Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Littafin Firistoci 19:16 ta ba da umurni cewa kada mutum ya “yi wani abin da zai zama hatsari ga ran” maƙwabcinsa. Mene ne wannan umurnin yake nufi? Kuma wane darasi ne za mu iya koya daga umurnin?

Jehobah ya umurci Isra’ilawa su zama masu tsarki. Saboda hakan ne ya ce musu: ‘Ba za ku baza maganar ɓata suna a kan wani ba, ko ku yi wani abin da zai zama hatsari ga ran maƙwabcinku. Ni ne Yahweh.’​—L. Fir. 19:​2, 16.

Furucin nan “zama hatsari” yana iya nufin “tayar wa mutum.” Amma me furucin yake nufi? Wani littafin Yahudawa da aka rubuta game da Littafin Firistoci ya ce: “Wannan sashen ayar yana da wuya a bayyana shi domin bai da sauƙi a tantance asalin ma’anar wannan adon maganar a Ibrananci. Fassarar adon maganar kai tsaye ita ce ‘kada ka saya a kan, ko kusa ko kuma a gefen wani.’”

Wasu masanan Littafi Mai Tsarki sun ce ayar tana da alaƙa da aya ta 15, wadda ta ce: “Ba za ku yi sonkai a cikin shari’a ba. Ba za ku nuna bambanci wa talakawa ko ku girmama masu arziki ba. A cikin gaskiya za ku shari’anta maƙwabcinku.” (L. Fir. 19:15) Don haka, dokar da ke aya ta 16 cewa kada Isra’ilawa su yi abin da zai “zama hatsari” ga ran maƙwabcinsu, tana iya nufin kada su yi wani abin da zai cutar da mutum a kotu, ko a kasuwanci ko kuma a iyali. Ƙari ga haka, kada su yi rashin gaskiya don amfanin kansu. Gaskiya ne cewa bai kamata mu yi abubuwan nan ba, amma akwai wata hanya kuma da ya kamata mu fahimci furucin nan da ke aya ta 16.

Ka yi la’akari da farkon aya ta 16. Jehobah ya ba wa mutanensa doka cewa kada su yi tsegumi. Gaskiya ne cewa idan mutum ya yi gulma zai iya jawo matsala ga wasu, amma tsegumi ya fi gulma muni. (K. Mag. 10:19; M. Wa. 10:​12-14; 1 Tim. 5:​11-15; Yak. 3:6) Mutumin da yake yin tsegumi yakan yi ƙarya a kan wasu da gangan don ya ɓata musu suna. Mutum mai tsegumi zai iya ba da shaidar ƙarya a kan wani ko da hakan zai sa ran mutumin a cikin haɗari. Ka tuna cewa shaidar ƙarya da wasu suka yi a kan Nabot ne ya sa aka jejjefe shi har ya mutu. (1 Sar. 21:​8-13) Hakika, mutum mai tsegumi zai iya yin abin da zai zama hatsari ga ran wani, kamar yadda sashe na biyu na Littafin Firistoci 19:16 ya faɗa.

Ƙari ga haka, mutum zai iya yin tsegumi a kan wani domin ya ƙi jininsa. Littafin 1 Yohanna 3:15 ta ce: “Duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, shi mai kisan kai ne. Kuma kun sani cewa ba mai kisan kai wanda yake da rai na har abada.” Ban da haka, bayan Allah ya ce kada mu yi wani ‘abin da zai zama hatsari ga ran maƙwabcinmu,’ sai ya ce: “Ba za ka ƙi ɗan’uwanka a zuciyarka ba.”​—L. Fir. 19:17.

Don haka, dokar da ke Littafin Firistoci 19:16 gargaɗi ne mai kyau ga Kiristoci. Dole ne mu guji yin tunani marar kyau da kuma yin tsegumi a kan wasu. A taƙaice, idan ka ɓata sunan wani domin ba ka son yadda yake ko kuma kana kishin sa, hakan zai iya nuna cewa ka ƙi jininsa. A matsayinmu na Kiristoci, dole ne mu guji ƙin jinin mutane.​—Mat. 12:​36, 37.