Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 31

“Ba Mu Fid da Zuciya Ba”!

“Ba Mu Fid da Zuciya Ba”!

“Saboda haka ba mu fid da zuciya ba.”​—2 KOR. 4:16.

WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Kiristoci suke bukatar su yi don su kammala tseren samun rai?

KIRISTOCI suna yin tsere na samun rai. Ko da ba mu daɗe da soma wannan tseren ba ko kuma mun daɗe, muna bukatar mu ci gaba da yin tseren har ƙarshe. Shawarar da manzo Bulus ya ba ’yan’uwan da ke Filibi za ta iya taimaka mana mu ci gaba da yin wannan tseren har ƙarshe. Wasu daga cikin ’yan’uwan da ke ikilisiyar Filibi sun daɗe suna bauta wa Jehobah kafin Bulus ya rubuta musu wasiƙar. ’Yan’uwan suna bauta wa Jehobah da aminci, amma Bulus ya tuna musu dalilin da ya sa suke bukatar su ci gaba da jimrewa yayin da suke yin tsere. Bulus yana so su bi misalinsa ta wajen ci gaba da “nacewa” don su sami lada.​—Filib. 3:14.

2. Me ya sa shawarar da Bulus ya ba ’yan’uwa a Filibi ta dace?

2 Shawarar da Bulus ya ba ’yan’uwan da ke Filibi ta dace sosai. Tun daga lokacin da aka kafa ikilisiyar, ’yan’uwan sun fuskanci tsanantawa sosai. Tsanantawar ta soma a wajen shekara ta 50, sa’ad da Bulus da Sila suka je wa’azi a “Makidoniya” yadda Jehobah ya umurce su. (A. M. 16:9) A wurin, sun haɗu da wata mata mai suna Lidiya wadda “Ubangiji ya buɗe zuciyarta” ta ji bishara. (A. M. 16:14) Ba da daɗewa ba, sai aka yi wa ita da dukan mazaunan gidanta baftisma. Amma nan da nan, Shaiɗan ya soma jawo musu matsaloli. Mazan garin suka kai Bulus da Sila gaban hukuma kuma suka ce suna ta da hankalin mutanen garin. Saboda haka, aka yi wa Bulus da Sila dūka, aka saka su a kurkuku, bayan haka, aka kore su daga birnin. (A. M. 16:​16-40) Shin hakan ya sa sun karaya ne? A’a! ’Yan’uwan da ke sabuwar ikilisiyar kuma fa? Su ma sun jimre tsanantawar da suka fuskanta! Hakika, misali mai kyau da Bulus da Sila suka kafa ya ƙarfafa su sosai.

3. Mene ne Bulus ya gano, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Bulus ya ƙuduri niyyar cewa ba zai karaya ba. (2 Kor. 4:16) Ya san cewa idan yana so ya kammala tseren samun rai, yana bukatar ya mai da hankali ga hidimarsa. Mene ne za mu iya koya daga misalin Bulus? Waɗanne misalai ne a zamaninmu za su iya taimaka mana mu jimre da matsaloli? Ta yaya abubuwan da muke sa zuciya cewa Allah zai yi a nan gaba za su taimaka mana kada mu karaya?

YADDA MISALIN BULUS ZAI TAIMAKA MANA

4. Ta yaya Bulus ya ci gaba da yin ƙwazo a hidima duk da yanayinsa?

4 Ka yi la’akari da yanayin da Bulus yake ciki sa’ad da ya rubuta wasiƙa ga Filibiyawa. An tsare shi a cikin gida a Roma. Saboda haka, ba zai iya zuwa wa’azi ba. Duk da haka, ya yi wa’azi ga baƙi kuma ya rubuta wasiƙu zuwa ikilisiyoyin da ke nesa. A yau ma, Kiristoci da yawa da ba sa iya fita waje saboda rashin lafiya, suna yin amfani da dukan damar da suka samu don yi wa mutanen da suka ziyarce su wa’azi. Ƙari ga haka, suna rubuta wasiƙu ga mutanen da ba a samun su a gida sa’ad da muke wa’azi.

5. Kamar yadda Filibiyawa 3:​12-14 suka nuna, mene ne ya taimaka wa Bulus ya mai da hankali ga maƙasudinsa?

5 Bulus bai bar abubuwan da ya cim ma ko kuma kurakuran da ya yi a dā su ɗauke hankalinsa ba. A maimakon haka, ya ce ya mance “da abin da ya riga ya wuce” domin ya kammala tseren. (Karanta Filibiyawa 3:​12-14.) Waɗanne abubuwa ne za su iya janye hankalin Bulus? Na ɗaya, Bulus ya cim ma abubuwa da yawa a Yahudanci kafin ya zama Kirista. Amma a ganinsa, dukan abubuwan da ya cim ma a dā “abin banza” ne. (Filib. 3:​3-8) Na biyu, bai ƙyale baƙin ciki don yadda ya tsananta wa Kiristoci ya hana shi bauta wa Jehobah ba. Na uku, bai yi tunani cewa ya kamata ya rage ƙwazo ba da yake ya riga ya cim ma abubuwa da yawa a hidimarsa. Bulus ya ci gaba da himma duk da cewa an saka shi a kurkuku, ya sha dūka da jifa, ya fuskanci hatsarin jirgin ruwa da rashin abinci da kuma rashin sutura. (2 Kor. 11:​23-27) Duk da abubuwan da Bulus ya cim ma da kuma matsalolin da ya fuskanta, ya san cewa yana bukatar ya ci gaba da bauta wa Jehobah. Mu ma muna bukatar yin hakan.

6. Waɗanne abubuwa ne da suka ‘riga suka wuce’ muke bukatar mu mance da su?

6 Ta yaya za mu bi misalin Bulus kuma mu mance “da abin da ya riga ya wuce”? Wasu a cikinmu suna bukatar su daina damuwa domin kurakuran da suka yi a dā. Idan haka ne, kana iya soma yin nazari a kan hadayar Yesu. Idan muka yi nazari da tunani sosai a kan abin da muka nazarta kuma muka yi addu’a, hakan yana iya taimaka mana mu daina damuwa don kurakuran da muka yi a dā. Ƙari ga haka, za mu daina damuwa a kan kurakuran da Jehobah ya riga ya yafe mana. Ka yi la’akari wani darasi da za mu iya koya daga Bulus. Wataƙila wasu a cikinmu sun bar aikin da zai iya sa su yi arziki domin su ƙara ƙwazo a hidimar Jehobah. Idan haka ne, bai kamata mu riƙa yin tunanin abubuwan da muka sadaukar ba. (L. Ƙid. 11:​4-6; M. Wa. 7:10) “Abin da ya riga ya wuce” ya haɗa da abubuwan da muka cim ma ko kuma matsalolin da muka jimre. Gaskiya ne cewa yin tunani a kan yadda Jehobah ya albarkace mu da kuma yadda ya taimaka mana yana iya sa mu kusace shi. Amma ba zai dace mu soma tunani cewa abubuwan da muka yi a hidimarmu ga Jehobah sun isa ba.​—1 Kor. 15:58.

A tseren rai, dole ne mu guji abubuwan da za su janye hankalinmu daga maƙasudinmu (Ka duba sakin layi na 7)

7. Kamar yadda 1 Korintiyawa 9:​24-27 suka nuna, me muke bukata don mu ci tsere na rai? Ka ba da misali.

7 Bulus ya fahimci furucin nan da Yesu ya yi cewa: “Ku yi ƙoƙari” sosai. (Luk. 13:​23, 24) Ya san cewa yana bukatar ya yi iya ƙoƙarinsa har ƙarshe yadda Yesu ya yi. Domin haka, ya kwatanta rayuwar Kirista da yin tsere. (Karanta 1 Korintiyawa 9:​24-27.) Alal misali, mutumin da ke yin tsere ba ya barin wani abu ya raba hankalinsa. Mutanen da ke tsere a cikin birnin a yau suna iya bi ta hanyar da akwai shagunan da ake sayar da abubuwa da yawa da kuma wasu abubuwan da za su iya jan hankalinsu. Kana ganin mutumin da ke tsere zai ɗan dakata don ya ga abubuwan da ake sayarwa a waɗannan shagunan ne? Ba zai yi haka ba idan yana so ya yi nasara! A tseren nan da muke yi, muna bukatar mu guji duk wani abu da zai iya raba hankalinmu. Idan muka mai da hankali ga maƙasudinmu, kuma muka yi ƙoƙari kamar yadda Bulus ya yi, za mu yi nasara!

YADDA ZA MU CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH DUK DA MATSALOLI

8. Waɗanne matsaloli guda uku ne za mu tattauna?

8 Bari mu tattauna abubuwa guda uku da za su iya sa mu yi sanyin gwiwa. Na ɗaya shi ne sa’ad da abubuwan da muke zato za su faru ba su faru ba. Na biyu shi ne sa’ad da ƙarfinmu ya fara raguwa yayin da muke tsufa. Na uku kuma shi ne sa’ad da muke fuskantar matsalolin da suka ƙi ƙarewa. Za mu amfana sosai idan muka koyi yadda wasu suka magance irin waɗannan matsalolin.​—Filib. 3:17.

9. Ta yaya abubuwan da muke zaton za su faru da ba su faru ba zai iya shafanmu?

9 Abubuwan da muke zato za su faru da ba su faru ba. Muna sa rai mu ga cikan alkawuran da Jehobah ya yi mana. Habakkuk ya bayyana yadda ya so Jehobah ya kawo ƙarshen muguntar da ake yi a Yahuda a zamaninsa, amma Jehobah ya gaya masa cewa ya “jira lokacinta.” (Hab. 2:3) Idan muka soma tunani cewa abubuwan da muke zato ba za su faru ba, hakan yana iya sa mu soma yin sanyin gwiwa, har ma mu fid da rai. (K. Mag. 13:12) Hakan ya taɓa faruwa da wasu ’yan’uwa a wajen shekara ta 1914. A wannan lokacin, shafaffu da yawa suna zaton cewa za su sami ladansu na yin rayuwa a sama. Amma da hakan bai faru ba, ta yaya amintattu suka bi da matsalar?

Abin da Ɗan’uwan Royal da Pearl Spatz suka sa rai zai faru a 1914 bai faru ba, amma sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci (Ka duba sakin layi na 10)

10. Mene ne wasu ma’aurata suka yi sa’ad da abin da suke zato bai faru ba?

10 Ka yi la’akari da misalin ’yan’uwa biyu masu aminci da suka fuskanci wannan matsalar. Ɗan’uwa Royal Spatz ya yi baftisma a shekara ta 1908 sa’ad da yake ɗan shekara 20. Yana da tabbaci cewa zai je sama nan ba da daɗewa ba. Don haka, sa’ad da yake so ya auri ’Yar’uwa Pearl a shekara ta 1911, ya gaya mata cewa: “Idan za mu yi aure, zai dace mu yi shi yanzu, kin san abin da zai faru a shekara ta 1914!” Shin waɗannan ma’aurata sun karaya sa’ad da ba su je sama a shekara ta 1914 ba? A’a, domin sun fi mai da hankali ga yin hidima ga Allah, maimakon ladan da za su samu. Sun ƙuduri niyyar jimrewa yayin da suke yin wannan tseren. Hakika, Ɗan’uwa Royal da matarsa sun yi hidimarsu da ƙwazo kuma sun riƙe aminci har lokacin da suka rasu. Babu shakka, kana son ganin lokacin da Jehobah zai tsarkake sunansa, ya nuna cewa Mulkinsa ne ya fi dacewa kuma ya cika dukan alkawuransa. Ka kasance da tabbaci cewa waɗannan abubuwan za su faru a daidai lokacin da Jehobah ya ƙayyade. Amma kafin wannan lokacin, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu ci gaba da bauta wa Allah, kuma kada mu bari abubuwan da muke zato da ba su faru ba su sa mu karaya.

Duk da cewa Ɗan’uwa Arthur Secord ya tsufa, ya ci gaba da saka ƙwazo a hidimarsa. (Ka duba sakin layi na 11)

11-12. Me ya sa za mu iya ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci ko da ba mu da ƙarfi kamar dā? Ka ba da misali.

11 Sa’ad da ƙarfinmu ya fara raguwa yayin da muke tsufa. Mutanen da suke tsere suna bukatar ƙarfi sosai. Amma ba ka bukatar ƙarfi domin ka ci gaba da inganta dangantakarka da Jehobah. Mutane da yawa da yanzu ba su da ƙarfin jiki sosai suna ci gaba da yin iya ƙoƙarinsu a hidimarsu ga Jehobah. (2 Kor. 4:16) Alal misali, akwai wani ɗan’uwa mai suna Arthur Secord wanda shi ɗan shekara 88 ne, kuma a lokacin, ya riga ya yi shekara 55 yana hidima a Bethel. Akwai ranar da wata nas ta zo wurinsa sa’ad da yake kwance a gado don ta kula shi. Sai ta ce masa: “Ɗan’uwa Secord, ka yi wa Jehobah hidima sosai.” Amma Ɗan’uwa Secord ba ya tunanin abubuwan da ya yi a dā, sai ya kalle ta ya yi murmushi kuma ya ce: “Hakan gaskiya ne. Amma ba abin da muka yi ba ne yake da muhimmanci. Kasancewa da aminci yanzu shi ne ya fi muhimmanci.”

12 Wataƙila ka daɗe kana bauta wa Jehobah amma yanzu kana rashin lafiya kuma ba za ka iya yin abubuwa yadda kake yi a dā ba. Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana daraja hidimar da ka yi masa da aminci a dā. (Ibran. 6:10) Amma yanzu, ka tuna cewa ba yawan abubuwan da muka yi a hidimarmu ga Jehobah ba ne zai nuna cewa muna ƙaunar sa ba. A maimakon haka, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah ta wajen kasancewa da ra’ayin da ya dace da kuma yin iya ƙoƙarinmu a hidimarsa. (Kol. 3:23) Jehobah ya san abin da za mu iya yi kuma ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu.​—Mar. 12:​43, 44.

Anatoly da Lidiya Melnik sun jimre kuma sun riƙe aminci duk da matsaloli (Ka duba sakin layi na 13)

13. Me ya faru da Anatoly da Lidiya, kuma ta yaya hakan ya ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah ko da muna fuskantar jarrabawa?

13 Matsalolin da muka daɗe muna fuskanta. Wasu a cikin bayin Jehobah sun jimre matsaloli da tsanantawa na shekaru da yawa. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Anatoly Melnik yana ɗan shekara 12 sa’ad da aka saka mahaifinsa a kurkuku. Bayan haka, sai aka tura mahaifinsa zaman bauta a Saiberiya, kuma wurin yana da nisa fiye da mil 4,000 daga wurin da iyalinsa suke a Moldova. Shekara ɗaya bayan haka, an tura Anatoly da mahaifiyarsa da kuma kakarsa zaman bauta a Saiberiya. Daga baya, sun sami damar halartan taro a wani ƙauye, amma sun bukaci yin tafiyar mil 20 kuma ana sanyi sosai. Bayan hakan, an raba Ɗan’uwa Melnik da matarsa da kuma ’yarsu mai shekara ɗaya sa’ad da aka saka shi a kurkuku na shekaru uku. Duk da matsalolin da Anatoly da iyalinsa suka fuskanta, sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Yanzu shekarar Ɗan’uwa Anatoly 82 ne, kuma yana yin hidima a matsayin memban kwamitin da ke kula da ofishin Shaidun Jehobah a Asiya ta Tsakiya. Kamar Anatoly da Lidiya, bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da bauta wa Jehobah da kuma jimrewa yadda muka yi a dā.​—Gal. 6:9.

MU MAI DA HANKALI GA ABUBUWAN DA MUKE ƊOKIN SAMU

14. Mene ne Bulus ya fahimci cewa yana bukatar ya yi don ya cim ma maƙasudinsa?

14 Bulus yana da gaba gaɗi cewa zai kammala tseren da yake yi kuma ya cim ma maƙasudinsa. A matsayinsa na shafaffe, yana ɗokin samun ladan “zuwa sama.” Amma kafin ya sami wannan ladan, Bulus ya fahimci cewa yana bukatar ya yi ƙoƙari sosai. (Filib. 3:14) Ya yi amfani da kwatanci mai kyau don ya taimaka wa ’yan’uwan da ke Filibi su mai da hankali ga maƙasudinsu.

15. Ta yaya Bulus ya yi amfani da batun zama ɗan ƙasa don ya ƙarfafa ’yan’uwan da ke Filibi su ci gaba da yin ƙoƙari a hidimarsu?

15 Bulus ya tuna wa ’yan’uwan da ke Filibi cewa su ’yan Mulkin sama ne. (Filib. 3:20) Me ya sa suke bukatar su tuna wannan? A zamanin, mutane suna son su zama ’yan ƙasar Roma domin idan mutum ɗan ƙasar Roma ne, zai amfana sosai. * Amma shafaffu suna ƙarƙashin gwamnatin da ta fi na Roma inganci, wadda za ta fi amfanar su! Saboda haka, Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwan da ke Filibi cewa su yi ‘zaman da ta cancanci labari mai daɗi na Almasihu.’ (Filib. 1:27) A yau, shafaffun Kiristoci suna kafa misali mai kyau a yadda suke ƙoƙari don su cim ma maƙasudinsu na yin rayuwa a sama.

16. Kamar yadda Filibiyawa 4:​6, 7 suka nuna, mene ne muke bukatar mu riƙa yi ko da muna ɗokin yin rayuwa a sama ko a duniya?

16 Ko da muna ɗokin yin rayuwa a sama ko kuma a aljanna a duniya, dukanmu muna bukatar mu ci gaba da ƙoƙartawa don mu cim ma maƙasudinmu. Ko da wace matsalar ce muke fuskanta, kada mu riƙa tuna abubuwan da suka faru a dā, ko kuma mu bar wani abu ya hana mu saka ƙwazo a hidimarmu ga Jehobah. (Filib. 3:16) Wataƙila mun daɗe muna jira mu ga cikar dukan alkawuran Jehobah ko mun soma tsufa kuma ba mu da ƙarfi kamar dā, ko kuma mun daɗe muna jimre matsaloli da kuma tsanantawa. Ko da a wane irin yanayi ne kake ciki, kada ka “damu da kome.” A maimakon haka, ka faɗa wa Allah bukatunka ta wurin addu’a da roƙo, Allah zai ba ka salama fiye da yadda kake zato.​—Karanta Filibiyawa 4:6, 7.

17. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Kamar yadda mai tsere yake ƙara ƙwazo yayin da ya kusan kammala tseren, mu ma muna mai da hankali ga alkawuran da Jehobah ya yi mana yayin da muke kusan kammala tseren samun rai. Mene ne muke bukatar mu yi don mu ci gaba da jimrewa? Talifi na gaba zai taimaka mana mu kafa maƙasudan da suka dace kuma mu mai da hankali ga “abin da ya fi kyau.”​—Filib. 1:​9, 10.

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 Ko da mun yi shekaru muna bauta wa Jehobah, muna so mu ci gaba da manyanta da kuma inganta ibadarmu. Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci cewa kada su yi sanyin gwiwa! Wasiƙar da ya rubuta wa ’yan’uwan da ke Filibi tana ɗauke da abubuwan da za su ƙarfafa mu don mu ci gaba da jimrewa yayin da muke yin tseren nan na samun rai. Wannan talifin zai nuna mana yadda za mu bi shawarar Bulus.

^ sakin layi na 15 Da yake ƙasar Filibi tana ƙarƙashin Roma, mutanen da ke Filibi suna da wasu ’yanci kamar ’yan ƙasar Roma. Saboda haka, ’yan’uwan da ke Filibi sun fahimci kwatancin da Bulus ya yi.