Yohanna Mai Baftisma—Darasin da Ya Koya Mana Game da Yin Farin Ciki
SHIN akwai wata hidima a ikilisiya da kake son yi amma ba za ka iya yi a yanzu ba? Wataƙila hidima ce da wani yake yi, ko kuma ƙila a dā ka yi hidimar. Amma wataƙila ka daina yin hidimar don tsufa ko rashin lafiya ko kuma kana neman biyan bukatun iyalinka. Ko kuma wataƙila canje-canje da aka yi a ƙungiyar Jehobah ne ya sa ka daina yin hidimar. Ko da mene ne ya faru, kana iya ji kamar ba ka yin iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah. Hakika, a irin yanayin nan, kana iya yin sanyin gwiwa. Me zai iya taimaka maka don kada ka yi sanyin gwiwa ko kuma fushi? Ta yaya za ka ci gaba da yin farin ciki?
Za mu iya koyan darassi mai muhimmanci game da yin farin ciki daga misalin Yohanna Mai Baftisma. Yohanna ya sami gata sosai a hidimarsa ga Allah, kuma bai yi zato zai fuskanci matsalolin da ya fuskanta ba. Wataƙila bai taɓa tunanin cewa lokacin da zai yi a kurkuku zai fi wanda zai yi yana wa’azi ba. Duk da haka, Yohanna ya ci gaba da yin farin ciki muddar ransa. Mene ne ya taimaka masa? Ta yaya za mu ci gaba da yin farin ciki ko da mun fuskanci yanayin da ba mu yi tsammani ba?
HIDIMAR DA TA SA SHI FARIN CIKI
A wajen watan Afrilu na shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu, Yohanna ya soma yin aikin da Jehobah ya ba shi, wato ya shirya mutane domin zuwan Almasihu. Ya ce: “Ku tuba, gama mulkin sama ya kusa!” (Mat. 3:2; Luk. 1:12-17) Mutane da yawa sun saurare shi. Da yawa sun zo daga wurare masu nisa domin su saurare shi, kuma mutane da yawa sun tuba kuma an yi musu baftisma. Ban da haka, Yohanna ya gargaɗi malaman addinai da suke da’awa su adalai ne cewa Allah zai hukunta su idan ba su tuba ba. (Mat. 3:5-12) Yohanna ya yi abu mai muhimmanci a hidimarsa sa’ad da ya yi wa Yesu baftisma a wajen watan Oktoba na shekara ta 29. Daga wannan lokacin, Yohanna ya soma gaya wa mutane su bi Yesu wanda shi ne Almasihu da aka yi alkawari zai zo.—Yoh. 1:32-37.
Yesu ya yi kalami game da aiki mai muhimmanci da Yohanna ya yi. Ya ce: “Ba a taɓa haifuwar wani a duniyar nan wanda ya kai Yohanna Mai Baftisma girma ba.” (Mat. 11:11) Babu shakka, Yohanna ya yi farin ciki domin albarkun da ya samu. Kamar Yohanna, mutane da yawa a yau sun sami albarku sosai. Ka yi la’akari da misalin Ɗan’uwa Terry. Shi da matarsa mai suna Sandra sun yi fiye da shekaru 50 suna yin hidima ta cikakken lokaci. Terry ya ce: “Na sami gata sosai a hidimar Jehobah. Na yi hidimar majagaba, na yi hidima a Bethel, na yi hidima a matsayin majagaba na musamman da mai kula da da’ira da kuma mai kula da gunduma. A yanzu ina yin hidima a matsayin majagaba na musamman.” Muna farin ciki idan muka sami gata a hidimar Jehobah, amma muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu ci gaba da yin farin ciki sa’ad da yanayinmu ya canja, kamar yadda misalin Yohanna zai nuna mana.
KA KASANCE MAI NUNA GODIYA
Yohanna ya yi farin ciki a hidimarsa domin ya nuna godiya don gata da yake da shi. Ka yi la’akari da wannan misalin. Bayan Yesu ya yi baftisma, almajiran Yohanna sun soma raguwa, amma almajiran Yesu sun soma ƙaruwa. Hakan ya dami mabiyan Yohanna kuma suka ce masa: “Malam, mutumin da kuke tare da shi a dā a ƙetaren Kogin Yodan, . . . ga shi can yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.” (Yoh. 3:26) Yohanna ya ce musu: ‘A bikin aure, ango ne mai amarya. Abokin ango wanda ya je auren kuwa yakan jira ne kurum ya ji muryar ango. Yakan kuma cika da farin ciki idan ya ji ango ya yi magana. A ta haka ne farin ciki nawa ya cika.’ (Yoh. 3:29) Yohanna bai gwada kansa da Yesu ba, kuma bai yi tunani cewa aikinsa bai da daraja domin aikin Yesu ya fi nasa muhimmanci ba. A maimakon haka, ya ci gaba da yin farin ciki domin ya daraja matsayinsa na “abokin ango.”
Ra’ayin da Yohanna ya kasance da shi ya taimaka masa ya ci gaba da yin farin ciki duk da cewa hidimarsa ba ta kasance da sauƙi ba. Alal misali, Yohanna Ba-nazari ne, don haka an haramta masa shan ruwan inabi. (Luk. 1:15) Yesu ya yi kalami game da irin salon rayuwa mai sauƙi da Yohanna ya yi. Ya ce: “Yohanna ya zo bai cika ci da sha ba.” Amma Yesu da almajiransa ba sa ƙarƙashin wannan dokar. (Mat. 11:18, 19) Ban da haka, Yohanna bai yi mu’ujizai ba, amma ya san cewa almajiran Yesu har da mabiyansa a dā sun sami ikon yin mu’ujiza. (Mat. 10:1; Yoh. 10:41) Maimakon Yohanna ya bar wannan bambanci ya ɗauke hankalinsa, ya ci gaba da yin aikin da Jehobah ya ba shi da ƙwazo.
Hakazalika, idan muna daraja aikin da Jehobah ya ba mu za mu ci gaba da yin farin ciki. Ɗan’uwa Terry da muka ambata ɗazun, ya ce, “Na mai da hankali ga kowane aiki da aka ba ni.” Da ya yi tunanin hidimar da ya yi, ya ce: “Ba na yin da-na-sani, amma abubuwa masu kyau da muka shaida kawai nake tunawa.”
Muna iya yin farin ciki idan muka yi tunanin dalilin da ya sa hidimarmu ga Jehobah take da muhimmanci. Gata ce mu zama “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9) Abu mai daraja zai ci gaba da kasancewa da kyau sosai idan muna kula da shi. Hakazalika, za mu ci gaba da farin ciki idan muna tuna cewa gata ce babba mu yi aiki tare da Jehobah. Hakan zai taimaka mana mu guji gwada hadaya da muka bayar da na wasu. Ƙari ga haka, ba za mu soma tunani cewa aikin wasu ya fi wanda Jehobah ya ba mu muhimmanci ba.—Gal. 6:4.
KA MAI DA HANKALI A KAN ABUBUWA NA IBADA
Wataƙila Yohanna ya san cewa hidimarsa ba za ta jima ba, amma ƙila bai san cewa hakan zai faru nan da nan ba. (Yoh. 3:30) Sarki Hiridus ya saka Yohanna a kurkuku a shekara ta 30, wato wajen watanni shida bayan ya yi wa Yesu baftisma. Duk da haka, Yohanna ya ci gaba da yin wa’azi. (Mar. 6:17-20) Mene ne zai taimaka masa ya ci gaba da yin farin ciki a wannan yanayin? Yohanna ya mai da hankali ga abubuwan ibada.
Sa’ad da Yohanna yake kurkuku, ya ji cewa Yesu yana samun ci gaba a hidimarsa. (Mat. 11:2; Luk. 7:18) Ya tabbata cewa Yesu ne Almasihu, amma wataƙila ya yi mamaki yadda Yesu zai cika dukan abubuwan da Nassosi suka ce Almasihu zai yi. Da yake Almasihu zai zama sarki, shin Yesu zai soma mulki ne nan da nan? Hakan zai sa a saki Yohanna daga kurkuku ne? Yohanna ya so ya san abubuwan da Yesu zai yi, don haka, sai ya tura almajiransa biyu su tambayi Yesu, suka ce: “Kai ne wanda zai zo, ko mu sa ido ga wani?” (Luk. 7:19) Da suka dawo, wataƙila Yohanna ya saurare su da kyau sa’ad da suke gaya masa cewa Yesu ya yi mu’ujizai, ya warkar da mutane kuma ya tura almajiran su gaya wa Yohanna cewa: “Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, masu cutar fatar jiki suna samun warkewa, kurame suna jin magana, ana tā da waɗanda suka mutu, ana kuma yi wa talakawa wa’azin labari mai daɗi.”—Luk. 7:20-22.
Babu shakka, abin da suka gaya wa Yohanna ya ƙarfafa shi sosai. Domin ya nuna cewa Yesu yana cika dukan annabce-annabce da aka yi game da Almasihu. Duk da cewa Yesu ba zai sa a saki Yohanna daga kurkuku ba, Yohanna ya san cewa hidimar da ya yi ba a banza ba ne. Duk da yanayin da yake ciki, ya yi farin ciki.
Kamar Yohanna, idan muka mai da hankali ga abubuwan ibada, za mu iya jimrewa kuma mu ci gaba da yin farin ciki. (Kol. 1:9-11) Muna iya yin hakan ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kan abin da muka karanta. Yin haka zai riƙa tuna mana cewa hidimarmu ba a banza ba ne. (1 Kor. 15:58) Sandra ta ce: “Karanta sura guda na Littafi Mai Tsarki a kowace rana yana taimaka mini in kusaci Jehobah sosai kuma yana sa in mai da hankali ga Jehobah ba kaina ba.” Ban da haka, muna iya mai da hankali ga labaran ’yan’uwanmu da suke wa’azi da kuma ci gabar da suke samu. Sandra ta ce: “Shirye-shiryen da ake yi a kowane wata a Tashar JW, yana taimaka mana mu kusaci ƙungiyar Jehobah kuma yana taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki a hidimarmu.”
A ɗan ƙanƙanin lokaci da Yohanna Mai Baftisma ya yi hidima, ya yi hakan da “ƙarfin zuciya kamar annabi Iliya,” kuma “Iliya ɗan Adam ne kamarmu.” (Luk. 1:17; Yaƙ. 5:17) Idan muka yi koyi da misalinsa na nuna godiya da kuma mai da hankali ga abubuwan ibada, mu ma za mu ci gaba da yin farin ciki a hidimarmu ko da mene ne ya faru.