Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka bincika ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Wane irin zunubi ne Yesu yake maganarsa a shawarar da ya ba da a littafin Matta 18:​15-17?

Yana maganar matsaloli da ya kamata Kiristoci su sasanta da kansu. Amma idan ba su sasanta ba zai zama zunubi mai tsanani da zai iya sa a yi wa mutum yankan zumunci. Alal misali, irin wannan zunubin ya ƙunshi ɓata sunan mutum ko kuma zamba.​—w16.05, shafi na 7.

Mene ne za ka iya yi don ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki?

Za ka iya yin waɗannan abubuwa: Ka karanta da niyyar koyan wani darasi. Ka nemi darussa da za ka yi amfani da su; ka yi wa kanka tambayoyi kamar ‘Ta yaya zan iya yin amfani da wannan umurnin don in taimaka wa wasu?’; kuma ka yi amfani da kayan bincike don ka yi bincike a kan abin da ka karanta.​—w16.05, shafuffuka na 24-26.

Ko da yake mun gaskata da tashin matattu, laifi ne mu yi makoki?

Yin imani cewa za a ta da mutane daga mutuwa ba ya kawar da baƙin ciki da Kirista yake yi idan aka yi masa rasuwa. Ibrahim ya yi makoki sa’ad da Saratu ta rasu. (Far. 23:⁠2) Amma da shigewar lokaci, mutum zai soma warwarewa.​—wp16.3, shafi na 4.

Wane ne mai riƙe da ƙaho na ajiyar tawada da kuma mutane shida masu makami da aka ambata a littafi Ezekiyel sura ta 9 suke wakilta?

Mun fahimci cewa suna wakiltar runduna na sama da suka halaka Urushalima kuma su ne za su halaka wannan muguwar duniyar Shaiɗan a lokacin yaƙin Armageddon. A cikar annabcin nan a zamaninmu, mutumin da yake riƙe da ƙaho na ajiyar tawada yana wakiltar Yesu Kristi. Shi ne yake saka wa mutanen da za su tsira shaida a goshinsu.​—w16.06, shafuffuka na 16-17.

Ta yaya aka kāre Littafi Mai Tsarki?

Na (1) littafi Mai Tsarki ya fuskanci ƙalubalen ruɓewar kayayyakin da aka yi amfani da su don a rubuta shi, kamar fata da takardar ganye; (2) hamayya daga ‘yan siyasa da malaman addinai da suka yi ƙoƙari su halaka Littafi Mai Tsarki; kuma na (3) wasu mafassara da masu kofe Littafi Mai Tsarki sun nemi su canja saƙon da ke cikinsa.​—wp16.4, shafuffuka na 4-7.

A waɗanne hanyoyi ne Kirista zai iya sauƙaƙa rayuwarsa?

Ka san ainihin abubuwan da kake bukata, kuma ka daina sayan abubuwan da ba su da muhimmanci. Ka tsai da shawara a kan abin da za ka saya a kowane mako ko wata da kuma yawan kuɗi da za ka kashe. Ka zubar ko ka kyautar da abubuwan da ba ka amfani da su. Ka biya bashin da ake bin ka. Kuma ka rage yawan aikin da kake yi, kuma ka shirya yadda za ka ƙara fita hidima sosai.​—w16.07, shafi na 10.

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce ya fi zinariya ko azurfa tamani?

Littafin Ayuba 28:​12, 15 ya faɗi cewa hikimar da Allah yake bayarwa ta fi zinariya ko azurfa tamani. Yayin da kake neman ta, ka yi ƙoƙari ka zama mai tawali’u kuma ka kasance da bangaskiya sosai.​—w16.08, shafuffuka na 18-19.

Shin ya dace ne wani ɗan’uwa ya bar gemu?

A wasu al’adu, ana amincewa da gemun da aka gyara da kyau, kuma hakan ba zai hana mutane saurarar saƙonmu ba. Amma, wasu suna iya tsai da shawara cewa ba za su bar gemu ba. (1 Kor. 8:⁠9) A wasu yankuna da kuma al’adu, bai dace masu wa’azi su riƙa barin gemu ba.​—w16.09, shafi na 21.

Me ya sa muka gaskata cewa labarin Dauda da Goliyat ya faru da gaske?

Tsayin Goliyat kamu shida ne wato inci goma sha bakwai da ɗigo biyar kuma ya fi mutum mafi tsayi a duniya a zamaninmu. Dauda ya wanzu da gaske, don masu tone-tonen ƙasa sun gano wani dutse inda aka ambata gidan Dauda. Ƙari ga haka, abin da Yesu ya faɗa game da Dauda ya nuna cewa ya wanzu da gaske. Rubuce-rubucen da aka yi sun tabbatar da hakan.​—wp16.5, shafi na 13.

Wane bambanci ne ke tsakanin hikima da ilimi da kuma fahimi?

Wanda yake nazari da kuma bincike sosai a kan abubuwa zai zama mai ilimi. Wanda yake da fahimi yana ganin alaƙar abin da ya koya da abin da ya sani a dā da kuma yadda hakan zai amfane shi. Amma wanda yake da hikima yana yin abin da ya koya a rayuwarsa.​—w16.10, shafi na 18.