar yadda za mu gani daga labarin Ribeiro da ya fito daga Brazil. Ribeiro ya bar gida sa’ad da yake matashi kuma da shigewar lokaci ya soma aiki a kamfanin sake sarrafa littattafai, inda ya soma karanta jaridun batsa. Sai ya ce: “A hankali, ba na iya zama ba tare da kallon batsa ba. Abin ya yi muni sosai da ba na iya jiran budurwata da muke zama tare ta bar gida kafin in soma kallon bidiyon batsa.” Amma wata rana a wurin aiki, Ribeiro ya ga wani littafi mai jigo Asirin Farinciki na Iyali a cikin tarin littattafai da suke so su sake sarrafawa. Sai ya ɗauki littafin kuma ya karanta shi. Abin da ya karanta ya sa ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, amma ya ɗauki dogon lokaci kafin ya daina wannan halin banza. Mene ne ya taimaka masa? Ya ce: “Yin addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan abin da na koya sun taimake ni sosai, kuma hakan ya sa na fahimci halayen Allah har na soma ƙaunar Jehobah sosai fiye da sha’awar kallon batsa.” Da taimakon Littafi Mai Tsarki da ruhun Allah, Ribeiro ya canja halinsa, ya yi baftisma kuma yanzu shi dattijo ne a ikilisiya.

11. Mene ne zai taimaka wa mutum ya guji kallon batsa?

11 Ka lura cewa Ribeiro ya yi wasu abubuwa, ba kawai yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Ya keɓe lokacin yin bimbini sosai a kan abin da ya karanta a Littafi Mai Tsarki kuma ya bar hakan ya ratsa zuciyarsa. Ya yi addu’a ga Jehobah ya taimaka masa. Waɗannan abubuwa sun sa Ribeiro ya yi ƙaunar Jehobah sosai, kuma hakan ya sa ya shawo kan sha’awarsa na kallon batsa. Ƙaunar Jehobah sosai da kuma tsanan halin banza za su taimaka mana mu guji kallon batsa.​—Karanta Zabura 97:10.

KA DAINA FUSHI DA ZAGE-ZAGE DA ƘARYA

12. Mene ne ya taimaka ma Stephen ya daina fushi da zage-zage?

12 Wasu mutane suna saurin fushi da zage-zage. Kuma hakan yana sa iyalansu ba sa farin ciki. Wani mahaifi mai suna Stephen daga Australiya ya ce: “Nakan yi wa mutane ashar kuma na yi fushi a kan abin da bai taka karya ya karya ba. Ni da matata mun rabu sau uku kuma muna shirin kashe aurenmu.” Sai waɗannan ma’auratan suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Mene ne ya faru sa’ad da Stephen ya soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki? Ya ce: “Rayuwar iyalinmu ta gyaru sosai. Da taimakon Jehobah, yanzu ina da salama kuma na natsu, amma a dā nakan yi fushi sosai a duk lokacin da aka ɓata min rai, har in ji kamar zan fashe kamar bam.” Yanzu Stephen bawa ne mai hidima kuma matarsa tana hidimar majagaba shekaru da yawa yanzu. Dattawa da ke ikilisiyarsu Stephen sun ce: “Stephen shuru-shuru ne, ɗan’uwa ne mai aiki da ƙwazo kuma mai tawali’u.” Ba su taɓa ganinsa yana fushi ba. Shin Stephen yana yaba wa kansa ne don yadda ya canja halinsa? Ya ce: “Ba zan samu waɗannan albarka a rayuwata ba da a ce Jehobah bai taimaka min in canja halina gabaki ɗaya ba.”

13. Me ya sa yawan fushi yake da lahani, kuma wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba da?

13 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu mu rabu da fushi da zage-zage da kuma faɗa. (Afis. 4:31) Waɗannan abubuwa sukan jawo ayyukan mugunta. Mutanen duniya ba sa ganin munin waɗannan halayen amma yana ɓata sunan Mahaliccinmu. Mutane da yawa sun kawar da waɗannan halayen banza kafin su ɗauki sabon hali.​—Karanta Zabura 37:​8-11.

14. Shin zai yiwu mai cin zali ya zama mai tawali’u?

14 Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Hans, shi dattijo ne a wata ikilisiya da ke ƙasar Ostiryia. Mai tsara ayyukan dattawa na ikilisiyar su Hans ya ce: “Yana cikin ’yan’uwa masu tawali’u da za ka so ka haɗu da su.” Amma ba haka Hans yake a dā ba, don sa’ad da yake matashi ya soma shan giya da yawa kuma ya zama mai cin zalin mutane. Akwai lokacin da ya sha giya ya bugu, hakan ya sa ya yi fushi har ya kashe budurwarsa. Sai aka yanke masa hukuncin shekara 20 a fursuna, amma hakan bai sa ya canja halinsa ba. Da shigewar lokaci, sai mahaifiyarsa ta gaya wa wani dattijo ya kai masa ziyara a fursuna, kuma Hans ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya ce: “Bai yi min sauƙi in canja halina na dā ba. Amma Nassosi da suka taimaka min su ne Ishaya 55:​7, da ta ce: ‘Mai-mugunta shi sāki hanyarsa’ da kuma 1 Korintiyawa 6:​11, da ta yi magana game da waɗanda suka canja halinsu cewa: ‘Waɗansu ma a cikinku dā haka kuke.’ Shekaru da yawa Jehobah ya taimaka min ta wurin ruhunsa mai tsarki don na canja halina.” Hans ya yi baftisma sa’ad da yake fursuna kuma aka sake shi bayan ya yi shekara 17 da rabi. Ya ce: “Ina godiya don yadda Jehobah ya nuna min jin ƙai kuma ya gafarta min.”

15. Me mutane suke yawan yi, amma me Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun?

15 Ban da zage-zage, yin ƙarya wani hali ne da ya kamata mu daina. Alal misali, mutane da yawa suna yin ƙarya don su guji biyan haraji ko kuma kada su ɗauki alhakin kuskurensu. Amma, Jehobah “Allah na gaskiya” ne. (Zab. 31:5) Saboda haka, yana son kowane bawansa ya riƙa ‘faɗa wa maƙwabtansa gaskiya’ ba “ƙarya” ba. (Afis. 4:25; Kol. 3:9) Hakan ya nuna cewa wajibi ne mu riƙa faɗin gaskiya ko ma muna cikin tsāka mai wuya.​—Mis. 6:​16-19.

YADDA SUKA SAMI ’YANCI

16. Ta yaya mutum zai yi nasara don ya canja halinsa?

16 Ba zai yiwu mutum ya canja halinsa da kansa ba tare da taimako ba. Sakura da Ribeiro da Stephen da kuma Hans da aka ambata ɗazu sun yi fama sosai kafin su canja halinsu. Kuma Kalmar Allah da ruhu mai tsarki ne suka taimaka musu. (Luk. 11:13; Ibran. 4:12) Don mu ma mu amfana, wajibi ne mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum, mu yi bimbini a kansa kuma mu riƙa yin addu’a a kai a kai don mu sami hikima da kuma ƙarfin bin shawarar Littafi Mai Tsarki. (Josh. 1:8; Zab. 119:97; 1 Tas. 5:17) Ƙari ga haka, za mu amfana daga Kalmar Allah da ruhu mai tsarki idan muka shirya taro kuma muka halarce su. (Ibran. 10:​24, 25) Kuma ya kamata mu yi amfani da abubuwa dabam-dabam da ƙungiyar Jehobah ke tanadinsu don mu zama abokan Jehobah.​—Luk. 12:42.

Ta yaya za mu yi nasara wajen canja halinmu? (Ka duba sakin layi na 16)

17. Me za a bincika a talifi na gaba?

17 Mun bincika mummunan ayyuka da yawa da wajibi ne Kiristoci su daina. Amma shin waɗannan abubuwa ne kawai ake bukata don mutum ya samu amincewar Allah? A’a. Wajibi ne mu ɗauki sabon hali. A talifi na gaba, za mu bincika fannoni da yawa na wannan sabon hali da kuma yadda za mu riƙa nuna su a rayuwarmu.

^ sakin layi na 7 An canja wasu sunayen da ke cikin wannan talifin.

^ sakin layi na 8 Ka duba shafuffuka na 218-219 a rataye na littafin nan Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah ƙarƙashin jigon nan Yi Nasara Bisa Tsaranci.