Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Sa’ad da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta ba za ta mutu ba, shin yana so ya koya mata cewa kurwa ba ta mutuwa ne?
A’a. Shaiɗan bai gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya haramta, za ta zama kamar mutum da ya mutu amma kurwarta za ta ci gaba da rayuwa a wani wuri ba. Sa’ad da Shaiɗan ya yi amfani da maciji ya yi magana da Hauwa’u, ya yi da’awa cewa idan ta ci ’ya’yan itacen, ‘ko kaɗan, ba za ta mutu ba.’ Shaiɗan yana nufin cewa Hauwa’u za ta ci gaba da more rayuwa a duniya kuma za ta sami ’yanci daga wurin Allah.—Far. 2:17; 3:3-5.
Idan koyarwar kurwa marar mutuwa ba ta samo asali a lambun Adnin ba, yaushe ne aka soma wannan koyarwar? Ba mu sani ba. Mun san cewa an hallaka dukan addinan ƙarya sa’ad da aka yi Ambaliya a zamanin Nuhu. Allah ya yi amfani da ambaliyar wajen hallaka dukan mabiyan addinan ƙarya, Nuhu da iyalinsa ne kaɗai suka tsira kuma suna bauta wa Jehobah.
Koyarwar kurwa marar mutuwa ta samo asali ne bayan Ambaliya a zamanin Nuhu. A lokacin da Allah ya dagula yaren da ake yi a Babel kuma mutanen suka ‘warwatsa ko’ina a fuskar duniya,’ babu shakka, sun kai koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa zuwa wuraren. (Far. 11:8, 9) Ko da daga ina ne wannan koyarwar ta samo asali, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Shaiɗan, wanda shi “uban ƙarya” ne ya yaɗa wannan koyarwa.—Yoh. 8:44.