HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Disamba 2019
Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 3 Fabrairu–1 ga Maris, 2020.
‘Akwai Lokacin’ Yin Aiki da Kuma Hutu
A wannan talifin, za a yi amfani da misalin Assabaci da Isra’ilawa suke yi don a taimaka mana mu bincika ra’ayinmu game da aiki da hutu.
Jehobah Yana Ba Ka ’Yanci
Bikin samun ʼyanci ya tuna mana tanadin da Jehobah ya yi mana.
Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
A dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, idan wani ya yi wa macen da an riga an yi alkawarin aure da ita fyade a fili kuma ta yi ihu, macen ba ta da laifi amma mutumin yana da shi. Me ya sa?
Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Sa’ad da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta ba za ta mutu ba, shin yana so ya koya mata cewa kurwa ba ta mutuwa ne?
Ka San Jehobah Sosai?
Mene ne yake nufi mu san Jehobah kuma wane darasi ne za mu iya koya game da kulla dangantaka mai kyau daga Musa da kuma Dauda?
Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Su Kaunaci Jehobah
Ta yaya iyaye za su iya koyar da yaransu su kaunaci Jehobah kuma su bauta masa?
Ku Zama “Masu Godiya”
Akwai dalilai da yawa da suka sa nuna godiya yake da kyau.
Ka Tuna?
Ka ji dadin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga abubuwan da za ka iya tunawa.
Fihirisar Hasumiyar Tsaro ta 2019
Fihirisar dukan talifofin da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro na 2019, an jera su bisa abin da suke magana a kai.