Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Ka karanta dukan fitowar Hasumiyar Tsaro na shekarar nan da kyau? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Wane tabbaci ne Yakub 5:11 ta ba mu sa’ad da ta ce Jehobah “mai yawan tausayi” ne da “jinƙai”?

Mun san cewa Jehobah yana son gafarta mana zunubanmu domin shi mai jinƙai ne. Littafin Yakub 5:11 ta tabbatar mana cewa Jehobah yana so ya taimaka mana sosai. Zai dace mu yi koyi da shi.​—w21.01, shafi na 21.

Me ya sa Jehobah ya ba wasu iko?

Jehobah ya kafa tsarin shugabanci domin yana ƙaunar iyalinsa. Hakan yana sa iyalin Jehobah su kasance da tsari da kuma kwanciyar hankali. Dukan iyalin da suke bin wannan tsarin sun san ko wane ne zai riƙa tsai da shawarwari da kuma tabbatar da cewa an bi shawarwarin.​—w21.02, shafi na 3.

Me ya sa ya kamata Kiristoci su yi hankali da yadda suke amfani da manhajar tura saƙonni?

Idan Kirista ya yanke shawarar yin amfani da manhajar tura saƙonni, yana bukatar ya yi hankali da irin mutanen da yake tarayya da su. Hakan zai iya yi masa wuya idan yana rukunin da akwai mutane da yawa. (1 Tim. 5:13) Ƙari ga haka, akan yaɗa labarai da aka ƙara gishiri a kansu a manhajar tura saƙonni, ko kuma waɗanda ba a san ko gaskiya ba ne. Wasu kuma sukan yi amfani da bayanan ’yan’uwansu don yin kasuwanci.​—w21.03, shafi na 31.

Waɗanne dalilai ne suka sa Allah ya ƙyale Yesu ya sha wahala kuma ya mutu?

Na farko, an rataye Yesu a kan gungume domin a kuɓutar da Yahudawa daga wata la’ana. (Gal. 3:​10, 13) Na biyu, Jehobah yana horar da Yesu ne don aikin da zai yi a nan gaba a matsayin Babban Firist. Na uku, yadda Yesu ya riƙe amincinsa har ƙarshe ya nuna cewa ’yan Adam za su iya riƙe amincinsu sa’ad da suke fuskantar jarrabawa mai tsanani. (Ayu. 1:​9-11)​—w21.04, shafuffuka na 16-17.

Me za ka iya yi don ka iya samun mutanen da ba a samun su a gida?

Ka ziyarci mutane a lokacin da za ka iya samun su, ko ka neme su a wurare dabam-dabam ko kuma ka yi amfani da hanyoyi dabam-dabam, kamar rubuta musu wasiƙa.​—w21.05, shafuffuka na 15-16.

Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: “Ta wurin Koyarwar Musa na zama matacce ga Koyarwar Musa”? (Gal. 2:19)

Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa ta nuna cewa ’yan Adam ajizai ne kuma ta taimaka wa Isra’ilawa su san Almasihu. (Gal. 3:​19, 24) Hakan ya sa Bulus ya ba da gaskiya ga Yesu Kristi. Ta hakan Bulus ya “zama matacce ga Koyarwar Musa,” wato ya fita daga ƙarƙashinta.​—w21.06, shafi na 31.

Ta yaya Jehobah ya kafa misali mai kyau na jimrewa?

Jehobah yana jimre yadda ake ɓata sunansa, yadda mutane da yawa suka ƙi shi da kuma mulkinsa, yadda wasu daga cikin yaransa suka yi tawaye, ƙaryar da Shaiɗan yake yi, yadda bayinsa suke shan wahala, kewar abokansa da suka mutu, yadda ’yan Adam masu mugunta suke sa wasu shan wahala, da kuma yadda ’yan Adam suke lalata duniya.​—w21.07, shafuffuka na 9-12.

Wane darasi game da haƙuri ne za mu iya koya daga Yusufu?

Ya jimre rashin adalcin da ’yan’uwansa suka yi masa. Wannan rashin adalcin ya sa an yi masa sharri kuma aka saka shi a kurkuku na shekaru da yawa a Masar.​—w21.08, shafi na 12.

Wace girgiza ce Haggai 2:​6-9, 20-22 suka annabta cewa zai faru?

Al’ummai sun ƙi su amince da wa’azin Mulkin Allah da muke yi, amma mun ga yadda mutane da yawa suka soma bauta wa Jehobah. Nan ba da daɗewa ba, al’ummai za su fuskanci girgiza ta ƙarshe sa’ad da za a hallaka su.​—w21.09, shafuffuka na 15-19.

Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa a yin wa’azi ba?

Jehobah yana ganin ƙoƙarinmu, kuma hakan yana faranta masa rai. Idan ba mu gaji ba, za mu sami rai na har abada.​—w21.10, shafuffuka na 25-26.

Ta yaya Littafin Firistoci sura 19 za ta taimaka mana mu bi shawarar nan: “Ku keɓe kanku da tsarki a cikin dukan ayyukanku”? (1 Bit. 1:15)

Da alama an yi ƙaulin Littafin Firistoci 19:2 ne a ayar nan. Sura ta 19 ta ba da misalan yadda za mu iya bin 1 Bitrus 1:15 a rayuwarmu ta yau da kullum.​—w21.12, shafuffuka na 3-4.