Kada Ku Shari’anta Mutane Bisa Abin da Kuka Gani
“Kada ku yi shari’a bisa ga yadda abubuwa suke a ganin ido, amma ku yi shari’a bisa ga abin da yake daidai.”—YOH. 7:24.
1. Mene ne Ishaya ya annabta game da Yesu kuma me ya sa hakan yake da ban-ƙarfafa?
ANNABCIN da Ishaya ya yi game da Yesu yana sa mu kasance da tabbaci da kuma bege. Ishaya ya ce Yesu ba “zai yi shari’a bisa ga ganin ido ba, ba zai yanke shawara bisa ga abin da kunnensa ya ji ba. Amma da adalci zai yi wa talakawa shari’a.” (Isha. 11:3, 4) Me ya sa haka yake da ban ƙarfafa sosai? Domin muna rayuwa a duniyar da ake ƙiyayya da nuna bambanci. Mun ƙosa samun Alƙali kamiltacce wanda ba zai shari’anta mu bisa ga ganin ido ba!
2. Mene ne Yesu ya umurce mu mu yi, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?
2 A kowace rana, muna shari’anta mutane. Amma da yake mu ajizai ne, ba za mu iya shari’anta mutane yadda Yesu ya yi ba. Muna yawan shari’anta mutane bisa ga abin da muka gani da ido. Shi ya sa sa’ad da Yesu yake duniya, ya ce: “Kada ku yi shari’a bisa ga yadda abubuwa suke a ganin ido, amma ku yi shari’a bisa ga abin da yake daidai.” (Yoh. 7:24) Babu shakka, Yesu yana so mu zama kamar shi kuma ba ya so mu riƙa shari’anta mutane bisa ga abin da muka gani da ido. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da abubuwan da mutane suke gani da ido suke shafan su. Wato launin fata ko ƙabila, wadata da shekaru. Sa’ad da muke tattauna kowannensu, za mu ga yadda za mu iya bin umurnin Yesu.
SHARI’ANTA MUTANE BISA LAUNIN FATA
3, 4. (a) Me ya sa Bitrus ya canja yadda yake ɗaukan mutanen da ba Yahudawa ba? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.) (b) Wane sabon canji ne Jehobah ya gaya wa Bitrus?
3 Ku yi tunanin yadda manzo Bitrus ya ji sa’ad da aka ce ya je gidan wani mutum da ba Bayahude ba mai suna Koneliyus a birnin Kaisariya. (A. M. 10:17-29) A lokacin, Yahudawa sun gaskata cewa mutanen da ba Yahudawa ba suna da ƙazamta. Amma Bitrus ya canja ra’ayinsa sa’ad da Allah ya saukar masa da wahayi. (A. M. 10:9-16) Mene ne Bitrus ya gani? A cikin wahayin, Bitrus ya ga wani mayafi cike da dabbobin da aka hana su ci. Sai wata murya daga sama ta ce masa: “Bitrus, tashi ka yanka ka ci.” Amma Bitrus ya ƙi ci. Sai muryar ta ce masa: “Abin da Allah ya tsabtace, kada ka ce da shi mai ƙazanta.” A lokacin da Bitrus ya farka, ya yi mamaki sosai a kan abin da muryar take neman ta gaya masa. A lokacin ne bayin Koneliyus suka zo wurin Bitrus. Ruhu mai tsarki ya umurce shi ya je gidan Koneliyus. Sai ya bi bayin Koneliyus zuwa gidan maigidansu.
4 Da a ce Bitrus yana shari’anta mutane bisa ga abubuwan da yake gani da ido, da bai je gidan Koneliyus ba. Haram ne Yahudawa su shiga gidajen mutanen da ba Yahudawa ba. Me ya sa Bitrus ya je gidan Koneliyus? Abin da ya gani a wahayin da kuma ja-gorancin ruhu mai tsarki da ya samu sun shafe shi sosai. Bayan da Bitrus ya saurari abin da Koneliyus ya ce, sai ya faɗa da tabbaci cewa: “Lallai, na gane Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.” (A. M. 10:34, 35) Wannan sabon canjin yana da ban-sha’awa sosai ga Bitrus! Amma ta yaya zai shafi dukan Kiristoci?
5. (a) Mene ne Jehobah yake so dukan Kiristoci su sani? (b) Mene ne za mu iya yin fama da shi duk da cewa mun san gaskiya?
5 Jehobah ya yi amfani da Bitrus wajen taimaka wa mutane su san cewa ba ya nuna bambanci. Babu ruwan Jehobah da launin fatanmu ko ƙabilarmu ko ƙasarmu ko kuma yarenmu. Yana amincewa da duk wani namiji ko ta mace da take tsoron sa kuma take da aminci. (Gal. 3:26-28; R. Yar. 7:9, 10) Babu shakka, ka san da hakan. Amma idan ka yi girma a ƙasa ko kuma a iyalin da ake nuna bambanci fa? Ko da yake za ka iya ganin cewa ba ka nuna bambanci, amma idan ka bincike kanka sosai, za ka iya ganin alamar hakan. Da akwai lokacin da Bitrus ya nuna bambanci, duk da cewa shi ne ya bayyana wa mutane cewa Jehobah ba ya nuna bambanci. (Gal. 2:11-14) Saboda haka, me zai taimaka mana mu guji nuna bambanci bisa ga abin da muke gani da ido?
6. (a) Mene ne zai iya taimaka mana mu daina nuna bambanci? (b) Mene ne rahoton da wani ɗan’uwa ya rubuta ya nuna game da shi?
6 Muna bukatar mu yi amfani da Kalmar Allah wajen bincika kanmu don mu gani ko muna nuna bambanci. (Zab. 119:105) Za mu kuma iya tambayi wani amininmu ya lura ko muna nuna bambanci tun da yake ba ma iya ganin kanmu. (Gal. 2:11, 14) Wannan halin zai iya zama mana jiki sosai har ba za mu san cewa muna hakan ba. Ka yi la’akari da misalin wani dattijo da ya aika wa wani ofishinmu rahoto game da wasu ma’aurata masu halin kirki da suke hidima ta cikakken lokaci. Ɗan’uwan da aka rubuta rahoton game da shi ɗan wata ƙabila ne da ake yawan rena su. Dattijon bai san cewa shi ma yana rena mutanen ƙabilar ba. A rahoton da ya rubuta, ya faɗi abubuwa da dama masu kyau game da ɗan’uwan. Amma ya kammala rahotonsa da cewa: “Ko da yake shi ɗan [ƙabilar nan ne], amma halinsa da salon rayuwarsa sun sa wasu sanin cewa ’yan [ƙabilar nan] za su iya kasancewa da tsabta kuma su rage ƙauyanci.” Wane darasi za mu iya koya daga misalin nan? Ko da wane irin matsayi ne muke da shi a cikin ƙungiyar Jehobah, wajibi ne mu riƙa bincika kanmu don mu ga ko muna nuna bambanci. Wane mataki ne kuma za mu iya ɗauka?
7. Ta yaya za mu nuna cewa muna buɗe zuciyarmu ga mutane?
7 Idan muna buɗe zuciyarmu ga mutane, ƙauna za ta sa mu daina nuna bambanci. (2 Kor. 6:11-13) Shin ka fi son yin cuɗanya da mutanen yarenku ko kuma ƙabilarku ne? Idan haka ne, ka riƙa buɗe zuciyarka kuma ka gayyaci mutanen wasu ƙabila ko yare don ku fita wa’azi tare. Ƙari ga haka, ka gayyace su gidanka don ku ci abinci tare. (A. M. 16:14, 15) Idan muna hakan, ƙauna za ta mamaye zuciyarmu sosai har ba za mu sami damar nuna bambanci ba. Amma da akwai wasu hanyoyin da muke shari’anta mutane ta abubuwan da muke gani da ido. Bari mu tattauna batun wadata.
SHARI’ANTA MUTANE BISA ARZIKINSU
8. Mene ne Littafin Firistoci 19:15 ya ce game da yadda wadata ko talauci zai shafi yadda muke ɗaukan mutane?
8 Wadata za ta iya shafan yadda muke bi da mutane. Littafin Firistoci 19:15 ya ce: “Ba za ku nuna bambanci wa talakawa ko ku girmama masu arziki ba. A cikin gaskiya za ku shari’anta maƙwabcinku.” Amma ta yaya yawan wadatar da mutum yake da ita ko kuma talaucinsa zai iya shafar yadda muke ɗaukan sa?
9. Wace gaskiya ce Sulemanu ya rubuta, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana?
9 Ruhu mai tsarki ya motsa Sarki Sulemanu ya rubuta wannan gaskiya game da ’yan Adam. Karin Magana 14:20 ya ce: “Ba wanda yake son matalauci, ko maƙwabcinsa ma ba ya sonsa, amma mai arziki yana da abokai da yawa.” Wane darasi ne wannan ayar ta koya mana? Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya so yin abokai da masu wadata kuma mu yi banza da talakawa. Me ya sa bai dace mu daraja mutum saboda wadatarsa ba?
10. Wace matsala ce Yaƙub ya gargaɗi Kiristoci a kai?
10 Idan muna shari’anta mutane bisa ga wadatarsu, za mu iya jawo halin nuna bambanci a cikin ikilisiya. Almajiri Yaƙub ya yi gargaɗi cewa wannan matsalar ta jawo rashin haɗin kai a ikilisiyoyi a ƙarni na farko. (Karanta Yaƙub 2:2-4.) Wajibi ne mu mai da hankali sosai don kada mu ƙyale hakan ya jawo matsaloli a ikilisiyoyinmu a yau. Ta yaya za mu guji shari’anta mutane bisa ga wadatarsu?
11. Shin wadata ko talauci yana da alaƙa da dangantakarmu da Jehobah? Ka bayyana.
11 Muna bukatar mu riƙa ɗaukan ’yan’uwanmu yadda Jehobah yake ɗaukan su. Jehobah ba ya daraja mutum domin shi mawadaci ne ko kuma matalauci. Wadatarmu ko talaucinmu bai da alaƙa da dangantakarmu da Jehobah. Ko da yake Yesu ya ce “zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama,” amma bai ce ba zai taɓa yiwuwa ba. (Mat. 19:23) Yesu ya kuma ce: “Masu albarka ne ku matalauta, gama mulkin Allah naku ne!” (Luk. 6:20) Amma hakan ba ya nufin cewa dukan talakawa sun sami albarka kuma sun saurari koyarwar Yesu. Akwai talakawa da yawa da ba su saurare shi ba. Gaskiyar batun shi ne, wadatar mutum ko kuma talaucinsa ba zai iya sa a san ko yana da dangantaka mai kyau da Jehobah ba.
12. Wane gargaɗi ne Kalmar Allah ta ba mawadata da matalauta?
12 Muna da ’yan’uwa maza da mata mawadata da matalauta kuma dukansu suna bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu. Littafi Mai Tsarki ya gaya wa mawadata cewa kada “su sa zuciyarsu a kan arziki marar tabbata. Amma su sa zuciyarsu ga Allah.” (Karanta 1 Timoti 6:17-19.) Kalmar Allah ta kuma gargaɗi dukan Kiristoci, wato talakawa da mawadata cewa kada su so kuɗi. (1 Tim. 6:9, 10) Hakika, idan muna ɗaukan ’yan’uwanmu yadda Jehobah yake ɗaukan su, za mu bi da su yadda ya dace ko da su mawadata ne ko kuma matalauta. Amma zai dace mu shari’anta mutum bisa ga shekarunsa? Bari mu gani.
SHARI’ANTA MUTANE BISA SHEKARUNSU
13. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya koya mana game da yi wa tsofaffi ladabi?
13 Jehobah yana yawan gaya mana a cikin Littafi Mai Tsarki cewa mu riƙa yi wa waɗanda suka manyanta ladabi. Littafin Firistoci 19:32 ya ce: “Za ku miƙe tsaye ku gai da mai furfurar kai, za ku girmama tsoho, gama kuna jin tsoron Allahnku.” Littafin Karin Magana 16:31 ma ya ce “furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.” Manzo Bulus ya gaya wa Timoti cewa kada ya tsawata wa tsoho, amma ya ɗauki ’yan’uwa maza tsofaffi a matsayin baba a gare shi. (1 Tim. 5:1, 2) Ko da yake Timoti yana da iko a kan waɗannan ’yan’uwa tsofaffi, amma yana bukatar ya bi da su cikin juyayi kuma ya riƙa yi musu ladabi.
14. A wane lokaci ne zai dace mu yi wa mutumin da ya manyanta gargaɗi?
14 Amma mene ne za mu yi idan wani da ya manyanta ya ƙarya dokar Jehobah? Jehobah zai hukunta duk mutumin da ke yin zunubi da gangan ko da ya manyanta kuma ana daraja shi. Ku lura da ƙa’idar da ke Ishaya 65:20. Ta ce: “Wanda kuma ya mutu bai kai shekara ɗari ba, za a ce da shi la’ananne ne.” Wahayin da Ezekiyel ya gani ma yana ɗauke da wannan ƙa’idar. (Ezek. 9:5-7) Abin da ya kamata ya fi muhimmanci a gare mu shi ne yin ladabi ga Jehobah, Allahn da Yake Tun Dā. (Dan. 7:9, 10, 13, 14) Idan muna yin hakan, ba za mu ji tsoron yin gargaɗi ga mutumin da ke bukata a yi masa gyara ba kome yawan shekarunsa.—Gal. 6:1.
15. Wane darasi ne muka koya daga manzo Bulus game da daraja matasa?
15 Shin hakan yana nufin cewa bai kamata mu yi ladabi ga ’yan’uwa matasa ba? A’a. Manzo Bulus ya gaya wa Timoti cewa: “Kada ka bar wani ya rena ƙuruciyarka, amma ka zama abin koyi ga sauran masu bi, cikin magana, da rayuwa, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsabtar rai.” (1 Tim. 4:12) Wataƙila Timoti ya ɗan fi shekara 30 sa’ad da Bulus ya rubuta masa waɗannan kalmomin. Duk da haka, Bulus ya ɗanka masa aiki mai muhimmanci. Ba mu san ainihin dalilin da ya sa Bulus ya yi masa wannan gargaɗin ba. Amma a bayyane ne cewa bai kamata mu shari’anta mutane bisa ga shekarunsu ba. Ya kamata mu tuna cewa dukan abubuwan da Yesu ya cim ma a duniya, ya yi su ne sa’ad da yake ɗan shekara 30 zuwa 33.
16, 17. (a) Ta yaya dattawa suke sani ko ɗan’uwa ya ƙware ya zama bawa mai hidima ko dattijo? (b) Ta yaya ra’ayinmu ko kuma al’adarmu za ta iya saɓa wa Kalmar Allah?
16 A wasu al’adu, mutane ba sa daraja matasa. Saboda haka, wasu dattawa ba sa yarda su naɗa matasa su zama bayi masu hidima ko kuma dattawa duk da cewa sun ƙware sosai. Amma ya kamata dukan dattawa su tuna cewa Littafi Mai Tsarki bai faɗi shekarun da ’yan’uwa za su kai kafin a naɗa su bayi masu hidima ko kuma dattawa ba. (1 Tim. 3:1-10, 12, 13; Tit. 1:5-9) Idan dattijo ya yi amfani da al’adarsu wajen kafa doka a cikin ikilisiya, to ya san cewa ba ya bin Kalmar Allah. Bai kamata dattawa su yi amfani da ra’ayinsu wajen naɗa ’yan’uwa a ikilisiya ba, amma su yi amfani da Kalmar Allah.—2 Tim. 3:16, 17.
17 Idan dattawa ba su bi ƙa’idar da ke Littafi Mai Tsarki ba, za su iya hana ’yan’uwan da suka ƙware zama bayi masu hidima ko kuma dattawa. Akwai wani bawa mai hidima a wata ƙasa da aka ba shi wasu ayyuka a cikin ikilisiya kuma yana yin su da kyau sosai. Dukan dattawa sun yarda cewa ya ƙware ya zama dattijo, amma sun ƙi a naɗa shi. Me ya sa? Wasu dattawa da suka manyanta sun ce ɗan’uwan ya yi ƙarami ainun. Don haka, mutane ba za su iya ɗaukan sa kamar dattijo ba. Abin baƙin ciki ne cewa an ƙi a naɗa shi saboda shekarunsa. Ko da yake wannan misali ɗaya ne kawai, amma rahotannin da muke samu sun nuna cewa wannan ra’ayin yana shafan dattawa da yawa a faɗin duniya. Yana da muhimmanci sosai mu riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki maimakon dogara da kanmu! Yin haka ne zai taimaka mana mu riƙa yin biyayya ga Yesu kuma mu daina shari’anta mutane bisa abin da muke gani da ido.
KA YI SHARI’A DA ADALCI
18, 19. Mene ne zai taimaka mana mu riƙa ɗaukan ’yan’uwanmu yadda Jehobah yake ɗaukan su?
18 Za mu iya koyan ɗaukan mutane yadda Jehobah yake ɗaukansu duk da yake mu ajizai ne. (A. M. 10:34, 35) Amma muna bukatar mu riƙa ƙoƙartawa sosai da kuma bin Kalmar Allah a kai a kai. Idan muna bin waɗannan tunasarwar, za mu riƙa bin umurnin da Yesu ya bayar cewa mu daina shari’anta mutane bisa ga abin da muke gani da ido.—Yoh. 7:24.
19 Nan ba da daɗewa ba, Sarkinmu, Yesu Kristi, zai hukunta ’yan Adam. Ba zai hukunta su bisa ga abin da ya gani da ido ba ko kuma abin da ya ji ba, amma zai yi shi da adalci. (Isha. 11:3, 4) Babu shakka, muna ɗokin ganin wannan lokacin!