Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Zama “Masu Godiya”

Ku Zama “Masu Godiya”

SHIN kai mutum ne mai nuna godiya? Dukanmu muna bukatar mu yi tunani sosai a kan wannan tambayar. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a kwanaki na ƙarshe, mutane za su zama “marasa godiya.” (2 Tim. 3:2) Wataƙila ka taɓa haɗuwa da mutanen da suke ganin cewa ya kamata a riƙa yi musu kyauta ko kuma wasu ayyuka. Kuma suna ganin ba sa bukatar su riƙa nuna godiya. Hakika, ba za ka so yin sha’ani da irin mutanen ba.

Saboda haka, Jehobah ya umurci bayinsa cewa: Su zama “masu godiya.” Muna bukatar mu riƙa nuna godiya a kowane abu. (Kol. 3:15; 1 Tas. 5:18) Nuna godiya yana amfanar mu. Da akwai dalilai da yawa da za su sa mu riƙa yin hakan.

NUNA GODIYA YANA SA MU FARIN CIKI

Wani dalili mai muhimmanci da ya sa ya kamata mu riƙa nuna godiya shi ne don yin hakan yana sa mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu. Mutumin da ya nuna godiya zai yi farin ciki, kuma wanda aka gode wa ma zai yi farin ciki. Ta yaya nuna godiya yake sa mu da kuma wanda aka gode wa farin ciki? Ka yi la’akari da wannan misalin: Idan wani ya yi amfani da lokacinsa don ya taya ka yin wani aiki, hakika ya yi hakan ne domin kana da daraja a gare shi kuma ya damu da kai. Idan ka fahimci hakan, za ka yi farin ciki. Wataƙila abin da ya faru da Ruth ke nan. Boaz ya nuna mata alheri sosai. Babu shakka, Ruth ta yi farin ciki da ta ga cewa Boaz ya damu da ita.​—Rut 2:​10-13.

Yana da muhimmanci sosai mu riƙa gode wa Allah. Hakika, a wasu lokuta kana yin tunani a kan abubuwan da ya yi maka. Ƙari ga haka, kana yin tunani a kan abubuwan da ke ƙarfafa dangantakarka da shi da ya tanadar da kuma yadda yake biyan bukatunka. (M. Sha. 8:​17, 18; A. M. 14:17) Zai dace ka ɗau lokaci don yin tunani sosai a kan yadda Allah yake yi wa kai da kuma iyalinka albarka. Yin hakan zai sa ka daɗa gode masa kuma ka fahimci cewa yana ƙaunar ka da kuma daraja ka.​—1 Yoh. 4:9.

Mu yi tunani a kan abubuwan da Jehobah yake ba mu kuma mu riƙa yi masa godiya sosai. (Zab. 100:​4, 5) Mutane suna faɗa cewa nuna godiya yana sa mutane matuƙan farin ciki.

NUNA GODIYA NA ƘARFAFA ABOKANTAKA

Wani dalili kuma da ya sa nuna godiya yake da muhimmanci shi ne don yana ƙarfafa abokantaka. Dukanmu muna so a riƙa daraja mu. Idan ka gode wa abokinka don alherin da ya yi maka, hakan zai sa ku kusaci juna. (Rom. 16:​3, 4) Ƙari ga haka, mutanen da suke nuna godiya suna iya taimaka wa wasu. Suna lura sa’ad da wani ya yi musu alheri kuma hakan yana motsa su su nuna alheri. Hakika taimaka wa mutane yana sa su farin ciki. Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—A. M. 20:35.

Wani darekta a makarantar jami’ar da ke Kalifoniya mai suna Robert Emmons ya yi nazari a kan nuna godiya. Ya ce: “Don mu riƙa nuna godiya, ya kamata mu fahimci cewa muna bukatar taimako. A wasu lokuta, mu ne za mu taimaka ma wasu, a wasu kuma su ne za su taimaka mana.” Gaskiyar ita ce, don mu ci gaba da rayuwa da kuma farin ciki, muna bukatar taimako. Alal misali, za a iya taimaka mana da abinci ko kuma magani. (1 Kor. 12:21) Mutum mai godiya yana daraja abin da aka yi masa. Tun da haka ne, kana nuna godiya domin abin da aka yi maka kuwa?

NUNA GODIYA NA SA KA ZAMA DA RA’AYIN DA YA DACE

Wani dalili kuma da ya sa ya kamata mu riƙa nuna godiya shi ne domin zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace. A alamance, zuciyarmu tana kama da rariya. Za ta taimaka mana mu yi tunani a kan abin da ya dace kuma ta kāre mu daga waɗanda ba su dace ba. Za ka kasance da ra’ayin da ya dace, kuma hakan zai sa ka daɗa godiya. Idan ka mai da hankali ga abubuwan da za ka iya godiya a kansu, hakan zai taimaka maka ka yi abin da manzo Bulus ya ce: “Ku yi farin ciki cikin Ubangiji kullum.”​—Filib. 4:4.

Nuna godiya za ta taimaka maka ka guji yin tunanin da bai dace ba. Ba za mu riƙa kishi ko kuma ɓacin rai ba idan muna nuna godiya. Ƙari ga haka, mutane masu nuna godiya ba sa biɗan kayan duniya. Sun gamsu da abubuwan da suke da shi kuma ba za su yi ƙoƙarin neman ƙari ba.​—Filib. 4:12.

KA YI TUNANIN ALBARKA DA KA SAMU!

A matsayinka na Kirista, ka san cewa Shaiɗan yana so ka karaya kuma ka riƙa baƙin ciki domin matsalolin da kake fuskanta. Yana so ka kasance da ra’ayin da bai dace ba kuma ka riƙa gunaguni. Idan haka halinka yake, zai yi wuya mutane su riƙa saurarar wa’azinka. Nuna godiya tana da alaƙa da halayen da ruhun Allah yake sa mu kasance da su. Alal misali, muna farin ciki sa’ad da muka ga abubuwan da Allah ya ba mu kuma mun gaskata cewa zai cika alkawuransa.​—Gal. 5:​22, 23.

A matsayinka na bawan Jehobah, babu shakka ka amince da abin da aka tattauna a wannan talifin game da nuna godiya. Duk da haka, a wasu lokuta yana iya yi mana wuya mu nuna godiya ko kuma mu kasance da ra’ayin da ya dace. Kada ka bari hakan ya sa ka sanyin gwiwa. Kana iya kasancewa da ra’ayin da ya dace. Ta yaya? Ka ɗau lokaci kowace rana don ka yi tunani a kan abubuwa a rayuwarka da za ka iya yin godiya a kai. Idan kana yin hakan, zai yi maka sauƙi ka zama mai godiya. Hakan zai sa ka farin ciki fiye da waɗanda suke mai da hankali ga matsalolinsu. Ka mai da hankali a kan abubuwa masu kyau da Allah da kuma wasu suke yi maka da suke ƙarfafa ka da kuma sa ka farin ciki. Wataƙila kana ma iya rubuta su. Kana iya rubuta abubuwa biyu ko uku da za ka yi godiya a kai.

Masu bincike sun gano cewa idan kana yawan gode wa mutane, yana iya canja yadda ƙwaƙwalwarka take aiki kuma ka soma farin ciki. Mutum mai nuna godiya yana farin ciki. Don haka, ka yi tunanin dukan abubuwa masu kyau da aka ba ka, ka more abubuwan da kake da su kuma ka riƙa nuna godiya! Maimakon ku riƙa nuna cewa ba ku damu ba da waɗannan abubuwan, “ku yi godiya ga Yahweh.” E, a cikin kowane hali ku zama “masu godiya.”​—1 Tar. 16:34; 1 Tas. 5:18.