Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Koyi Darasi Daga Amintattun Bayin Jehobah

Ka Koyi Darasi Daga Amintattun Bayin Jehobah

“Me ne Ubangiji yake biɗa gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinƙai, ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?”—MIKAH 6:8.

WAƘOƘI: 63, 43

1, 2. Ta yaya Dauda ya nuna cewa ya kasance da aminci ga Allah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

SAUL da sojojinsa 3,000 suna neman Dauda a cikin jejin Yahuda don su kashe shi. Amma wata rana da dare, Dauda da mutanensa suka gano wurin da Saul da sojojinsa suka kafa sansaninsu. Dukansu suna barci, sai Dauda da Abishai suka taka a hankali suka wuce sojojin kuma suka je wurin da Saul yake kwance. Abishai ya yi wa Dauda magana a kunne cewa: “Ka bar ni in nashe shi da māshi, bugu ɗaya in sha zaransa da ƙasa, ba ni sāke bugunsa na biyu kuma.” Amma Dauda bai bar shi ya kashe Saul ba. Ya gaya wa Abishai cewa: “Kada a hallaka shi: gama wa ke da iko shi miƙa hannunsa a kan shafaffe na Ubangiji, ya zama marar-laifi?” Sai ya bayyana cewa: “Ubangiji ya sawaƙa in miƙa hannuna a kan shafaffe na Ubangiji.”​—⁠1 Sama’ila 26:​8-12.

2 Dauda ya fahimci abin da kasancewa da aminci ko kuma yin biyayya ga Jehobah yake nufi. Ya san cewa yana bukata ya daraja Saul kuma bai kamata ya yi tunanin yi masa rauni ba. Me ya sa? Domin Allah ya zaɓe Saul ya zama sarkin Isra’ila. A yau ma, Jehobah ya bukaci bayinsa su kasance da aminci a gare shi kuma su riƙa daraja masu iko.​—⁠Karanta Mikah 6:⁠8.

3. Ta yaya Abishai ya kasance da aminci ga Dauda?

3 Abishai ya daraja Dauda don ya san cewa Allah ne ya zaɓe Dauda ya zama Sarki. Duk da haka, bayan Dauda ya zama sarki, ya yi zunubai masu tsanani. Ya kwana da matar Uriah, sai ya gaya wa Joab cewa ya tabbata an kashe Uriah a yaƙi. (2 Sama’ila 11:​2-4, 14, 15; 1 Labarbaru 2:16) Joab ɗan’uwan Abishai ne, saboda haka, wataƙila Abishai ya ji abin da Dauda ya yi, amma ya ci gaba da daraja Dauda. Ƙari ga haka, Abishai shugaban sojoji ne kuma zai iya yin amfani da ikonsa ya mai da kansa Sarki, amma bai yi hakan ba. A maimakon haka, ya yi wa Dauda hidima kuma ya kāre shi daga maƙiyansa.​—⁠2 Sama’ila 10:10; 20:6; 21:​15-17.

4. (a) Ta yaya Dauda ya kafa misalin kasancewa da aminci ga Allah? (b) Waɗanne misalai ne za mu tattauna?

4 Dauda ya kasance da aminci duk rayuwarsa. Sa’ad da yake matashi, ya kashe ƙaton nan Goliath wanda yake zagin Jehobah da kuma Isra’ilawa. (1 Sama’ila 17:​23, 26, 48-51) A lokacin da Dauda yake sarauta, Jehobah ya tura annabi Nathan ya tsauta masa don zunubai da ya yi. Nan da nan, Dauda ya amince cewa ya yi zunubi kuma ya tuba. (2 Sama’ila 12:​1-5, 13) Daga baya, sa’ad da Dauda ya tsufa, ya ba da gudummawar abubuwa masu tamani da yawa don a yi amfani da su wajen gina haikalin Jehobah. (1 Labarbaru 29:​1-5) Hakika, Dauda ya yi zunubai masu tsanani a rayuwarsa, amma bai daina kasancewa da aminci ga Allah ba. (Zabura 51:​4, 10; 86:⁠2) A wannan talifin, za mu tattauna misalan Dauda da wasu mutane a zamaninsa kuma za mu koyi yadda za mu kasance da aminci ga Jehobah maimakon ‘yan Adam. Ƙari ga haka, za mu tattauna wasu halaye da za su taimaka mana mu kasance da aminci.

ZA KA KASANCE DA AMINCI GA JEHOBAH KUWA?

5. Wane darasi ne muka koya daga kuskuren da Abishai ya yi?

5 Sa’ad da Abishai yake so ya kashe Saul, yana so ya nuna biyayyarsa ga Dauda ne. Amma Dauda ya san cewa kashe “shafaffe na Ubangiji” zunubi ne. Saboda haka, bai yarda Abishai ya kashe sarki Saul ba. (1 Sama’ila 26:​8-11) Darasi mai muhimmanci da za mu koya a nan shi ne: Sa’ad da muke bukata mu yanke shawara a kan ko wane ne za mu yi masa biyayya, ya kamata mu yi tunani a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana a yanayin.

Ya fi muhimmanci mu kasance da aminci ga Jehobah fiye da kowa

6. Ko da yake mukan so nuna aminci ga ‘yan gidanmu da abokanmu, me ya sa ya kamata mu yi hattara?

6 Mukan so nuna aminci ga waɗanda muke ƙauna, kamar abokanmu ko kuma ‘yan gidanmu. Amma da yake mu ajizai ne, zuciyarmu za ta iya rinjayar mu. (Irmiya 17:⁠9) Saboda haka, idan wanda muke ƙauna yana yin abin da ba shi da kyau kuma ya bar ƙungiyar Jehobah, wajibi ne mu tuna cewa kasancewa da aminci ga Jehobah ya fi faranta wa mutane rai muhimmanci.​—⁠Karanta Matta 22:⁠37.

7. Ta yaya wata ‘yar’uwa ta kasance da aminci ga Allah a wani yanayi mai wuya?

7 Idan aka yi wa wani a gidanku yankan zumunci, za ka iya nuna wa Jehobah cewa kana da aminci a gare shi. Alal misali, an yi wa mahaifiyar wata mai suna Anne yankan zumunci, sai ta kira Anne a waya cewa tana so ta ziyarce ta. [1] (Ka duba ƙarin bayani.) Mahaifiyar Anne ta ce ranta ya ɓace don kowa a iyalin ya ƙi ya yi mata magana. Anne ba ta ji daɗi ba kuma ta gaya wa mahaifiyarta cewa za ta rubuta mata wasiƙa. Kafin ta rubuta wasiƙar, Anne ta yi bimbini a kan wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (1 Korintiyawa 5:11; 2 Yohanna 9-11) Sai ta rubuta wasiƙar kuma ta bayyana cikin sanin yakamata cewa mahaifiyarta ce ta yi watsi da iyalin sa’ad da ta yi zunubi kuma ta ƙi tuba. Anne ta gaya wa mahaifiyarta cewa ta tuba kuma ta komo ga Jehobah don hakan ne zai sa ta sake yin farin ciki.​—⁠Yaƙub 4:⁠8.

8. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu kasance da aminci ga Allah?

8 Amintattun bayin Jehobah a zamanin Dauda sun kasance da tawali’u da kirki da kuma ƙarfin zuciya. Bari mu tattauna yadda waɗannan halayen za su taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah.

WAJIBI NE MU ZAMA MASU TAWALI’U

9. Me ya sa Abner ya yi ƙoƙarin kashe Dauda?

9 Ɗan Saul, wato Jonathan da kuma shugaban sojojin Isra’ila, Abner sun ga lokacin da Dauda ya kawo kan Goliath zuwa wurin Sarki Saul. Jonathan ya zama abokin Dauda kuma ya kasance da aminci a gare shi. (1 Sama’ila 17:57–18:⁠3) Amma Abner bai yi hakan ba. Daga baya ma, ya taimaka wa Saul a lokacin da yake so ya kashe Dauda. (1 Sama’ila 26:​1-5; Zabura 54:⁠3) Jonathan da Abner sun san cewa Allah ne ya zaɓi Dauda ya zama sarkin Isra’ila bayan Saul. Amma bayan mutuwar Saul, Abner bai goyi bayan Dauda ba. A maimakon haka, ya yi ƙoƙarin sa ɗan Saul mai suna Ish-bosheth ya zama sarki. Daga baya, wataƙila, Abner ya yi ƙoƙarin mai da kansa sarki, mai yiwuwa shi ya sa ya kwana da ɗaya daga cikin matan Saul. (2 Sama’ila 2:​8-10; 3:​6-11) Me ya sa Jonathan da Abner suka kasance da ra’ayi dabam-dabam game da Dauda? Domin Jonathan ya kasance da aminci ga Jehobah kuma shi mai tawali’u ne. Amma Abner maci amana ne kuma mai girman kai.

10. Me ya sa Absalom bai kasance da aminci ga Allah ba?

10 Ɗan Sarki Dauda mai suna Absalom bai da aminci ga Allah don shi ba mai tawali’u ba ne. Ya so ya zama sarki, saboda haka, ya “shirya karusa da dawakai domin kansa, da mutum hamsin masu-gudu a gabansa.” (2 Sama’ila 15:⁠1) Ƙari ga haka, ya rinjayi Isra’ilawa da yawa su goyi bayansa. Har ma ya yi ƙoƙarin kashe mahaifinsa duk da cewa ya san Jehobah ne ya sa Dauda ya zama sarkin Isra’ila.​—⁠2 Sama’ila 15:​13, 14; 17:​1-4.

11. Ta yaya za mu amfana daga labarin Abner da Absalom da kuma Baruch da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

11 Idan mutum ba mai tawali’u ba ne kuma yana neman ƙarin girma, zai yi wuya ya kasance da aminci ga Allah. Ko da yake muna ƙaunar Jehobah kuma ba ma so mu kasance da son zuciya kamar waɗannan mugaye, wato Abner da Absalom, wajibi ne mu yi hattara don kada mu soma sha’awar kuɗi ko kuma aikin da zai sa mu ɗauki kanmu da muhimmanci ainun. Hakan zai ɓata dangantakarmu da Jehobah. Baruch sakataren Irmiya ya yi sha’awar abin da bai da shi kuma saboda haka, ya daina farin ciki a ibadarsa ga Jehobah. Sai Jehobah ya gaya wa Baruch: “Duba, abin da na gina, shi zan rushe; abin da na dasa kuma, shi zan tumɓuke; wannan kuwa ko’ina a cikin ƙasar nan. Kana fa biɗa wa kanka manyan abu? Kada ka biɗe su.” (Irmiya 45:​4, 5) Baruch ya saurari Jehobah. Hakazalika, ya kamata mu saurare Jehobah don nan ba da daɗewa ba, zai halaka wannan muguwar duniya.

Sa’ad da ka shawarci ɗan’uwanka ya je ya gaya wa dattawa abin da ya yi, kana taimakonsa ne kuma kana biyayya ga Jehobah

12. Ka bayyana dalilin da ya sa ba za mu iya kasancewa da aminci ga Allah ba idan mu masu son zuciya ne.

12 Wani ɗan’uwa a Mexico mai suna Daniel ya fuskanci matsalar kasancewa da aminci ga Jehobah. Yana so ya auri wadda ba ta bauta wa Jehobah. Daniel ya ce: “Na ci gaba da rubuta mata wasiƙa duk da cewa na soma hidimar majagaba.” Amma sai ya gane cewa yana yin abin da yake so ne don son zuciya. Ba ya biyayya ga Allah, kuma yana bukatar ya zama mai tawali’u. Saboda haka, ya gaya wa wani dattijon da ya ƙware game da yarinyar. Daniel ya ce: “Ya taimaka min in fahimci cewa ina bukata in kasance da aminci ga Allah kuma in daina rubuta mata wasiƙa. Bayan na yi addu’a da hawaye sosai, sai na daina rubuta mata wasiƙa. Ba da daɗewa ba, sai na soma yin farin ciki a hidimata.” Yanzu, Daniel ya auri mace mai ƙaunar Jehobah, kuma yana hidimar mai kula da da’ira.

AMINCI GA ALLAH ZAI TAIMAKA MANA MU ZAMA MASU ALHERI

Idan ka gane cewa abokinka ya yi zunubi mai tsanani, shin za ka ba shi shawara ya je ya sami dattawa don su taimaka masa kuma za ka tabbata cewa ya yi hakan? (Ka duba sakin layi na 14)

13. Ta yaya Nathan ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma Dauda sa’ad da Dauda ya yi zunubi?

13 Idan muka kasance da aminci ga Jehobah, hakan zai sa mu kasance da aminci ga wasu kuma mu taimaka musu a hanyar da ta fi dacewa. Annabi Nathan ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma Dauda. Bayan Dauda ya ƙwace matar wani mutum kuma ya kashe shi, Jehobah ya tura Nathan ya yi wa Dauda gargaɗi. Nathan ya yi ƙarfin zuciya kuma ya bi umurnin Jehobah. Amma ya nuna hikima ta yadda ya yi wa Dauda magana cikin sanin yakamata. Yana son ya taimaka wa Dauda ya san cewa Dauda ya yi zunubai masu tsanani. Saboda haka, ya gaya masa labarin wani mutum mai kuɗi da ya ƙwace ɗan rago tilo na wani talaka. Sa’ad da Dauda ya ji hakan, sai ya fusata sosai don abin da mai arzikin ya yi. Nathan ya ce: “Kai ne mutumin nan.” Sai Dauda ya fahimta cewa ya yi zunubi ga Jehobah.—2 Sama’ila 12:1-7, 13.

14. Ta yaya za ka iya kasancewa da aminci ga Jehobah da abokinka ko kuma danginka?

14 Kai ma za ka iya kasancewa da aminci ga Jehobah kuma ka kasance da aminci ga wasu ta wajen taimaka musu. Alal misali, za ka iya kasancewa da hujja cewa ɗan’uwanka ya yi zunubi mai tsanani. Wataƙila ba za ka so ka ɓata zumunci da ke tsakaninku ba, musamman ma idan mutumin abokinka ne na kud da kud ko kuma ɗan gidanku ne. Amma ka san cewa kasancewa da aminci ga Jehobah shi ne ya fi muhimmanci. Saboda haka, ka yi biyayya ga Jehobah kuma ka taimaka wa ɗan’uwanka. Ka gaya masa cewa ya je ya gaya wa dattawa abin da ya yi ba tare da ɓata lokaci ba. Idan ya ƙi zuwa, sai ka je ka gaya wa dattawa da kanka. Ta yin hakan, kana biyayya ga Jehobah. Ƙari ga haka, kana taimaka wa ɗan’uwanka ne, don dattawa za su iya taimaka masa ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. Za su yi masa gyara a hankali kuma a cikin sanin yakamata.​—⁠Karanta Levitikus 5:1; Galatiyawa 6:⁠1.

MUNA BUKATAR ƘARFIN ZUCIYA DON MU KASANCE DA AMINCI GA ALLAH

15, 16. Me ya sa Hushai ya bukaci ƙarfin zuciya don ya kasance da aminci ga Jehobah?

15 Hushai wani amintaccen abokin Sarki Dauda ne. Sa’ad da mutane suke son su naɗa Absalom sarki, Hushai yana son ya kasance da aminci ga Dauda da kuma Allah, amma yana bukatar ƙarfin zuciya don ya yi hakan. Ya san cewa Absalom ya je Urushalima da sojojinsa kuma Dauda ya tsere. (2 Sama’ila 15:13; 16:15) Amma mene ne Hushai ya yi? Ya juya bayansa ga Dauda don ya goyi bayan Absalom ne? A’a. Ko da yake Dauda ya tsufa kuma mutane da yawa suna so su kashe shi, Hushai ya kasance da aminci ga Dauda don Jehobah ne ya naɗa Dauda sarki. Saboda haka, Hushai ya je ya sami Dauda a Dutsen Zaitun.​—⁠2 Sama’ila 15:​30, 32.

16 Dauda ya gaya wa Hushai ya koma Urushalima kuma ya nuna kamar yana goyon bayan Absalom don hakan zai sa Absalom ya saurari shawararsa a maimakon shawarar Ahithophel. Hushai ya yi ƙarfin zuciya kuma ya sa ransa cikin haɗari don ya yi biyayya ga Dauda kuma ya kasance da aminci ga Jehobah. Dauda ya yi addu’a don Jehobah ya taimaka wa Hushai kuma abin da ya faru ke nan. Absalom ya bi shawarar Hushai a maimakon na Ahithophel.​—⁠2 Sama’ila 15:31; 17:⁠14.

17. Me ya sa muke bukatar ƙarfin zuciya don mu kasance da aminci?

17 Muna bukatar mu kasance da ƙarfin zuciya kuma mu yi biyayya ga Jehobah maimakon mu yi abin da ‘yan gidanmu ko abokan aikinmu ko hukuma take so mu yi. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Taro a ƙasar Japan ya faranta wa iyayensa rai tun lokacin da yake yaro. Yana musu biyayya da kuma kasance da aminci a gare su don yana ƙaunarsu. Amma sa’ad da Shaidun Jehobah suka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, iyayensa sun yi ƙoƙarin hana shi. Hakan ya sa shi baƙin ciki kuma ya yi fargabar gaya musu cewa zai soma halartar taro. Ɗan’uwa Taro ya ce: “Sun ɓata rai sosai kuma sun hana ni ziyararsu a gida a cikin shekaru da dama. Na yi ta addu’a don in sami ƙarfin zuciya kuma in manne wa shawarar da na yi. Yanzu, sun ɗan canja ra’ayinsu kuma ina ziyararsu a kai a kai.”​—⁠Karanta Misalai 29:⁠25.

18. Ta yaya ka amfana daga nazarin wannan talifin?

18 Dauda da Jonathan da Nathan da kuma Hushai sun kasance da aminci ga Jehobah kuma sun yi farin ciki. Mu ma za mu yi farin ciki idan muka yi hakan. Kada mu zama kamar Abner da Absalom da suka ci amana. Gaskiya ne cewa mu ajizai ne kuma mukan yi kuskure. Amma mu ƙudiri niyyar kasancewa da aminci ga Jehobah kuma mu nuna cewa yin hakan ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu.

^ [1] (sakin layi na 7) An canja wasu sunaye.