TALIFIN NAZARI NA 48
“Ku Zama da Tsarki”
“Ku keɓe kanku da tsarki a cikin dukan ayyukanku.”—1 BIT. 1:15.
WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Wace shawara ce manzo Bitrus ya ba wa Kiristoci, kuma me ya sa za mu iya ɗauka kamar hakan ba zai yiwu ba?
KO DA muna da begen yin rayuwa har abada a sama ko a duniya, za mu iya amfana daga shawarar da manzo Bitrus ya ba wa shafaffun Kiristoci a ƙarni na farko. Bitrus ya ce: “Da yake Allah wanda ya kira ku mai tsarki ne, sai ku keɓe kanku da tsarki a cikin dukan ayyukanku. A rubuce yake cewa, ‘Sai ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.’ ” (1 Bit. 1:15, 16) Abin da manzo Bitrus ya faɗa ya nuna mana cewa za mu iya yin koyi da Jehobah wanda shi ne ya fi kowa tsarki. Dole ne mu kasance da tsarki a halayenmu kuma za mu iya yin hakan. Za mu iya ɗauka cewa hakan ba zai yiwu ba domin mu ajizai ne. Bitrus da kansa ya yi kurakurai da yawa, amma misalinsa ya nuna mana cewa za mu iya “zama da tsarki.”
2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifin nan?
2 A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyin nan: Mene ne kasancewa da tsarki yake nufi? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yadda Jehobah yake da tsarki? Ta yaya za mu zama da tsarki a halinmu? Kuma wace alaƙa ce ke tsakanin zama da tsarki da kuma dangantakarmu da Jehobah?
MENE NE ZAMA DA TSARKI YAKE NUFI?
3. A wasu wurare, yaya mutane da yawa suka fahimci kalmar nan tsarki, amma a ina ne za mu iya samun bayani na gaskiya?
3 A wasu wurare, idan aka yi maganar mutum mai tsarki, mutane sukan yi tunanin mutumin da ba ya murmushi, ba ya wasa kuma yake saka rigar limaman addinai a kullum. Amma hakan ba gaskiya ba ne. An kwatanta Jehobah a matsayin “Allah mai farin ciki.” (1 Tim. 1:11, New World Translation) An kwatanta waɗanda suke bauta masa a matsayin “masu albarka” ko kuma farin ciki. (Zab. 144:15) Yesu ya yi tir da mutanen da suke saka riguna na musamman kuma suke yin alheri domin mutane su gan su. (Mat. 6:1; Mar. 12:38) A matsayinmu na Kiristoci, mun san abin da zama da tsarki yake nufi domin abin da muka koya game da Jehobah. Mun san cewa Allah yana ƙaunar mu kuma ba zai ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. Shi ya sa muka gaskata cewa za mu iya bin umurnin da Jehobah ya ba mu cewa: ‘Sai ku zama da tsarki.’ Hakika, kafin mu zama masu tsarki, wajibi ne mu san abin da hakan yake nufi.
4. Mene ne kalmar nan “tsarki” take nufi?
4 Me ake nufi da tsarki? A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “tsarki” tana nufin tsabta ta ibada da ta ɗabi’a. Ban da haka, kalmar tana iya nufin keɓe wani abu ko mutum don bautar Allah. Za mu iya cewa mu masu tsarki ne idan muna da ɗabi’u masu kyau, muna bauta wa Jehobah a hanyar da yake so kuma muna da dangantaka mai kyau da shi. Abin mamaki ne cewa Jehobah yana so mu ajizai mu zama aminansa, duk da cewa shi mai tsarki ne ciki da waje.
“MAI TSARKI, MAI TSARKI, MAI TSARKI” NE JEHOBAH
5. Mene ne za mu iya koya game da Jehobah daga mala’iku masu aminci?
5 Jehobah mai tsarki ne ta kowace hanya. Mun san hakan ne daga abin da mala’iku da ke kusa da kursiyinsa suka faɗa. Wasun su sun ce: “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki [ne] Yahweh Mai Runduna!” (Isha. 6:3) Kafin mala’ikun nan su ƙulla dangantaka mai kyau da Allahnsu mai tsarki, dole ne su ma su zama da tsarki. Da yake mala’iku suna da tsarki, wasu wuraren da suka taka a duniya sukan zama da tsarki. Abin da ya faru a lokacin da Musa ya ga wani ƙaramin itace yana ci da wuta ke nan.—Fit. 3:2-5; Yosh. 5:15.
6-7. (a) Kamar yadda Fitowa 15:1, 11 suka nuna, ta yaya Musa ya nuna cewa Allah mai tsarki ne? (b) Mene ne yake tuna wa Isra’ilawa cewa Allah mai tsarki ne? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
6 Bayan da Musa ya ja-goranci Isra’ilawa su ƙetare Jar Teku, ya nanata musu cewa Jehobah Allah ne mai tsarki. (Karanta Fitowa 15:1, 11.) Hakika Masarawa da suke bauta wa gumaka ba mutane masu tsarki ba ne. Haka ma Kan’aniyawa da suke bauta wa gumaka. Bautar Kan’aniyawa ta ƙunshi yin hadaya da yara da kuma lalata. (L. Fir. 18:3, 4, 21-24; M. Sha. 18:9, 10) Amma Jehobah ba zai taɓa gaya wa bayinsa su yi abin da zai ƙazantar da su ba. Shi mai tsarki ne ciki da waje. Abin da aka rubuta a ƙaramin allo na zinariya da babban firist yake sakawa a rawaninsa ya nuna hakan. Rubutun ya ce: “An keɓe da tsarki ga Yahweh.”—Fit. 28:36-38.
7 Abin da aka rubuta a kan allon zai nuna wa duk wanda ya gani cewa da gaske Jehobah mai tsarki ne. Amma mene ne zai faru idan Ba’isra’ile ya kasa ganin rubutun domin bai iya ya je kusa da babban firist ba? Zai san cewa Jehobah mai tsarki ne? Ƙwarai kuwa! Kowane Ba’isra’ile yakan ji saƙon nan sa’ad da ake karanta Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa a gaban maza da mata da kuma yara. (M. Sha. 31:9-12) Da a ce kana wurin, da ka ji wannan furucin cewa: “Ni ne Yahweh . . . Allahnku. Sai ku zama masu tsarki, gama ni mai tsarki ne.” “Ku keɓe kanku da tsarki, ku zama masu tsarki, gama ni ne Yahweh Allahnku.”—L. Fir. 11:44, 45; 20:7, 26.
8. Mene ne muka koya daga Littafin Firistoci 19:2 da 1 Bitrus 1:14-16?
Littafin Firistoci 19:2. Jehobah ya gaya wa Musa cewa: “Faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila waɗannan ƙa’idodi. ‘Ku zama masu tsarki, gama ni Yahweh Allahnku ni mai tsarki ne.’ ” Wataƙila manzo Bitrus ya yi ƙaulin wannan ayar ne a lokacin da ya ƙarfafa Kiristoci su “zama da tsarki.” (Karanta 1 Bitrus 1:14-16.) Hakika a yau, ba ma bin Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa. Duk da haka, abin da Bitrus ya rubuta ya tabbatar da abin da ke Littafin Firistoci 19:2, cewa Jehobah mai tsarki ne kuma dole ne dukan masu ƙaunar sa su zama da tsarki, ko da suna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya.—1 Bit. 1:4; 2 Bit. 3:13.
8 Bari mu ga abin da Jehobah ya ce a riƙa karanta wa Isra’ilawa a“KU KEƁE KANKU DA TSARKI A CIKIN DUKAN AYYUKANKU”
9. Ta yaya za mu amfana daga yin nazarin Littafin Firistoci sura 19?
9 Da yake muna so mu faranta ran Allahnmu mai tsarki, muna yin iya ƙoƙarinmu mu san yadda za mu zama masu tsarki. Jehobah ya ba mu shawara a kan yadda za mu zama masu tsarki. Za mu iya samun shawarwarin a Littafin Firistoci sura 19. Wani masani Bayahude mai suna Marcus Kalisch ya rubuta cewa: “Wannan ita ce sura mafi muhimmanci a Littafin Firistoci, da kuma littattafai biyar na farko a Littafi Mai Tsarki.” Ka tuna cewa Littafin Firistoci sura 19 ta soma da furucin nan “Ku zama masu tsarki.” Yanzu za mu tattauna wasu ayoyi da za su nuna mana yadda za mu iya zama masu tsarki a kullum.
10-11. Mene ne Littafin Firistoci 19:3 ta ce mu yi, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
10 Bayan Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa su zama masu tsarki, sai ya daɗa cewa: ‘Kowannenku ya girmama mamarsa da babansa . . . ni ne Yahweh Allahnku.’—L. Fir. 19:2, 3.
11 Hakika, muna bukatar mu bi umurnin da Allah ya bayar cewa mu daraja iyayenmu. Ku tuna abin da Yesu ya faɗa sa’ad da wani mutum ya tambaye shi Mat. 19:16-19) Yesu ya yi Allah wadai da Farisawa da marubuta domin suna yin iya ƙoƙarinsu don su guji kula da iyayensu. Ta yin hakan sun “mai da maganar Allah banza.” (Mat. 15:3-6) “Maganar Allah” ta haɗa da doka ta biyar cikin Dokoki Goma da ke Littafin Firistoci 19:3. (Fit. 20:12) Ka lura cewa an ba da umurnin da ke Littafin Firistoci 19:3 cewa mutum ya daraja mamarsa da babansa, bayan da aka ce “Ku zama masu tsarki, gama ni Yahweh Allahnku ni mai tsarki ne.”
cewa: “Wane abu mai kyau ne zan yi domin in sami rai na har abada?” Ɗaya daga cikin abubuwan da Yesu ya ce ya yi shi ne ya daraja iyayensa. (12. Bisa ga ƙa’idar da ke Littafin Firistoci 19:3, waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu?
12 Idan muka yi tunanin umurnin da Jehobah ya ba mu game da daraja iyayenmu, muna iya tambayar kanmu, ‘Ina daraja iyayena kuwa?’ Idan ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara, sai ka yi hakan yanzu. Ba za ka iya canja abin da ya faru a baya ba, amma za ka iya yin iya ƙoƙarinka yanzu don ka riƙa taimaka wa iyayenka. Za ka iya ɗaukan lokaci don ka kasance tare da su, ko ka taimaka musu su sayi abin da suke bukata, ko kuma su ci gaba da bauta ma Jehobah. Ƙari ga haka, za ka iya ƙarfafa su. Yin hakan ya jitu da abin da ke Littafin Firistoci 19:3.
13. (a) Wane umurni ne kuma yake Littafin Firistoci 19:3? (b) Ta yaya za mu iya bin misalin Yesu da ke Luka 4:16-18 a yau?
13 Littafin Firistoci 19:3 ta koya mana wani abu kuma game da yadda za mu zama da tsarki. Ayar ta ambaci kiyaye ranar hutu ko kuma Assabaci. Da yake ba ma bin Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, ba ma kiyaye Assabaci. Duk da haka, za mu iya koyan darussa daga yadda Isra’ilawa suka kiyaye Assabaci da kuma yadda suka amfana. A ranar Assabaci, Isra’ilawa sukan huta daga ayyukan da suke yi kuma su mai da hankali ga bauta wa Allah. * Shi ya sa a ranar Assabaci Yesu yakan je majami’ar da ke garinsu don ya karanta Kalmar Allah. (Fit. 31:12-15; karanta Luka 4:16-18.) Ya kamata umurnin da Allah ya ba wa Isra’ilawa a Littafin Firistoci 19:3 cewa su kiyaye “Ranar Hutu ta Mako,” ya motsa mu mu riƙa keɓe lokaci a kullum don ayyukan ibada. Shin kana bukatar ka yi wasu canje-canje don ka iya bin wannan umurnin? Idan kana keɓe lokaci a kai a kai don ayyukan ibada, za ka daɗa kusantar Jehobah, kuma hakan zai taimaka maka ka zama mai tsarki.
KA ƘARFAFA DANGANTAKARKA DA JEHOBAH
14. Wane muhimmin batu ne aka nanata a Littafin Firistoci sura 19?
14 Sau da yawa Littafin Firistoci sura 19 ta faɗi muhimmin abin da zai taimaka mana mu zama masu tsarki. An kammala aya 4 da furucin nan, “Ni ne Yahweh Allahnku.” Wannan furucin ko kuma makamancinsa ya bayyana sau 16 a surar. Hakan ya tuna mana doka ta farko cewa: “Ni ne Yahweh Allahnku. . . . Ba za ka yi sujada ga waɗansu alloli ba sai ni kaɗai.” (Fit. 20:2, 3) Kowane Kirista da yake so ya nuna cewa shi mai tsarki ne, dole ne ya tabbata cewa ba abin da zai shiga tsakaninsa da Jehobah. Kuma da yake ana kiran mu Shaidun Jehobah, muna bukatar mu guji duk abin da zai ɓata sunan Allah mai tsarki.—L. Fir. 19:12; Isha. 57:15.
15. Mene ne ayoyin da suka yi magana game da hadayu a Littafin Firistoci sura 19 za su sa mu yi?
15 Isra’ilawa za su nuna cewa sun amince da Jehobah a matsayin Allahnsu ta wajen bin umurninsa. Littafin Firistoci 18:4, ta ce: “Za ku yi biyayya da umarnaina, ku kiyaye ƙa’idodina, ku kuma yi tafiya a cikinsu. Ni ne Yahweh Allahnku.” Wasu ‘ƙa’idodin’ da Jehobah ya ba wa Isra’ilawa suna sura ta 19. Alal misali, ayoyi 5-8, 21, 22 sun yi magana game da yin hadayu da dabbobi. Isra’ilawan za su yi hadayun a hanyar da ba za ta mai “da hadaya mai tsarki ta Yahweh” ta zama banza ba. Karanta ayoyin za su sa mu yi iya ƙoƙarinmu don mu faranta wa Jehobah rai kuma mu miƙa masa hadaya ta yabo kamar yadda littafin Ibraniyawa 13:15 ta ƙarfafa mu mu yi.
16. Wace ƙa’ida ce za ta tuna mana bambancin da ke tsakanin waɗanda suke bauta wa Jehobah da waɗanda ba sa bauta masa?
16 Kafin mu zama masu tsarki, dole ne mu bambanta da sauran mutane. Yin hakan zai iya yi mana wuya. A wasu lokuta, ’yan makarantarmu ko abokan aikinmu ko kuma danginmu za su iya matsa mana mu yi abin da Jehobah ya haramta. Idan hakan ya faru, za mu bukaci mu yanke shawarar da ta dace. Me zai taimaka mana mu yi hakan? Ka yi la’akari da ƙa’idar da ke Littafin Firistoci 19:19 da ta ce: “Ba za ka sa rigar da an ɗinka da yadi wanda an haɗa zare iri biyu a kan juna ba.” Dokar ta bambanta Isra’ilawa da mutanen ƙasashen da ke kewaye da su. Da yake ba ma bin Dokar, za mu iya saka rigar da aka ɗinka da zare iri biyu. Amma muna guje wa bin ra’ayin ’yan makarantarmu da abokan aikinmu da kuma danginmu da ba sa bauta wa Jehobah. Muna ƙaunar danginmu da kuma maƙwabtanmu. Amma shawarwarin da muke yankewa suna nuna cewa za mu yi biyayya ga Jehobah ko da hakan zai sa mu yi dabam da sauran mutane. Hakan yana da muhimmanci, domin idan muna so mu zama masu tsarki, wajibi ne mu keɓe kanmu domin yin nufin Allah.—2 Kor. 6:14-16; 1 Bit. 4:3, 4.
17-18. Wane darasi ne za mu iya koya daga Littafin Firistoci 19:23-25?
17 Ya kamata furucin nan “Ni ne Yahweh Allahnku” ya sa Isra’ilawa su sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu. Ta yaya za su yi hakan? Littafin Firistoci 19:23-25 sun nuna wata hanya da za su yi hakan. (Karanta.) Ka yi la’akari da abin da wannan furucin yake nufi ga Isra’ilawa bayan sun shiga ƙasar alkawari. Idan mutum ya dasa itace, bai kamata ya ci ’ya’yan itacen ba har sai bayan shekaru uku. A shekara ta huɗu, zai kai ’ya’yan itatuwan mazauni don ya ba da su kyauta. Sai a shekara ta biyar ne mai gonar zai iya cin ’ya’yan itatuwan. Ya kamata wannan doka ta taimaka wa Isra’ilawa su gane cewa ba bukatunsu ne za su sa a kan gaba ba. Jehobah yana so su san cewa zai kula da su kuma yana so su sa bautarsa farko a rayuwarsu. Kuma Allah ya ƙarfafa su su riƙa ba da kyauta hannu sake a wurin da suke bauta masa.
18 Dokar da ke Littafin Firistoci 19:23-25 ta tuna mana abin da Yesu ya faɗa a huɗubarsa a kan dutse. Ya ce: “Kada ku damu . . . game da abin da za ku ci ko abin da za ku sha.” Sai ya daɗa cewa: “Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatar duk waɗannan abubuwan.” Allah zai yi mana tanadi kamar yadda yake yi wa tsuntsaye. (Mat. 6:25, 26, 32) Mun ba da gaskiya cewa Jehobah zai kula da mu. Shi ya sa muke ba da kyauta ga mabukata ba tare da nuna wa mutane ba. Ban da haka, muna ba da gudummawa don ayyukan ikilisiya. Jehobah yana ganin yadda muke ba da kyauta kuma zai sāka mana da alheri. (Mat. 6:2-4) Idan muka yi haka, za mu nuna cewa mun fahimci abin da ke Littafin Firistoci 19:23-25.
19. Ta yaya ka amfana daga yin nazarin wannan surar a Littafin Firistoci?
19 A wannan talifin, mun tattauna wasu ayoyi daga Littafin Firistoci sura 19 kuma mun ga wasu hanyoyi da za mu iya zama masu tsarki kamar Allahnmu. Idan muka yi ƙoƙari mu bi misalinsa, za mu nuna cewa muna so mu zama masu ‘tsarki a cikin dukan ayyukanmu.’ (1 Bit. 1:15) Mutane da yawa da ba sa bauta wa Jehobah suna ganin halayenmu masu kyau. Hakan ya ma sa wasu su ɗaukaka Jehobah. (1 Bit. 2:12) Amma da sauran darussa da za mu iya koya daga Littafin Firistoci sura 19. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu ayoyi daga surar da za su taimaka mana mu ga hanyoyi da ya kamata mu zama da tsarki kamar yadda manzo Bitrus ya ƙarfafa mu mu yi.
WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’
^ sakin layi na 5 Muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu faranta masa rai. Jehobah mai tsarki ne, kuma yana so bayinsa ma su kasance da tsarki. Shin hakan zai yiwu? Ƙwarai kuwa! Tattauna shawarar da manzo Bitrus ya ba wa Kiristoci da kuma umurnin da Jehobah ya ba wa Isra’ilawa a zamanin dā zai taimaka mana mu san yadda za mu zama masu tsarki.
^ sakin layi na 13 Don samun ƙarin bayani game da ranar Assabaci da kuma darussan da za mu iya koya, ka duba talifin nan “‘Akwai Lokacin’ Yin Aiki da Kuma Hutu,” a Hasumiyar Tsaro ta Disamba 2019.
^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wani mutum ya kai matarsa da ’yarsa su je su gai da iyayensa kuma yana ƙoƙari ya riƙa kiran iyayensa a kowane lokaci.
^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Wani Ba’isra’ile yana duba ’ya’yan itacen da ya shuka.