Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 49

Littafin Firistoci Ya Nuna Mana Yadda Za Mu Bi da Mutane

Littafin Firistoci Ya Nuna Mana Yadda Za Mu Bi da Mutane

“Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”​—L. FIR. 19:18.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me muka tattauna a talifi na baya kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

A TALIFI na baya, mun tattauna shawarar da ke Littafin Firistoci sura 19. Alal misali, kamar yadda aka rubuta a aya 3, Jehobah ya umurci Isra’ilawa su girmama iyayensu. Mun tattauna yadda za mu iya bin wannan shawarar a yau ta wajen taimaka wa iyayenmu idan suna da bukata, da ƙarfafa su da kuma taimaka musu su ci gaba da bauta wa Jehobah. Har ila a ayar, an tuna wa mutanen Allah muhimmancin kiyaye ranar Assabaci. Mun koyi cewa ko da yake ba ma bin dokar Assabaci, za mu iya bin ƙa’idar da ta sa aka ba da dokar ta wajen keɓe lokaci don yin ayyukan ibada kowace rana. Idan muna yin hakan, za mu nuna cewa muna ƙoƙari mu zama masu tsarki kamar yadda Littafin Firistoci 19:2 da kuma 1 Bitrus 1:15 suka ce mu yi.

2 A wannan talifin, za mu ci gaba da tattauna wasu ayoyi daga Littafin Firistoci sura 19. Mene ne surar za ta koya mana game da nuna alheri ga naƙasassu, da yin gaskiya a kasuwanci da kuma nuna ƙauna ga mutane? Ya kamata mu zama masu tsarki domin Allah yana da tsarki. Don haka, bari mu ga abin da za mu koya.

YADDA ZA MU NUNA ALHERI GA NAƘASASSU

Yaya Littafin Firistoci 19:14 ta ce mu bi da makafi da kurame? (Ka duba sakin layi na 3-5) *

3-4. Bisa ga Littafin Firistoci 19:​14, yaya ya kamata Isra’ilawa su bi da makafi da kurame?

3 Karanta Littafin Firistoci 19:14. Jehobah ya gaya wa mutanensa su nuna alheri ga naƙasassu. Alal misali, ya hana su zagin kurame. Wannan zagin ya ƙunshi yi wa mutum barazana ko faɗan mummunar abu game da shi. Hakan mugun abu ne. Kurma ba zai iya jin abin da aka faɗa game da shi ba, don haka, ba zai iya kāre kansa ba.

4 Ƙari ga haka, a aya ta 14, mun koyi cewa bai kamata bayin Allah su “sa wa makaho abin da zai yi tuntuɓe a kai ya faɗi ba.” Wani littafi da yake magana game da naƙasassu ya ce: “A zamanin dā a yankin Gabas ta Tsakiya, ana wulaƙanta naƙasassu sosai.” Mai mugunta zai iya saka abu a gaban makaho don ya faɗi a kai ya ji rauni, ko domin yana so ya yi wa makahon dariya. Wannan mugunta ce sosai! Ta wannan dokar, Jehobah ya nuna cewa yana so mutanensa su nuna alheri ga naƙasassu.

5. Ta yaya za mu nuna tausayi ga naƙasassu?

5 Yesu ya tausaya wa naƙasassu. Ka tuna saƙon da ya tura wa Yohanna Mai Baftisma, ya ce: “Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, masu cutar fatar jiki suna samun warkewa, kurame suna jin magana, ana tā da waɗanda suka mutu.” Bayan da mutane suka ga mu’ujizai da Yesu ya yi, “sai duka suka yabi Allah.” (Luk. 7:​20-22; 18:43) Kiristoci suna bin misalin Yesu na tausaya wa naƙasassu. Don haka, suna nuna alheri ga naƙasassu kuma suna haƙuri da su. Hakika, Jehobah bai ba mu ikon yin mu’ujizai kamar yadda Yesu ya yi ba. Amma muna da gatan gaya wa naƙasassu da waɗanda ba su san Allah ba albishiri game da aljanna, inda kowa zai zama kamiltacce kuma ya kasance da dangantaka mai kyau da Allah. (Luk. 4:18) Wannan labari mai daɗi yana taimaka wa mutane su yabi Allah.

KA YI GASKIYA A KASUWANCI

6. Ta yaya Littafin Firistoci sura 19 ta taimaka mana mu ƙara fahimtar Dokoki Goma?

6 Wasu ayoyi a Littafin Firistoci sura 19 sun ba da ƙarin bayani a kan abin da aka faɗa a cikin Dokoki Goma. Alal misali, Doka ta 8 ta ce: “Ba za ka yi sata ba.” (Fit. 20:15) Mutum zai iya cewa idan bai ɗauki kayan wani ba, yana bin dokar ke nan. Duk da haka, zai iya yin sata a wasu hanyoyi dabam.

7. A wace hanya ce ɗan kasuwa zai iya taka doka ta takwas game da sata?

7 Ɗan kasuwa zai iya ɗauka cewa bai yi sata ba da yake bai ɗauki kayan wani ba. Amma yana yin kasuwanci tsakaninsa da Allah? A Littafin Firistoci 19:​35, 36, Jehobah ya ce: “Ba za ku yi rashin gaskiya wajen yin amfani da ma’auni na ƙarya ba, ko awon tsawo, ko na nauyi, ko na yawan wani abu. Sai ma’auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon yawan wani abu su zama na gaskiya.” Don haka, idan ɗan kasuwa yana amfani da mudun awon da ba daidai ba don ya cuci kwastomominsa yana musu sata ke nan. Wasu ayoyi a Littafin Firistoci 19 sun daɗa bayyana hakan.

Bisa ga Littafin Firistoci 19:​11-13, waɗanne tambayoyi ne ya kamata Kirista ya yi wa kansa game da kasuwanci? (Ka duba sakin layi na 8-10) *

8. Ta yaya Littafin Firistoci 19:​11-13 suka taimaka wa Yahudawa su bi ƙa’idar da ke doka ta takwas, kuma ta yaya za su taimaka mana?

8 Karanta Littafin Firistoci 19:​11-13. A farkon Littafin Firistoci 19:​11, an ce: “Ba za ku yi sata ba.” A aya ta 13 kuma, an nuna cewa akwai alaƙa tsakanin sata da rashin gaskiya a kasuwanci. Wurin ya ce: “Ba za ku cuci wani ba.” Don haka, yin cuci a kasuwanci ɗaya ne da yin sata. Doka ta takwas ta ce yin sata zunubi ne. Bayanin da ke Littafin Firistoci ya taimaka wa Yahudawa su ga yadda za su bi ƙa’idar da ya sa aka ba da dokar, wato, Jehobah yana so su yi gaskiya a kome da suke yi. Yana da kyau mu yi tunanin ra’ayin Jehobah game da yin rashin gaskiya da kuma sata. Za mu iya tambayar kanmu: ‘Bisa ga abin da ke Littafin Firistoci 19:​11-13, shin akwai abubuwa da ya kamata in canja a rayuwata, musamman yadda nake kasuwanci ko aiki?’

9. Ta yaya dokar da ke Littafin Firistoci 19:13 take kāre ma’aikata?

9 Akwai wata ƙa’ida kuma da Kiristan da yake da ma’aikata ya kamata ya bi. Littafin Firistoci 19:13 ya kammala da cewa: “Ba za ku bar lokacin biyan ladan aikin ma’aikaci ya kai sai gobe ba.” A Isra’ila, yawancin mutane suna aiki a gonaki ne kuma ana biyan su a ƙarshen kowace rana. Idan ba a biya ma’aikaci bayan ya gama aiki a rana ba, ba zai iya ciyar da iyalinsa a ranar ba. Jehobah ya bayyana cewa: “[Mutumin] matalauci ne, kuma ransa ya dogara a kan wannan ladan aikin ne.”​—M. Sha. 24:​14, 15; Mat. 20:8.

10. Wane darasi ne za mu iya koya daga Littafin Firistoci 19:13?

10 A yau, ana biyan ma’aikata da yawa sau ɗaya ko sau biyu a wata, ba kullum ba ne ake biyan su. Amma ƙa’idar da ke Littafin Firistoci 19:13 tana da amfani har wa yau. Wasu da suke ɗaukan mutane su yi musu aiki sukan yi musu rashin adalci ta wajen biyan su abin da bai kai kome ba. Sun san cewa ma’aikatan nan suna cikin yanayi mai wuya kuma suna ci gaba da yin aikin ne domin ba su da na yi. Za mu iya cewa irin mutanen nan suna ƙin biyan ladan ma’aikata. Ya kamata Kiristan da ya ɗauki mutane su yi masa aiki ya biya su abin da ya dace da aikin da suka yi. Yanzu bari mu ga wasu abubuwa dabam da za mu iya koya daga sura ta 19.

KA ƘAUNACI MUTANE KAMAR YADDA KAKE ƘAUNAR KANKA

11-12. Mene ne Yesu ya nanata sa’ad da ya yi ƙaulin Littafin Firistoci 19:​17, 18?

11 Bayan Allah ya ce kada mu cuci mutane, akwai wani abu kuma da ya ce ya kamata mu yi. Mun ga tabbacin hakan a Littafin Firistoci 19:​17, 18. (Karanta.) A wurin, Jehobah ya bayyana dalla-dalla cewa: “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” Wajibi ne Kirista ya bi wannan ƙa’idar idan yana so ya faranta ran Allah.

12 Yesu ya nuna cewa dokar da ke Littafin Firistoci 19:18 tana da muhimmanci sosai. Akwai lokacin da wani Bafarisi ya tambayi Yesu ya ce: “Wace doka ce ta fi girma a cikin dokoki?” Yesu ya amsa ya ce “doka ta farko, kuma mafi girma” ita ce ka ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka. Sai Yesu ya yi ƙaulin Littafin Firistoci 19:18 inda ya ce: “Ta biyun ma kamar ta farkon take, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.’ ” (Mat. 22:​35-40) Akwai hanyoyi da yawa na nuna ƙauna ga mutane. Za mu iya koyan wasu hanyoyin nan a Littafin Firistoci sura ta 19.

13. Ta yaya labarin Yusufu ya bayyana abin da ke Littafin Firistoci 19:18?

13 Wata hanya da za mu iya nuna wa mutane ƙauna ita ce ta wurin bin shawarar da ke Littafin Firistoci 19:18. Wurin ya ce: “Ba za ka nemi hanyar ramuwa ko ka riƙe wani a zuciya ba.” Yawancinmu mun san mutanen da suka yi shekaru suna riƙe wani abokin aikinsu ko abokin makarantarsu ko kuma wani memban iyalinsu a zuciya. Ka tuna cewa ’yan’uwan Yusufu sun riƙe shi a zuciya kuma hakan ya sa sun yi masa mugunta. (Far. 37:​2-8, 25-28) Amma Yusufu bai yi musu mugunta ba! A lokacin da ya sami damar ramuwa, bai yi hakan ba, maimakon haka ya nuna musu jinƙai. Ƙari ga haka, Yusufu bai riƙe su a zuciya ba, amma ya bi abin da Littafin Firistoci 19:18 ta ce mu yi.​—Far. 50:​19-21.

14. Me ya nuna cewa ya kamata mu bi ƙa’idodin da ke Littafin Firistoci 19:18 a yau?

14 Kiristoci da suke so su faranta wa Allah rai za su bi misalin Yusufu wanda ya gafarta wa ’yan’uwansa maimakon ya yi ramako. Abin da Yesu ma ya faɗa ke nan a cikin addu’ar misali, inda ya ce mu gafarta ma waɗanda suka yi mana laifi. (Mat. 6:​9, 12) Manzo Bulus ma ya ba Kiristoci shawara cewa: “Kada ku zama masu ramuwa, ’yan’uwana.” (Rom. 12:19) Ƙari ga haka, ya ce musu: “Kuna ta yin haƙuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku zunubanku, haka ma ku ma ku gafarta wa juna.” (Kol. 3:13) Ƙa’idodin Jehobah ba sa canjawa. Saboda haka, ya kamata mu ci gaba da bin ƙa’idodin da ke Littafin Firistoci 19:18.

Kamar yadda bai da kyau mutum ya yi ta tattaɓa rauni, haka ma bai da kyau mu yi ta tunanin laifin da aka yi mana. Ya kamata mu manta da laifin (Ka duba sakin layi na 15) *

15. Wane kwatanci ne ya nuna abin da ya sa ya kamata mu mance da laifin da aka yi mana kuma mu gafarta?

15 Ga wani misali: Za mu iya kwatanta fushi da jin rauni. Wasu rauni ba su da girma; wasu kuma suna da girma. Alal misali, a ce kana yanka ganyen miya, sai ka ɗan yanka hannunka. Hakan zai iya maka zafi sosai, amma ba da daɗewa ba za ka daina jin zafin. Bayan kwana ɗaya ko biyu, za ka iya mantawa gaba ɗaya cewa ka ji rauni. Haka ma, wasu laifin da aka yi mana ba su da girma. Alal misali, wani abokinmu zai iya faɗa ko kuma yi abin da zai ɓata mana rai, duk da haka, za mu iya gafarta masa. Amma idan yankan ya shiga sosai, za mu bukaci likita ya ɗinka raunin. Idan mun yi ta tattaɓa raunin, zai yi wuya ya warke, kuma zai ƙara yin tsanani. Abin baƙin ciki shi ne, mutum zai iya yin abu makamancin tattaɓa rauni idan aka ɓata masa rai sosai. Zai yi ta yin tunanin abin da aka yi masa. Amma waɗanda suke riƙe mutane a zuciya suna wahalar da kansu ne kawai. Zai fi ma wanda aka ɓata wa rai ya bi shawarar da ke Littafin Firistoci 19:18.

16. Bisa ga abin da ke Littafin Firistoci 19:​33, 34, yaya ya kamata Isra’ilawa su kula da baƙi, kuma mene ne za mu iya koya daga hakan?

16 Umurnin da Jehobah ya ba wa Isra’ilawa cewa su ƙaunaci mutane, ba ya nufin cewa su ƙaunaci Isra’ilawa ’yan’uwansu ne kaɗai. Ya ce su ƙaunaci baƙin da suke zama tsakanin su. An bayyana hakan da kyau a Littafin Firistoci 19:​33, 34. (Karanta.) Ya kamata Isra’ilawa su ɗauki baƙo ‘kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansu’ kuma su “ƙaunace shi” kamar yadda suke ƙaunar kansu. Alal misali, ya kamata a bar talakawa da ke tsakanin Isra’ilawan, har da baƙi, su yi kāla. (L. Fir. 19:​9, 10) Ƙa’idar da aka bayar game da ƙaunar baƙi abu ne da ya kamata Kiristoci a yau su bi. (Luk. 10:​30-37) Ta yaya za ka bi ƙa’idar? Akwai miliyoyin baƙi a ƙasashe dabam-dabam a yau kuma wataƙila wasu suna zama kusa da kai. Yana da kyau mu daraja waɗannan maza da mata da yara da suka zama baƙi a ƙasarmu.

AIKI MAI MUHIMMANCI DA BA A AMBATA A LITTAFIN FIRISTOCI 19 BA

17-18. (a) Mene ne Littafin Firistoci 19:2 da 1 Bitrus 1:15 suka ƙarfafa mu mu yi? (b) Wane aiki mai muhimmanci ne manzo Bitrus ya ƙarfafa mu mu yi?

17 A littafin 1 Bitrus 1:15 da kuma Littafin Firistoci 19:​2, an umurci mutanen Allah su zama masu tsarki. Ayoyi da yawa a cikin Littafin Firistoci 19 za su iya taimaka mana mu ga abin da ya kamata mu yi idan muna so mu sami amincewar Jehobah. Mun tattauna wasu ayoyi da suka nuna mana abubuwan da ya kamata mu yi da waɗanda bai kamata mu yi ba. * Nassosin Helenanci sun nuna cewa Jehobah yana so mu ci gaba da bin ƙa’idodin nan har wa yau. Amma da wani abu kuma da manzo Bitrus ya faɗa.

18 Za mu iya bauta wa Jehobah kuma mu yi abubuwa masu kyau wa mutane. Amma akwai wani aiki mai muhimmanci kuma da Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci su yi. Kafin ya gaya mana mu zama masu tsarki a dukan halinmu, ga abin da ya faɗa, ya ce: “Ku shirya tunaninku domin aiki.” (1 Bit. 1:​13, 15) Mene ne hakan ya ƙunsa? Bitrus ya ce shafaffun Kiristoci za su ‘yi shelar manyan al’amura na ban mamaki na wanda ya kira’ su. (1 Bit. 2:9) Wannan aiki mai muhimmanci yana taimaka wa mutane fiye da duk wani aikin da muke yi. Babban gata ne mutanen Allah masu tsarki suka samu na yin wa’azi da ƙwazo da kuma koyar da mutane a kullum! (Mar. 13:10) Idan muna yin iya ƙoƙarin mu mu bi ƙa’idar da ke Littafin Firistoci sura 19, za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma mutane. Kuma za mu nuna cewa mun ‘keɓe kanmu da tsarki a cikin dukan ayyukanmu.’

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

^ sakin layi na 5 Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, amma dokar ta nuna abubuwan da ya kamata mu yi da waɗanda bai kamata mu yi ba. Koyan abubuwan nan zai taimake mu mu san yadda za mu ƙaunaci mutane kuma mu faranta ran Allah. A talifin nan, za mu tattauna yadda za mu amfana daga wasu darussa a Littafin Firistoci sura 19.

^ sakin layi na 17 A wannan talifin da kuma na baya, ba mu tattauna ayoyin da suka yi magana game da son kai, da tsegumi, da cin jini, da yin sihiri, da yin dūba, da kuma lalata ba.​—L. Fir. 19:​15, 16, 26-29, 31.​—Ka duba “Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaron nan.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTO: Wani Mashaidi yana taimaka ma wani ɗan’uwa kurma ya yi magana da likitansa.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa da yake da kamfanin yin fenti yana ba wa ma’aikacinsa albashi.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa za ta iya mancewa da ƙaramin rauni da ta ji. Amma za ta iya mantawa da rauni mai girma?