Jehobah Yana Sāka wa Wadanda Suke Bidarsa
“Mai-zuwa wurin Allah dole ya ba da gaskiya cewan yana da rai, kuma shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.”—IBRAN. 11:6.
WAƘOƘI: 85, 134
1, 2. (a) Wace dangantaka ke tsakanin ƙauna da kuma bangaskiya? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?
MUNA ƙaunar Jehobah ‘domin shi ya fara ƙaunar mu.’ (1 Yoh. 4:19) Hanya ɗaya da Jehobah ya sāka wa bayinsa ita ce ƙaunar da ya nuna mana. Idan muka ci gaba da ƙaunar Allah, za mu kasance da tabbaci cewa yana wanzuwa kuma ba zai taɓa manta ya sāka wa bayinsa da yake ƙauna ba.—Karanta Ibraniyawa 11:6.
2 Jehobah ba zai taɓa manta ya sāka wa bayinsa masu aminci ba. Ba za mu ce muna da bangaskiya ba idan ba mu tabbata cewa Allah yana sāka wa mutanen da suke biɗarsa ba. Me ya sa? Domin “bangaskiya fa ainihin abin da muke begensa ne.” (Ibran. 11:1) Babu shakka, bangaskiya ta ƙunshi tabbacin da muke da shi cewa Allah zai ba mu duk abubuwan da ya yi mana alkawarinsu. To, ta yaya yin begen abubuwan da aka yi mana alkawarinsu zai amfane mu? Ta yaya Jehobah ya sāka wa bayinsa a dā da kuma yanzu? Bari mu bincika.
JEHOBAH YA YI ALKAWARI ZAI ALBARKACI BAYINSA
3. Wane alkawari ne aka yi mana a Malakai 3:10?
3 Jehobah ya yi alkawari cewa zai albarkaci bayinsa masu aminci. Don haka, ya ƙarfafa mu mu yi ƙoƙari don mu cancanci samun albarkar. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku gwada ni, . . . in ji Ubangiji mai-runduna, ko ba zan buɗe maku sakatan sama ba, in zuba maku da albarka, har da ba za a sami wurin da za a karɓa ba.” (Mal. 3:10) Muna nuna cewa mun amince da wannan gayyatar idan muka yarda mu gwada shi.
4. Me ya sa za mu tabbata da abin da Yesu ya faɗa a littafin Matta 6:33?
4 Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa idan suka saka al’amura na Mulki a kan gaba, Allah zai taimaka musu. (Karanta Matta 6:33.) Yesu ya faɗi hakan domin ya san cewa Jehobah yakan cika alkawuransa. (Isha. 55:11) Mu ma muna da tabbaci cewa idan muka kasance da bangaskiya ga Jehobah, zai cika alkawarin da ya yi mana cewa: “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” (Ibran. 13:5, Littafi Mai Tsarki) Wannan furucin ya yi daidai da abin da Yesu ya faɗa cewa mu fara biɗan Mulkin Allah da adalcinsa, ko ba haka ba?
5. Me ya sa amsar da Yesu ya ba Bitrus abin ƙarfafa ne a gare mu?
5 Manzo Bitrus ya yi wa Yesu tambaya cewa: “Mun bar abubuwa duka, mun bi ka; me za mu samu?” (Mat. 19:27) Maimakon Yesu ya tsauta wa Bitrus don ya yi wannan tambayar, ya tabbatar wa almajiransa cewa za su sami albarka don sadaukarwa da suka yi. Manzanninsa masu aminci da wasu za su yi sarauta tare da shi a sama. Ko a yanzu ma zai albarkace mu. Yesu ya ce: “Kowanene ya bar gidaje, ko ‘yan’uwa maza, ko ‘yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ‘ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.” (Mat. 19:29) Albarkar da almajiransa za su samu zai fi sadaukarwa da suka yi. Don iyaye da ‘yan’uwa da kuma yara da muke da su a ƙungiyar Jehobah sun fi abubuwan da muka bari don mu saka al’amura na Mulki a kan gaba?
“ANKA NA RAI”
6. Me ya sa Jehobah ya yi wa bayinsa alkawari cewa zai albarkace su?
6 Alkawarin da Allah ya yi wa bayinsa yana taimaka mana mu kasance da bangaskiya sa’ad da muke fuskantar gwaji. Ban da albarkar da bayin Allah masu aminci suke samuwa yanzu, suna marmarin samun wasu har ila a nan gaba. (1 Tim. 4:8) Hakika, tabbacin da muke da shi cewa Jehobah “mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa” zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya sosai.—Ibran. 11:6.
7. Ta yaya begenmu yake kamar anka?
7 A Huɗubar da Yesu ya yi a kan dutse, ya ce: “Ku yi farin ciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama: gama hakanan suka tsananta ma annabawan da suka rigaye ku.” (Mat. 5:12) Ban da ladan zuwan sama da wasu za su samu, waɗanda suke da begen rayuwa a duniya su ma suna ‘farin ciki, da . . . murna ƙwarai.’ (Zab. 37:11; Luk. 18:30) Ko muna cikin waɗanda za su je sama ko kuma yin rayuwa a duniya, begen da muke da shi yana kamar ‘anka na rai, tabbatacen bege mai-tsayawa.’ (Ibran. 6:17-20) Kamar yadda anka take riƙe jirgin ruwa da kyau sa’ad da ake guguwa, albarkar da ke jiranmu za ta taimaka mana mu kasance da bangaskiya sosai. Ƙari ga haka, za ta taimaka mana mu iya jimre wahala.
8. Ta yaya begen da muke da shi yake taimaka mana mu rage alhini ko damuwa?
8 Begen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu rage yin alhini ko damuwa. Alkawuran Allah suna taimaka mana mu sami kwanciyar hankali. Shi ya sa yake da kyau mu ‘zuba nawayarmu bisa Ubangiji,’ don mun tabbata cewa ‘za ya taimake mu.’ (Zab. 55:22) Hakika, mun san cewa Allah zai yi mana fiye da “dukan abin da muke roƙo ko tsammani.” (Afis. 3:20) Hakan abin ƙarfafa ne domin Jehobah ya ce ba wai zai yi abin da muke roƙo kawai ba amma zai yi fiye da “dukan abin da muke roƙo.”
9. Ta yaya muka tabbata cewa Jehobah zai albarkace mu?
9 Ya kamata mu kasance da bangaskiya ga Jehobah kuma mu riƙa bin umurninsa. Musa ya gaya wa al’ummar Isra’ila cewa: “Hakika Ubangiji za ya albarkace ka cikin ƙasa wanda Ubangiji Allahnka ke ba ka gādo domin ka ci mulkinta; idan za ka kasa kunne da himma ga muryar Ubangiji Allahnka, garin ka kiyaye dukan wannan doka wadda na umurce ka yau. Gama Ubangiji Allahnka za ya albarkace ka kamar yadda ya alkawarta maka.” (K. Sha. 15:4-6) Shin kana da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka idan ka ci gaba da bauta masa da aminci? Babu shakka, kana da dalili mai kyau na kasancewa da wannan tabbacin.
JEHOBAH YA SĀKA MUSU
10, 11. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Yusufu?
10 An rubuta Littafi Mai Tsarki don Rom. 15:4) Yusufu ya kafa mana misali mai kyau. An saka shi a fursuna domin mugun ƙulli da ‘yan’uwansa suka yi masa da sharrin da matar shugabansa ta yi masa. Shin hakan ya hana shi bauta wa Allah ne? A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji yana tare da Yusufu, ya gwada masa alheri . . . abin da ya yi kuma, Ubangiji yana albarkatar da shi.” (Far. 39:21-23) Amma Yusufu ya dogara ga Allahnsa a lokacin da yake shan wahala.
ya amfane mu. Yana ɗauke da labaran yadda Allah ya albarkaci bayinsa masu aminci. (11 Bayan wasu shekaru, Fir’auna ya saki Yusufu daga fursuna kuma ya saka shi ya zama mataimakinsa a Masar. (Far. 41:1, 37-43) A lokacin da matar Yusufu ta haifa masa yara biyu, “ya kira sunan ɗan farin Manasseh: Gama, in ji shi, Allah ya sa na manta da dukan wahalata, da dukan gidan ubana. Na biyu kuma ya kira sunansa Ifraimu: Gama Allah ya arzuta ni cikin ƙasar ƙaskancina.” (Far. 41:51, 52) Da yake Yusufu ya kasance da aminci ga Allah, an albarkace shi sosai kuma hakan ya sa ya ceci Isra’ilawa da kuma mutanen ƙasar Masar daga yunwa. Duk da haka, Yusufu ya san cewa Jehobah ne ya albarkace shi.—Far. 45:5-9.
12. Ta yaya Yesu ya kasance da aminci sa’ad da aka jarabce shi?
12 Yesu ma ya kasance da aminci sa’ad da aka jarabce shi amma Allah ya albarkace shi. Mene ne ya taimaka masa ya jimre? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Domin farin zuciya da aka sa gabansa, yana rena kunya.” (Ibran. 12:2) Yesu ya yi farin ciki domin yana tsarkake sunan Allah. Ƙari ga haka, Allah ya albarkace shi kuma ya ba shi ayyuka da yawa. Littafi Mai Tsarki ya ce, “ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.” A wani wuri kuma ya daɗa cewa: “Domin wannan Allah kuma ya ba shi mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna.”—Filib. 2:9.
JEHOBAH BA ZAI TAƁA MANTA DA HIDIMARMU BA
13, 14. Yaya Jehobah yake ji game da yadda muke taimaka wa mutane?
13 Muna da tabbaci cewa Jehobah yana jin daɗin ƙoƙarin da muke yi don mu bauta masa. Yana fahimtar yanayinmu sa’ad da muke shakka ko kuma jin tsoro. Yana taimaka mana sa’ad da matsalar kuɗi ko ciwo ya sa ba ma iya bauta masa yadda muka saɓa yi. Kuma muna da tabbaci cewa Jehobah yana kula da bayinsa da suke bauta masa da aminci.—Karanta Ibraniyawa 6:10, 11.
14 Har ila, ya kamata mu riƙa tuna cewa idan muka gaya wa “mai-jin addu’a” damuwarmu, zai taimaka mana. (Zab. 65:2) Littafi Mai Tsarki ya ce shi “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya” ne. Don haka, zai taimaka mana wataƙila ta wurin ‘yan’uwanmu. (2 Kor. 1:3) Jehobah yana farin ciki idan muka taimaka wa mutane. Kalmar Allah ta ce: “Mai-jin tausayin fakirai yana ba da rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” (Mis. 19:17; Mat. 6:3, 4) Saboda haka, idan muka taimaka wa mutanen da suke shan wahala, Jehobah yana gani kamar rance muka ba shi. Kuma ya yi alkawari cewa zai sāka mana.
ZAI SĀKA MANA YANZU DA KUMA NAN GABA
15. Wane abu ne kake begensa? (Ka duba hoton da ke shafi na 24.)
15 Shafaffun Kiristoci suna da begen samun ‘rawanin adalci, wanda Ubangiji, 2 Tim. 4:7, 8) Saboda haka, idan ba ka da wannan begen, bai kamata ka ga kamar ba ka da amfani ba. Miliyoyin “waɗansu tumaki” na Yesu za su sami rai na har abada a duniya kuma suna farin ciki don haka. Ban da haka ma, “za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Yoh. 10:16; Zab. 37:11.
adalin mai-shari’a, za ya ba su a wannan rana.’ (16. Wace ƙarfafa muka samu a littafin 1 Yohanna 3:19, 20?
16 A wasu lokuta, za mu ji kamar ba ma iya ƙoƙarinmu ko kuma mu riƙa shakka cewa Jehobah yana amincewa da hidimar da muke masa. Za mu iya gani kamar ba mu isa mu sami wani lada ba ma. Amma bai kamata mu manta cewa “Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” (Karanta 1 Yohanna 3:19, 20.) Yana sāka ma waɗanda suke masa ibada da bangaskiya da kuma ƙauna ko da suna ji kamar hidimar da suke yi ba ya bakin kome.—Mar. 12:41-44.
17. Waɗanne abubuwa muke morewa yanzu?
17 A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Jehobah yana yi wa bayinsa albarka. Yana tabbata cewa an koyar da mu sosai kuma muna farin ciki cewa muna da ‘yan’uwa a faɗin duniya. (Isha. 54:13) Kuma kamar yadda Yesu ya yi mana alkawari, Jehobah zai albarkace mu yanzu ta wurin ba mu zarafin kasancewa cikin iyalinsa da ke dukan duniya. (Mar. 10:29, 30) Ƙari ga haka, waɗanda suke biɗarsa za su sami kwanciyar hankali, su yi wadar zuci kuma su yi farin ciki.—Filib. 4:4-7.
18, 19. Yaya bayin Jehobah suke ji don albarkar da suke samu?
18 Bayin Jehobah a faɗin duniya suna samun albarka. Alal misali, wata mai suna Bianca daga ƙasar Jamus ta ce: “Na gode wa Jehobah don yadda yake taimaka min a kowace rana sa’ad da nake damuwa. Mutanen duniya suna fuskantar matsaloli kuma ba su da bege. Amma da yake ina bauta wa Jehobah, ina samun kāriya. A duk lokacin da na yi wata sadaukarwa, yana sāka min sosai.”
19 Ka yi la’akari da labarin Paula mai shekara 70 da ke ƙasar Kanada. Tana ciwon kashin baya da ake kira spina bifida. Ta ce: “Rashin tafiya wurare da yawa ba ya hana ni wa’azi. Ina yin wa’azi da tarho da yin wa’azi sa’ad da nake ayyuka na yau da kullum. Ƙari ga haka, don in riƙa samun ƙarfafa, ina da wani littafin da nake rubuta nassosi da kuma wasu furuci da na karanta daga littattafanmu. Ina kiransa ‘Littafin da Yake Ƙarfafa Ni.’ Idan muka mai da hankali ga alkawuran Jehobah, sanyin gwiwa ba zai shawo kanmu ba. Jehobah zai taimaka mana ko yaya yanayinmu.” Ko da yake yanayinka ba zai iya zama ɗaya da na Bianca ko Paula ba. Duk da haka, za ka iya yin tunanin wasu hanyoyin da Jehobah ya albarkace ka da kuma wasu. Yana da kyau mu riƙa yin tunani a kan yadda Jehobah yake yi mana albarka yanzu da kuma yadda zai yi mana nan gaba, ko ba haka ba?
20. Mene ne za mu samu idan muka ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci da kuma zuciya ɗaya?
20 Kada ka manta cewa za ka sami “sakamako mai-girma” idan ka yi wa Allah addu’a da zuciya ɗaya. (Ibran. 10:35, 36) Saboda haka, bari mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu riƙa bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Muna da tabbaci cewa zai albarkace mu.—Karanta Kolosiyawa 3:23, 24.