Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 51

Ka San Jehobah Sosai?

Ka San Jehobah Sosai?

“Waɗanda suka san Sunanka suna dogara gare ka, gama ba ka ƙyale masu neman saninka, ya Yahweh.”​—ZAB. 9:10.

WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda labarin Angelito ya nuna, mene ne kowannenmu zai yi?

IYAYENKA Shaidun Jehobah ne? Idan haka ne, ka tuna cewa ba za ka ƙulla abota da Jehobah domin suna yin hakan ba. Wajibi ne kowannenmu ya ƙulla nasa dangantaka da Allah ko da iyayenmu suna bauta masa ko a’a.

2 Ka yi la’akari da labarin wani ɗan’uwa mai suna Angelito. Dukan iyalinsa suna bauta wa Jehobah. Amma sa’ad da yake matashi, ya san cewa bai kusaci Allah sosai ba. Ya ce: “Ina bauta wa Jehobah domin ina so in yi abin da ’yan gidanmu suke yi.” Sai Angelito ya tsai da shawara ya ƙara ba da lokaci wajen karanta Kalmar Allah kuma ya yi bimbini sosai. Ƙari ga haka, ya soma yin addu’a ga Jehobah a kai a kai. Mene ne ya koya? Angelito ya ce, “Na koya cewa zan kusaci Jehobah idan na san shi sosai.” Abin da Angelito ya faɗa ya sa mu tunani game da wasu tambayoyi masu muhimmanci: Wane bambanci ne ke tsakanin sanin wasu abubuwa game da Jehobah da kuma sanin shi sosai? Mene ne za mu yi don mu san Jehobah sosai?

3. Wane bambanci ne ke tsakanin sanin Jehobah da kuma sanin sa sosai?

3 Muna iya tunanin cewa mun san Jehobah domin mun san sunansa ko kuma wasu abubuwan da ya yi ko ya faɗa. Amma hakan ba ya nufin mun san Jehobah sosai. Muna bukatar mu keɓe lokaci don mu koya game da Jehobah da halayensa masu ban al’ajabi. Sa’an nan za mu iya fahimtar abin da ya sa ya faɗi wani abu ko ya ɗauki wani mataki. Hakan zai taimaka mana mu san ko ya amince da ra’ayinmu da shawarwarinmu da kuma ayyukanmu. Muddin mun san abin da Jehobah yake so mu yi, muna bukatar mu yi abin da muka koya.

4. Ta yaya tattauna misalan da ke Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana?

4 Wasu mutane suna iya yi mana ba’a don muna bauta wa Jehobah ko kuma su tsananta mana sa’ad da muka soma halartan taro. Amma idan muka dogara ga Jehobah, ba zai taɓa yasar da mu ba kuma za mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. Shin za mu iya sanin Jehobah sosai? E, za mu iya! Misalan da Musa da Sarki Dauda suka kafa ya nuna cewa hakan zai yiwu. Yayin da muke tattauna ayyukansu, za mu amsa waɗannan tambayoyi biyu: Ta yaya suka san Jehobah? Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga misalansu?

MUSA YA GA “WANDA IDO BA YA IYA GANI”

5. Mene ne Musa ya zaɓi ya yi?

5 Musa ya zaɓi ya bauta wa Allah. Sa’ad da Musa yake ɗan shekara 40, ya zaɓi ya yi cuɗanya da mutanen Allah, wato Isra’ilawa, maimakon a san shi a matsayin “ɗan ’yar Fir’auna.” (Ibran. 11:24) Musa ya yasar da matsayi mai girma. Kuma ya san Fir’auna zai yi fushi sosai sa’ad da ya goyi bayan Isra’ilawa da suke zaman bauta a Masar. Fir’auna sarki ne mai iko sosai, kuma Masarawa suna ganin shi allah ne. Wannan ya nuna cewa Musa yana da bangaskiya sosai! Musa ya dogara ga Jehobah, kuma hakan ya sa ya ƙulla dangantaka na kud da kud da shi muddar ransa.​—K. Ma 3:5.

6. Mene ne muka koya daga misalin Musa?

6 Wane darasi ne muka koya? Kamar Musa, ya kamata dukanmu mu tsai da shawara: Shin za mu zaɓi mu bauta wa Allah kuma mu yi cuɗanya da mutanensa? Wataƙila za mu yi sadaukarwa don mu bauta wa Allah, kuma waɗanda ba su san Jehobah ba za su tsananta mana. Amma, Jehobah zai tallafa mana idan muka dogara gare shi!

7-8. Mene ne Musa ya ci gaba da koya?

7 Musa ya ci gaba da koya game da halayen Jehobah da kuma nufinsa. Alal misali, Jehobah ya gaya wa Musa cewa ya ja-goranci Isra’ilawa daga ƙasar Masar, amma ya gaya wa Jehobah sau da yawa cewa hakan ya fi ƙarfinsa. Amsar da Allah ya ba shi ya nuna cewa ya ji tausayin sa, kuma ya taimaka masa. (Fit. 4:​10-16) Saboda haka, ya iya aiwatar da saƙon hukunci ga Fir’auna. Musa ya ga yadda Jehobah ya yi amfani da ikonsa sa’ad da ya ceci Isra’ilawa kuma ya halaka Fir’auna da rundunarsa a Jar Teku.​—Fit. 14:​26-31; Zab. 136:15.

8 Isra’ilawa sun yi gunaguni a kai a kai bayan da Musa ya fito da su daga Masar. Ban da haka, Musa ya lura cewa Jehobah mai haƙuri ne sosai sa’ad da yake sha’ani da mutanen da ya sa suka sami ’yanci. (Zab. 78:​40-43) Musa kuma ya lura cewa Jehobah mai tawali’u ne sosai domin bai halaka Isra’ilawa ba bayan ya ba shi haƙuri.​—Fit. 32:​9-14.

9. Kamar yadda Ibraniyawa 11:27 ta nuna, wane irin abokantaka ne Musa da Jehobah suka ƙulla?

9 Bayan Isra’ilawa sun fito daga Masar, dangantakar Musa da Jehobah ta yi danƙo sosai, har kamar yana iya ganin Ubansa da ke sama. (Karanta Ibraniyawa 11:27.) Littafi Mai Tsarki ya nuna irin abota da ke tsakaninsu cewa: “Yahweh yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda aboki yakan yi magana da abokinsa.”​—Fit. 33:11.

10. Mene ne muke bukatar mu yi don mu san Jehobah sosai?

10 Wane darasi ne muka koya? Don mu san Jehobah sosai muna bukatar mu koya game da halayensa kuma mu yi nufinsa. Nufin Jehobah a yau shi ne, “dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:​3, 4) Hanya ɗaya da za mu yi nufin Allah ita ce ta wurin koya wa mutane game da Jehobah.

11. Ta yaya muke sanin Jehobah sosai yayin da muke koya wa mutane game da shi?

11 Sau da yawa, sai lokacin da muke koya wa mutane game da Jehobah ne muke sanin sa sosai. Alal misali, muna ganin cewa Jehobah mai tausayi ne sosai sa’ad da ya taimaka mana mu sami waɗanda suke so su zama abokansa. (Yoh. 6:44; A. M. 13:48) Muna ganin cewa Kalmar Allah tana da iko domin tana taimaka ma ɗalibanmu su daina halayen banza kuma su yi canje-canje a rayuwarsu. (Kol. 3:​9, 10) Ƙari ga haka, muna ganin cewa Allah mai haƙuri ne sa’ad da yake sa mu je mu taimaka wa mutane a yankinmu su koya game da shi kuma su sami ceto.​—Rom. 10:​13-15.

12. Kamar yadda aka nuna a Fitowa 33:​13, mene ne Musa ya roƙa kuma me ya sa?

12 Musa bai yi wasa da dangantakarsa da Jehobah ba. Duk da cewa Jehobah ya yi amfani da Musa don ya yi ayyuka masu ban mamaki, ya gaya wa Jehobah yana so ya san shi sosai. (Karanta Fitowa 33:13.) Musa ya wuce shekara 80 sa’ad da ya yi wannan roƙon, amma ya san cewa har ila yana da abubuwa da yawa da zai koya game da Jehobah.

13. A wace hanya ce za mu nuna ba ma wasa da abokantakarmu da Jehobah?

13 Wane darasi ne muka koya? Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, bai kamata mu yi wasa da dangantakarmu da shi ba. Hanya ta musamman da za mu nuna cewa ba ma wasa da abokantakarmu da Jehobah ita ce ta yin addu’a.

14. Me ya sa addu’a take da muhimmanci idan muna so mu ƙara koya game da Allah?

14 Idan muna so mu ƙulla abota na kud da kud da wani, za mu riƙa hira da mutumin sosai. Saboda haka, ka kusaci Allah ta wurin yin addu’a a kai a kai. Kada ka ji tsoron gaya masa tunaninka da yadda kake ji. (Afis. 6:18) Wata ’yar’uwa mai suna Krista da take zama a ƙasar Turkiya ta ce: “Ina ƙara ƙaunar Jehobah da kuma dogara a gare shi a kowane lokaci da na gaya masa abin da ke zuciyata sa’ad da nake addu’a. Kuma ina ganin yadda yake taimaka min. Ganin yadda Jehobah yake amsa addu’o’ita ya taimaka mini in ɗauke shi a matsayin Ubana da Abokina.”

MUTUMIN DA JEHOBAH YAKE ƘAUNA ƘWARAI

15. Mene ne Jehobah ya ce game da Sarki Dauda?

15 An haifi Sarki Dauda a al’ummar da ke bauta wa Jehobah. Amma Dauda bai bauta wa Jehobah domin iyayensa suna hakan ba. Ya ƙulla tasa dangantakar da Allah, kuma Jehobah ya ƙaunace shi sosai. Jehobah ya ce Dauda ‘mutum ne mai zuciya irin tasa.’ (A. M. 13:22) Ta yaya Dauda ya kusaci Jehobah?

16. Mene ne Dauda ya koya game da Jehobah ta wajen lura da halittu?

16 Dauda ya koya game da Jehobah ta wajen lura da halittu. A lokacin da Dauda yake matashi, ya yi sa’o’i da yawa yana kiwon tumakin mahaifinsa. Wataƙila a lokacin ne ya soma lura da halittun Jehobah. Alal misali, sa’ad da Dauda ya kalli sama daddare, bai ga damin taurari kaɗai ba, amma ya lura da halayen Allahn da ya halicce su. Hakan ya motsa Dauda ya rubuta cewa: “Sammai suna shelar ɗaukakar Allah! Sararin sama yana sanar da ayyukan hannuwansa!” (Zab. 19:​1, 2) Sa’ad da Dauda ya yi tunani a kan yadda Allah ya halicci mutane, ya ga irin hikimar da Jehobah yake da shi. (Zab. 139:14) Ƙari ga haka, sa’ad da Dauda ya yi tunanin abubuwan da Jehobah ya halitta, ya ga cewa Jehobah ya fi shi girma sosai.​—Zab. 139:6.

17. Mene ne za mu iya koya idan muka lura da halittu?

17 Wane darasi ne za mu iya koya? Ka yi marmarin koyan abubuwa daga halittu. Ka ɗauki lokaci don ka lura da duniya mai kyau da Jehobah ya halitta! Ka yi tunani a kan abubuwan da shuke-shuke da dabbobi suke koya maka game da Jehobah. Idan ka yi hakan, za ka koya game da Ubanmu mai ƙauna a kowace rana. (Rom. 1:20) Ƙari ga haka, za ka ga cewa ƙaunarka ga Jehobah tana daɗa ƙaruwa.

18. Kamar yadda Zabura ta 18 ta nuna, mene ne Dauda ya fahimta?

18 Dauda ya san cewa Jehobah yana taimaka masa. Alal misali, sa’ad da Dauda ya kāre tumakin mahaifinsa daga namomin daji, ya san cewa Jehobah ne ya taimaka masa ya kashe waɗannan mugayen dabbobin. Sa’ad da ya yi nasara a kan Goliyat, ya sani sarai cewa Jehobah ne ya taimaka masa. (1 Sam. 17:37) Ƙari ga haka, sa’ad da Dauda ya tsira daga hannun Sarki Saul da ke so ya kashe shi saboda ƙishi, ya ce Jehobah ne ya cece shi. (Rubutun da ke saman Zabura ta 18.) Da a ce Dauda mai girman kai ne, zai yi tunanin cewa shi ne ya yi dukan waɗannan abubuwan. Amma Dauda mai sauƙin kai ne, kuma ya fahimci cewa Jehobah ne ya taimaka masa.​—Zab. 138:6.

19. Mene ne za mu iya koya daga misalin Dauda?

19 Wane darasi ne za mu iya koya? Ba neman taimakon Jehobah kaɗai muke bukatar mu yi ba. Muna bukatar mu san yadda Jehobah yake taimaka mana da kuma lokaci da yake hakan. Idan muna da sauƙin kai, za mu fahimci cewa muna da kasawa. Jehobah yana taimaka mana mu yi abubuwan da ba za mu iya da kanmu ba. A duk lokacin da muka ga yadda Jehobah ya taimaka mana, dangantakarmu da shi za ta yi ƙarfi. Wani ɗan’uwa mai suna Isaac a tsibirin Fiji, ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah. Ya ce: “Sa’ad da na yi tunanin abubuwan da suka faru a rayuwata, ina ganin yadda Jehobah ya taimaka mini daga lokacin da na soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki har zuwa yau. A sakamakon haka, dangantakata da Jehobah ta yi ƙarfi.”

20. Me ya taimaki Dauda ya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah kuma me za mu iya koya daga misalinsa?

20 Dauda ya yi koyi da halayen Jehobah. Jehobah ya halicce mu da baiwar yin koyi da halayensa. (Far. 1:26) Idan mun san halayen Jehobah, za mu so mu yi koyi da shi. Dauda ya san Jehobah sosai, hakan ya sa ya yi koyi da shi sa’ad da yake sha’ani da mutane. Ka yi la’akari da wannan misalin. Dauda ya yi zunubi ga Jehobah sa’ad da ya yi zina da Bath-sheba kuma ya sa aka kashe mijinta. (2 Sam. 11:​1-4, 15) Amma Jehobah ya nuna wa Dauda jinƙai, domin ya yi koyi da Jehobah ta wajen nuna wa mutane jinƙai. Domin Dauda yana da dangantaka mai kyau da Jehobah, Isra’ilawa sun ƙaunace shi sosai kuma Jehobah ya yi amfani da shi a matsayin zakaran gwaji ga sauran sarakunan Isra’ila.​—1 Sar. 15:11; 2 Sar. 14:​1-3.

21. Kamar yadda Afisawa 4:24 da 5:1 suka nuna, wane sakamako ne za mu samu idan muka yi koyi da Allah?

21 Wane darasi ne za mu iya koya? Muna bukatar mu riƙa yin koyi da Allah. Idan muka yi hakan, za mu amfana kuma za mu san shi sosai. Ƙari ga haka, idan muka yi koyi da halayen Allah, muna nuna cewa mu ’ya’yansa ne.​—Karanta Afisawa 4:24; 5:1.

MU CI GABA DA KOYO GAME DA JEHOBAH

22-23. Mene ne zai faru idan muka yi amfani da abubuwan da muka koya game da Jehobah?

22 Kamar yadda muka gani, Jehobah yana bayyana mana halayensa masu kyau ta halittu da kuma Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan bayin Allah masu aminci kamar Musa da Dauda da za mu iya yin koyi da su. Jehobah ya yi mana tanadin abubuwan da za su iya taimaka mana. Muna bukatar mu ƙoƙarta don mu ci gaba da koyo game da shi.

23 Ba za mu taɓa daina koyo game da Jehobah ba. (M. Wa. 3:11) Yin amfani da abubuwan da muka sani game da Jehobah ya fi sanin abubuwa da yawa game da shi muhimmanci. Idan muka yi amfani da abubuwan da muka koya kuma muka yi ƙoƙarin yin koyi da halayen Jehobah, zai ci gaba da kusantar mu. (Yaƙ. 4:8) Ta Kalmarsa, Jehobah ya tabbatar mana da cewa ba zai taɓa yasar da waɗanda suke ƙoƙarin sanin sa ba.

WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’

^ sakin layi na 5 Mutane da yawa sun yi imani cewa akwai Allah, amma ba su san shi sosai ba. Mene ne sanin Jehobah yake nufi, mene ne za mu iya koya daga Musa da kuma Sarki Dauda game da yadda za mu ƙulla abokantaka ta kud da kud da Jehobah? Za a amsa waɗannan tambayoyi a wannan talifi.