TALIFIN NAZARI NA 49
Za A Yi Tashin Matattu!
“Ina sa zuciya ga Allah . . . cewa, za a tā da matattu.”—A. M. 24:15.
WAƘA TA 151 Zai Kira Su
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1-2. Wane bege ne bayin Jehobah suke da shi?
YANA da muhimmanci mu kasance da bege. Wasu mutane suna sa rai cewa za su ji daɗin aurensu, su yi renon yara masu ƙoshin lafiya ko kuma su daina rashin lafiya mai tsanani. Mu ma za mu iya kasancewa da irin wannan begen. Amma muna sa rai cewa za mu samu abubuwan da suka fi waɗannan muhimmanci. Muna sa rai cewa za mu rayu har abada kuma Allah zai ta da matattu.
2 Manzo Bulus ya ce: “Ina sa zuciya ga Allah . . . cewa, za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (A. M. 24:15) Ba Bulus ba ne ya fara yin magana game da begen tashin matattu. Ayuba ma ya tabbata cewa Allah zai tuna da shi kuma ya ta da shi daga mutuwa.—Ayu. 14:7-10, 12-15.
3. Ta yaya 1 Korintiyawa sura 15 za ta iya taimaka mana?
3 “Tashin matattu” ne ‘tushe’ ko “koyarwar nan ta farko” da dukan Kiristoci suka yi imani da shi. (Ibran. 6:1, 2) An rubuta abin da Bulus ya faɗa game da tashin matattu a Korintiyawa na ɗaya sura 15. Babu shakka cewa abin da Bulus ya rubuta ya ƙarfafa Kiristoci a ƙarni na farko. Kuma wannan sura tana iya ƙarfafa mu ko da mun daɗe da kasancewa da wannan begen.
4. Mene ne ya tabbatar mana da cewa za a yi tashin matattu?
4 Tashin Yesu daga matattu ya tabbatar mana da cewa idan ’yan’uwanmu suka mutu, za a ta da su. Wannan yana cikin ‘labari mai daɗi’ da Bulus ya sanar wa Korintiyawa. (1 Kor. 15:1, 2) Bulus ya ce bangaskiyar Kirista banza ce idan bai yi imani da tashin matattu ba. (1 Kor. 15:17) Yin imani cewa Yesu ya tashi daga matattu ne dalilin da ya sa muka tabbata cewa za a ta da matattu.
5-6. Ta yaya kalmomin da ke 1 Korintiyawa 15:3, 4 suka shafe mu?
5 Bulus ya ambata abubuwa uku masu muhimmanci game da tashin matattu a wasiƙarsa. Ya ce: (1) “Almasihu ya mutu saboda zunubanmu.” (2) “An binne shi.” (3) “An tā da shi a rana ta uku, kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa.”—Karanta 1 Korintiyawa 15:3, 4.
6 Ta yaya mutuwar Yesu da jana’izarsa da kuma tashinsa daga matattu suka shafe mu? Annabi Ishaya ya annabta cewa za a “kawar da shi [Almasihu] daga duniyar masu rai” kuma a “yi kabarinsa tare da na mugaye.” Ban da haka, Ishaya ya daɗa cewa Almasihu zai “ɗauki laifofin mutane da yawa.” Yesu ya yi hakan ta wajen ba da ransa hadaya. (Isha. 53:8, 9, 12; Mat. 20:28; Rom. 5:8) Saboda haka, mutuwar Yesu da jana’izarsa da kuma tashinsa daga matattu sun tabbatar mana cewa za mu samu ’yanci daga zunubi da mutuwa. Ƙari ga haka, za a ta da ’yan’uwanmu da abokanmu da suka mutu.
ABIN DA SHAIDU DA YAWA SUKA TABBATAR
7-8. Mene ne ya tabbatar wa Kiristoci cewa an ta da Yesu daga matattu?
7 Don mu gaskata cewa za a yi tashin matattu, wajibi ne mu fara ba da gaskiya cewa an ta da Yesu daga matattu. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah ya ta da Yesu?
8 Mutane da yawa sun shaida cewa an ta da Yesu daga mutuwa, su kuma sun gaya wa mutane hakan. (1 Kor. 15:5-7) Bitrus, wato Kefas ne mutum na farko da Bulus ya ambata cewa ya ga an ta da Yesu. Wasu almajirai sun ce Bitrus ya ga Yesu bayan an ta da Yesu daga matattu. (Luk. 24:33, 34) Ƙari ga haka, manzannin Yesu guda goma “sha biyun” sun gan shi bayan an ta da shi daga mutuwa. Sa’an nan Yesu “ya bayyana ga ’yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda,” wataƙila a taron da aka yi a Galili da aka ambata a Matiyu 28:16-20. Yesu ya kuma “bayyana ga Yakub,” ɗan’uwansa da bai ba da gaskiya gare shi ba a matsayin Almasihu. (Yoh. 7:5) Yaƙub ya gaskata cewa Yesu ne Almasihu sa’ad da ya ga cewa an ta da Yesu daga mutuwa. Sa’ad da Bulus ya rubuta wannan wasiƙar a misalin shekara ta 55, mutane da yawa da suka shaida cewa an ta da Yesu suna da rai. Saboda haka, ba wanda zai yi mūsu cewa an ta da Yesu, domin akwai shaidu.
9. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 9:3-5 suka nuna, mene ne ya faru da Bulus da ya tabbatar da cewa an ta da Yesu daga matattu?
9 Daga baya, Yesu ya bayyana ga Bulus. (1 Kor. 15:8) Bulus yana hanya zuwa Dimashƙu sa’ad da ya ji muryar Yesu da aka ta da daga matattu kuma ya ga wahayinsa. (Karanta Ayyukan Manzanni 9:3-5.) Hakan ya nuna cewa an ta da Yesu daga mutuwa da gaske.—A. M. 26:12-15.
10. Mene ne Bulus ya yi domin ya gaskata cewa an ta da Yesu daga matattu?
10 Wasu mutane za su so su saurari Bulus domin a dā ya tsananta wa Kiristoci. Bayan Bulus ya tabbatar da cewa an ta da Yesu daga mutuwa, ya yi aiki tuƙuru don ya koyar da wannan gaskiyar. Sa’ad da yake wa’azi game da mutuwar Yesu da kuma tashiwarsa, an yi masa dūka, an saka shi a kurkuku kuma ya yi hatsarin 1 Kor. 15:9-11; 2 Kor. 11:23-27) Bulus ya tabbata sosai cewa an ta da Yesu daga matattu har yana a shirye ya mutu a kan gaskiyar nan. Babu shakka, wannan shaida daga Kiristoci na farko ya taimaka mana mu gaskata cewa an ta da Yesu. Ƙari ga haka, hakan ya tabbatar mana cewa za a yi tashin matattu a nan gaba.
jirgin ruwa. (AN FALLASA KOYARWAR ƘARYA
11. Me ya sa wasu a Korinti suke da ra’ayin da bai dace ba game da tashin matattu?
11 Wasu Kiristoci a birnin Korinti suna da ra’ayin da bai dace ba game da tashin matattu, wasu ma suna cewa ba za a yi “tashin matattu” ba. Me ya sa? (1 Kor. 15:12) Wasu ’yan falsafa a birnin Atina sun ce ba a ta da Yesu daga matattu ba. Irin wannan ra’ayin ya shafi wasu a Korinti. (A. M. 17:18, 31, 32) Wataƙila wasu sun yi tunani cewa tashin matattun ba a zahiri ba ne. Maimakon haka, suna ganin cewa masu zunubi ne ake kira matattu amma an “tā da” su sa’ad da suka zama Kiristoci domin an gafarta musu zunubansu. Ko da mene ne ya sa mutanen nan ba su gaskata da tashin matattu ba, bangaskiyarsu banza ce. Idan Allah bai ta da Yesu daga matattu ba, hakan yana nufin cewa Yesu bai ba da ransa hadaya ba kuma Allah bai gafarta zunubanmu ba. Saboda haka, waɗanda suka ƙi amincewa da tashin matattu ba su da bege.—1 Kor. 15:13-19; Ibran. 9:12, 14.
12. Kamar yadda aka nuna a 1 Bitrus 3:18, 22, ta yaya yadda aka ta da Yesu daga matattu ya bambanta da wanda aka yi da farko?
12 Bulus ya san cewa “an tā da Almasihu daga matattu.” Tashin Yesu daga matattu ya fi waɗanda aka yi kafin na Yesu domin mutanen sun sake mutuwa. Bulus ya ce Yesu “ne kuwa nunan fari daga matattu.” A wace hanya ce Yesu ya zama nunan fari? Shi ne aka fara ta da daga matattu da jiki na ruhu kuma shi ne mutum na farko da aka ta da zuwa sama.—1 Kor. 15:20; A. M. 26:23; karanta 1 Bitrus 3:18, 22.
MUTANEN DA “ZA A TĀ DA”
13. Wane bambanci ne Bulus ya ce ke tsakanin Adamu da Yesu?
13 Ta yaya mutuwar mutum ɗaya zai sa miliyoyi su rayu? Bulus ya ba da amsar dalla-dalla. Ya bayyana bambanci tsakanin abin da ya faru da ’yan Adam domin zunubin Adamu da abin da aka cim ma ta hadayar Kristi. Bulus ya ce game da Adamu: “Mutuwa ta zo ne ta wurin mutum.” Sa’ad da Adamu ya yi zunubi, ya jawo mutuwa ga kansa da kuma zuriyarsa. Har ila, muna shan wahala don rashin biyayya da Adamu ya yi. Amma muna da bege yin rayuwa har abada domin Allah ya ta da Ɗansa daga mutuwa! Bulus ya ce: ‘Tashin matattu ya zo ne ta wurin mutum. Gama kamar yadda duka suke mutuwa saboda Adam, haka za a tā da duka saboda Almasihu.’—1 Kor. 15:21, 22.
14. Za a ta da Adamu daga matattu? Ka bayyana.
14 Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce dukan mutane suna “mutuwa saboda Adam”? Yana magana ne game da dukan ’yan Adam da suka gāji zunubi da ajizanci daga Adamu kuma za su mutu a sakamakon hakan. (Rom. 5:12) Adamu ba ya cikin waɗanda “za a tā da” daga mutuwa. Ba zai amfana daga hadayar Kristi ba, domin shi kamili ne sa’ad da ya yi wa Allah rashin biyayya. Abin da ya faru da Adamu zai faru da dukan waɗanda “Ɗan Mutum” zai shari’anta a matsayin “awaki” kuma za a “halaka su har abada.”—Mat. 25:31-33, 46, New World Translation; Ibran. 5:9.
15. Su waye ne “duka” da “za a tā da”?
15 Bulus ya ce ‘za a tā da duka saboda Almasihu.’ (1 Kor. 15:22) Bulus ya rubuta wasiƙar ne ga Kiristoci shafaffu a Korinti waɗanda za a ta da zuwa sama. An “keɓe su da tsarki cikin Almasihu Yesu,” kuma an ‘kira su su zama tsarkaka.’ Bulus ya kuma ambata ‘waɗanda suka mutu cikin Almasihu.’ (1 Kor. 1:2; 15:18; 2 Kor. 5:17) A wata wasiƙa, Bulus ya ce waɗanda suka “zama ɗaya da shi [Yesu] cikin irin mutuwarsa” za su “zama ɗaya da shi cikin tashinsa daga matattu.” (Rom. 6:3-5) An ta da Yesu da jiki na ruhu kafin ya je sama. Haka ne za a ta da dukan shafaffun Kiristoci “cikin Almasihu.”
16. Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya kira Yesu “nunan fari”?
16 Bulus ya ce an ta da Kristi a matsayin “nunan fari daga matattu.” Ka tuna cewa an ta da mutane kamar su Li’azaru daga matattu, amma Yesu ne na farko da aka ta da da jikin ruhu kuma ya sami rai na har abada. Ana iya kamanta shi da nunan fari da Isra’ilawa suke ba da hadaya ga Allah a lokacin da suka yi girbi. Ƙari ga haka, ta wajen kiran Yesu “nunan fari,” Bulus yana nufin cewa za a ta da wasu mutane su yi rayuwa a sama bayan Yesu. Da shigewar lokaci, za a ta da manzannin Yesu da shafaffun Kiristoci don su yi rayuwa a sama kamar Yesu.
17. A wane lokaci ne shafaffu za su sami ladarsu na zuwa sama?
17 A lokacin da Bulus ya rubuta wannan wasiƙar zuwa ga Korintiyawa, ba a soma ta da shafaffu zuwa sama ba. Shi ya sa Bulus ya nuna cewa hakan zai faru a nan gaba. Ya ce: ‘Za a tā da kowanne bi da bi, Almasihu shi ne nunan fari, sa’an nan waɗanda suke nasa’ a lokacin bayyanuwarsa. (1 Kor. 15:23; 1 Tas. 4:15, 16) A yau, muna rayuwa a lokacin bayyanuwar Kristi. Manzannin Yesu da kuma shafaffu da suka mutu za su jira har sai lokacin bayyanuwarsa don su sami ladarsu na zuwa sama don su “zama ɗaya da shi cikin tashinsa daga matattu.”
ALLAH ZAI CIKA ALKAWARINSA!
18. (a) Me ya sa muka ce za a yi wani tashin matattu bayan shafaffu sun je sama? (b) Kamar yadda 1 Korintiyawa 15:24-26 suka nuna, mene ne zai faru a sama?
18 Me zai faru da waɗanda ba su da begen R. Yar. 20:6) Hakan yana nuna cewa za a yi wani tashin matattu bayan wannan. Kuma ya yi daidai da abin da Ayuba ya ce zai faru da shi a nan gaba. (Ayu. 14:15) “Waɗanda suke” na Kristi za su kasance a sama da shi sa’ad da zai kawar da dukan gwamnatoci da kuma hukumomi. Sa’an nan za a kawar da “abokiyar gaba ta ƙarshe.” Dukan waɗanda suka je sama ba za su taɓa mutuwa ba. Mene ne zai faru da sauran ’yan Adam?—Karanta 1 Korintiyawa 15:24-26.
zuwa sama? Su ma suna da begen tashi daga matattu. Littafi Mai Tsarki ya ce waɗanda za su je sama suna da ‘rabo cikin wannan farkon tashin matattu.’ (19. Mene ne zai faru da waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya?
19 Mene ne zai faru da waɗanda suke da begen zama a duniya? Abin da Bulus ya ce zai sa su kasance da bege, ya ce: “Ina sa zuciya . . . cewa, za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (A. M. 24:15) Hakika, mutane marasa adalci ba za su je sama ba. Saboda haka, furucin Bulus ya nuna cewa za a yi tashin matattu a duniya a nan gaba.
20. Ta yaya wannan talifin ya ƙarfafa bangaskiyarka?
20 Babu shakka, “za a tā da matattu”! Waɗanda aka ta da za su sami damar yin rayuwa har abada a duniya. Kana iya gaskata cewa Allah zai cika wannan alkawarin, kuma hakan zai ƙarfafa ka cewa za a ta da ’yan’uwanka da abokanka da suka mutu. Za a ta da su a lokacin da Yesu da shafaffu za su “yi mulki tare . . . har shekaru dubu.” (R. Yar. 20:6) Kai ma za ka iya kasancewa da bege cewa za a ta da kai idan ka mutu kafin lokacin sarautar Yesu na shekara dubu. Wannan begen ba zai “zama abin banza ba ko kaɗan.” (Rom. 5:5) Wannan begen zai ƙarfafa ka kuma ya sa ka farin ciki a hidimarka ga Allah. Kamar yadda za mu tattauna a talifi na gaba, da akwai abubuwan da za mu ƙara koya a Korintiyawa na ɗaya sura ta 15.
WAƘA TA 147 Alkawarin Rai Na Har Abada
^ sakin layi na 5 Littafin Korintiyawa na ɗaya sura 15 ya mai da hankali a kan batun tashin matattu. Me ya sa wannan koyarwar take da muhimmanci a gare mu, kuma me ya sa muke da tabbaci cewa an ta da Yesu daga mutuwa? Za a tattauna wannan tambaya da kuma wasu masu muhimmanci game da tashin matattu.
^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Yesu ne na farko da ya je sama. (A. M. 1:9) Wasu almajiransa kamar su Toma da Yaƙub da Lidiya da Yohanna da Maryamu da kuma Bulus za su kasance tare da shi a sama.
^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Matar wani ɗan’uwa da suka daɗe suna hidima tare ta rasu. Ɗan’uwan yana da bege cewa za ta tashi daga matattu. Hakan ya sa ya ci gaba da bauta wa Jehobah.