Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 32

Ka Bauta wa Allah Cikin Saukin Kai

Ka Bauta wa Allah Cikin Saukin Kai

“Ka yi tafiyarka da Allahnka cikin sauƙin kai.”​—MIK. 6:8.

WAƘA TA 31 Ka Bi Allah!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Dauda ya ce game da sauƙin kan Jehobah?

JEHOBAH mai sauƙin kai ne kuwa? Ƙwarai. Dauda ya ce: “Ya Yahweh, ka ba ni garkuwar nasara, hannun damanka ya riƙe ni, taimakonka [“sauƙin kanka,” NW ] ya girmama ni.” (2 Sam. 22:36; Zab. 18:35) Sa’ad da Dauda ya rubuta wannan ayar, wataƙila ya tuna da lokacin da Sama’ila ya zo gidansu don ya naɗa wanda zai zama sarkin Isra’ila. Duk da cewa Dauda ne auta cikin yara takwas, Jehobah ya zaɓe shi ya zama sarki maimakon Sarki Saul.​—1 Sam. 16:​1, 10-13.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Babu shakka, Dauda ya amince da abin da wani marubucin zabura ya ce game da Jehobah. Ya ce: “Yakan sunkuya daga can bisa yana kallon sammai da duniya? Yakan tā da talakawa daga ƙura, . . . ya sa su ci tare da ’ya’yan sarki.” (Zab. 113:​6-8) A wannan talifin, za mu fara koyan darussa masu muhimmanci game da sauƙin kai ta wajen tattauna yadda Jehobah ya nuna wannan halin. Bayan haka, za mu koya game da sauƙin kai daga Sarki Saul da annabi Daniyel da kuma Yesu.

WANE DARASI NE ZA MU IYA KOYA DAGA JEHOBAH?

3. Ta yaya Jehobah yake sha’ani da mu, kuma mene ne hakan ya nuna?

3 Jehobah ya nuna shi Allah ne mai sauƙin kai ta yadda yake sha’ani da bayinsa ajizai. Yana amincewa da bautarmu kuma yana ɗaukan mu a matsayin abokansa. (Zab. 25:14) Jehobah ya aiko da Ɗansa ya mutu a madadinmu don mu iya zama abokansa. Babu shakka, Jehobah mai jinƙai ne sosai!

4. Mene ne Jehobah ya ba mu, kuma me ya sa?

4 Ka yi tunanin wata hanyar da Jehobah yake nuna sauƙin kai. A matsayin Mahalicci, Jehobah yana da iko ya halicce mu yadda ba za mu iya zaɓan abin da za mu yi da rayuwarmu ba. Amma bai yi hakan ba. Jehobah ya halicce mu a surarsa kuma ya ba mu ’yancin zaɓan abin da za mu yi. Yana so mu bauta masa da zuciya ɗaya domin muna ƙaunar sa kuma mun san cewa za mu amfana idan muka yi masa biyayya. (M. Sha. 10:12; Isha. 48:​17, 18) Ya kamata mu riƙa godiya cewa Jehobah, Allah ne mai sauƙin kai!

Jesus is depicted in the heavens. Next to him stand some of his corulers. Together they look at a vast number of angels. Some angels are going toward the earth to carry out their assignments. Jehovah delegated authority to all shown in this picture (See paragraph 5)

5. Ta yaya Jehobah ya koya mana mu zama masu sauƙin kai? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

5 Jehobah ya koya mana mu zama masu sauƙin kai ta yadda yake sha’ani da mu. Jehobah ya fi kowa hikima. Duk da haka, yana a shirye ya karɓi shawara daga halittunsa. Alal misali, Jehobah ya sa Ɗansa ya taimaka masa sa’ad da yake halittan dukan abubuwa. (K. Mag. 8:​27-30; Kol. 1:​15, 16) Ƙari ga haka, duk da cewa Jehobah ne Maɗaukaki, ya ba halittunsa wasu ayyuka da za su yi. Alal misali, ya naɗa Yesu Sarkin Mulkinsa, kuma zai ba mutane 144,000 da za su yi sarauta da Yesu iko. (Luk. 12:32) Jehobah ya koyar da Yesu ya zama Sarki da kuma Babban Firist. (Ibran. 5:​8, 9) Ban da haka, ya koyar da abokan sarautar Yesu su yi aikinsu, amma ba ya sa musu ido. A maimakon haka, yana da tabbaci cewa za su yi nufinsa.​—R. Yar. 5:10.

Muna yin koyi da Jehobah sa’ad da muka koyar da ʼyan’uwa kuma muka ba su aiki (Ka duba sakin layi na 6-7) *

6-7. Mene ne za mu iya koya daga Jehobah game da ba mutane aikin da za su yi?

6 Idan Jehobah da ba ya bukatar taimako daga wurin halittunsa, yana ba su ayyukan da za su yi, ya kamata mu ma mu yi koyi da shi! Kai magidanci ne ko kuma dattijo a ikilisiya? Ka yi koyi da Jehobah ta wajen ba wasu ayyukan da za su yi kuma ka guji sa musu ido. Idan ka yi koyi da Jehobah, za ka yi aikin kuma za ka koyar da wasu. Ban da haka, za ka taimaka musu su ƙara kasancewa da gaba gaɗin yin aikin. (Isha. 41:10) Mene ne kuma waɗanda suke da iko za su iya koya daga Jehobah?

7 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana saurarar ra’ayin mala’iku. (1 Sar. 22:​19-22) Iyaye, ta yaya za ku iya yin koyi da Jehobah? Ku tambayi yaranku ra’ayinsu game da yadda za a yi wani aiki. Kuma ku bi shawarwarinsu a lokacin da yin hakan ya dace.

8. Ta yaya Jehobah ya yi haƙuri da Ibrahim da Saratu?

8 Wata hanya da Jehobah yake nuna shi Allah ne mai sauƙin kai ita ce ta yin haƙuri da mutane. Alal misali, Jehobah yana haƙuri sa’ad da bayinsa suka yi shakkar shawarwarin da ya tsai da. Jehobah ya saurari Ibrahim sa’ad da ya furta yadda yake ji game da shawarar da Allah ya tsai da cewa zai halaka Saduma da Gwamarata. (Far. 18:​22-33) Kuma ka tuna yadda Jehobah ya yi sha’ani da Saratu. Bai yi fushi ba sa’ad da ta yi dariya don alkawarin da ya yi mata cewa za ta yi juna biyu ko da yake ta tsufa. (Far. 18:​10-14) Maimakon haka, ya daraja Saratu.

9. Ta yaya iyaye da dattawa za su yi koyi da Jehobah?

9 Iyaye da dattawa, wane darasi ne za ku iya koya daga Jehobah? Mene za ka yi sa’ad da yaranka ko wasu a ikilisiya suka ƙi bin shawarwarinka? Kana saurin kāre shawararka? Ko kuma kana yin ƙoƙari ka fahimci ra’ayinsu? Iyalai da ’yan’uwa a ikilisiyoyi za su amfana sa’ad da dattawa suka yi koyi da Jehobah. Mun tattauna abin da za mu iya koya game da sauƙin kai daga Jehobah. Yanzu, za mu koyi yadda za mu kasance da tawali’u daga wasu mutane a Littafi Mai Tsarki.

MENE NE ZA MU IYA KOYA DAGA WASU?

10. Ta yaya Jehobah yake amfani da misalin wasu don ya koyar da mu?

10 Da yake Jehobah ‘Malaminmu’ ne Mafi Girma, ya tanadar mana misalai a Kalmarsa don ya koyar da mu. (Isha. 30:​20, 21) Muna koyon darussa yayin da muke yi bimbini a kan labaran Littafi Mai Tsarki game da waɗanda suke da halayen da ke faranta ran Allah, har da tawali’u. Ban da haka, muna koyan darasi yayin da muka bincika abin da ya faru da waɗanda suka ƙi kasancewa da halayen nan masu kyau.​—Zab. 37:37; 1 Kor. 10:11.

11. Mene ne za mu iya koya daga mugun misalin Saul?

11 Ka yi tunani a kan abin da ya faru da Sarki Saul. Shi matashi ne mai tawali’u. Ya san kasawarsa kuma ya yi jinkirin karɓan ƙarin matsayi. (1 Sam. 9:21; 10:​20-22) Amma, da shigewar lokaci Saul ya zama mai girman kai. Ya nuna wannan mugun halin ba da daɗewa ba bayan ya zama sarki. Akwai lokacin da ya ƙi yin haƙuri sa’ad da yake jiran annabi Sama’ila. Maimakon Saul ya bi umurnin Jehobah, ya miƙa hadayar ƙonawa duk da cewa ba shi da izinin yin hakan. Saboda haka, Saul ya ɓata ran Jehobah kuma ya ƙi shi a matsayin sarki. (1 Sam. 13:​8-14) Zai dace mu koyi darasi daga wannan misalin kuma mu guji yin abubuwan da ba mu da ikon yi.

12. Ta yaya Daniyel ya kasance da tawali’u?

12 Akasin Saul, annabi Daniyel ya kafa misali mai kyau. A dukan rayuwarsa, Daniyel ya kasance da sauƙin kai, kuma yakan nemi ja-gorancin Jehobah. Alal misali, sa’ad da Jehobah ya yi amfani da shi don ya bayyana mafarkin Nebukadnezzar, Daniyel bai yi da’awa cewa ya yi hakan da ƙarfinsa ba. Maimakon haka, ya ɗaukaka Jehobah. (Dan. 2:​26-28) Wane darasi ne muka koya? Ya kamata mu riƙa ɗaukaka Jehobah idan ’yan’uwa suna son jawabanmu ko kuma mutane suna saurarar wa’azinmu sosai. Zai dace mu fahimci cewa ba za mu iya yin waɗannan abubuwa da ƙarfinmu ba. (Zab. 46:1) Idan muka yi hakan, muna yin koyi da Yesu. Ta yaya?

13. Mene ne muka koya game da tawali’u daga kalmomin Yesu da ke Yohanna 5:​19, 30?

13 Duk da cewa Yesu Ɗan Allah ne, kuma shi kamiltacce ne, ya dogara ga Jehobah. (Karanta Yohanna 5:​19, 30.) Bai yi ƙoƙarin ƙwace iko daga Jehobah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ko da yake Yesu “ya kasance cikin surar Allah, bai yi tunanin zama daidai da Allah ba.” (Filib. 2:​6, NW ) Tun da yake Yesu Ɗa ne mai yin biyayya, ya san kasawarsa kuma ya daraja ikon Jehobah.

Yesu ya san kasawarsa (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne Yesu ya yi sa’ad da aka ce ya yi abin da ba shi da ikon yi?

14 Ka yi la’akari da abin da Yesu ya ce sa’ad da Yaƙub da Yohanna da mahaifiyarsu suka ce Yesu ya yi wani abu da ba shi da ikon yi. Yesu ya gaya musu cewa Jehobah ne kaɗai yake da ikon zaɓan wanda zai zauna a hannun damar Yesu ko kuma a hagunsa a Mulkin sama. (Mat. 20:​20-23) Yesu ya san kasawarsa, shi mai tawali’u ne. Bai taɓa yin abin da Jehobah bai ba shi ikon yin ba. (Yoh. 12:49) Ta yaya za mu iya yin koyi da shi?

Ta yaya za mu zama masu tawali’u kamar Yesu? (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15-16. Ta yaya za mu bi shawarar da ke 1 Korintiyawa 4:6?

15 Muna yin koyi da Yesu ta wajen bin shawarar da ke 1 Korintiyawa 4:6. Ayar ta ce: “Kada ku wuce abin da aka rubuta.” Saboda haka, sa’ad da wani ya nemi shawararmu, bai kamata mu nace su bi ra’ayinmu ko kuma mu yi magana ba tare da yin tunani ba. Maimakon haka, ya kamata mu ce su bi shawarar da ke Kalmar Allah da kuma littattafanmu. Ta yin hakan, muna nuna cewa mun san kasawarmu, kuma da yake mu masu tawali’u ne muna yabon ‘ayyukan adalci’ na Maɗaukaki.​—R. Yar. 15:​3, 4.

16 Ban da ɗaukaka Jehobah, da akwai wasu dalilai masu kyau da za su sa mu zama masu tawali’u. Yanzu za mu tattauna yadda zama masu sauƙin kai da tawali’u zai sa mu farin ciki kuma ya taimaka mana mu zauna lafiya da mutane.

ME YA SA YA DACE MU ZAMA MASU TAWALI’U?

17. Me ya sa masu tawali’u da sauƙin kai suke farin ciki?

17 Idan mu masu tawali’u ne da sauƙin kai, za mu fi yin farin ciki. Me ya sa? Idan mun san kasawarmu, za mu riƙa godiya da kuma farin ciki don yadda mutane suka taimaka mana. Alal misali, ka yi tunanin lokacin da Yesu ya warkar da kutare guda goma. Mutum ɗaya cikinsu ne kaɗai ya dawo ya gode wa Yesu don ya warkar da shi. Mutumin ya san ba zai iya warkar da kansa ba. Wannan mutum mai tawali’u da sauƙin kai, ya nuna godiya don taimakon da ya samu kuma ya ɗaukaka Allah don hakan.​—Luk. 17:​11-19.

18. Ta yaya sauƙin kai yake taimaka mana mu zauna lafiya da mutane? (Romawa 12:10)

18 Masu sauƙin kai sukan yi zaman lafiya da mutane kuma suna ƙulla abota na kud da kud. Me ya sa? Suna farin cikin sanin cewa wasu sun fi su halin kirki kuma suna tabbata da su. Masu sauƙin kai suna farin ciki sa’ad da wasu suka yi nasara a duk aikin da suka samu, kuma suna saurin yaba musu da kuma daraja su.​—Karanta Romawa 12:10.

19. Waɗanne dalilai ne suka sa ya dace mu guji yin fahariya?

19 Akasin haka, yana yi wa mutane masu fahariya wuya su yaba ma wasu, sun fi so a yabe su. Suna gwada kansu da wasu kuma suna ƙoƙarin nuna sun fi kowa. Maimakon su horar da wasu da kuma ba su iko, sukan ce, “Idan kana so a yi abu da kyau, gwamma ka yi da kanka.” Mutum mai fahariya yakan zama mai son matsayi da kuma kishin wasu. (Gal. 5:26) Irin waɗannan mutane ba sa samun aminai. Idan mun ga cewa mu masu fahariya ne, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mana mu canja wannan mugun halin don kada ya zama mana jiki.​—Rom. 12:2.

20. Me ya sa ya dace mu zama masu tawali’u da sauƙin kai?

20 Muna godiya don yadda Jehobah ya kafa mana misali mai kyau! Mun ga cewa shi Allah ne mai sauƙin kai ta yadda ya yi sha’ani da bayinsa, kuma ya kamata mu yi koyi da shi. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi koyi da mutane masu tawali’u da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Bari mu riƙa yabon Jehobah a kowane lokaci kuma mu ɗaukaka shi. (R. Yar. 4:11) Idan muka yi hakan, za mu cancanci yin tafiya da Jehobah, wanda yake ƙaunar masu tawali’u da kuma sauƙin kai.

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

^ sakin layi na 5 Mai sauƙin kai yana jin tausayin mutane da kuma nuna juyayi. Shi ya sa muka ce Jehobah mai sauƙin kai ne. Kamar yadda za a nuna a wannan talifin, za mu iya zama masu sauƙin kai ta yin koyi da Jehobah. Ban da haka, za mu tattauna yadda za mu iya kasancewa da sauƙin kai ta yin koyi da Sarki Saul da annabi Daniyel da kuma Yesu.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo ya keɓe lokaci don ya horar da wani ɗan’uwa matashi ya riƙa kula da yankuna da ikilisiya ke wa’azi. Amma bayan haka, dattijon bai sa wa ɗan’uwan ido ba.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa ta tambayi wani dattijo ko ya dace ta karɓi gayyata zuwa bikin aure a coci. Dattijon bai gaya mata ra’ayinsa ba amma ya nuna mata wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.