Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

Jehobah Yana Ba Ka ’Yanci

Jehobah Yana Ba Ka ’Yanci

“Za a kuwa yi shelar samun ’yanci a dukan ƙasar ga dukan mazaunanta.”​—L. FIR. 25:10.

WAƘA TA 22 Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Mene ne bikin samun ’yanci? (Ka duba akwatin nan “ Mece ce Shekara ta Samun ’Yanci?”) (b) Kamar yadda Luka 4:​16-18 suka nuna, mene ne Yesu ya yi magana a kai?

A WASU ƙasashe, ana keɓe ranar da za a yi bikin cika shekara hamsin da sarki ko sarauniya ke mulki. Mutane suna iya ɗaukan kwana ɗaya ko mako ɗaya ko kuma fiye da hakan suna yin wannan bikin. Amma a ƙarshe, ana kammala bikin kuma mutane su mance da batun.

2 Za mu tattauna wani bikin samun ’yanci mai muhimmanci da ya fi wanda Isra’ilawa suke yi kowace shekara hamsin a dā. Me ya sa muke bukatar mu tattauna wannan batun? Domin bikin samun ’yanci da Isra’ilawa suka yi zai tuna mana tanadi na musamman da Jehobah ya yi. Wannan tanadin zai sa mu sami ’yanci na har abada kuma za mu iya amfana daga wannan tanadin a yanzu, Yesu ma ya yi magana game da tanadin.​—Karanta Luka 4:​16-18.

Mutane suna farin ciki sosai a shekara ta samun ’yanci domin waɗanda suka zama bayi suna komawa ga iyalinsu da kuma filayensu (Ka duba sakin layi na 3) *

3. Kamar yadda Littafin Firistoci 25:​8-12 suka nuna, ta yaya Isra’ilawa suka amfana daga shekara ta samun ’yanci?

3 Za mu fi fahimtar abin da Yesu yake nufi sa’ad da ya yi magana game da ’yanci idan muka tattauna shekara ta samun ’yanci da Allah ya ce Isra’ilawa su riƙa yi. Jehobah ya gaya musu cewa: ‘Za a keɓe wannan shekara ta hamsin da tsarki. Za a kuwa yi shelar samun ’yanci a dukan ƙasar ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekara ta samun ’yanci a gare ku. Kowa zai koma ga kayan gādon iyalinsa, kowa kuma ga iyalinsa.’ (Karanta Littafin Firistoci 25:​8-12.) A talifin da ya gabata, mun tattauna yadda Isra’ilawa suka amfana daga ranar Assabaci. Ta yaya Isra’ilawa suka amfana daga shekara ta samun ’yanci? Alal misali, a ce Ba’isra’ile ya ci bashi kuma hakan ya sa ya sayar da filinsa don ya biya bashin. A shekarar samun ’yanci, za a mayar masa da filinsa. Hakan yana nufin cewa mutumin zai sami “kayan gādon iyalinsa,” kuma a nan gaba yaransa za su gāji filin. Ƙari ga haka, idan wani ya ci bashi kuma hakan ya sa ya sayar da ɗaya cikin yaransa ya zama bawa ko kuma shi da kansa ya zama bawa don ya biya bashin, zai koma “ga iyalinsa” a shekara ta samun ’yanci. Hakan yana nufin cewa babu wanda zai zama bawa muddar ransa! Wannan tsarin ya nuna cewa Jehobah ya damu da mutanensa sosai!

4-5. Me ya sa yake da muhimmanci mu koya game da shekara ta samun ’yanci?

4 Ta yaya kuma suka amfana daga shekara ta samun ’yanci? Jehobah ya ce: “Hakika Yahweh Allahnku zai albarkace ku a cikin ƙasar da yake ba ku gādo ku mallake ta. Ba za a sami masu bukata a cikinku ba.” (M. Sha. 15:4) Hakan ya bambanta da abin da ke faruwa a yau! Muna yawan ganin mawadata suna ƙara yin arziki, matalauta kuma suna daɗa talaucewa!

5 A matsayinmu na Kiristoci, ba ma bin dokar da Allah ya ba Isra’ilawa. Ba ma bin tsarin shekara ta samun ’yanci, wato ʼyantar da bayi ko yafe wa mutane bashi da kuma mayar da fili ga masu shi. (Rom. 7:4; 10:4; Afis. 2:15) Amma yana da muhimmanci mu koya game da shekara ta samun ’yanci. Me ya sa? Domin za mu iya samun ’yanci da ke tuna mana tanadin da Jehobah ya yi wa Isra’ilawa.

YESU YA YI SHELAR SAMUN ’YANCI

6. Daga mene ne ’yan Adam suke bukatar ’yanci?

6 Dukanmu muna bukatar ’yanci domin mu bayi ne ga zunubi, wato bauta mafi muni. Da yake mu masu zunubi ne, muna tsufa da rashin lafiya da kuma mutuwa. Mutane da yawa suna ganin hakan sa’ad da suka kalli kansu a madubi ko kuma suka je wurin likita domin suna rashin lafiya. Ƙari ga haka, muna yin sanyin gwiwa sa’ad da muka yi zunubi. Manzo Bulus ya ce an ‘ɗaure shi ga ƙa’idar nan ta zunubi’ kuma ya ƙara ce: “Kaitona! Abin tausayi ne ni! Wane ne zai cece ni daga jikin nan mai kai ga mutuwa?”​—Rom. 7:​23, 24.

7. Wane annabci ne Ishaya ya yi game da samun ’yanci?

7 Abin farin ciki, Allah ya shirya yadda za mu sami ’yanci daga zunubi. Yesu ne ya sa hakan ya yiwu. Fiye da shekara 700 kafin Yesu ya zo duniya, annabi Ishaya ya yi annabci game da ’yancin da ya fi na zamanin Isra’ilawa sosai. Ya ce: ‘Ruhun Ubangiji Yahweh yana a kaina, domin Yahweh ya keɓe ni in yi shelar labari mai daɗi ga talakawa, in warkar da waɗanda suka fid da zuciya, in yi shelar ’yanci ga waɗanda suke a ɗaure.’ (Isha. 61:1) Su wane ne wannan annabci ya shafa?

8. Waye ne annabcin Ishaya ya shafa?

8 Wannan annabci mai muhimmanci game da samun ’yanci ya soma cika ne sa’ad da Yesu ya soma hidimarsa a duniya. A lokacin da ya je majami’a a garinsu Nazarat, Yesu ya karanta wa Yahudawan da ke wurin annabcin nan da Ishaya ya yi. Ya ce: “Ruhun Ubangiji yana a kaina, domin ya keɓe ni in kawo wa matalauta labari mai daɗi. Ya aike ni in yi shela cewa waɗanda suke a ɗaure za a sake su, makafi za su sami ganin gari, waɗanda aka danne za su sami ’yanci. In kuma yi shelar wa kowa cewa lokaci ya yi da Ubangiji zai ceci mutanensa.” (Luk. 4:​16-19) Ta yaya Yesu ya cika wannan annabci?

MUTANE DA ZA SU FARA SAMUN ’YANCI

Yesu ya yi shelar samun ’yanci a majami’a a Nazarat (Ka duba sakin layi na 8-9)

9. Wane irin ’yanci ne mutane da yawa a zamanin Yesu suke nema?

9 A zamanin Yesu, mutane sun soma samun ’yancin da Ishaya ya yi annabcinsa da kuma Yesu ya karanta. Mun tabbatar da hakan domin Yesu ya ce: ‘Wannan Rubutacciyar Maganar Allah ta cika a kunnenku a yau.’ (Luk. 4:21) Wataƙila mutane da yawa da suka ji abin da Yesu ya karanta suna neman ’yanci ne daga mulkin Roma. Wataƙila sun yi tunani kamar maza biyu da suka ce: “Muna sa zuciya cewa shi ne zai fanshi Isra’ila!” (Luk. 24:​13, 21) Mun san cewa Yesu bai ƙarfafa mabiyansa su yi tawaye ga mulkin Roma ba. A maimakon haka, ya umurce su su “ba Kaisar abin da yake na Kaisar.” (Mat. 22:21) Ta yaya Yesu ya sa mutane suka sami ’yanci a lokacin?

10. Daga mene ne Yesu ya sa mutane su sami ’yanci?

10 Ɗan Allah ya zo don ya taimaka wa mutane su sami ’yanci a hanyoyi biyu. Na farko, ’yanci daga koyarwa ƙarya da malaman addinai ke yi. A lokacin, an tilasta wa Yahudawa da yawa su riƙa bin al’adu da kuma koyarwa ƙarya. (Mat. 5:​31-37; 15:​1-11) Mutanen da ke da’awa cewa suna taimaka wa mutane su bauta wa Allah ba sa bauta masa yadda yake so, kamar dai makafi ne su. Domin sun ƙi Almasihu da koyarwarsa, sun ci gaba da kasancewa cikin duhu kuma ba a gafarta zunubansu ba. (Yoh. 9:​1, 14-16, 35-41) Amma Yesu ya koyar da gaskiya kuma ya kafa misali mai kyau, ya nuna wa mutane masu tawali’u yadda za su sami ’yanci daga koyarwar ƙarya.​—Mar. 1:22; 2:23–3:5.

11. A wace hanya ta biyu ce Yesu ya ’yantar da mutane?

11 Hanya ta biyu da Yesu ya sa mutane su sami ’yanci ita ce ta wajen ’yantar da ’yan Adam daga bauta ga zunubin da muka gāda. Saboda hadayar da Yesu ya yi, Allah zai yafe zunubin waɗanda suka ba da gaskiya kuma suka amince da tanadin fansa da ya yi. (Ibran. 10:​12-18) Yesu ya ce: “Saboda haka idan Ɗan ya ’yantar da ku za ku sami ’yanci na gaske.” (Yoh. 8:36) Hakika wannan ’yanci yana da muhimmanci fiye da wanda Isra’ilawa suke samu a shekara ta samun ’yanci! Alal misali, mutumin da ya sami ’yanci a shekara ta samun ’yanci yana iya sake zama bawa, kuma a ƙarshe ya mutu.

12. Su waye ne suka fara amfana daga shelar samun ’yanci da Yesu ya yi?

12 A ranar Fentakos ta 33, Jehobah ya shafe manzannin Yesu da kuma wasu maza da mata masu aminci. Ya zaɓe su su zama ’ya’yansa domin a nan gaba su yi mulki tare da Yesu a sama. (Rom. 8:​2, 15-17) Waɗannan su ne mutane na farko da suka amfana daga ’yancin da Yesu ya yi shelarsa a majami’a a Nazarat. Waɗannan maza da mata sun sami ’yanci daga koyarwar ƙarya da kuma ayyukan da ba su dace ba da malaman addinin Yahudawa suke yi. Ƙari ga haka a wajen Allah, sun sami ’yanci daga zunubi da ke jawo mutuwa. Shekarar samun ʼyanci ta alama da ta soma sa’ad da aka shafe almajiran Yesu a shekara ta 33 za ta ƙare a ƙarshen Sarautar Yesu ta Shekara Dubu. Mene ne za a cim ma a wannan lokacin?

MILIYOYIN MUTANE ZA SU SAMI ’YANCI

13-14. Ban da Kiristoci shafaffu, su waye ne kuma za su iya amfana daga ’yancin da Yesu ya yi shelarsa?

13 A yau, miliyoyin mutane da suka fito daga al’ummai dabam-dabam suna cikin “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Allah bai zaɓe su su yi mulki tare da Yesu a sama ba. A maimakon haka, suna da begen yin rayuwa a duniya har abada. Kai ma kana da wannan begen?

14 A yau, kana amfana daga albarkun da shafaffu za su samu. Domin ka ba da gaskiya ga fansar da Yesu ya yi, kana iya roƙon Jehobah ya gafarta zunubanka. A sakamakon haka, za ka sami amincewar Jehobah da ke kawo kwanciyar rai. (Afis. 1:7; R. Yar. 7:​14, 15) Ƙari ga haka, ka yi tunanin albarkun da kake samu domin ka sami ’yanci daga koyarwar ƙarya. Yesu ya ce: “Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yoh. 8:32) Hakika, samun wannan ’yancin yana sa mu farin ciki!

15. Wane irin ’yanci da kuma albarka ne za mu samu a nan gaba?

15 Za ka sami ’yanci sosai a nan gaba. Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai halaka addinan ƙarya da kuma gwamnatocin ’yan Adam. Allah zai kāre “babban taro” da suka bauta masa. Bayan haka, zai sa su more rayuwa a aljanna a duniya har abada. (R. Yar. 7:​9, 14) Za a ta da mutane da yawa daga mutuwa kuma za su sami ’yanci daga zunubin da Adamu ya jawo.​—A. M. 24:15.

16. Wane ’yanci na musamman ne ’yan Adam za su samu a nan gaba?

16 A lokacin Sarautar Yesu ta Shekara Dubu, shi da abokan mulkinsa za su taimaka wa ’yan Adam su sami ƙoshin lafiya kuma su zama ’ya’yan Allah. Wannan lokacin zai zama kamar shekara ta samun ’yanci a zamanin Isra’ilawa. Dukan mutanen da suka bauta wa Jehobah da aminci za su zama kamiltattu kuma ba za su riƙa zunubi ba.

A sabuwar duniya, za mu ji daɗin yin aiki mai kyau da kuma mai gamsarwa (Ka duba sakin layi na 17)

17. Mene ne Ishaya 65:​21-23 ya ce zai faru da mutanen Allah? (Ka duba bangon gaba.)

17 An kwatanta yadda rayuwa za ta kasance a duniya a Ishaya 65:​21-23. (Karanta.) A lokacin, ba za mu zama masu ƙyuya ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane za su riƙa yin aiki mai kyau da zai sa su sami gamsuwa. A ƙarshen wannan lokacin, za mu kasance da tabbaci “cewa halitta da kanta za ta sami tsira daga bautar da take wa ruɓewa, za ta kuma sami ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.”​—Rom. 8:21.

18. Me ya sa muka san cewa za mu yi farin ciki sosai a nan gaba?

18 Kamar yadda Jehobah ya tabbatar da cewa Isra’ilawa sun sami lokacin aiki da kuma hutu, zai yi hakan ma a lokacin Sarautar Yesu ta Shekara Dubu. Hakika, za a sami lokacin yin ayyukan ibada. Bauta wa Jehobah ne yake sa mu farin ciki a yau, kuma a sabuwar duniya, za mu sami lokacin yin hakan sosai. Babu shakka, dukan mutane musu aminci za su yi farin ciki a lokacin Sarautar Yesu ta Shekara Dubu, za mu yi aikin da zai sa su sami gamsuwa kuma za mu bauta wa Allah.

WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

^ sakin layi na 5 A zamanin dā, Jehobah ya yi tanadin hanya ta musamman da Isra’ilawa za su sami ’yanci. Kiristoci ba sa bin dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, amma za mu iya koyan darasi daga bikin samun ’yanci da suka yi. A wannan talifin, za mu ga yadda bikin samun ’yanci da Isra’ilawa suka yi zai tuna mana tanadin da Jehobah ya yi da kuma yadda za mu amfana daga tanadin.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: A shekara ta samun ’yanci, bayi suna samun ’yanci kuma su koma ga iyalinsu da kuma filayensu.