TALIFIN NAZARI NA 51
Jehobah Yana Taimaka wa Waɗanda Suka Yi Sanyin Gwiwa
“Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.”—ZAB. 34:18.
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1-2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
A WASU lokuta, muna tunani a kan yadda kwanakin rayuwarmu ba su da yawa. Da kuma yadda rayuwarmu ke cike da “wahala.” (Ayu. 14:1) Babu shakka, hakan na sa mu sanyin gwiwa. Bayin Jehobah da yawa ma a dā sun yi sanyin gwiwa. Wasu ma sun gwammace su mutu. (1 Sar. 19:2-4; Ayu. 3:1-3, 11; 7:15, 16) Amma Jehobah, Allahn da muke dogara gare shi yana ƙarfafa mu a kowane lokaci. Jehobah ya sa a rubuta labaransu domin idan mun karanta su, za mu sami ƙarfafa.—Rom. 15:4.
2 A wannan talifin, za mu tattauna game da wasu bayin Jehobah da suka fuskanci matsaloli. Wato Yusufu ɗan Yakubu da Naomi wata gwauruwa da surkuwarta Ruth, da wani Balawi da ya rubuta Zabura ta 73 da kuma manzo Bitrus. Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa su? Kuma waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarinsu? Amsoshin da za mu samu za su nuna cewa Jehobah “yana kusa” da waɗanda ba su da “ƙarfin gwiwa,” kuma yana “kuɓutar da masu fid da zuciya.”—Zab. 34:18.
YUSUFU YA JIMRE RASHIN ADALCI
3-4. Mene ne ya faru sa’ad da Yusufu yake matashi?
3 A lokacin da Yusufu yake wajen ɗan shekara 17, Allah ya sa ya yi mafarkai guda biyu. Mafarkan sun nuna cewa Yusufu zai zama mutum mai iko sosai, kuma iyalinsa za su riƙa daraja shi. (Far. 37:5-10) Amma jim kaɗan bayan Yusufu ya yi mafarkan, rayuwarsa ta canja farat ɗaya. A lokacin, yayyensa ba sa daraja shi. Saboda haka, sun sayar da shi kuma ya zama bawan Fotifar a ƙasar Masar. (Far. 37:21-28) A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, rayuwar Yusufu ta canja gabaki ɗaya. Ba ya tare da babansa da ke ƙaunar sa, kuma ya zama bawan wani mutum a ƙasar Masar da ba ya bauta wa Jehobah, kuma ana wulaƙanta shi sosai.—Far. 39:1.
4 Wani abu ya faru da ya ƙara tsananta yanayin Yusufu. Matar Fotifar ta ɗora masa sharri cewa yana so ya yi mata fyaɗe. A lokacin da Fotifar ya ji labarin, bai yi bincike don ya san gaskiyar lamarin ba. Ya yanke hukunci a kan Yusufu kuma ya jefa shi cikin kurkuku. (Far. 39:14-20; Zab. 105:17, 18) Yusufu matashi ne a lokacin. Saboda haka, ka yi tunanin yadda ya ji sa’ad da aka yi masa sharri cewa yana so ya yi wa wata fyaɗe. Kuma ka yi tunanin yadda hakan ya ɓata sunan Jehobah. Babu shakka, abubuwan nan sun sa Yusufu sanyin gwiwa sosai.
5. Mene ne Yusufu ya yi don ya rage sanyin gwiwa?
5 A lokacin da Yusufu ya zama bawa, da kuma sa’ad da aka saka shi cikin kurkuku, ba shi da ikon canja yanayinsa. Mene ne ya taimaka masa ya kasance da ra’ayin da ya dace? Yusufu bai mai da hankali a kan abubuwan da bai iya yi ba. Maimakon haka, ya mai da hankali a kan ayyukan da aka ba shi. Mafi muhimmanci ma, Yusufu ya mai da hankalinsa a kan faranta ran Jehobah. Saboda haka, Jehobah ya albarkaci dukan abubuwan da Yusufu ya yi.—Far. 39:21-23.
6. Ta yaya mafarkan Yusufu suka ƙarfafa shi?
6 Wataƙila yin tunani a kan mafarkan da ya yi ya taimaka wa Yusufu ya jimre. Mafarkan sun nuna cewa zai sake ganin iyalinsa, kuma yanayinsa zai canja. Abin da ya faru ke nan. A lokacin da Yusufu yake wajen shekara 37, mafarkansa sun fara cika a hanyoyi masu ban-mamaki.—Far. 37:7, 9, 10; 42:6, 9.
7. Kamar yadda 1 Bitrus 5:10 ta nuna, mene ne zai taimaka mana mu jimre da matsaloli?
7 Darussan da muka koya. Labarin Yusufu ya koya mana cewa akwai mugayen mutane da yawa a wannan duniyar, kuma Zab. 62:6, 7; karanta 1 Bitrus 5:10.) Ka tuna cewa shekarun Yusufu wajen 17 ne a lokacin da Jehobah ya sa ya yi mafarkan nan guda biyu. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana daraja matasa da ke bauta masa. A yau, muna da matasa da yawa kamar Yusufu. Suna da bangaskiya ga Jehobah. An saka wasu cikinsu a kurkuku domin sun ƙi su daina bauta wa Jehobah.—Zab. 110:3.
za su iya wulaƙanta mu. Har ’yan’uwa a ikilisiya za su iya ɓata mana rai. Amma idan mun dogara ga Jehobah, ba za mu yi sanyin gwiwa ba ko kuma mu daina bauta masa. (MATA BIYU DA SUKA YI BAƘIN CIKI SOSAI
8. Mene ne ya faru da Ruth da Naomi?
8 Naomi da iyalinta sun bar Yahudiya zuwa ƙasar Mowab, domin ana yunwa sosai a ƙasarsu. A lokacin da suke ƙasar Mowab, sai maigidanta Elimelek ya mutu ya bar da ta da yara maza biyu. Da shigewar lokaci, sai yaran suka auri mata ’yan ƙasar Mowab, masu suna Ruth da Orfa. Bayan wajen shekara goma, sai yaran nan biyu suka rasu ba tare da sun haifi ’ya’ya ba. (Rut 1:1-5) Ka yi tunanin irin baƙin cikin da matan nan uku suka yi! Ruth da Orfa za su iya sake aure domin ba su tsufa ba tukun. Amma Naomi fa? Wa zai kula da ita da yake ta soma tsufa? Naomi ta yi baƙin ciki sosai, har akwai lokacin da ta ce: “Kada ku ce da ni Na’omi, wato mai jin daɗi. Ku ce da ni Mara, wato mai ɗaci, domin Mai Iko Duka ya sa rayuwata ta zama da ɗaci.” Bayan abubuwan nan sun faru, Naomi ta yanke shawara cewa za ta koma ƙasarsu Bai’talami, kuma Ruth ta bi ta.—Rut 1:7, 18-20.
9. Kamar yadda Rut 1:16, 17, 22 suka nuna, a wace hanya ce Ruth ta ƙarfafa Naomi?
9 Mene ne ya taimaka wa Naomi ta jimre da waɗannan matsalolin? Ƙauna ce. Alal misali, Ruth ta nuna wa Naomi cewa tana ƙaunar ta domin ba ta rabu da ita ba. (Karanta Rut 1:16, 17, 22.) A lokacin da suke Bai’talami, Ruth ta yi kalar hatsi domin ita da Naomi su samu abincin da za su ci. A sakamakon haka, mutanen garin sun lura cewa Ruth mace mai ce kirki kuma tana aiki tuƙuru.—Rut 3:11; 4:15.
10. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mabukata kamar Ruth da Naomi?
10 Jehobah ya ba Isra’ilawa doka da ta nuna cewa yana tausaya wa talakawa kamar Ruth da Naomi. Ya gaya musu cewa sa’ad da suke girbin gonakinsu, kada su yi girbi har gefe-gefen gonakin domin talakawa su sami abin da za su yi kala. (L. Fir. 19:9, 10) Hakan zai sa Naomi da Ruth su sami abinci ba sai sun yi bara ba.
11-12. Ta yaya Boaz ya sa Naomi da Ruth farin ciki?
11 Mutumin da Ruth ta je kala a gonarsa mai arziki ne sosai, kuma sunansa Boaz. Yadda Ruth take da aminci ga Naomi kuma take ƙaunar ta sosai ya burge shi. Haka ya sa ya auri Ruth, kuma ya sayi filin da a dā, na iyalin su Naomi ne. Hakan zai sa ya yiwu yaran Ruth su gāji filin. (Rut 4:9-13) Boaz da Ruth sun haifi ɗa kuma shi ne ya zama kakan Sarki Dauda.—Rut 4:17.
12 Babu shakka, Naomi ta yi farin ciki sosai yayin da ta ɗauki jaririn kuma ta miƙa godiya ga Jehobah da dukan zuciyarta! Amma Naomi da Ruth za su fi farin ciki a nan gaba. A lokacin da za a ta da matattu, za su koyi cewa Obed ne ya zama kakan Almasihu, wato Yesu Kristi!
13. Waɗanne darussa masu muhimmanci ne za mu iya koya daga labarin Naomi da Ruth?
13 Darussan da muka koya. Za mu iya yin sanyin gwiwa sa’ad da muke fuskantar matsaloli, kuma za mu iya gani kamar ba mu K. Mag. 17:17.
da mafita. A waɗannan lokuta, ya kamata mu dogara ga Jehobah kuma mu kusaci ’yan’uwanmu a ikilisiya. Gaskiya ne cewa ba a kowane lokaci Jehobah yake magance matsalolinmu ba. Alal misali, bai ta da mijin Naomi da kuma ’ya’yanta biyu daga matattu ba. Amma zai taimaka mana mu jimre. Zai iya yin amfani da ’yan’uwanmu Kiristoci don ya yi hakan.—WANI BALAWIN DA YA KUSAN DAINA BAUTA WA JEHOBAH
14. Me ya sa wani Balawi ya yi sanyin gwiwa sosai?
14 Wani Balawi ne ya rubuta Zabura ta 73. Saboda haka, yana da damar yin hidima a haikalin Jehobah. Amma akwai wani lokaci da ya yi sanyin gwiwa. Me ya sa? Ya soma kishin mugaye da masu girman kai domin yana gani kamar suna samun ci gaba. (Zab. 73:2-9, 11-14) Yana gani suna da wadata, suna jin daɗin rayuwa, kuma ba su da matsaloli. Sa’ad da Balawin ya ga hakan, ya yi sanyin gwiwa sosai har ya ce: “Hakika, a banza ne na tsabtace zuciyata, na wanke hannuna in nuna rashin laifina.” Babu shakka, hakan zai iya sa ya daina bauta wa Jehobah.
15. Kamar yadda Zabura 73:16-19, 22-25 suka nuna, me ya taimaka wa Balawin ya daina baƙin ciki?
15 Karanta Zabura 73:16-19, 22-25. Balawin ya “shiga Wuri Mai Tsarki na Allah.” Sa’ad da yake wurin nan da ake bauta wa Jehobah, hankalinsa ya kwanta kuma ya sami damar yin addu’a ga Jehobah. A sakamakon haka, ya ga cewa tunaninsa bai dace ba kuma hakan zai iya sa ya daina bauta wa Jehobah. Ya kuma lura cewa mugaye suna tsaye a wuri mai “santsi” kuma dukansu za su “halaka kakaf.” Wannan Balawin yana bukatar ya kasance da ra’ayin Jehobah domin hakan zai taimaka masa ya daina sanyin gwiwa da kuma kishin mugayen mutane. Sa’ad da ya yi hakan, hankalinsa ya kwanta kuma ya sake farin ciki. Ya ce: “A duniya ma, ba abin da nake so in ban da kai” Jehobah.
16. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga wani Balawi?
16 Darussan da muka koya. Kada mu taɓa yin kishin mugaye domin muna gani M. Wa. 8:12, 13) Idan mun yi kishin su za mu yi sanyin gwiwa, kuma za mu ɓata dangantakarmu da Jehobah. Saboda haka, idan ka lura cewa kana kishin mugaye, ka yi abin da wannan Balawi ya yi. Ka bi shawarar Allah, kuma ka yi cuɗanya da mutanen da suke bauta wa Jehobah. Idan kana ƙaunar Jehobah fiye da kome, za ka yi farin ciki na gaske. Kuma za ka kasance a hanyar rai, wanda shi ne “ainihin rai.”—1 Tim. 6:19.
kamar suna samun ci gaba. Farin cikin da suke yi ba na gaske ba ne, ba zai dawwama ba. (KURAKUREN BITRUS SUN SA SHI SANYIN GWIWA
17. Waɗanne abubuwa ne suka sa Bitrus sanyin gwiwa?
17 Manzo Bitrus mutum ne mai ƙwazo sosai. Amma a wasu lokuta, yana ɗaukan mataki ba tare da ya yi tunani sosai ba. Saboda haka, a wasu lokuta, ya faɗa da kuma yi wasu abubuwan da daga baya, ya yi da-na-sani. Alal misali, sa’ad da Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa zai sha wahala kuma ya mutu, Bitrus ya tsawata masa ya ce: “Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba.” (Mat. 16:21-23) Bayan haka, sai Yesu ya yi wa Bitrus gyara. Sa’ad da taron ’yan iska suka zo su kama Yesu, Bitrus ya ɗauki mataki ba tare da yin tunani ba. Kuma ya yanke kunnen bawan babban firist. (Yoh. 18:10, 11) A wannan lokacin ma, Yesu ya yi wa wannan almajirinsa gyara. Ƙari ga haka, Bitrus ya yi burga cewa ko da sauran almajiran za su bar Yesu, shi ba zai taɓa barin sa ba! (Mat. 26:33) Amma duk ciccika baki ne kawai Bitrus yake yi. Domin daga baya ya ji tsoro, kuma ya yi mūsun sanin Yesu har sau uku. Hakan ya sa Bitrus sanyin gwiwa sosai, kuma “ya fita waje ya yi kuka mai zafi.” (Mat. 26:69-75) Wataƙila ya ɗauka cewa Yesu ba zai taɓa gafarta masa ba.
18. Ta yaya Yesu ya taimaka wa Bitrus ya daina sanyin gwiwa?
18 Amma Bitrus bai ƙyale baƙin ciki ya Yoh. 21:1-3; A. M. 1:15, 16) Mene ne ya taimaka masa? Ya tuna cewa Yesu ya yi addu’a a madadinsa don kada bangaskiyarsa ta kasa. Kuma Yesu ya gaya wa Bitrus cewa ya ƙarfafa ’yan’uwansa. Babu shakka, Jehobah ya amsa addu’ar Yesu. Daga baya, Yesu ya bayyana ga Bitrus don ya ƙarfafa shi. Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan sun wuni suna neman su kama kifi, amma ba su kama kome ba. (Luk. 22:32; 24:33, 34; 1 Kor. 15:5) A wannan lokacin, Yesu ya ba Bitrus zarafin gaya masa ko yana ƙaunar sa da gaske. Yesu ya gafarta wa abokinsa, kuma ya ba shi ƙarin aiki.—Yoh. 21:15-17.
hana shi bauta wa Jehobah ba. Bayan ya yi wannan kuskuren, ya ci gaba da yin cuɗanya da sauran almajiran Yesu. (19. Ta yaya Zabura 103:13, 14, suka koya mana yadda Jehobah yake ɗaukanmu sa’ad da muka yi zunubi?
19 Darussan da muka koya. Yadda Yesu ya yi sha’ani da Bitrus ya nuna cewa Yesu mai tausayi ne sosai, kuma yana koyi da halayen Jehobah. Saboda haka, a duk lokacin da muka yi zunubi, kada mu ɗauka cewa Jehobah ba zai taɓa gafarta mana ba. Mu tuna cewa Shaiɗan ne yake so mu ji hakan. Maimakon haka, mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu, ya san kasawarmu, kuma yana so ya gafarta mana. Saboda haka, ya kamata mu yi koyi da shi sa’ad da mutane suka ɓata mana rai.—Karanta Zabura 103:13, 14.
20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
20 Misalan Yusufu da Naomi da Ruth da Balawin da muka tattauna da kuma Bitrus, sun koya mana cewa Jehobah yana kusa da ‘waɗanda aka karya musu ƙarfin gwiwa.’ (Zab. 34:18) A wasu lokuta, yana barin mu mu sha wahala ko kuma mu yi sanyin gwiwa. Amma idan mun jimre matsaloli, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi. (1 Bit. 1:6, 7) A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka wa bayinsa masu aminci sa’ad da suke sanyin gwiwa saboda ajizancinsu ko kuma suna cikin wani mawuyacin yanayi.
WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu
^ sakin layi na 5 Yusufu da Naomi da Ruth da wani Balawi da manzo Bitrus sun fuskanci abubuwa da suka sa su sanyin gwiwa. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah ya ta’azantar da su kuma ya ƙarfafa su. Za mu kuma koyi darussa daga labarinsu da kuma yadda Jehobah ya tausaya musu.
^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Naomi da Ruth da kuma Orfa sun yi baƙin ciki don rasuwar mazansu. Daga baya, Naomi da Ruth da kuma Boaz sun yi farin ciki don haihuwar Obed.