Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Yaya ya kamata mu bi da shafaffu Kiristoci?

Muna alfahari da su don bangaskiyarsu, amma, ba ma daraja su fiye da kima. Ya kamata mu guji yin sha’awar mutane. (Yahu. 16) Kuma kada mu yi musu tambayoyi game da begensu.​—w20.01, shafi na 29.

Mene ne ya kamata ya tabbatar maka da cewa Jehobah ya san da kai?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya san ka tun kafin a haife ka. Kuma yana saurarar dukan addu’o’inka. Ya san abin da ke zuciyarka da abin da kake tunani a kai, kuma ayyukanka na shafan sa. (1 Tar. 28:9; K. Mag. 27:11) Jehobah ne ya jawo ka gare shi.​—w20.02, shafi na 12.

A wane lokaci ne ya kamata mu yi magana, a wane ne kuma ya kamata mu yi shiru?

Muna farin cikin gaya wa mutane game da Jehobah. Za mu yi magana sa’ad da muka ga wani yana so ya yi abin da bai dace ba. Sa’ad da wani yake bukatar gargaɗi, dattawa suna yin hakan. Ba ma faɗa ko kuma yi tambaya game da yadda ake yin ayyukanmu a ƙasashen da aka saka wa aikinmu takunkumi. Ba ma faɗin batutuwan sirri.​—w20.03, shafuffuka na 20-21.

Wane bambanci ne ke tsakanin farin da aka ambata a Yowel sura 2 da na Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 9?

Yowel 2:​20-29 sun ce Allah zai kawar da fārin kuma zai mayar da duk abin da suka ci. Bayan haka, Allah ya zuba ruhunsa. Annabcin nan ya cika sa’ad da Babila ta kai wa Isra’ila hari da kuma bayan haka. Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 9:​1-11 na bayyana shafaffun Kiristoci a zamaninmu yayin da suke sanar da saƙon hukuncin Jehobah a kan mugaye kuma saƙon yana tayar da hankalin mugayen sosai.​—w20.04, shafuffuka na 3-6.

Wane ne sarkin arewa a yau?

Ƙasar Rasha ce da magoya bayanta. Sun kai wa bayin Allah hari ta wajen saka wa aikinsu takunkumi da kuma tsananta musu. Suna yin jayayya da sarkin kudu.​—w20.05, shafi na 13.

Shin ʼya’yan ruhu guda tara da aka ambata a Galatiyawa 5:​22, 23 ne kaɗai ʼya’yan da ruhun Allah yake haifarwa?

A’a. Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu kasance da halaye masu kyau, kamar aminci. (Afis. 5:​8, 9)​—w20.06, shafi na 17.

Wane haɗari ne ke tattare da saka abubuwa game da kanka a Intane?

Abubuwan da ka saka zai iya sa mutane su ɗauka cewa kana ji da kanka kuma ba ka da sauƙin kai.​—w20.07, shafuffuka na 6-7.

Wane darasi ne masu shela za su iya koya daga masu kamun kifi?

Suna yin aiki a lokaci da kuma wurin da za su iya samun kifi. An koya musu yin amfani da kayan aikin da ya dace. Kuma suna aiki da ƙarfin zuciya a kowane yanayi. Za mu iya yin hakan a hidimarmu.​—w20.09, shafi na 5.

A waɗanne hanyoyi ne za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su ƙaunaci Jehobah sosai?

Za mu iya ƙarfafa su su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma su yi bimbini a kan abin da suka karanta. Kuma za mu iya koya musu yin addu’a.​—w20.11, shafi na 4.

Su waye ne furucin nan ya shafa: ‘Za a tā da duka saboda Almasihu.ʼ​—1 Kor. 15:22.

Manzo Bulus ba ya nufin cewa za a ta da dukan ʼyan Adam. Yana yin magana ne game da Kiristoci shafaffu waɗanda “aka keɓe su da tsarki cikin Almasihu Yesu.” (1 Kor. 1:2; 15:18)​—w20.12, shafuffuka na 5-6.

Mene ne shafaffu za su yi bayan sun canja “farat ɗaya, da ƙyiftawar ido, da jin ƙarar ƙaho na ƙarshe”?​—1 Kor. 15:​51-53.

Su da Yesu za su yi mulki da sandan ƙarfe. (R. Yar. 2:​26, 27)​—w20.12, shafuffuka na 12-13.