Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 34

Kana da Muhimmanci a Kungiyar Jehobah!

Kana da Muhimmanci a Kungiyar Jehobah!

“Gama kamar yadda jiki yake ɗaya, yake kuma da gaɓoɓi da yawa, ko da yake gaɓoɓin suna da yawa, su jiki ɗaya ne. To, haka yake ga Almasihu.”​—1 KOR. 12:12.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wace gata ce muke da ita?

GATA ce babba mu kasance a ƙungiyar Jehobah! Muna da kwanciyar rai kuma muna farin ciki yayin da muke bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu. Wane aiki ne kake da shi a ikilisiya?

2. Wane kwatanci ne manzo Bulus ya yi amfani da shi a wasiƙun da ya rubuta?

2 Muna iya koyan darussa da yawa game da wannan batun daga misalin da manzo Bulus ya yi amfani da shi a wasiƙun da ya rubuta. A wasiƙun, Bulus ya kamanta ikilisiya da jikin mutum. Kuma ya kamanta ’yan’uwa a ikilisiya da gaɓoɓin jikin mutum.​—Rom. 12:​4-8; 1 Kor. 12:​12-27; Afis. 4:16.

3. Waɗanne darussa uku ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu koyi darussa guda uku daga kwatancin Bulus. Na farko, za mu koyi cewa kowannenmu yana da aiki * a ikilisiya. Na biyu, za mu tattauna abin da za mu yi idan muna ganin cewa ba mu da muhimmanci a ikilisiya. Na uku, za mu tattauna abin da ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali ga aikin da Jehobah ya ba mu a ikilisiya.

KOWANNENMU YANA DA AIKI A IKILISIYA

4. Mene ne muka koya daga Romawa 12:​4, 5?

4 Darasi na farko da za mu iya koya daga kwatancin da Bulus ya yi shi ne cewa kowannenmu yana da aiki mai muhimmanci a ƙungiyar Jehobah. Bulus ya soma kwatancin da cewa: “Muna da gaɓoɓi da yawa cikin jiki guda, kuma duk gaɓoɓin nan suna da aikinsu dabam-dabam. Haka kuma, mu da muke mutane masu yawa, mun zama jiki ɗaya cikin Almasihu, kowane ɗayanmu kuwa gaɓar ɗan’uwansa ne.” (Rom. 12:​4, 5) Mene ne Bulus yake nufi? Aikin kowannenmu a ikilisiya ya bambanta, amma kowannenmu yana da muhimmanci.

Dukanmu muna da aiki dabam-dabam a ikilisiya, amma kowannenmu yana da amfani (Ka duba sakin layi na 5-12) *

5. Wace “baiwa” ce Jehobah ya ba ʼyan’uwa a ikilisiya?

5 Idan aka ambata waɗanda suke da aiki a ikilisiya, kana iya soma tunanin ’yan’uwa da ke ja-goranci. (1 Tas. 5:12; Ibran. 13:17) Gaskiya ne cewa Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya ba da “baiwa” ga ikilisiya. (Afis. 4:8) Wannan “baiwa” ta haɗa da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da masu taimaka musu da Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu da masu kula da da’ira da masu koyarwa a makarantun ƙungiyar Jehobah da dattawa da kuma bayi masu hidima. An naɗa duka ’yan’uwan nan da ruhu mai tsarki don su kula da tumakin Jehobah kuma su ƙarfafa su.​—1 Bit. 5:​2, 3.

6. Kamar yadda 1 Tasalonikawa 2:​6-8 suka nuna, mene ne ’yan’uwan da aka naɗa da ruhu mai tsarki suke yi?

6 Ana naɗa ’yan’uwa da ruhu mai tsarki don su yi ayyuka dabam-dabam a ikilisiya. Kamar yadda gaɓoɓin jiki, wato hannaye da ƙafafu suke aiki tare don jikin mutum gabaki ɗaya ya amfana, haka ma ’yan’uwan da aka naɗa su da ruhu mai tsarki suke aiki tuƙuru don ’yan’uwa a ikilisiya su amfana. Ba sa yin hakan don a riƙa ɗaukaka su. A maimakon haka, suna iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa ’yan’uwa. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:​6-8.) Muna yi wa Jehobah godiya don waɗannan ’yan’uwa da suka fi mai da hankali ga bukatun wasu fiye da nasu!

7. Wace albarka ce ’yan’uwa da yawa da suke hidima ta cikakken lokaci suke samu?

7 Ana iya naɗa wasu a ikilisiya su zama masu wa’azi a ƙasar waje ko majagaba na musamman ko kuma majagaba na kullum. ’Yan’uwa da yawa a faɗin duniya suna yin hidima ta cikakken lokaci. Ta yin hakan, sun taimaka wa mutane da yawa su zama mabiyan Yesu. Ko da yake waɗannan ’yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci ba su da kuɗi sosai, Jehobah ya ba su abubuwa masu kyau. (Mar. 10:​29, 30) Muna ƙaunar waɗannan ’yan’uwan kuma muna farin ciki cewa membobin ikilisiya ne su!

8. Me ya sa kowanne mai shela yake da daraja ga Jehobah?

8 Shin ʼyan’uwan da aka naɗa da ruhu mai tsarki da kuma waɗanda suke yin hidima ta cikakken lokaci ne kaɗai suke da aiki a ikilisiya? A’a! Kowanne mai shela yana da muhimmanci ga Allah da kuma ikilisiya. (Rom. 10:15; 1 Kor. 3:​6-9) Domin maƙasudi mafi muhimmanci na ’yan’uwa a ikilisiya shi ne taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. (Mat. 28:​19, 20; 1 Tim. 2:4) Duk waɗanda suke yin wa’azi, suna ƙoƙari su sa yin wa’azi ya zama aikin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu.​—Mat. 24:14.

9. Me ya sa muke daraja ’yan’uwa mata?

9 Jehobah ya ba ’yan’uwa mata aiki a ikilisiya. Yana daraja matan aure da iyaye mata da gwauraye da kuma mata da ba su yi aure ba da suke bauta masa da aminci. A Littafi Mai Tsarki, ana yawan ambata mata da suka faranta wa Allah rai. An yaba musu domin hikimarsu da bangaskiyarsu da himmarsu da ƙarfin zuciyarsu da karimcinsu da kuma ayyukansu masu kyau. (Luk. 8:​2, 3; A. M. 16:​14, 15; Rom. 16:​3, 6; Filib. 4:3; Ibran. 11:​11, 31, 35) Muna godiya sosai ga Jehobah don ’yan’uwa mata da ke ikilisiyarmu da ke da waɗannan halaye masu kyau!

10. Me ya sa ’yan’uwa tsofaffi suke da daraja?

10 Ban da haka, muna farin ciki cewa muna da tsofaffi da yawa a ikilisiya. A wasu ikilisiyoyi, akwai tsofaffi maza da mata da suke bauta wa Jehobah tun suna matasa. Wataƙila wasu sun soma bauta wa Jehobah sa’ad da suka tsufa. Da yawa daga cikin waɗannan ’yan’uwa tsofaffi suna fama da rashin lafiya. Matsalolin nan suna iya hana su yin abubuwa da yawa a ikilisiya da kuma wa’azi. Waɗannan ’yan’uwa tsofaffi suna yin iya ƙoƙarinsu a wa’azi, kuma suna yin amfani da dukan ƙarfinsu don su ƙarfafa da kuma horar da ’yan’uwa! Muna amfana daga hikimarsu. Jehobah yana ƙaunar su sosai kuma mu ma muna ƙaunar su.​—K. Mag. 16:31.

11-12. Ta yaya matasa a ikilisiyarku suke ƙarfafa ka?

11 Matasa ma suna fuskantar matsaloli sosai. Suna rayuwa a duniyar da Shaiɗan yake mulki kuma yake yaɗa mugayen ƙarairayi. (1 Yoh. 5:19) Duk da haka, muna farin ciki sa’ad da muka ga matasa suna kalami a taro da fita wa’azi da kuma kāre imaninsu da ƙarfin zuciya. Hakika, matasa ma suna da aiki mai muhimmanci a ikilisiya.​—Zab. 8:2.

12 Yana yi wa wasu ’yan’uwa wuya su amince cewa suna da amfani a ikilisiya. Me zai taimaka mana mu ga cewa kowannenmu yana da aiki a ikilisiya? Bari mu gani.

KANA DA AMFANI A IKILISIYA

13-14. Me ya sa wasu suke tunanin cewa ba su da amfani a ikilisiya?

13 Ka lura da darasi na biyu da za mu iya koya daga kwatancin Bulus. Ya yi magana a kan batun da ke shafan mutane da yawa a yau. Mutane da yawa suna tunanin cewa ba su da amfani a ikilisiya. Bulus ya ce: “Da ƙafa za ta ce, ‘Don ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce.’ Wannan ba zai sa ta ta daina zama gaɓar jiki ba. Haka kuma idan kunne ya ce, ‘Ni ba ido ba ne, domin haka ni ba gaɓar jiki ba ne,’ wannan ba zai sa ya daina zama gaɓar jiki ba.” (1 Kor. 12:​15, 16) Mene ne Bulus yake nufi?

14 Idan ka soma gwada kanka da wasu, hakan zai sa ka soma tunanin cewa ba ka da amfani a ikilisiya. Wasu a ikilisiya sun iya koyarwa sosai ko tsara abubuwa ko kuma sun iya ƙarfafawa da ta’azantarwa sosai. Wataƙila kana tunanin cewa ba za ka iya yin abubuwa kamar yadda suke yi ba. Irin wannan tunanin ya nuna cewa kai mutum ne mai sauƙin kai. (Filib. 2:3) Amma ka yi hattara. Idan kana yawan gwada kanka da ’yan’uwan da ke da baiwa da yawa, hakan yana iya sa ka yi sanyin gwiwa. Kuma kamar yadda Bulus ya ambata, kana iya tunanin cewa ba ka da amfani a ikilisiya. Mene ne zai taimaka maka ka daina jin hakan?

15. Kamar yadda 1 Korintiyawa 12:​4-11 suka nuna, mene ne muke bukatar sani game da baiwar da muke da ita?

15 Ka yi la’akari da wannan: Jehobah ya ba wasu Kiristoci a ƙarni na farko baiwar yin mu’ujizai, amma ba dukan Kiristoci ne aka ba wannan baiwar ba. (Karanta 1 Korintiyawa 12:​4-11.) Jehobah ya ba su baiwa dabam-dabam, amma dukansu suna da daraja a gare shi. A yau, ba mu da baiwar yin mu’ujizai, amma wannan ƙa’idar ta shafe mu. Dukanmu ba mu da baiwa iri ɗaya, amma kowannenmu yana da daraja ga Jehobah.

16. Wace shawarar Bulus ce muke bukatar mu bi?

16 Maimakon mu riƙa gwada kanmu da wasu Kiristoci, muna bukatar mu bi shawarar da manzo Bulus ya bayar. Ya ce: “Amma bari kowa ya gwada aikinsa ya gani. Idan ya yi kyau, sa’an nan zai iya taƙama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.”​—Gal. 6:4.

17. Ta yaya za mu amfana idan muka bi shawarar Bulus?

17 Idan muka bi shawarar Bulus kuma muka duba ayyukanmu, hakan yana iya taimaka mana mu ga cewa muna da baiwa da wasu ba su da ita. Alal misali, wataƙila wani dattijo bai iya jawabi a kan daƙalin magana sosai ba, amma ya iya wa’azi sosai. Ko kuma wataƙila bai iya tsara abubuwa da kyau kamar sauran dattawa ba, amma yana da alheri sosai kuma shi dattijo ne mai ƙauna da ’yan’uwa suke iya neman shawara wurinsa. Ko kuma an san shi da nuna karimci sosai. (Ibran. 13:​2, 16) Idan mun san cewa mu ma muna da baiwa, hakan zai taimaka mana mu riƙa farin ciki don abubuwan da muke yi a ikilisiya. Kuma zai sa mu guji yin kishin ’yan’uwan da suke da baiwar da ba mu da ita.

18. Ta yaya za mu inganta baiwar da muke da ita?

18 Ko da wane aiki ne muke yi a ikilisiya, dukanmu muna bukatar mu ci gaba da inganta hidimarmu da kuma baiwarmu. Don mu iya yin hakan, Jehobah ya yi amfani da ƙungiyarsa don ya yi mana tanadin abubuwan da za su taimaka mana. Alal misali, a taron tsakiyar mako, muna koyan yadda za mu riƙa yin wa’azi da kyau. Kana yin amfani da abubuwan da ake koyarwa a wannan taron?

19. Ta yaya za ka cim ma maƙasudin halartan Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki?

19 Wani abu kuma da Jehobah ya yi tanadi don ya horar da mu shi ne Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. ’Yan’uwa maza da mata ’yan shekara 23 zuwa 65 da suke hidima ta cikakken lokaci za su iya halartar makarantar. Kana iya tunanin cewa ba za ka taɓa cim ma wannan maƙasudin ba. Maimakon ka yi tunanin dalilan da za su hana ka halartar makarantar, ka yi tunanin dalilan da suka sa kake so ka halarta. Bayan haka, sai ka tsara abubuwan da za ka yi da za su taimaka maka ka cancanci halartan wannan makarantar. Idan ka yi iya ƙoƙarinka, Jehobah zai taimaka maka ka yi abin da kake gani ya fi ƙarfinka.

KA YI AMFANI DA BAIWARKA DON ƘARFAFA ’YAN’UWA

20. Mene ne za mu koya daga Romawa 12:​6-8?

20 Darasi na uku da za mu iya koya daga kwatancin Bulus yana littafin Romawa 12:​6-8. (Karanta.) A ayoyin, Bulus ya sake ambata cewa kowa a ikilisiya yana da baiwa dabam-dabam. Amma ya nanata cewa mu yi amfani da baiwarmu don mu ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya.

21-22. Wane darasi ne za mu iya koya daga Robert da Felice?

21 Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa da za mu kira Robert. Bayan ya yi hidima a wata ƙasa, sai aka komar da shi hidima a Bethel a ƙasarsu. Ko da yake an tabbatar masa da cewa bai yi wani laifi ba, amma ya ce: “Na yi watanni ina baƙin ciki, kuma na yi tunanin cewa ban yi hidimar yadda ya dace ba. A wasu lokuta, na so in daina yin hidima a Bethel.” Me ya taimaka masa ya daina baƙin ciki? Wani dattijo ya tuna masa cewa Jehobah ya horar da mu a hidimar da muka yi a dā, don ya yi amfani da mu a sabuwar hidimar da ya ba mu. Robert ya fahimci cewa yana bukatar ya daina mai da hankali a kan abin da ya riga ya wuce, amma ya soma mai da hankali ga abin da yake yi a yanzu.

22 Wani ɗan’uwa mai suna Felice Episcopo ya fuskanci irin wannan matsala. Shi da matarsa sun halarci Makarantar Gilead a shekara ta 1956, kuma sun yi hidimar mai kula da da’ira a ƙasar Bolivia. A shekara ta 1964, sun haifi ɗa. Felice ya ce: “Barin hidimarmu ya yi mana wuya sosai. Na ɗau kusan shekara ɗaya ina baƙin ciki, amma da taimakon Jehobah, na daina hakan kuma na mai da hankali ga sabon aikin da na samu.” Shin kana ji kamar Robert ko kuma Felice? Ka soma sanyin gwiwa ne don ba ka yin irin hidimar da kake yi a dā? Idan haka ne, za ka fi yin farin ciki idan ka mai da hankali ga abin da za ka iya yi yanzu, wato bauta wa Jehobah da kuma taimaka wa ’yan’uwa. Ka ci gaba da saka ƙwazo a hidimarka kuma ka riƙa yin amfani da baiwarka don taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Yin haka zai sa ka farin ciki sosai.

23. Mene ne muke bukatar mu yi, kuma me za mu tattauna a talifi na gaba?

23 Jehobah yana ƙaunar kowannenmu. Yana so mu kasance cikin iyalinsa. Idan muka yi tunanin abubuwan da za mu iya yi don mu ƙarfafa ’yan’uwa kuma muka yi aiki tuƙuru don mu yi hakan, za mu ga cewa muna da aiki a ikilisiya! Amma yadda muke ɗaukan ’yan’uwa a ikilisiya kuma fa? Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja su? A talifi na gaba, za mu tattauna wannan batu mai muhimmanci.

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

^ sakin layi na 5 Dukanmu muna so Jehobah ya ɗauke mu da daraja. Amma a wasu lokuta, muna iya tunanin cewa ba mu da amfani. Wannan talifin zai taimaka mana mu ga cewa dukanmu muna da muhimmanci a ikilisiya.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Aikin da muke da shi a ikilisiya yana nufin ƙoƙarin da muke yi mu ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya. Launin fatarmu ko yarenmu ko tattalin arzikinmu ko al’adarmu ko kuma iliminmu, ba za su hana mu yin wannan aikin ba.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: Hotuna ukun suna nuna abin da ke faruwa kafin taro, da sa’ad da ake taro da kuma bayan an kammala taro. Hoto na 1: Wani dattijo yana gai da baƙon da ya halarci taro, wani matashi yana gyara makarufo, wata ’yar’uwa kuma tana tattaunawa da wata tsohuwa. Hoto na 2: Matasa da tsofaffi suna yin kalami a nazarin Hasumiyar Tsaro. Hoto na 3: Wasu ma’aurata suna share Majami’ar Mulki. Wata mahaifiya tana taimaka wa ’yarta ta saka gudummawa a akwati. Wani matashi yana kula da littattafai, wani ɗan’uwa kuma yana ƙarfafa wata ’yar’uwa tsohuwa.