Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 32

Bari Kaunarku ga Juna Ta Rika Karuwa

Bari Kaunarku ga Juna Ta Rika Karuwa

“Addu’ata ita ce ƙaunarku ta yi ta yalwata.”​—FILIB. 1:9.

WAƘA TA 106 Mu Riƙa Nuna Ƙauna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Su waye ne suka taimaka a kafa ikilisiya a Filibi?

A LOKACIN da manzo Bulus da Sila da Luka da kuma Timoti suka je Filibi, sun haɗu da mutane da yawa da suke son jin wa’azi game da Mulkin Allah. Waɗannan ’yan’uwa masu ƙwazo sun sa an kafa Ikilisiya a wurin, kuma wataƙila sun soma yin taro a gidan wata ’yar’uwa mai suna Lidiya da take da karimci sosai.​—A. M. 16:40.

2. Wane ƙalubale ne ’yan’uwa a ikilisiyar Filibi suka fuskanta?

2 Ba da daɗewa ba, ikilisiyar ta soma fuskantar matsaloli. Shaiɗan ya sa mutanen da ba sa son wa’azin Mulkin Allah su tsananta wa Bulus da kuma sauran ’yan’uwan. An kama Bulus da Sila, aka yi musu bulala kuma aka saka su a kurkuku. Bayan an sake su, sun ziyarci sababbin Kiristoci kuma suka ƙarfafa su. Sai Bulus da Sila da kuma Timoti suka bar birnin, amma wataƙila Luka ya ci gaba da zama a wurin. Mene ne waɗannan sababbin Kiristoci za su yi? Jehobah ya taimaka musu da ruhunsa kuma sun ci gaba da bauta masa da ƙwazo. (Filib. 2:12) Hakan ya sa Bulus yin alfahari da su!

3. Kamar yadda Filibiyawa 1:​9-11 suka nuna, wane batu ne Bulus ya yi addu’a a kai?

3 Bayan wajen shekara goma, Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan’uwan da ke Filibi. Yayin da kake karanta wannan wasiƙar, ka lura da yadda Bulus yake ƙaunar ’yan’uwan. Ya ce: Ina “marmarinku duka da ƙaunar Almasihu.” (Filib. 1:8) Ya gaya musu cewa yana yin addu’a a madadinsu. Bulus ya roƙi Jehobah cewa ya taimaka musu su ƙarfafa ƙaunar da suka yi wa juna, su mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, su zama masu tsarki, su guji sa wasu yin tuntuɓe kuma su zama masu adalci. A yau, mu ma za mu iya koyan darussa daga kalmomin Bulus. Bari mu karanta wasiƙar da Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa a Filibi. (Karanta Filibiyawa 1:​9-11.) Bayan haka, za mu tattauna abubuwan da ya ambata da kuma yadda za mu iya yin amfani da kowannensu.

KU CI GABA DA ƘAUNAR JUNA

4. (a) Kamar yadda 1 Yohanna 4:​9, 10 suka nuna, ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah?

4 Jehobah ya nuna mana cewa yana ƙaunar mu sosai ta wajen turo Ɗansa duniya don ya fanshe mu. (Karanta 1 Yohanna 4:​9, 10.) Ƙaunar da Allah yake yi mana yana sa mu ƙaunace shi. (Rom. 5:8) Ta yaya za mu ƙaunaci Allah? Yesu ya amsa wannan tambayar sa’ad da ya gaya wa Farisiyawa cewa: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.” (Mat. 22:​36, 37) Muna so mu ƙaunaci Allah da dukan zuciyarmu, kuma muna so ƙaunar da muke yi masa ta ci gaba da yin ƙarfi a kowace rana. Bulus ya gaya wa ’yan’uwan da ke Filibi cewa su bari ‘ƙaunarsu ta yi ta yalwata.’ Mene ne za mu yi don mu sa ƙauna da muke yi wa Allah ta yi ƙarfi?

5. Me zai sa ƙaunarmu ta ci gaba da yin ƙarfi?

5 Muna bukatar mu san Allah kafin mu ƙaunace shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda ba ya nuna ƙauna, bai san Allah ba sam, gama Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Manzo Bulus ya bayyana cewa ƙaunarmu ga Allah za ta yi ƙarfi idan muka ‘san Allah da kuma kowace irin ganewa’ game shi. (Filib. 1:9) Sa’ad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, mun soma ƙaunar Jehobah duk da cewa ba mu san abubuwa da yawa game da shi ba. Yayin da muka ci gaba da koya game da Jehobah, ƙaunar da muke masa za ta yi ƙarfi. Shi ya sa yake da muhimmanci mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kan abin da muka karanta.​—Filib. 2:16.

6. Kamar yadda 1 Yohanna 4:​11, 20, 21 suka nuna, ta yaya za mu sa ƙaunarmu ta ƙaru?

6 Ƙaunar da Allah yake yi mana za ta motsa mu mu ƙaunaci ’yan’uwanmu. (Karanta 1 Yohanna 4:​11, 20, 21.) Da yake muna bauta wa Jehobah kuma muna ƙoƙarin yin koyi da halayensa, muna iya yin tunani cewa zai kasance da sauƙi mu ƙaunaci ’yan’uwanmu. Ƙari ga haka, muna bin misalin Yesu wanda ƙauna ta sa ya ba da ransa a madadinmu. Amma a yawancin lokaci, yana iya yi mana wuya mu bi umurnin nan cewa mu ƙaunaci juna. Ka yi la’akari da wani misali a ikilisiyar da ke Filibi.

7. Mene ne muka koya daga shawarar da Bulus ya ba Afodiya da Sintiki?

7 Afodiya da Sintiki ’yan’uwa ne masu ƙwazo da suka yi hidima tare da manzo Bulus. Amma wataƙila Afodiya da Sintiki sun sami saɓani kuma hakan ya sa suka daina abokantaka. A wasiƙar da Bulus ya rubuta wa ikilisiyar da waɗannan matan suke hidima, ya ambata sunan Afodiya da Sintiki kuma ya shawarce su cewa “su shirya da juna.” (Filib. 4:​2, 3) Bulus ya ga cewa ya kamata ya shawarci ikilisiyar. Ya ce: “Duk abin da za ku yi, kada ku yi shi da gunaguni ko gardama.” (Filib. 2:14) Hakika, wannan shawarar ta taimaka wa waɗannan ’yan’uwa mata da kuma ’yan’uwa a ikilisiyar su ci gaba da ƙaunar juna.

Me ya sa muke bukatar mu kasance da ra’ayi mai kyau game da ’yan’uwanmu? (Ka duba sakin layi na 8) *

8. Me zai iya sa ya yi mana wuya mu ƙaunaci ’yan’uwanmu, kuma me zai iya taimaka mana mu magance matsalar?

8 A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu ƙaunaci ’yan’uwanmu idan muka yi abin da Afodiya da Sintiki suka yi, wato mai da hankali ga laifin da mutane suka yi mana. Dukanmu muna yin kuskure a kowace rana. Idan muka mai da hankali ga ajizanci wasu, hakan zai sa mu kasa ƙaunar su. Alal misali, idan wani ɗan’uwa ya manta ya taimaka wajen share Majami’ar Mulki, hakan yana iya ɓata mana rai. Idan muka soma lissafa dukan kurakuran da ɗan’uwan, ya yi hakan yana iya daɗa ɓata mana rai kuma ya sa mu daina ƙaunar sa. Idan ka sami kanka a irin wannan yanayin, zai dace ka tuna cewa Jehobah ya san kurakuran da mu da kuma ’yan’uwanmu muke yi. Duk da haka, yana ƙaunar ’yan’uwanmu kuma yana ƙaunar mu. Saboda haka, muna bukatar mu yi koyi da yadda Jehobah yake ƙaunar mu kuma mu kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwanmu. Idan muka yi ƙoƙari sosai don mu ƙaunaci ’yan’uwanmu, hakan zai sa mu kasance da haɗin kai.​—Filib. 2:​1, 2.

KU MAI DA HANKALI GA “ABIN DA YA FI KYAU”

9. Mene ne “abin da ya fi kyau” da Bulus ya ambata a wasiƙarsa ga ’yan’uwan da ke Filibi ya ƙunsa?

9 Jehobah ya hure Bulus ya umurci ’yan’uwan da ke Filibi cewa su mai da hankali ga “abin da ya fi kyau.” (Filib. 1:10) Abin da ya fi kyau da Bulus ya ambata ya ƙunshi tsarkake sunan Jehobah da yadda Jehobah zai cika alkawuransa da kuma kasancewa da haɗin kai da salama a ikilisiya. (Mat. 6:​9, 10; Yoh. 13:35) Idan waɗannan abubuwan suna da muhimmanci a gare mu, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah.

10. Mene ne muke bukatar yi don mu zama masu tsarki?

10 Bulus ya ce mu “zama masu tsarki.” Hakan ba ya nufin cewa dole sai mun zama kamilai. Ba za mu iya zama masu tsarki kamar yadda Jehobah yake da tsarki ba. Amma Jehobah zai ɗauke mu a matsayin masu tsarki idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa nuna ƙauna kuma muka mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci. Hanya ɗaya da za mu nuna ƙauna ita ce ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu guji sa ’yan’uwa yin tuntuɓe.

11. Me ya sa muke bukatar mu guji sa wasu yin tuntuɓe?

11 Umurnin nan cewa mu guji sa wasu yin tuntuɓe yana da tsanani sosai. Ta yaya za mu iya sa wani ya yi tuntuɓe? Muna iya yin hakan ta nishaɗin da muke yi ko irin tufafin da muke sakawa ko kuma irin aikin da muke yi. Wataƙila Jehobah bai haramta abin da muke yi ba, amma idan zaɓin da muka yi ya dami wasu kuma suka yi tuntuɓe, wannan batu ne mai tsanani. Yesu ya ce maimakon mu sa ɗan’uwa ya ɓata dangantakarsa da Jehobah, zai fi dacewa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarmu, a kuma nitsar da mu a cikin teku!​—Mat. 18:6.

12. Wane darasi ne muka koya daga wannan ma’aurata majagaba?

12 Ku yi la’akari da yadda wasu ma’aurata majagaba suka bi umurnin Yesu. Suna ikilisiya ɗaya da wasu ma’aurata da ba su daɗe da yin baftisma ba kuma an rene su ne a iyalin da ba a yarda su saka hannu a wasu harkoki ba. Waɗannan ma’aurata da ba su daɗe da yin baftisma ba sun gaskata cewa bai dace Kirista ya je gidan-fim ba, ko da fim mai kyau ne ake nunawa. Sun yi mamaki sosai sa’ad da suka ji cewa waɗannan ma’aurata majagaba sun je gidan-fim. Bayan haka, waɗannan ma’aurata majagaba sun daina zuwa gidan-fim har sai bayan da waɗancan ma’auratan sun daɗa manyanta. (Ibran. 5:14) Ta hakan, ma’auratan sun nuna cewa suna ƙaunar ’yan’uwansu da gaske.​—Rom. 14:​19-21; 1 Yoh. 3:18.

13. Ta yaya za mu iya sa wani ya yi zunubi?

13 Wata hanya kuma da za mu iya sa wani ya yi tuntuɓe ita ce ta wajen ƙarfafa shi ya yi zunubi. Ta yaya hakan zai iya faruwa? Ka yi la’akari da wannan misalin. Wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya daina yin maye da giya bayan ya yi fama sosai. Ɗalibin ya yanke shawara cewa zai daina shan giya gabaki ɗaya. Ya sami ci gaba kuma ya yi baftisma. Bayan haka, wani ɗan’uwa ya gayyace shi liyafa kuma ya ƙarfafa shi cewa: “Yanzu kai Kirista ne, kana da ruhun Jehobah kuma ɗaya daga cikin ’ya’yan ruhun shi ne kame kai. Idan ka kame kanka za ka iya shan giya daidai wa daida.” Abin taƙaici ne idan ɗan’uwan ya saurari wannan shawarar da ba ta dace ba kuma ya soma shan giya!

14. Ta yaya halartan taro yake taimaka mana mu bi umurnin da ke Filibiyawa 1:10?

14 Halartan taro yana taimaka mana mu bi umurnin da ke Filibiyawa 1:10 a hanyoyi da yawa. Na ɗaya, abubuwan da ake tattaunawa a taro yana taimaka mana mu san abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah. Na biyu, muna koyan darussan da za su taimaka mana mu zama masu tsarki. Na uku, muna ƙarfafa “juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta.” (Ibran. 10:​24, 25) Idan ’yan’uwanmu suna ƙarfafa mu, ƙaunar da muke yi musu da kuma Allah zai ci gaba da yin ƙarfi. Idan muna ƙaunar Allah da kuma ’yan’uwanmu da dukan zuciya, hakan zai sa mu guji sa su yi tuntuɓe.

KU CI GABA DA YIN ‘ADALCI’

15. Mene ne zama masu ‘adalci’ yake nufi?

15 Bulus ya yi addu’a sosai cewa ’yan’uwan da ke Filibi su zama masu ‘adalci.’ (Filib. 1:11) Babu shakka, zama masu ‘adalci’ ya ƙunshi ƙaunarsu ga Jehobah da mutanensa. Ƙari ga haka, ya ƙunshi yin magana game da imaninsu ga Yesu da kuma albarkun da suke sa rai cewa za su samu. A littafin Filibiyawa 2:​15, Bulus ya gaya musu cewa su riƙa haskakawa “kamar haskoki a duniya.” Hakan ya dace domin Yesu ya ce mabiyansa “hasken duniya” ne. (Mat. 5:​14-16) Ƙari ga haka, ya umurci mabiyansa cewa su sa mutane ‘su zama almajiransa.’ Kuma ya sake cewa su ‘zama shaidunsa . . . har zuwa iyakar duniya.’ (Mat. 28:​18-20; A. M. 1:8) Muna yin ‘adalci’ idan muka saka hannu sosai a wannan aiki mafi muhimmanci.

Sa’ad da aka tsare Bulus a gida a Roma, ya rubuta wasiƙa ga ikilisiyar da ke Filibi. Ban da haka, Bulus ya yi amfani da wannan damar don ya yi wa masu gadi da kuma waɗanda suka ziyarce shi wa’azi (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya Filibiyawa 1:​12-14 suka nuna cewa za mu iya haskakawa ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu? (Ka duba bangon gaba.)

16 Ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu, muna iya zama haske a cikin duniya. A wasu lokuta, abubuwan da muke gani cewa za su hana mu yin wa’azi, suna iya ba mu damar yin wa’azi. Alal misali, an tsare manzo Bulus a gida a Roma sa’ad da ya rubuta wasiƙa ga ’yan’uwan da ke Filibi. Duk da haka, Bulus bai daina yi wa masu gadi da kuma waɗanda suka ziyarce shi wa’azi ba. Ya yi wa’azi da ƙwazo a wannan yanayin kuma hakan ya sa ’yan’uwan su kasance da gaba gaɗi “su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.”​—Karanta Filibiyawa 1:​12-14; 4:22.

A kullum ka riƙa neman hanyoyin yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Ta yaya wasu suka ci gaba da yin wa’azi duk da cewa suna fuskantar matsaloli?

17 ’Yan’uwanmu da yawa a yau suna nuna ƙarfin zuciya kamar Bulus. Suna yin rayuwa a ƙasashen da gwamnati ta hana mu yin wa’azi ga jama’a da kuma gida-gida. Duk da haka, ʼyan’uwanmu suna neman wasu hanyoyin yin wa’azi. (Mat. 10:​16-20) A wata ƙasa da gwamnati ta hana mu yin wa’azi, mai kula da da’ira a wurin ya ba ’yan’uwan shawara cewa su riƙa yi wa danginsu da maƙwabtansu da abokan makarantarsu da kuma abokan aikinsu wa’azi. A cikin shekara biyu, ikilisiyoyi a wannan da’irar sun ƙaru sosai. Wataƙila gwamnati ba ta hana yin wa’azi a ƙasar da muke ba. Duk da haka, za mu iya koyan darassi mai kyau daga misalin ’yan’uwanmu. Idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka yi wa’azi, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba ka ƙarfin ci gaba da yin hakan ko da kana fuskantar matsaloli.​—Filib. 2:13.

18. Mene ne muke bukatar mu ƙuduri niyyar yi?

18 Yanzu ne muke bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu bi shawarar da Bulus ya ba ’yan’uwan da ke Filibi. Muna bukatar mu mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, mu zama masu tsarki kuma mu zama masu adalci. Idan muka yi hakan, ƙaunarmu ga Jehobah za ta yi ƙarfi kuma za mu ɗaukaka shi.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

^ sakin layi na 5 Yanzu ne muke bukatar mu ƙarfafa ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu. Wasiƙar da Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwan da ke Filibi za ta taimaka mana mu ga yadda za mu ci gaba da nuna ƙauna ko da muna fuskantar matsaloli.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Sa’ad da ake share Majami’ar Mulki, wani ɗan’uwa mai suna Joe, ya daina aikin don ya tattauna da wani ɗan’uwa da yaronsa. Hakan ya sa Mike wanda ke shara fushi. A ganinsa ‘ya kamata Joe ya yi aiki ba tattaunawa ba.’ Daga baya, Mike ya lura cewa Joe yana taimaka wa wata ’yar’uwa tsohuwa. Hakan ya taimaka wa Mike ya fahimci cewa yana bukatar ya mai da hankali ga halayen masu kyau na ɗan’uwansa.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: A wata ƙasa da aka hana mu wa’azi, wani ɗan’uwa yana yi wa wani wa’azi ba tare da ya jawo hankalin mutane ba. Bayan haka, sa’ad suka fita shan iska a wurin aiki, ɗan’uwan ya yi wa abokan aikinsa wa’azi.