Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 51

Ku Ci-gaba da Saurarar Sa

Ku Ci-gaba da Saurarar Sa

“Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”​—MAT. 17:5.

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Mene ne aka umurci manzannin Yesu guda uku su yi, kuma mene ne suka yi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

BAYAN Idin Ƙetarewa na shekara ta 32 bayan haihuwar Yesu, manzo Bitrus da Yakub da Yohanna, sun ga wani wahayi mai ban mamaki. Sa’ad da suke tare da Yesu a kan dutsen Harmon, sai suka ga kamanninsa ya canja. “Fuskarsa ta yi haske kamar rana, sai rigunan da ya sa suka yi fari fat.” (Mat. 17:​1-4) A kusan ƙarshen wahayin, manzannin sun ji Allah ya ce: “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!” (Mat. 17:5) Yadda manzannin suka yi rayuwa bayan hakan ya nuna cewa sun saurari Yesu. Ya kamata mu yi koyi da su.

2 A talifin baya, mun koyi cewa saurarar muryar Yesu, yana nufin daina yin wasu abubuwa. Amma a wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyu da Yesu ya ce mu yi.

“KU SHIGA TA ƘARAMAR ƘOFA”

3. Bisa ga Matiyu 7:​13, 14, mene ne ya kamata mu yi?

3 Karanta Matiyu 7:​13, 14. Ka lura cewa a ayoyin, Yesu ya ambata ƙofofi biyu da suke kai mutane hanyoyi biyu, wato “ƙaramar” hanya da kuma mai “faɗi.” Hanyoyi biyu ne kawai, babu na uku. Mu ne za mu zaɓa wa kanmu hanyar da za mu bi. Wannan ne zaɓi mafi muhimmanci da za mu iya yi, domin hanya ɗaya ce take kai ga samun rai na har abada.

4. Ta yaya za ka bayyana hanya mai ‘faɗin’?

4 Muna bukatar mu riƙa tuna bambancin da ke tsakanin hanyoyi biyun nan. Mutane da yawa ne suke tafiya a hanya mai faɗin, domin tana da sauƙin tafiya a kai. Abin baƙin ciki, mutane da yawa sun zaɓi su bi wannan hanyar, kuma su riƙa yin abin da kowa a hanyar yake yi. Ba su san cewa Shaiɗan ne yake sa mutane su riƙa bin wannan hanyar da ke kai wa ga mutuwa ba.​—1 Kor. 6:​9, 10; 1 Yoh. 5:19.

5. Mene ne wasu suka yi don su nemi “ƙaramar” hanyar kuma su soma bin ta?

5 Amma Yesu ya ce ɗayan hanyar “ƙarama” ce, kuma mutane kaɗan ne suke samun ta. Me ya sa? A aya ta gaba, Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi cewa su guji annabawan ƙarya. (Mat. 7:15) Mutane sun ce akwai dubban addinai, kuma yawancinsu suna da’awar cewa suna koyar da gaskiya. Miliyoyin mutane sun yi sanyin gwiwa ko kuma sun rikice domin akwai addinai da yawa. Shi ya sa ba su damu su nemi hanyar da ke kai wa ga samun rai ba. Amma za su iya samun hanyar. Yesu ya ce: “In dai kun ci gaba da riƙe koyarwata, ku almajiraina ne na gaske. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yoh. 8:​31, 32) Yana da kyau da ba ka yin abin da mutane da yawa suke yi. Amma ka nemi gaskiya, ka soma nazarin Kalmar Allah sosai don ka koyi abubuwan da yake bukata daga gare mu, kuma ka saurari koyarwar Yesu. Wasu daga cikin abubuwan da ka koya su ne cewa Jehobah yana so mu guje wa koyarwar addinan ƙarya, da kuma yin bukukuwan da suka samo tushe daga bautar ƙarya. Ƙari ga haka, ka koyi cewa yin rayuwa yadda Jehobah yake so ba zai kasance maka da sauƙi ba. (Mat. 10:​34-36) Wataƙila bai yi maka sauƙi ka yi canje-canje a salon rayuwarka ba. Amma ka yi iya ƙoƙarinka don kana ƙaunar Ubanka na sama kuma kana so ya amince da kai. Babu shakka kana sa shi farin ciki!​—K. Mag. 27:11.

YADDA ZA MU CI GABA DA TAFIYA A ƘARAMAR HANYAR

Ƙa’idodin Allah da shawarwarinsa suna taimaka mana mu ci gaba da bin “ƙaramar” hanyar (Ka duba sakin layi na 6-8) *

6. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da tafiya a ƙaramar hanyar? (Zabura 119:​9, 10, 45, 133)

6 Idan mun riga mun soma tafiya a kan ƙaramar hanyar, me zai taimaka mana kada mu bar hanyar? Ka yi tunani a kan wannan misalin. A wasu ƙasashe, akan saka abin kāriya a gefen hanyoyin da ke kan tuddai. Abin kāriyar yana taimaka wa motoci kada su faɗi a cikin rami. Babu direban da zai yi gunaguni yana cewa abin kāriyar yana hana shi faɗuwa. Ƙa’idodin Jehobah suna kama da wannan abin kāriyar. Suna taimaka mana mu ci gaba da tafiya a ƙaramar hanyar.​—Karanta Zabura 119:​9, 10, 45, 133.

7. Yaya ya kamata matasa su ɗauki ƙaramar hanyar?

7 Matasa, a wasu lokuta kuna ji kamar ƙa’idodin Jehobah suna hana ku yin abubuwan da kuke so ku yi? Haka Shaiɗan yake so ku ji. Yana so ku mai da hankali ga waɗanda suke tafiya a hanya mai faɗi, domin ku ga kamar suna jin daɗi da gaske. Yana so ku ji kamar ba kwa jin daɗin rayuwa kamar yadda ’yan makarantarku suke yi ko kuma mutane a intane. Yana so ku ga kamar ƙa’idodin Jehobah suna hana ku jin daɗin rayuwa. * Ka tuna cewa Shaiɗan ba ya son waɗanda suke tafiya a hanya mai faɗin su san yadda ƙarshensu zai kasance. Amma Jehobah ya bayyana maka dalla-dalla abin da za ka samu idan ka ci gaba da yin tafiya a hanyar rai.​—Zab. 37:29; Isha. 35:​5, 6; 65:​21-23.

8. Wane darasi ne matasa za su iya koya daga misalin Olaf?

8 Ku yi la’akari da darasin da za ku iya koya daga wani matashi mai suna Olaf. * Abokan ajinsu sun yi ƙoƙari su sa shi ya yi lalata. Da ya bayyana musu cewa yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, sai wasu ’yan mata a ajinsu suka daɗa matsa masa ya yi lalata da su. Amma Olaf ya ƙi. Ba ’yan ajinsu ne kaɗai suka matsa masa ba. Olaf ya ce: “Malamanmu sun matsa mini cewa in je makarantar jami’a, cewa abin da zai sa mutane su daraja ni ke nan. Sun ce idan ban yi hakan ba, ba zan yi nasara a rayuwa ba.” Me ya taimaka wa Olaf ya shawo kan matsi da ya fuskanta? Ya ce: “Na ƙulla abokantaka da ’yan’uwa a ikilisiya. Sun zama kamar iyalina. Ban da haka, na soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Yayin da nake daɗa nazari mai zurfi, sai na ƙara gane cewa abin da nake koya gaskiya ne. A sakamakon haka, na ƙudiri niyyar bauta ma Jehobah.”

9. Mene ne ake bukata daga waɗanda suke so su ci gaba da bin ƙaramar hanyar?

9 Shaiɗan yana so ka daina bin hanyar rai. Yana so ka bi sauran ’yan Adam ka yi tafiya a hanyar “zuwa halaka.” (Mat. 7:13) Amma za mu iya ci gaba da yin tafiya a ƙaramar hanyar idan muka ci gaba da saurarar Yesu, da kuma ɗaukan hanyar a matsayin kāriya. Yanzu bari mu tattauna wani abu kuma da Yesu ya ce mu yi.

KA YI SULHU DA ƊAN’UWANKA

10. Bisa ga Matiyu 5:​23, 24 mene ne Yesu ya ce mu yi?

10 Karanta Matiyu 5:​23, 24. A ayoyin nan, Yesu ya yi magana a kan wani abu da ke da muhimmanci ga Yahudawa da suke saurararsa. A ce wani ya je haikali, kuma yana dab da miƙa wa firist dabba don hadaya. Idan a daidai wannan lokacin mutumin ya tuna cewa akwai wani ɗan’uwansa da yake fushi da shi, zai bar hadayar kuma ya koma. Me ya sa? Domin akwai abin da yake bukatar ya yi da ya fi hadayar muhimmanci. Yesu ya faɗa dalla-dalla cewa: “Ka je ka shirya da ɗan’uwanka.”

Za ka bi misalin Yakubu wanda ya nuna sauƙin kai kuma ya sulhunta da ɗan’uwansa? (Ka duba sakin layi na 11-12) *

11. Ka bayyana abin da Yakubu ya yi don ya sulhunta da Isuwa.

11 Za mu iya koyan yadda za mu yi sulhu da ’yan’uwanmu ta wajen bincika rayuwar Yakubu. Bayan Yakubu ya yi wajen shekara 20 da barin ƙasar da aka haife shi, sai Allah ya gaya masa ta bakin wani mala’ika cewa ya koma ƙasar. (Far. 31:​11, 13, 38) Amma da matsala. Ɗan’uwansa Isuwa ya so ya kashe shi. (Far. 27:41) Yakubu ya “ji tsoro sosai ya kuma damu” cewa wataƙila har yanzu ɗan’uwansa yana fushi da shi. (Far. 32:7) Mene ne Yakubu ya yi don ya sulhunta da ɗan’uwansa? Da farko, ya yi addu’a sosai game da batun. Sai ya tura wa Isuwa kyaututtuka da yawa. (Far. 32:​9-15) A ƙarshe, Yakubu ya daraja ɗan’uwansa sa’ad da ya haɗu da shi. Ya rusuna wa Isuwa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma har sau bakwai! Yakubu ya nuna sauƙin kai kuma ya daraja Isuwa, hakan ya sa suka sulhunta.​—Far. 33:​3, 4.

12. Mene ne za mu iya koya daga misalin Yakubu?

12 Za mu iya koyan darasi daga shirin da Yakubu ya yi kafin ya haɗu da ɗan’uwansa, da kuma abin da ya yi sa’ad da suka haɗu. Yakubu ya yi abin da ya yi addu’a a kai ta wajen ɗaukan matakan da za su taimaka masa ya sulhunta da ɗan’uwansa. Da suka haɗu, Yakubu bai yi gardama da Isuwa a kan wanda yake da laifi ba. Burin Yakubu shi ne ya sulhunta da ɗan’uwansa. Ta yaya za mu iya yin koyi da Yakubu?

YADDA ZA MU SULHUNTA DA MUTANE

13-14. Idan muka ɓata ma wani ɗan’uwanmu rai, mene ne ya kamata mu yi?

13 Idan muna so mu ci gaba da yin tafiya a hanyar rai, muna bukatar mu zauna lafiya da ’yan’uwanmu. (Rom. 12:18) Me ya kamata mu yi idan muka gano cewa mun ɓata ma ɗan’uwanmu rai? Kamar yadda Yakubu ya yi, mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Za mu iya roƙansa ya taimaka mana mu sulhunta da ’yan’uwanmu.

14 Ƙari ga haka, ya kamata mu ɗauki lokaci mu bincika kanmu. Za mu iya yi wa kanmu tambayoyin nan: ‘Ina a shirye in ba da haƙuri don mu sulhunta? Yaya Jehobah da Yesu za su ji idan na ɗau matakin sulhuntawa da ’yan’uwana?’ Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu saurari Yesu ta wajen yin sulhu da ’yan’uwanmu. Ta yin hakan, muna bin misalin Yakubu ne.

15. Ta yaya bin ƙa’idar da ke Afisawa 4:​2, 3, zai taimaka mana mu sulhunta da ’yan’uwanmu?

15 Me zai faru da a ce Yakubu ya nuna girman kai sa’ad da ya haɗu da ɗan’uwansa? Da ba su yi sulhu ba. Idan muka je wurin ɗan’uwanmu domin mu yi sulhu, muna bukatar mu ƙaskantar da kanmu. (Karanta Afisawa 4:​2, 3.) Karin Magana 18:19 ta ce: “Ɗan’uwan da aka yi masa laifi, yana da wuya ya karɓi haƙuri, kamar katangar birni mai wuyan shiga. Gardama tana raba mutane kamar ƙarfen tsare ƙofofin gidan sarki.” Amma idan muka ba wa mutumin haƙuri sosai, zai so ya sulhunta da mu.

16. Me ya kamata mu tuna, kuma me ya sa?

16 Yana da kyau mu yi tunanin abin da za mu faɗa ma ɗan’uwanmu da kuma yadda za mu faɗe shi tun kafin mu isa wurinsa. Idan mun shirya, mu yi masa magana yadda zai sa ya daina fushi kuma ya yi sulhu da mu. Da farko zai iya faɗan abin da zai ɓata mana rai. Hakan zai iya sa mu yin fushi, amma yin fushi zai sa mu sulhunta da shi? A’a. A maimakon ka yi ƙoƙarin nuna cewa ba kai ne da laifi ba, ka tuna cewa sulhuntawa ne ya fi muhimmanci.​—1 Kor. 6:7.

17. Mene ne ka koya daga labarin Gilbert?

17 Wani ɗan’uwa mai suna Gilbert ya yi iya ƙoƙarinsa don ya biɗi zaman lafiya. Ya ce: “Na sami saɓani da ’yata. Na yi fiye da shekaru biyu ina iya ƙoƙarina don mu sulhunta.” Me kuma Gilbert ya yi? Ya ce: “A duk lokacin da zan same ta don mu tattauna, nakan yi addu’a kuma in tuna wa kaina cewa bai kamata in yi fushi a kan duk wata baƙar magana da za ta yi mini ba. Na bukaci in kasance a shirye don in gafarta mata. Na gane cewa bai kamata in yi ƙoƙarin nuna cewa ba ni da laifi ba, amma in yi iya ƙoƙarina in sulhunta da ita.” Wane sakamako ne hakan ya jawo? Gilbert ya ce: “A yau, ina da kwanciyar hankali domin ina da dangantaka mai kyau da kowa a iyalina.”

18-19. Idan muka ɓata ma wani rai, me ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

18 Me ya kamata ka yi idan ka gano cewa ka ɓata ma wani ɗan’uwanka Kirista rai? Ka bi umurnin da Yesu ya bayar kuma ka sulhunta da ɗan’uwanka. Ka yi addu’a game da batun kuma ka roƙe Jehobah ya ba ka ruhunsa mai tsarki don ka iya biɗan zaman lafiya. Idan ka yi hakan, za ka yi farin ciki kuma za ka nuna cewa kana saurarar Yesu.​—Mat. 5:9.

19 Muna godiya don yadda Jehobah yake nuna mana ƙauna ta wajen yin amfani da kan ikilisiya, wato Yesu, don ya yi mana ja-goranci. (Afis. 5:23) Kamar yadda manzo Bitrus, da Yakub da Yohanna suka yi, bari mu ma mu ƙuduri niyyar saurarar Yesu. (Mat. 17:5) Mun riga mun tattauna yadda za mu iya yin hakan, wato ta wurin sulhuntawa da ’yan’uwanmu da muka ɓata musu rai. Idan muka sulhunta da ’yan’uwanmu kuma muka ci gaba da bin ƙaramar hanyar rai, za mu yi farin ciki a yanzu, kuma a nan gaba za mu ji daɗin rayuwa har abada.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Yesu ya umurce mu cewa mu bi ta ƙaramar hanya wadda take kai wa ga samun rai na har abada. Ban da haka, ya umurce mu mu yi zaman lafiya da ’yan’uwanmu. Waɗanne ƙalubale ne za mu iya fuskanta sa’ad da muke ƙoƙarin bin shawarar Yesu, kuma ta yaya za mu shawo kansu?

^ sakin layi na 7 Ka duba tambaya ta 6 a ƙasidar nan Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi,Ta Yaya Zan Ki Matsi Daga Tsarana?” da bidiyon zanen allon nan Ka Jimre da Matsi Daga Tsaranka! a www.pr418.com. (Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA.)

^ sakin layi na 8 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Idan muka ci gaba da bin ‘ƙaramar’ hanya da Allah ya saka abin kāriya a kai, za mu guje wa haɗarurruka kamar batsa, yin tarayya da masu lalata da kuma matsin zuwa makarantar jami’a.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Yakubu ya rusuna a gaban ɗan’uwansa Isuwa sau da yawa.