Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Sami Albarka Sosai don Na Jimre da Tsanantawa

Na Sami Albarka Sosai don Na Jimre da Tsanantawa

WANI ɗan sandan ciki ya dāka mini tsawa ya ce: “Wane irin mugun mutum ne kai, ka bar matarka da ciki da kuma ’yarka, waye ne zai riƙa kula da su da kuma biyan bukatunsu? Ka musanta imaninka don a sake ka ka koma gida.” Sai na ce masa: “Ban bar iyalina ba, ku kuka kama ni, ba gaira ba dalili!” Ɗan sandan ya ce: “Babu wani laifin da ya fi muni kamar zama Mashaidin Jehobah.”

Wannan abin ya faru ne a shekara ta 1959 kuma a lokacin ina kurkuku a birnin Irkutsk da ke ƙasar Rasha. Bari in gaya muku dalilin da ya sa ni da matata Maria muka kasance a shirye don mu “sha wuya sabili da adalci.”​—1 Bit. 3:​13, 14.

An haife ni a ƙasar Yukiren a shekara ta 1933, a ƙauyen Zolotniki. A shekara ta 1937 kanwar mamata da mijinta da Shaidun Jehobah ne sun zo daga Faransa don su ziyarce mu kuma suka ba mu littattafan nan Government da kuma Deliverance da Shaidun Jehobah suka wallafa. Da mahaifina ya karanta littattafan, sai ya soma son Allah. Abin taƙaici mahaifina ya soma rashin lafiya mai tsanani a shekara ta 1939, amma kafin ya mutu, ya faɗa wa mahaifiyata cewa: “Ki sa yaranmu su bi wannan addini don shi ne addini na gaskiya.”

MUN SOMA WA’AZI A SAIBERIYA

A watan Afrilu na shekara ta 1951, hukuma ta soma tura Shaidun Jehobah daga yammacin Tarayyar Soviet zuwa zaman bauta a Saiberiya. An kore ni da ƙanena mai suna Grigory da kuma mahaifiyarmu daga ƙasar Yukiren. Bayan mun yi tafiya da jirgin ƙasa na wajen kilomita 6,000 sai muka iso birnin Tulun da ke ƙasar Saiberiya. Bayan makonni biyu yayana mai suna Bogdan ya zo sansani da muke a kusa da birnin Angarsk. An yanke masa hukuncin yin shekara 25 a sansanin da ake aiki sosai.

Ni da mahaifiyata da kuma Grigory mun yi wa mutanen da suke zama a kusa da garin Tulun wa’azi, amma muna bukatar mu yi hakan da dabara. Alal misali, muna tambayarsu cewa: “Akwai wanda yake da shanun sayarwa?” Idan muka sami wanda yake son ya sayar da shanu sai mu gaya masa yadda Allah ya halicci shanun a hanya mai ban al’ajabi. Kafin ka sani, sai mu soma masa wa’azi game da Mahalicci. A lokacin sai ’yan jarida suka soma yaɗawa cewa Shaidun Jehobah suna ce suna so su sayi shanu amma ainihi tumaki suke nema. Kuma da gaske mun sami tumaki, wato waɗanda suke son wa’azinmu. Mun ji daɗin koya wa mutane masu kirki Littafi Mai Tsarki a wajen da ba a yawan yin wa’azi. Amma a yau muna da ikilisiya da take da masu shela fiye da 100 a Tulun.

YADDA MARIA TA SHA WAHALA

Matata Maria ta zama Mashaidiyar Jehobah a Yukiren a lokacin da ake Yaƙin Duniya na Biyu. A lokacin da take ’yar shekara 18, wani ɗan sandan ciki ya yi ƙoƙarin ya sa ta yi lalata da shi, amma ta ƙi yin hakan. Wata rana da Maria ta shiga ɗakinta sai ta gan shi yana kwance a kan gadonta sai ta fita da gudu. Hakan ya sa shi fushi sosai, sai ya ce zai sa a ƙulle ta da yake ita Mashaidiyar Jehobah ce. Kuma da gaske a shekara ta 1952 an yanke wa Maria hukuncin yin shekaru goma a fursuna. Ta ji kamar Yusufu da aka saka shi a fursuna don bangaskiyarsa. (Far. 39:​12, 20) Amma direban da ya kai ta fursuna ya ce mata: “Kar ki ji tsoro. Mutane da yawa suna zuwa fursuna kuma a sake su ba tare da sun zub da mutuncinsu ba.” Waɗannan kalaman sun ƙarfafa ta sosai.

An saka Maria a sansanin da ake aiki sosai da ke kusa da birnin Gorkiy (da yanzu ake kira Nizhniy Novgorod) a ƙasar Rasha a tsakanin shekara ta 1952 zuwa 1956. An sa ta riƙa tumɓuke itatuwa har a lokacin da ake sanyi sosai. Ta sha wuya sosai amma a shekara ta 1956 aka sake ta kuma ta koma garin Tulun.

AN RABA NI DA MATATA DA KUMA YARANA

Sa’ad da wani ɗan’uwa ya gaya min cewa wata ’yar’uwa tana zuwa, sai na je tashar da kekena don in ganta kuma in taimaka mata da kayanta. Na so Maria tun ranar farko da na ganta. Sai da na dage kafin ta yarda ta aure ni. Mun yi aure a shekara ta 1957. Bayan shekara ɗaya muka haifi ’yarmu mai suna Irina. Amma ba mu kasance tare sosai ba don an kama ni kuma aka kai ni kurkuku a shekara ta 1959 don ina buga littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. Na yi wata shida a tsare kuma ni kaɗai ne a ɗakin. Nakan yi addu’a da waƙa da kuma gwada yadda zan yi wa’azi don in sami kwanciyar hankali.

A lokacin da nake zama a sansani a shekara ta 1962

Akwai lokacin da wani ɗan sanda yake min tambayoyi a fursuna sai ya ce da munafurci, “Ba da daɗewa ba za mu kore ku kamar yadda ake koran ɓeraye.” Sai na ce, “Yesu ya ce dole SAI an yi wa’azin bisharar Mulkin a dukan duniya kuma babu wanda zai hana mu yin hakan.” Da mutumin ya ga hakan, sai ya soma wata dabara don ya sa in musanta imanina kamar yadda na ambata da farko. Sa’ad da suka ga cewa ban faɗa tarkon su ba, sai suka yanke min hukuncin yin shekaru bakwai a fursuna a sansanin da ake aiki sosai kusa da birnin Saransk. Da nake kan hanyar zuwa sansanin sai na sami labari cewa matata ta haifi ’yarmu ta biyu mai suna Olga. Ko da yake matata da yaranmu suna nesa da ni, na yi farin ciki cewa mun bauta wa Jehobah da aminci.

Maria da yaranmu Olga da Irina a shekara ta 1965

Maria takan kawo min ziyara sau ɗaya a kowace shekara, duk da cewa tafiya daga Tulun zuwa inda nake yana ɗaukan kwanaki goma sha biyu ta jirgin ƙasa. Ban da haka ma, idan tana zuwa takan saya min sabon takalmi, kuma a ƙarƙashin takalmin sai ta saka Hasumiyar Tsaro da aka wallafa ba da daɗewa ba. Akwai wata shekarar da na yi farin cikin sosai da zuwanta, don ta taho da yaranmu mata biyu. Babu shakka, ganinsu da kuma kasancewa tare da su ya sa ni farin ciki sosai.

MATSALOLIN DA MUKA FUSKANTA A WURIN DA MUKA ƘAURA

A shekara ta 1966, an sake ni daga sansanin da ake aiki sosai, kuma ni da mata da yaranmu muka ƙaura zuwa birnin Armavir da ke kusa da Baƙar Teku. A wurin ne aka haifi yaranmu maza biyu masu suna Yaroslav da kuma Pavel.

Ba mu daɗe da ƙaura ba da ’yan sanda suka soma zuwa bincika gidanmu suna neman littattafan Shaidun Jehobah. Suna bincika ko’ina har ma cikin abincin dabbobi. Akwai wata rana da ’yan sandan suka zo yin irin wannan binciken, suna gumi kuma ƙura ta rufe su. Hakan ya sa Maria ta ji tausayin su don ta san doka suke bi. Sai ta ba su ruwan lemu kuma ta kawo musu ruwa a kwano da buroshi da kuma tawul don su goge jikinsu da shi. Da shugabansu ya zo sai ’yan sanda suka faɗa masa irin kirkin da aka yi musu. Da suke barin gidanmu shugaban ya yi mana murmushi kuma ya yi mana ban kwana. Mun yi farin ciki sosai don mun ga sakamakon ‘rinjayar mugunta da nagarta.’​—Rom. 12:21.

Duk da binciken da ake yi a gidanmu, mun ci gaba da yin wa’azi a Armavir. Ban da haka ma, mun taimaka wa ƙaramin rukunin da ke kusa da garin Kurganinsk. Ina farin ciki sosai, don yanzu akwai ikilisiyoyi guda shida a Armavir, guda huɗu kuma a Kurganinsk.

Akwai wasu lokutan da muka yi sanyin gwiwa. Amma muna yi wa Jehobah godiya don ya yi amfani da ’yan’uwa masu aminci ya taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Zab. 130:3) Ban da haka, jarraba ne sosai a gare mu muna bauta wa Jehobah tare da ’yan sandan ciki da suka zo su leƙi asirinmu ba tare da saninmu ba. Waɗannan mutane sun yi kamar suna da ƙwazo sosai a yin wa’azi, har wasunsu ma sun sami hakki a ƙungiyar Jehobah, amma daga baya an gano su.

Maria ta sake yin juna biyu a shekara ta 1978 sa’ad da take ’yar shekara 45, amma saboda tana da wani mugun ciwon zuciya likitoci suka ce ta zub da cikin. Maria ta ƙi yin hakan. Don haka, wasu likitoci suka soma bin ta da sirinji duk inda ta je a cikin asibitin don su yi mata alluran da za ta sa ta haifi yaron kafin lokacin yin hakan. Saboda Maria tana son ta kāre yaron sai ta gudu daga asibitin.

Don haka, ’yan sanda suka ce mu bar garin. Sai muka ƙaura zuwa wani ƙauyen da yake kusa da birnin Tallinn da ke ƙasar Estonia wanda a dā yana cikin tarayyar soviet. Duk da cewa likitoci a birnin Tallinn sun ce Maria za ta mutu idan ba ta zub da cikin ba, ta haifi yaro lafiya lau kuma sunansa Vitaly.

Daga baya muka ƙaura daga Estonia zuwa garin Nezlobnaya a kudancin Rasha. Muna yin wa’azi da basira a garuruwan da ake shaƙatawa kusa da wurin da muke kuma mutane daga birane dabam-dabam daga ƙasar ne suke zuwa wurin. Ko da yake wasu sun zo jinya ne a wurin, amma sun ji albishiri da ya sa su kasance da begen samun rai na har abada.

YADDA MUKA RENI YARANMU SU BAUTA WA JEHOBAH

Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu koya wa yaranmu su yi ƙaunar Jehobah kuma su bauta masa. Muna gayyatar ’yan’uwa masu ibada sosai kuma hakan ya taimaka wa yaranmu. Ɗan’uwana mai suna Grigory yana ziyartarmu a kai a kai kuma ya yi hidimar mai kula da da’ira daga shekara ta 1970 zuwa 1995. Dukanmu muna jin daɗin ziyararsa don shi mai fara’a ne kuma yana ba da dariya. Idan muka yi baƙi muna amfani da Littafi Mai Tsarki don mu wasa ƙwaƙwalwarmu kuma hakan ya sa yaranmu sun so labaran Littafi Mai Tsarki.

Yaranmu maza da matansu.

Daga hagu zuwa dama, layin baya: Yaroslav da Pavel, Jr. da kuma Vitaly

Layin gaba: Alyona da Raya da kuma Svetlana

A shekara ta 1987, yaronmu mai suna Yaroslav ya ƙaura zuwa birnin Riga a Latvia kuma a wurin ya yi wa’azi ba tare da matsala ba. Amma da ya ƙi shiga soja, sai aka tsare shi na shekara ɗaya da rabi kuma ya yi zama a gidan yari dabam-dabam guda tara. Labarin da na ba shi na yadda na jimre sa’ad da nake fursuna ya taimaka masa sosai. Daga baya sai ya soma hidimar majagaba. A shekara ta 1990, sai yaronmu mai suna Pavel da yake shekara 19 a lokacin ya ce yana son ya je hidimar majagaba a Sakhalin, wani tsibiri da ke arewacin Jafan. Da farko, ba mu yarda ya je ba don masu shela guda 20 ne kawai a wurin kuma daga gun zuwa gidanmu kilomita 9,000 ne. Amma daga baya sai muka bar shi ya tafi. Kuma mutanen da suke zama a wurin suna jin wa’azi sosai. Bayan wasu shekaru, sai aka kafa ikilisiyoyi takwas a wurin. Pavel ya yi hidima a wurin har zuwa shekara ta 1995. Kuma a lokacin ɗan autanmu mai suna Vitaly ne ya rage a gida. Tun yana yaro yana son karanta Littafi Mai Tsarki. Da ya kai shekara 14, sai ya soma hidimar majagaba kuma ni ma na yi hidimar tare da shi na shekara biyu. Mun ji daɗin hidima tare. A lokacin da Vitaly ya kai shekara 19, sai ya soma hidimar majagaba na musamman.

A shekara ta 1952, wani ɗan sandan ciki ya gaya wa Maria cewa: “Idan ba ki ce kin daina zama Mashaidiyar Jehobah ba, za ki yi shekaru goma a fursuna. Kuma za ki tsufa ki kaɗaita idan kika fito.” Amma abin da ya faɗa bai faru ba sam. Ban da haka ma, mun ga yadda Jehobah da yaranmu da kuma waɗanda muka taimaka musu su san gaskiya suka nuna mana ƙauna. Ni da matata Maria mun ziyarci yaranmu a wuraren da suke hidima kuma mun ji daɗin hakan. Kuma mun ga cewa mutanen da yaranmu suka taimaka musu su soma bauta wa Jehobah ma suna farin ciki.

INA FARIN CIKI DON ALHERIN JEHOBAH

A shekara ta 1991 ne gwamnati ta ba wa Shaidun Jehobah ’yancin yin wa’azi a wurin. Hakan ya sa ’yan’uwa suka soma wa’azi da ƙwazo. Mun tara kuɗi a ikilisiyarmu muka sayi bas da za mu riƙa zuwa birane da ƙauyuka don wa’azi a kowane ƙarshen mako.

Ni da matata a shekara ta 2011

Ina farin ciki cewa Yaroslav da matarsa Alyona da kuma Pavel da matarsa Raya suna hidima a Bethel. Vitaly da matarsa Svetlana kuma suna hidimar masu kula da da’ira. ’Yar mu ta fari mai suna Irina da iyalinta suna zama a Jamus. Maigidanta Vladimir da yaransu guda uku dattawa ne. Wata ’yarmu mai suna Olga tana zama a Estonia kuma muna hira kullum ta waya. Matata Maria ta rasu a shekara ta 2014 kuma na yi baƙin ciki sosai. Ina son in ganta a lokacin da za a ta da mutanen da suka mutu. Ko da yake ina zama a birnin Belgorod, ’yan’uwan da suke wurin suna taimaka mini sosai.

Da yake na yi shekaru da yawa ina bauta wa Jehobah na koyi cewa bai da sauƙi mutum ya riƙe aminci. Amma irin kwanciyar hankali da Jehobah yake sa mu kasance da shi babu kamarta. Ba zan iya kwatanta irin albarkar da ni da matata Maria muka samu don mun riƙe aminci ba. Muna da masu shela guda 40,000 a lokacin da mulkin tarayyar Soviet ta wargaje a shekara ta 1991. Amma yanzu muna da masu shela fiye da 400,000 a ƙasashen da a dā suke bangaren mulkin tarayyar Soviet. Ko da yake shekaruna 83 yanzu, har ila ni dattijo ne a ikilisiyarmu. Jehobah ya taimaka mini in jimre. Hakika, Jehobah ya albarkace ni sosai.​—Zab. 13:​5, 6.