Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 31

Kana Jiran “Birnin Nan Wanda Yake da Tushe”?

Kana Jiran “Birnin Nan Wanda Yake da Tushe”?

“Ya sa zuciya a kan birnin nan wanda yake da tushe, wanda Allah ne mai shirya, shi ne kuma mai gina shi.”​—IBRAN. 11:10.

WAƘA TA 22 Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne sadaukarwa ne mutane da yawa suka yi, kuma me ya sa suka yi hakan?

BAYIN Jehobah da yawa a yau suna yin sadaukarwa. ’Yan’uwa maza da mata da yawa sun yanke shawara cewa ba za su yi aure ba. Ma’aurata sun yanke shawarar cewa ba za su haifi yara yanzu ba. Iyalai kuma sun sauƙaƙa rayuwarsu. Dukansu sun yanke wannan shawara mai muhimmanci ne domin suna so su daɗa ƙwazo a bautarsu ga Jehobah. Sun dogara ga Jehobah cewa zai biya bukatunsu. Shin za su yi da-na-sani ne? A’a! Mene ne ya tabbatar mana da hakan? Dalili guda shi ne cewa Jehobah ya albarkaci Ibrahim wanda shi ne “uban masu ba da gaskiya ga Allah.”​—Rom. 4:11.

2. (a) Kamar yadda Ibraniyawa 11:​8-10, 16 suka nuna, me ya sa Ibrahim ya zaɓi ya bar birnin Ur? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ibrahim ya bar rayuwar jin daɗi a birnin Ur kuma ya yi hakan da son ransa. Me ya sa? Domin yana jiran “birnin nan wanda yake da tushe.” (Karanta Ibraniyawa 11:​8-10, 16.) Mene ne “birnin” nan? Waɗanne ƙalubale ne Ibrahim ya fuskanta yayin da yake jira a gina birnin nan? Ta yaya za mu zama kamar Ibrahim da kuma waɗanda suka yi koyi da shi a zamaninmu?

MENE NE “BIRNIN NAN WANDA YAKE DA TUSHE”?

3. Mene ne birnin nan da Ibrahim ya jira?

3 Mulkin Allah ne birnin nan da Ibrahim ya jira. Yesu ne Sarkin wannan Mulkin, kuma zai yi sarauta tare da Kiristoci shafaffu 144,000. Bulus ya kira Mulkin nan “birnin Allah Mai Rai, wato Urushalima ta sama.” (Ibran. 12:22; R. Yar. 5:​8-10; 14:1) Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a Mulkin Allah ya zo, don a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama.​—Mat. 6:10.

4. Kamar yadda Farawa 17:​1, 2, 6 suka nuna, mene ne Ibrahim ya sani game da birnin ko kuma Mulkin da Allah ya yi alkawarinsa?

4 Shin Ibrahim ya san yadda za a tsara Mulkin Allah ne? A’a. A lokacin, wannan bayanin sirri ne. (Afis. 1:​8-10; Kol. 1:​26, 27) Amma Ibrahim ya san cewa wasu cikin jikokinsa za su zama sarakuna. Jehobah ya yi masa alkawari cewa hakan zai faru. (Karanta Farawa 17:​1, 2, 6.) Ibrahim ya amince da alkawuran Allah, har kamar yana ganin Almasihu wanda zai zama Sarkin Mulkin Allah. Saboda haka, Yesu ya gaya wa Yahudawa a zamaninsa cewa: “Ga shi Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki sosai don dai ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya kuma yi murna.” (Yoh. 8:56) Hakika, Ibrahim ya san cewa Jehobah zai yi amfani da zuriyarsa don ya kafa Mulki, kuma ya kasance a shirya ya jira lokacin da Allah zai cika alkawarin.

Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa ya amince da alkawuran Allah? (Ka duba sakin layi na 5)

5. Ta yaya muka san cewa Ibrahim ya jira birnin nan da Allah ya kafa?

5 Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa yana jiran birnin nan ko kuma Mulkin da Allah zai kafa? Na farko, Ibrahim bai goyi bayan wani mulkin ’yan Adam ba. Yana tafiye-tafiye, ba shi da gidan kansa kuma bai goyi bayan kowane sarki ɗan Adam ba. Ƙari ga haka, bai yi ƙoƙarin kafa nasa mulkin ba. A maimakon haka, ya ci gaba da yi wa Jehobah biyayya kuma ya jira ya cika alkawarinsa. Ta yin hakan, Ibrahim ya nuna bangaskiya ga Jehobah sosai. Bari mu tattauna wasu ƙalubale da ya fuskanta don mu ga darussan da za mu iya koya.

WAƊANNE ƘALUBALE NE IBRAHIM YA FUSKANTA?

6. Wane irin birni ne Ur?

6 Birnin Ur da Ibrahim ya bari yana da kāriya sosai, mutanen birnin masu arziki ne kuma suna jin daɗin rayuwa. Birnin yana da ganuwa da kuma tafki kewaye da shi domin tsaro. Mutanen birnin Ur sun ƙware a fannin rubutu da lissafi. Kuma wataƙila mutane da yawa sun yi kasuwanci a birnin domin masana sun tona rubuce-rubuce da aka yi don kasuwanci. An gina gidaje a birnin da bulo kuma aka yi masa feshi da farin fenti. Wasu cikin gidajen nan suna da ɗakuna 13 ko 14 kuma an yi daɓe a tsakar gidan.

7. Me ya sa Ibrahim ya bukaci ya dogara ga Jehobah don ya kāre shi da iyalinsa?

7 Ibrahim yana da tabbaci cewa Jehobah zai kāre shi da iyalinsa. Me ya sa? Ka tuna cewa Ibrahim da Saratu sun bar gidansu mai kyau a birnin Ur, kuma sun je suna zama a tanti a Ka’ana. Hakan yana nufin cewa babu ganuwa ko tafki da za su riƙa kāre shi da iyalinsa. Saboda haka, maƙiya suna iya kawo musu hari a sauƙaƙe.

8. Wace matsala ce Ibrahim ya fuskanta?

8 Ibrahim ya yi nufin Allah, amma a wasu lokuta, bai sami isashen abincin da zai ciyar da iyalinsa ba. An yi ƙarancin abinci a birnin da Jehobah ya ce Ibrahim ya je. Yanayin ya yi tsananin sosai kuma hakan ya sa Ibrahim ya tsai da shawarar ƙaura zuwa ƙasar Masar. A lokacin da Ibrahim yake ƙasar Masar, Fir’auna ya so ya auri Saratu. Hakika, Ibrahim ya yi farin ciki sosai sa’ad da Jehobah ya sa Fir’auna ya maido masa da matarsa Saratu.​—Far. 12:​10-19.

9. Waɗanne matsaloli ne Ibrahim ya jimre da su?

9 Ibrahim ya fuskanci wasu matsaloli sosai a iyalinsa. Matarsa Saratu da yake ƙauna ba ta haihu ba. Sun yi shekaru da yawa suna baƙin ciki domin hakan. Daga baya, Saratu ta ba Ibrahim baiwarta Hajaratu don ta haifa musu yara. Amma sa’ad da Hajaratu ta yi juna-biyu, sai ta soma rena Saratu. Yanayin ya yi muni sosai da har Saratu ta kori Hajaratu daga gida.​—Far. 16:​1-6.

10. Me ya faru da Isma’ilu da kuma Ishaƙu da zai iya hana Ibrahim dogara ga Jehobah?

10 A ƙarshe, Saratu ta yi juna biyu kuma ta haifa wa Ibrahim ɗa mai suna Ishaƙu. Ibrahim ya ƙaunaci Isma’ilu da kuma Ishaƙu. Amma Jehobah ya gaya masa ya kori Isma’ilu da Hajaratu domin Isma’ilu yana cin zalin Ishaƙu. (Far. 21:​9-14) Daga baya, Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi hadaya da Ishaƙu. (Far. 22:​1, 2; Ibran. 11:​17-19) A dukan yanayin nan, Ibrahim ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi game da yaransa.

11. Me ya sa Ibrahim ya jira Jehobah ya cika alkawarinsa?

11 A waɗannan lokuta, Ibrahim ya jira don Jehobah ya cika alkawarinsa. Wataƙila Ibrahim ya wuce shekara 70 sa’ad da shi da iyalinsa suka bar birnin Ur. (Far. 11:31–12:4) Kuma ya yi wajen shekaru ɗari yana zama a tanti da kuma yin tafiye-tafiye a ƙasar Ka’ana. Ibrahim ya mutu sa’ad da yake ɗan shekara 175. (Far. 25:7) Bai ga lokacin da Jehobah ya cika alkawarin da ya yi cewa zai ba zuriyarsa ƙasar ba. Kuma bai ga birnin, wato Mulkin da Allah ya kafa ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim ya mutu “cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa.” (Far. 25:​8, Littafi Mai Tsarki) Duk da matsalolin da Ibrahim ya fuskanta, ya kasance da bangaskiya sosai kuma ya yi farin cikin jiran lokacin da Jehobah zai cika alkawarinsa. Mene ne ya taimaka masa ya jimre? Domin Jehobah ya kāre Ibrahim kuma ya ɗauke shi a matsayin abokinsa.​—Far. 15:1; Isha. 41:8; Yaƙ. 2:​22, 23.

Kamar Ibrahim da Saratu, ta yaya bayin Allah suke nuna bangaskiya da haƙuri? (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Mene ne muke jira, kuma mene ne za mu tattauna?

12 Kamar Ibrahim, muna jiran birnin nan wanda yake da tushe. Amma ba ma jira a kafa shi, don an riga an kafa shi a shekara ta 1914 kuma sarkin ya soma mulki a sama. (R. Yar. 12:​7-10) Amma muna jira mazaunan duniya su soma amfana daga mulkin. Yayin da muke jira hakan ya faru, za mu fuskanci matsaloli da yawa kamar Ibrahim. Shin da akwai bayin Jehobah a yau da suke yin koyi da Ibrahim da Saratu? Labaran da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ya nuna cewa kamar Ibrahim da Saratu, ’yan’uwa da yawa a yau suna da bangaskiya kuma suna jiran lokacin da Jehobah zai cika alkawuransa. Bari mu tattauna wasu daga cikin labaran kuma mu ga darasin da za mu iya koya.

WASU DA SUKA YI KOYI DA IBRAHIM

Bill Walden ya yi sadaukarwa kuma Jehobah ya albarkace shi

13. Mene ne ka koya daga labarin Ɗan’uwa Walden?

13 Ka kasance a shirye don ka yi sadaukarwa. Idan muna so Mulkin Allah ya fi muhimmanci a rayuwarmu, wajibi ne mu zama kamar Ibrahim wanda ya yi sadaukarwa da yawa don ya faranta wa Allah rai. (Mat. 6:33; Mar. 10:​28-30) Ka yi la’akari da labarin wani mai suna Bill Walden. * A shekara ta 1942, Ɗan’uwa Walden ya soma nazari da Shaidun Jehobah, sa’ad da yake gab da kammala koyan zane-zane a jami’a a Amirka. Ɗaya daga cikin malaman Walden, ya shirya masa aikin da zai yi bayan ya sauke karatu, amma Walden ya ƙi. Ya bayyana wa malamin cewa ba zai yi aikin ba domin yana so ya bauta wa Allah. Ba da daɗewa, gwamnati ta tilasta wa Walden ya shiga aikin soja amma ya ƙi shiga. A sakamako haka, aka ci masa tarar dala 10,000 kuma aka ce zai yi shekara biyar a kurkuku. An sake shi bayan ya yi shekara uku. Daga baya, aka gayyace shi Makarantar Gilead kuma aka tura shi hidima a Afirka. Sai Walden ya auri matarsa Eva kuma suka yi hidima a Afirka. Yin hakan na bukatar yin sadaukarwa sosai. A ƙarshe, sun koma Amirka don su kula da mahaifiyar Walden. Sa’ad da Walden yake taƙaita labarinsa, ya ce: “Nakan zub da hawaye sa’ad da na tuna gatar da na samu na yi wa Jehobah hidima fiye da shekaru 70. Ina yawan gode masa don yadda ya taimaka mini in yi amfani da rayuwata a hidimarsa.” Shin za ka so ka yi amfani da rayuwarka don yi wa Jehobah hidima ta cikakken lokaci?

Eleni da Aristotelis Apostolidis sun ga cewa Jehobah ya ƙarfafa su

14-15. Mene ne ka koya daga labarin Ɗan’uwa Apostolidis da matarsa?

14 Kada ka yi zaton cewa ba za ka fuskanci matsaloli a rayuwa ba. Labarin Ibrahim ya koya mana cewa har waɗanda suka yi amfani da rayuwarsu don yi wa Jehobah hidima za su fuskanci matsala. (Yaƙ. 1:2; 1 Bit. 5:9) Abin da ya faru da Aristotelis Apostolidis ke nan. * Ya yi baftisma a shekara ta 1946 a ƙasar Girka, kuma a shekara ta 1952, ya auri wata ’yar’uwa mai suna Eleni kuma dukansu suna so su yi hidima ta cikakken lokaci. Amma Eleni ta soma rashin lafiya kuma aka gano cewa tana da tsiro a ƙwaƙwalwarta. Sai aka yi mata tiyata, amma bayan ’yan shekaru da suka yi aure, sai tsiron ya sake dawowa. Likitoci sun sake yi mata tiyata, amma jikinta ya shanye, kuma ba ta iya yin magana sosai. Ta ci gaba da saka ƙwazo a wa’azi duk da cewa tana rashin lafiya kuma gwamnati tana tsananta wa ’yan’uwanmu a lokacin.

15 Ɗan’uwa Aristotelis ya yi shekaru 30 yana kula da matarsa. A wannan lokacin shi dattijo ne, yana aiki tare da kwamitin taron yanki kuma ya taimaka a gina Majami’ar Babban Taro. A shekara ta 1987, ƙofa ta ji wa Eleni rauni sa’ad da take wa’azi. Ta yi shekaru uku ba ta cikin hayyacinta, bayan haka, sai ta rasu. Ɗan’uwa Aristotelis ya kammala labarinsa da cewa: “Na fuskanci matsaloli da yawa, wasu sun auko mini ba zato-ba-tsammani. Don haka, na ƙuduri niyyar jimrewa kuma ban bar matsalolina su sa ni sanyin gwiwa ba. Jehobah ya ba ni ƙarfin jimre waɗannan matsaloli.” (Zab. 94:​18, 19) Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke yin iya ƙoƙarinsu a hidimarsa duk da cewa suna fuskantar matsaloli!

Audrey Hyde ta kasance da ra’ayin da ya dace ta wajen mai da hankali ga nan gaba

16. Wace shawara mai kyau ce Ɗan’uwa Knorr ya ba matarsa?

16 Ka riƙa tunani game da nan gaba. Ibrahim ya mai da hankali ga ladan da Jehobah zai ba shi a nan gaba kuma hakan ya taimaka masa ya jimre da matsalolinsa. ’Yar’uwa Audrey Hyde ta kasance da irin wannan ra’ayin duk da cewa mijinta na farko Nathan H. Knorr ya mutu sanadiyyar cutar kansa. Mijinta na biyu Glenn Hyde kuma ya mutu sanadiyyar ciwon mantuwa. * ’Yar’uwar ta ce abin da Ɗan’uwa Knorr ya gaya mata ’yan makonni kafin ya mutu ya taimaka mata. Ta ce: “Nathan ya tuna mini cewa: ‘Bayan mun mutu, muna da bege cewa za a ta da mu daga matattu kuma ba za mu sake shan azaba ba.’ Sai kuma ya ƙarfafa ni cewa: ‘Ki ci gaba da jira domin za ki sami lada a nan gaba.’ . . . Ya ƙara cewa: ‘Ki yi ƙoƙari don ki yi amfani da rayuwarki wajen taimaka wa mutane. Yin hakan zai sa ki farin ciki.’ ” Hakika, wannan shawara ce mai kyau cewa taimaka wa mutane zai sa mu “yi farin ciki.”​—Rom. 12:12.

17. (a) Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga nan gaba? (b) Ta yaya bin shawarar da ke Mika 7:7 zai taimaka mana mu more albarku a nan gaba?

17 A yau, da akwai dalilai da yawa da ya kamata su sa mu mai da hankali ga nan gaba. Abubuwan da ke faruwa a duniya sun nuna cewa muna ƙarshen kwanaki na ƙarshe. Nan ba da daɗewa ba, ba za mu bukaci sake jiran lokacin da Mulkin Allah zai soma sarauta ba. Wani daga cikin albarkun da za mu mora shi ne haɗuwa da ’yan’uwanmu da suka rasu. A lokacin, Allah zai albarkaci Ibrahim don bangaskiyarsa da jimirinsa kuma zai ta da shi da iyalinsa daga matattu. Za ka kasance a wurin don ka marabce su? Za ka yi hakan idan kamar Ibrahim, kana a shirye ka yi sadaukarwa don Mulkin Allah, ka kasance da bangaskiya duk da matsaloli kuma ka ci gaba da jiran lokacin da Jehobah zai cika alkawuransa.​—Karanta Mika 7:7.

WAƘA TA 74 Mu Rera Waƙar Mulkin Allah!

^ sakin layi na 5 Yayin da muke jira Allah ya cika alkawuransa, muna iya zama marasa haƙuri kuma bangaskiyarmu tana iya yin sanyi. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Ibrahim don mu ci gaba da jira Allah ya cika alkawuransa? Wane misali mai kyau ne bayin Jehobah a yau suka kafa?

^ sakin layi na 13 An wallafa labarin Ɗan’uwa Walden a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 2013, shafuffuka na 8-10.

^ sakin layi na 14 An wallafa labarin Ɗan’uwa Apostolidis a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2002, shafuffuka na 24-28.

^ sakin layi na 16 An wallafa labarin ’Yar’uwa Hyde a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2004, shafuffuka na 23-29.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ma’aurata tsofaffi sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci duk da cewa suna fuskantar matsaloli. Sun kasance da bangaskiya ta wajen mai da hankali ga alkawuran Jehobah game da nan gaba.