Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kai Abokin Aiki Nagari Ne?

Kai Abokin Aiki Nagari Ne?

“INA nan tare da shi, kamar gwanin aiki. . . . Ina farin ciki a gabansa.” (K. Mag. 8:30) Wannan ayar ta bayyana yadda Yesu ya yi aiki da Ubansa na shekaru da yawa kafin ya zo duniya. Mun koya daga ayar nan cewa Yesu ya yi “farin ciki” sa’ad da yake aiki tare da Jehobah.

Sa’ad da Yesu yake sama, ya koyi abubuwan da suka taimaka masa ya zama abokin aiki nagari. Shi ya sa sa’ad da ya zo duniya, ya kafa mana misali mai kyau a kan yadda za mu yi aiki da wasu. Ta yaya za mu amfana daga misalin Yesu? Ta wajen bincika misalinsa, za mu ga ƙa’idodi uku da za su taimaka mana mu zama abokan aiki nagari. Ƙa’idodin za su taimaka mana mu yi aiki da ’yan’uwanmu cikin haɗin kai.

Ku bi misalin Jehobah da Yesu ta wajen gaya wa abokan aikinku abubuwan da kuka sani

ƘA’IDA TA 1: ‘KU GIRMAMA JUNA’

Abokin aiki nagari yana da sauƙin kai. Ya san cewa abokan aikinsa suna da muhimmanci kuma ba ya ƙoƙarin yin abubuwa don mutane su ɗaukaka shi kawai. Abin da Yesu ya koya daga wurin Ubansa ke nan. Ko da yake Jehobah ne kaɗai ya cancanci a kira shi Mahalicci, Jehobah ya gaya mana aiki mai muhimmanci da Ɗansa ya yi, ya ce: ‘Bari mu yi mutum a kamanninmu.’ (Far. 1:26) Wannan abin da Jehobah ya faɗa ya nuna wa Yesu cewa Jehobah mai sauƙin kai ne.​—Zab. 18:​35, New World Translation.

Yesu ya nuna irin wannan sauƙin kai sa’ad da yake duniya. Da aka yaba masa don abubuwan da ya cim ma, ya miƙa yabon ga Jehobah. (Mar. 10:​17, 18; Yoh. 7:​15, 16) Yesu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya zauna lafiya da almajiransa, kuma ya ɗauke su a matsayin abokai, ba bayi ba. (Yoh. 15:15) Ya ma wanke ƙafafunsu don ya koya musu sauƙin kai. (Yoh. 13:​5, 12-14) Mu ma ya kamata mu riƙa daraja abokan aikinmu maimakon mu riƙa tunanin kanmu kawai. Za mu yi nasara sosai a aikinmu idan mun daraja mutane, maimakon mu yi abubuwa domin a daraja mu kawai.​—Rom. 12:10.

Mutum mai sauƙin kai ya san cewa “tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.” (K. Mag. 15:22) Kome iyawarmu, dole mu tuna cewa ba za mu iya sanin kome da kome ba. Ko Yesu da kansa ma ya ce akwai abubuwa da bai sani ba. (Mat. 24:36) Ƙari ga haka, akwai lokacin da ya tambayi almajiransa ra’ayinsu. (Mat. 16:​13-16) Shi ya sa abokan aikinsa sun ji daɗin aiki da shi! Idan muna da sauƙin kai kuma muka tuna cewa ba kome da kome ba ne muka sani, kuma muka saurari shawarar wasu, za mu zauna lafiya da mutane, kuma tare, za mu ‘ci nasara.’

Ya kamata dattawa musamman su bi misalin Yesu na nuna sauƙin kai yayin da suke aiki tare. Suna bukatar su tuna cewa ruhu mai tsarki zai iya amfani da kowannen su. Yayin da dattawa suke taro, ya kamata su tabbata cewa kowannen su zai iya saki jiki kuma ya ba da shawara. Idan suka yi hidima cikin haɗin kai, za su yanke shawarar da za ta amfani ikilisiya.

ƘA’IDA TA 2: “KU NUNA SANIN YAKAMATA A KOWANE LOKACI”

Abokin aiki nagari yana nuna sanin yakamata yayin da yake aiki da abokan aikinsa. Sau da yawa, Yesu ya ga yadda Ubansa yake nuna sanin yakamata. Alal misali, Jehobah ya aiko shi ya zo ya ceto ’yan Adam daga mutuwar da suka gāda.​—Yoh. 3:16.

Yesu ba ya nacewa a kan ra’ayinsa. Ka tuna da yadda ya taimaka ma wata ’yar ƙasar Kan’ana duk da cewa al’ummar Isra’ila ce ya zo ya taimaka wa. (Mat. 15:​22-28) Ban da haka, bai bukaci manzanninsa su yi abin da ya fi ƙarfinsu ba. Bayan da amininsa manzo Bitrus, ya musanta saninsa a fili, Yesu ya gafarta masa. Daga baya, ya danƙa wa Bitrus ayyuka masu muhimmanci ya yi. (Luk. 22:32; Yoh. 21:17; A. M. 2:14; 8:​14-17; 10:​44, 45) Misalin Yesu ya nuna mana cewa, dole ne mu “nuna sanin yakamata a kowane lokaci” ba tare da nacewa a kan ra’ayinmu ba.​—Filib. 4:​5NW.

Sanin yakamata zai taimaka mana mu daidaita yanayinmu don mu yi aiki da mutane cikin salama. Yesu ya nuna wa kowa alheri sosai, har maƙiyansa suka ce shi “abokin masu karɓan haraji da masu zunubi” ne, wato waɗanda suka saurari wa’azinsa. (Mat. 11:19) Shin za mu iya yin aiki da waɗanda suka fito daga wuri dabam da mu kamar yadda Yesu ya yi? Wani ɗan’uwa mai suna Louis, da ya yi aiki da ’yan’uwa dabam-dabam sa’ad da yake hidimar mai kula da da’ira, da kuma sa’ad da ya je Bethel, ya ce: “Yin aiki da mutane ajizai yana kamar gina katanga da duwatsu da girmansu ya bambanta. Da yake girman duwatsun ya bambanta, gina katangar zai iya yin wuya. Amma duk da haka, za a iya yin katangar ta miƙe da kyau. Nakan yi canje-canje don mu samu mu yi aiki lami lafiya kuma mu yi nasara a aikin.” Wannan hali ne mai kyau!

Abokin aiki nagari ba zai ɓoye wa abokan aikinsa abin da ya sani domin yana so ya riƙa jujjuya su kamar waina ba

A waɗanne lokuta ne za mu iya nuna sanin yakamata ga ’yan’uwa a ikilisiyarmu? Za mu iya yin hakan sa’ad da muke tare da rukuninmu na yin wa’azi. Za mu iya yin wa’azi tare da waɗanda suka fito daga iyalai dabam-dabam, da waɗanda shekarunmu ba ɗaya ba. Za mu iya amfani da salon wa’azin da suka fi so, ko mu rage sauri yayin da muke tafiya tare da su don su ma su ji daɗin yin wa’azi.

ƘA’IDA TA 3: KU RIƘA “TAIMAKON WAƊANSU”

Abokin aiki nagari yana a shirye ya ‘taimaki waɗansu.’ (1 Tim. 6:18) Da alama sa’ad da Yesu yake aiki da Jehobah, ya lura cewa Ubansa ba mai ɓoye-ɓoye ba ne. Yesu yana nan a lokacin da Jehobah “ya yi sammai” kuma ya koyi abubuwa daga wurin shi. (K. Mag. 8:27) Daga baya, Yesu ma ya gaya wa almajiransa abin da ya ‘ji daga wurin’ Ubansa. (Yoh. 15:15) Don haka, zai dace mu ma mu riƙa gaya wa abokan aikinmu abubuwa da muka sani. Abokin aiki nagari ba zai ɓoye wa abokan aikinsa abin da ya sani domin yana so ya riƙa jujjuya su kamar waina ba. Zai yi farin cikin gaya ma wasu abin da ya koya.

Za mu kuma iya ƙarfafa abokan aikinmu. Idan wani ya ga ƙoƙarinmu kuma ya nuna godiya, hakan yana sa mu farin ciki, ko ba haka ba? Yesu ya gaya wa abokan aikinsa halayensu da ke burge shi. (Ka duba misalin da ke Matiyu 25:​19-23; Luka 10:​17-20.) Ya kuma gaya musu cewa za su “yi ayyukan da suka fi” waɗanda da ya yi. (Yoh. 14:12) A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya yaba wa manzanninsa ta wajen cewa: “Ku ne kuka tsaya da aminci tare da ni a duk gwaje-gwajen da na sha.” (Luk. 22:28) Ka yi tunanin yadda kalmominsa suka ratsa zuciyarsu, kuma hakan ya sa suka yi abin da ya gaya musu! Idan mun yaba ma abokan aikinmu, babu shakka hakan zai sa su farin ciki kuma za su ƙara ƙoƙari.

ZA KA IYA ZAMA ABOKIN AIKI NAGARI

Wani ɗan’uwa mai suna Kayode ya ce, “Ba sai mutum ya zama kamili kafin ya iya zama abokin aiki nagari ba. Idan yana sa abokan aikinsa farin ciki kuma yana sa aikinsu ya yi musu sauƙi, shi abokin aiki nagari ne.” Abin da kake yi ke nan? Za ka iya tambayar ’yan’uwan da kake aiki da su su gaya maka ko wane irin abokin aiki ne kai. Idan suna jin daɗin yin aiki tare da kai kamar yadda almajiran Yesu suka ji daɗin aiki da shi, za ka iya faɗan abin da manzo Bulus ya faɗa cewa: “Muna aiki ne tare, domin ku yi farin ciki.”​—2 Kor. 1:24.