Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 33

Masu Saurarar Ku Za Su Tsira

Masu Saurarar Ku Za Su Tsira

“Ka lura sosai da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da yin waɗannan abubuwa, domin in ka yi haka, za ka ceci kanka da kuma masu jinka.”​—1 TIM. 4:16.

WAƘA TA 67 Mu Yi “Wa’azin Kalmar Allah”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne muke so danginmu su yi?

WATA ’yar’uwa mai suna Pauline * ta ce: “Tun daga lokacin da na koyi gaskiya, burina shi ne kowa a iyalinmu ya shiga Aljanna. Na so ni da mijina Wayne da kuma ɗanmu mu riƙa bauta wa Jehobah tare.” Shin kana da dangin da ba sa bauta wa Jehobah? Kamar Pauline, wataƙila kana so kai da danginka ku riƙa bauta wa Jehobah.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ba za mu iya tilasta wa danginmu su saurari wa’azin Mulkin Allah ba, amma muna iya ƙarfafa su su yi tunani a kan abin da ke Kalmar Allah kuma su faɗi ra’ayinsu. (2 Tim. 3:​14, 15) Me ya sa muke bukatar mu yi wa danginmu wa’azi? Me ya sa muke bukatar mu nuna muna jin tausayin su? Mene ne za mu yi don mu taimaka wa danginmu su soma ƙaunar Jehobah kamar yadda muke ƙaunar sa? Kuma ta yaya kowa a ikilisiya zai iya taimaka mana?

ME YA SA MUKE BUKATAR MU YI WA DANGINMU WA’AZI?

3. Kamar yadda 2 Bitrus 3:9 ta nuna, me ya sa muke so mu yi wa danginmu wa’azi?

3 Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo ƙarshen wannan zamani. Dukan mutanen da “suke da zuciya ta samun rai na har abada” ne kaɗai za su tsira. (A. M. 13:​48, New World Translation) Muna saka ƙwazo sosai don yin wa’azi ga mutanen da ba mu sani ba da suke zama a yankinmu. Saboda haka, za mu so danginmu ma su bauta wa Jehobah. Jehobah Ubanmu mai ƙauna “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.”​—Karanta 2 Bitrus 3:9.

4. Wane kuskure ne za mu iya yi sa’ad da muke yi wa danginmu wa’azi?

4 Muna bukatar mu riƙa tuna cewa akwai hanyar da ta dace mu yi wa mutane wa’azi da kuma hanyar da ba ta dace ba. Alal misali, sa’ad da muke yi wa mutanen da ba mu sani ba wa’azi, muna yin hakan da fara’a, amma wataƙila ba ma yin hakan sa’ad da muke wa danginmu wa’azi.

5. Mene ne muke bukatar mu riƙa tunawa sa’ad da muke so mu yi wa danginmu wa’azi?

5 Mai yiwuwa muna yin da-na-sani don maganganun da muka yi wa danginmu a lokaci na farko da muka yi musu wa’azi. Manzo Bulus ya umurci Kiristoci cewa: ‘A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma daɗin ji, domin ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.’ (Kol. 4:​5, 6) Zai dace mu riƙa tuna wannan shawarar sa’ad da muke so mu yi wa danginmu wa’azi. Domin idan ba mu yi hakan ba, muna iya sa su fushi maimakon mu sa su saurare mu.

ME ZA MU YI DON MU TAIMAKA WA DANGINMU?

Yadda kake nuna tausayi da kuma ayyukanka za su iya sa danginka su canja ra’ayinsu (Ka duba sakin layi na 6-8) *

6-7. Ka ba da misalin da ya nuna yadda za mu iya nuna mun fahimci yanayin da abokin aurenmu da ba ya bauta wa Jehobah ke ciki.

6 Ka nuna kana tausaya musu. Pauline wadda aka ambata ɗazun ta ce: “Da farko, ina son tattaunawa da mijina game da Allah da Littafi Mai Tsarki ne kawai, ba ma yin hira game da waɗansu abubuwa.” Amma mijin Pauline mai suna Wayne bai san abin da ke Littafi Mai Tsarki ba sosai, kuma ba ya fahimtar abin da matarsa take cewa. A ganinsa, addininta ne kaɗai take tunani a kai. Don haka, ya soma damuwa cewa ta shiga ƙungiya mai haɗari kuma an ruɗe ta.

7 Pauline ta bayyana cewa a yawanci lokaci tana tare da ’yan’uwa, tana tare da su da yamma da kuma a ƙarshen mako sa’ad da ta halarci taro da a wa’azi da kuma sa’ad da suka shirya liyafa. Pauline ta ce: “A wasu lokuta, Wayne ba ya samun kowa a gida sa’ad da ya dawo kuma hakan yana sa ya kaɗaita.” Hakika, Wayne yana so matarsa da yaronsu su riƙa kasancewa tare da shi. Bai san mutanen da suke tare da matarsa ba, kuma kamar dai sababbin abokan matarsa sun fi shi muhimmanci a gare ta. Hakan ya sa Wayne yin barazanar kashe aurensu. Za ka iya yin tunanin wasu hanyoyin da Pauline za ta iya nuna ta fahimci yanayin da mijinta ke ciki?

8. Me zai fi taimaka wa danginmu, kamar yadda 1 Bitrus 3:​1, 2 suka nuna?

8 Ka kafa misali mai kyau. A yawanci lokaci, danginmu suna lura da abubuwan da muke yi fiye da abubuwan da muke faɗa. (Karanta 1 Bitrus 3:​1, 2.) Pauline ta fahimci hakan daga baya. Ta ce: “Na san cewa Wayne yana ƙaunar mu kuma ba da gaske yake sa’ad da ya ce zai kashe aurenmu ba. Amma barazanar da ya yi ya sa na ga cewa ina bukatar in soma yin amfani da shawarwarin da Jehobah ya ba ma’aurata. Zai fi dacewa in kasance da halaye masu kyau, maimakon in riƙa yi masa wa’azi kawai.” Pauline ta daina tilasta wa mijinta su tattauna abin da ke Littafi Mai Tsarki, kuma ta soma yin hira da shi game da abubuwan yau da kullum. Wayne ya lura cewa matarsa ta zama mai son salama, kuma ya lura cewa ɗansu ya soma yin fara’a da kuma biyayya. (K. Mag. 31:​18, 27, 28) Sa’ad da Wayne ya lura da yadda Littafi Mai Tsarki yake shafan iyalinsa a hanya mai kyau, ya soma son saƙon da ke cikinsa.​—1 Kor. 7:​12-14, 16.

9. Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa danginmu?

9 Ka ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa danginka. Jehobah ya kafa mana misali mai kyau a wannan batun. Yana ba mutane damar saurarar wa’azi “a kai a kai” don su sami rai. (Irm. 44:4) Kuma manzo Bulus ya gaya wa Timoti cewa ya ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa mutane. Me ya sa? Domin ta yin hakan, zai tsira kuma waɗanda suka saurare shi ma za su tsira. (1 Tim. 4:16) Muna ƙaunar danginmu, kuma muna so su san gaskiyar da ke Kalmar Allah. Bayan ɗan lokaci, kalmomin Pauline da kuma ayyukanta, sun taimaka wa iyalinta. A yanzu, tana farin ciki domin ita da mijinta suna bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, dukansu suna yin hidimar majagaba, kuma mijinta dattijo ne.

10. Me ya sa muke bukatar mu zama masu haƙuri?

10 Ka zama mai haƙuri. Sa’ad da muka soma yin rayuwar da ta jitu da Kalmar Allah, muna yin canje-canje sosai a rayuwarmu. Yana iya yi wa danginmu wuya su aminci da waɗannan canje-canje. A yawancin lokaci, abu na farko da suke yawan lura shi ne cewa mun daina saka hannu a bukukuwan addini da kuma siyasa. Hakan yana iya ɓata musu rai. (Mat. 10:​35, 36) Amma kada mu yi tunanin cewa ba za su taɓa canjawa ba. Idan muka daina ƙoƙarin taimaka musu su fahimci abin da muka yi imani da shi, kamar dai mun riga mun shari’anta su ne cewa ba su cancanci samun rai na har abada ba. Jehobah bai ba mu izinin shari’anta mutane ba, Yesu ne ya ba wannan aikin. (Yoh. 5:22) Idan muka zama masu haƙuri, hakan yana iya sa danginmu su so jin wa’azinmu.​—Ka duba akwatin nan “ Ka Yi Amfani da Dandalinmu don Ka Koyar da Mutane.”

11-13. Me ka koya daga yadda Alice ta bi da iyayenta?

11 Ka nuna alheri, amma kada ka bar danginka su sa ka canja shawarar da ka yanke. (K. Mag. 15:2) Ka yi la’akari da misalin wata mai suna Alice. Ta soma bauta wa Jehobah sa’ad da take zama a wata ƙasa, iyayenta ba su aminci da wanzuwar Allah ba kuma su ’yan siyasa ne. Ta fahimci cewa tana bukatar ta gaya wa iyayenta abin da take koya ba tare da ɓata lokaci ba. Ta ce: “Idan ka jinkirta gaya wa danginka cewa ka canja salon rayuwarka da kuma imaninka, hakan yana iya sa su fushi.” Alice ta yi ƙoƙarin neman batutuwan da take gani cewa iyayenta za su so tattaunawa, kamar batun ƙauna. Sai ta rubuta wasiƙa ga iyayenta, kuma ta ambata abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batutuwan kuma ta tambaye su ra’ayinsu. (1 Kor. 13:​1-13) Ta gode wa iyayenta don renonta da kuma kula da ita da suka yi, kuma a wasu lokuta takan tura musu kyauta. Sa’ad da ta ziyarci iyayenta, ta yi ƙoƙari sosai don ta taimaka wa mahaifiyarta da aikace-aikace a gida. Da farko, iyayenta ba su yi farin ciki ba sa’ad da ta gaya musu cewa ta soma bauta wa Jehobah.

12 Sa’ad da take gidan iyayenta, Alice ta ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana. Ta ce: “Yin hakan ya taimaka wa mahaifiyata ta fahimci cewa Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci a gare ni.” Mahaifin Alice yana so ya san kurakuren da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma dalilin da ya sa halin ’yarsa ya canja sosai. Saboda haka, sai ya soma nazarta Littafi Mai Tsarki. Alice ta ce: “Na ba shi Littafi Mai Tsarki, kuma na yi rubutu na saka a cikin.” Wane sakamako ne hakan ya kawo? Maimakon ya sami kurakurai, abin da mahaifin Alice ya karanta a Littafi Mai Tsarki ya ratsa zuciyarsa sosai.

13 Muna bukatar mu nuna alheri, amma kada mu bar danginmu su sa mu canja shawarar da muka yanke. (1 Kor. 4:12b) Alal misali, Alice ta jimre tsanantawa daga mahaifiyarta. Ta ce: “Sa’ad da na yi baftisma, mahaifiyata ta ce ‘Ba na ƙaunar ta.’ ” Mene ne Alice ta yi? Ta ce: “Ban daina tattaunawa game da sabon addinina ba, amma da ladabi na bayyana cewa na yanke shawarar zama Mashaidiyar Jehobah, kuma ba zan canja shawarar ba. Na yi ƙoƙarin tabbatar wa mahaifiyata cewa ina ƙaunar ta. Sai mu biyu muka yi kuka kuma na dafa mata abinci mai daɗi. Tun daga lokacin, ta soma lura cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa na zama mutumiyar kirki.”

14. Me ya sa bai kamata mu bar danginmu su sa mu daina bauta wa Jehobah ba?

14 Yana iya ɗaukan lokacin kafin danginmu su fahimci cewa bauta wa Jehobah yana da muhimmanci sosai a gare mu. Alal misali, sa’ad da Alice ta zaɓi ta yi hidimar majagaba maimakon ta je jami’ar da iyayenta suka ce ta je, hakan ya sake sa mahaifiyarta kuka. Amma Alice ta kasance da ƙarfin zuciya. Ta ce: “Idan ka bar danginka su sa ka canja zaɓin da ka yi, za su so su ci gaba da yin hakan. Idan ka nuna alheri, amma ba ka bari su sa ka canja shawarar da ka yanke ba, wasu a cikinsu za su so su saurare ka.” Abin da ya faru da Alice ke nan. Yanzu iyayenta majagaba ne kuma mahaifin dattijo ne.

TA YAYA ’YAN’UWA A IKILISIYA ZA SU TAIMAKA?

Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su iya taimaka wa danginmu da ba sa bauta wa Jehobah? (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Kamar yadda Matiyu 5:​14-16 da 1 Bitrus 2:12 suka nuna, ta yaya “ayyuka masu kyau” na ’yan’uwa za su taimaka wa danginmu?

15 Jehobah yana yin amfani da “ayyuka masu kyau” na bayinsa don ya sa mutane su kusace shi. (Karanta Matiyu 5:​14-16; 1 Bitrus 2:12.) Idan matarka ko mijinki ba ya bauta wa Jehobah, shin ya taɓa haɗuwa da membobin ikilisiyarku kuwa? Pauline wadda aka ambata ɗazun ta gayyace ’yan’uwa maza da mata a ikilisiyarsu zuwa gidansu domin mijinta ya san su. Wayne ya tuna yadda wani ɗan’uwa ya taimaka masa ya fahimci ko waɗanne irin mutane ne Shaidun Jehobah. Ya ce: “Ɗan’uwan ya ɗau hutu daga wurin aikinsa don ya zo mu kalli wasa a talabijin. Hakan ya sa ni tunani cewa ‘Ba abubuwan ibada kaɗai ya mai da wa hankali ba!’ ”

16. Me ya sa ya kamata mu gayyaci danginmu zuwa taro?

16 Wata hanya mai kyau da za mu iya taimaka wa danginmu ita ce ta wajen gayyatar su su halarci taro a ikilisiya. (1 Kor. 14:​24, 25) Taro na farko da Wayne ya halarta shi ne taron Tuna da Mutuwar Yesu. Ya yi hakan ne domin taron ba zai ɗau lokaci ba kuma bayan ya tashi daga aiki ne za a soma taron. Ya ce: “Ban fahimci abin da aka tattauna a taron ba, amma na tuna mutanen, sun zo sun marabce ni kuma muka sha hannu. Na san cewa mutanen kirki ne.” Akwai wasu ma’aurata da suka nuna wa Pauline alheri, suna taimaka wa yaronta a taro da kuma a wa’azi. Don haka, sa’ad da Wayne ya yanke shawarar yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ya gaya wa ɗan’uwan ya yi nazari da shi.

17. Wane laifi ne bai kamata mu ɗora wa kanmu ba, amma me ya sa bai kamata mu daina ƙoƙarin taimaka wa danginmu ba?

17 Muna fatan cewa dukan danginmu za su bauta wa Jehobah tare da mu. Amma duk da ƙoƙarin da muke yi mu taimaka musu su bauta wa Allah, wataƙila ba za su yi hakan ba. Idan haka ne, kada mu ɗora wa kanmu laifi don zaɓin da suka yi. Domin ba za mu iya tilasta wa mutane su bi addininmu ba. Duk da haka, idan danginka suka ga yadda kake farin ciki domin kana bauta wa Jehobah, hakan yana iya shafan su. Ka yi addu’a a madadinsu. Ka tattauna da su da basira. Kada ka daina ƙoƙarin taimaka musu. (A. M. 20:20) Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka domin ƙoƙarin da kake yi. Kuma idan danginka suka saurare ka, za su tsira!

WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi

^ sakin layi na 5 Muna so danginmu su bauta wa Jehobah, amma su ne za su zaɓa su bauta masa ko a’a. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da za mu iya yi don ya yi wa danginmu sauƙi su saurare mu.

^ sakin layi na 1 An canja sunayen.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana taimaka wa mahaifinsa da ba Mashaidi ba gyaran mota. Da ya sami dama, ya nuna wa mahaifinsa bidiyo daga jw.org®.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa tana saurarar mijinta da ba Mashaidi ba ne sa’ad da yake gaya mata abubuwan da ya fuskanta. Daga baya, ta fita hutu da iyalinta.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: ’Yar’uwar ta gayyaci ’yan’uwa daga ikilisiya zuwa gidanta. ’Yan’uwan sun yi ƙoƙarin sanin mijinta. Daga baya, ya halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu.