Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Koyi da Abokan Jehobah na Kud da Kud

Ka Yi Koyi da Abokan Jehobah na Kud da Kud

“Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi.”—ZABURA 25:14, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 106, 118

1-3. (a) Me ya sa muke da tabbaci cewa za mu iya zama abokan Allah? (b) Labarin su waye ne za mu tattauna a wannan talifin?

AN AMBATA a cikin Littafi Mai Tsarki sau uku cewa Ibrahim abokin Allah ne. (2 Labarbaru 20:7; Ishaya 41:8; Yaƙub 2:23) Ibrahim ne kaɗai Littafi Mai Tsarki ya kira abokin Allah kai tsaye. Shin hakan yana nufin cewa shi ne kaɗai ya taɓa zama abokin Jehobah? A’a. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukanmu za mu iya samun wannan gatan.

2 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran amintattun maza da mata da yawa masu tsoron Allah, da suka yi imani da shi kuma suka zama abokansa na kud da kud. (Karanta Zabura 25:​14, LMT.) Suna cikin “taron shaidu mai-girma” da manzo Bulus ya ambata. Waɗannan mutanen suna da halaye dabam-dabam, amma dukansu sun zama abokan Allah.—Ibraniyawa 12:⁠1.

3 Bari mu yi la’akari da mutane guda uku da Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sun zama abokan Jehobah: (1) Gwauruwa mai aminci da ta fito daga ƙasar Moab mai suna Ruth, da (2) Hezekiya, amintaccen Sarkin Yahuda, da kuma (3) Maryamu, mace mai tawali’u da ta zama mahaifiyar Yesu. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda kowannensu ya zama abokin Allah?

TA NUNA ƘAUNA DA AMINCI

4, 5. Wace shawara mai wuya ce Ruth take bukata ta yanke, kuma me ya sa yanke shawarar ya kasance mata da wuya? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.)

4 Naomi tare da surukanta mata, Ruth da Orpah suna wata tafiya mai nisa daga ƙasar Moab zuwa ƙasar Isra’ila. Sa’ad da suke hanya, Orpah ta yanke shawarar koma garinsu Moab. Amma Naomi ta ƙudiri niyyar zuwa inda ta fito, wato ƙasar Isra’ila. Wannan yanayin ya sa Ruth ta sami kanta a tsaka mai wuya. Shin mene ne za ta yi? Za ta koma ƙasar Moab don ta kasance tare da danginta ne, ko kuma za ta bi surkuwarta Naomi zuwa Bai’talami?​—⁠Ruth 1:​1-8, 14.

5 Dangin Ruth suna zama a ƙasar Moab. Za ta iya komawa wurinsu, kuma wataƙila za su kula da ita. Ta san mutanen Moab da yaren da kuma al’adarsu. Naomi ba za ta iya tabbatar mata cewa za ta ji daɗin zama a Bai’talami ba. Ƙari ga haka, Naomi tana tsoro cewa ba za ta iya samo mata miji ba. Saboda haka, Naomi ta gaya wa Ruth ta koma ƙasar Moab. Kamar yadda muka gani, Orpah ‘ta koma wurin danginta, da kuma allahnta.’ (Ruth 1:​9-15) Amma Ruth ta ƙi ta koma wurin mutanenta da allolinsu na ƙarya.

6. (a) Wace shawara mai kyau ce Ruth ta yanke? (b) Me ya sa Boaz ya ce Ruth ta nemi mafaka a ƙarƙashin Jehobah?

6 Mai yiwuwa Ruth ta koyi game da Jehobah daga wurin mijinta ko kuma daga Naomi. Ta koyi cewa Jehobah ya bambanta da allolin Moab. Tana ƙaunar Jehobah kuma ta san cewa ya cancanci ta ƙaunace shi kuma ta bauta masa. Saboda haka, Ruth ta yanke shawara mai kyau. Ta gaya wa Naomi cewa: “Danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.” (Ruth 1:16) Idan muka yi tunanin yadda Ruth take ƙaunar Naomi, hakan yana ratsa zuciyarmu. Amma abin da ya fi burgewa shi ne yadda Ruth take ƙaunar Jehobah. Hakan ya burge Boaz kuma ya yabe ta don yadda ta yi imani da Jehobah kuma ta ‘nemi mafaka a ƙarƙashin fukafukansa.’ (Karanta Ruth 2:12.) Kalaman da Boaz ya yi amfani da su sun tuna mana yadda ɗan tsuntsu yakan nemi mafaka a ƙarƙashin fukafukan mahaifiyarsa. (Zabura 36:7; 91:​1-4) Hakazalika, Jehobah ya tanadar wa Ruth mafaka kuma ya albarkace ta saboda bangaskiyarta. Ruth ba ta yi nadama cewa ta yanke shawarar bauta wa Jehobah ba.

7. Mene ne zai iya taimaka wa waɗanda suke jinkirin ba da kansu ga Jehobah?

7 Mutane da yawa suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ba sa so su nemi mafaka a wurin Jehobah. Suna jinkirin ba da kansu ga Jehobah kuma su yi baftisma. Idan ka sami kanka a cikin wannan yanayin, ka yi tunanin dalilin da ya sa kake jinkiri. Kowa yana da abin da yake bauta masa. (Joshua 24:15) Shawara mai kyau da za ka yanke ita ce shawarar bauta wa Allah na gaskiya. Idan ka ba da kanka ga Jehobah, kana nuna cewa ka tabbata cewa zai taimake ka. Kuma zai taimaka maka ka ci gaba da bauta masa ko da kana fama da wasu matsaloli. Abin da Allah ya yi wa Ruth ke nan.

“YA MANNE WA UBANGIJI”

8. Ka bayyana abubuwan da suka faru da Hezekiya sa’ad da yake yaro.

8 Tarbiyyar da aka yi wa Hezekiya ta bambanta da na Ruth sosai. An haife shi a cikin al’ummar da ke bauta wa Allah. Amma ba dukan Isra’ilawa ba ne suka kasance da aminci. Mahaifin Hezekiya, wato sarki Ahaz mugun mutum ne. Bai girmama haikalin Allah ba, kuma ya rinjayi mutanen su soma bauta wa allolin ƙarya. Ƙari ga haka, ya yi hadaya da ‘yan’uwan Hezekiya ga allolin ƙarya ta wajen ƙona su a wuta. Hakika, sa’ad da Hezekiya yake yaro, ya shaida munanan abubuwa ba kaɗan ba!​—⁠2 Sarakuna 16:​2-4, 10-17; 2 Labarbaru 28:​1-3.

9, 10. (a) Me ya sa Hezekiya zai iya yin saurin fushi? (b) Me ya sa bai kamata mu yi fushi da Allah ba? (c) Me ya sa bai dace mu ɗauka cewa yadda aka yi mana tarbiyya ne yake sa mu zama mutanen kirki ko mugaye ba?

9 Mugayen abubuwan da Ahaz ya yi za su iya sa ɗansa Hezekiya ya yi fushi da Jehobah. Wasu a yau da ba su fuskanci irin abin da Hezekiya ya fuskanta ba suna jin cewa suna da ƙwaƙƙwarar dalilin na yin “gunaguni da Ubangiji” ko kuma su yi fushi da ƙungiyarsa. (Misalai 19:⁠3) Waɗansu suna ganin cewa rashin tarbiyya mai kyau na ‘yan gidansu zai iya sa su yi abubuwan da ba su dace ba a rayuwarsu ko kuma su yi abubuwan da iyayensu suka yi da ba su da kyau. (Ezekiyel 18:​2, 3) Amma, shin hakan gaskiya ne?

10 Rayuwar Hezekiya ta nuna cewa hakan ba gaskiya ba ce! Babu wani dalili da zai sa mu yi fushi da Jehobah. Domin ba ya sa mugayen abubuwa su sami mutane. (Ayuba 34:10) Gaskiya ne cewa iyaye suna iya koya wa yaransu su yi abubuwa masu kyau da marasa kyau. (Misalai 22:6; Kolosiyawa 3:21) Hakan ba ya nufin cewa lallai tarbiyyar da aka yi mana ne ya sa muka zama yadda muke a yau. Me ya sa? Domin Jehobah ya halicce mu da damar yin abin da muke so, kuma hakan yana nufin cewa za mu iya zaɓan mu yi nagarta ko kuma mugunta. (Kubawar Shari’a 30:19) Ta yaya Hezekiya ya yi amfani da wannan baiwa?

Matasa da yawa sun soma bauta wa Jehobah duk da cewa iyayensu ba Shaidun Jehobah ba ne (Ka duba sakin layi na 9, 10)

11. Me ya sa Hezekiya ya kasance ɗaya daga cikin sarakuna mafi kyau a Yahuda?

11 Ko da yake mahaifinsa yana cikin sarakunan Yahuda da suka fi mugunta, Hezekiya ya zama ɗaya daga cikin sarakuna masu kirki sosai. (Karanta 2 Sarakuna 18:​5, 6.) Bai bi mugun misalin mahaifinsa ba. Maimakon haka, ya saurari annabawan Jehobah, kamar su Ishaya, Mikah, da Hosiya. Ya saurari shawararsu da kuma gyaran da suka yi masa. Hakan ya motsa shi ya gyara abubuwa da yawa da ba su dace ba da mahaifinsa ya yi. Ya tsabtace haikalin, kuma ya roƙi Allah ya gafarta wa mutanensa zunubansu, ya kuma halakar da dukan gumakan da ke cikin ƙasar. (2 Labarbaru 29:​1-11, 18-24; 31:⁠1) Daga baya, lokacin da sarkin Assuriya mai suna Sennacherib ya yi barazanar kai hari ga Urushalima, Hezekiah ya nuna cewa shi mai gaba gaɗi ne da kuma bangaskiya. Ya dogara ga Jehobah cewa zai kāre shi kuma ya ƙarfafa mutanensa. (2 Labarbaru 32:​7, 8) A wani lokaci, Hezekiya ya nuna girman kai, amma lokacin da Jehobah ya yi masa gyara, sai ya ƙaskantar da kansa. (2 Labarbaru 32:​24-26) Hakika, ya kamata mu yi koyi da Hezekiya. Bai yarda yanayin gidansu ya ɓata rayuwarsa ba. Maimakon haka ya nuna cewa shi aminin Jehobah ne.

12. Kamar Hezekiya, ta yaya mutane da yawa a yau suka zama abokan Jehobah?

12 Duniya tana cike da mugunta da kuma rashin ƙauna, saboda haka yara da yawa a yau sun yi girma ba tare da iyaye masu ƙaunarsu da kuma kula da su ba. (2 Timotawus 3:​1-5) Ko da yake Kiristoci da yawa a yau sun fito ne daga gida da ‘yan gidansu ba su da tarbiyya mai kyau, amma sun zaɓa su ƙulla abokantaka na kud da kud da Jehobah. Kamar Hezekiya sun nuna cewa tarbiyyar ‘yan gidansu ba za ta nuna irin mutane da za su zama a nan gaba ba. Allah ya ba mu ‘yancin zaɓan abin da muke son mu yi, kuma za mu iya zaɓan ko za mu bauta wa Allah kuma mu ɗaukaka shi, kamar yadda Hezekiya ya yi.

“GA NI, BAIWAR UBANGIJI”

13, 14. Me ya sa za mu iya ce aikin da aka ba wa Maryamu ba mai sauƙi ba ne, duk da haka, wace amsa ce ta ba wa mala’ika Jibra’ilu?

13 Shekaru da yawa bayan zamanin Hezekiya, wata budurwa mai suna Maryamu ta yi abota ta kud da kud da Jehobah kuma ta sami wani aiki na musamman daga wurinsa. Za ta yi juna biyu ta haifi Ɗan Allah kuma ta yi rainonsa! Hakika, Jehobah ya ƙaunaci Maryamu kuma ya amince da ita, shi ya sa ya ba ta wannan gatan. Amma mene ne ta yi sa’ad da aka gaya mata cewa za ta sami wannan gatan?

“Ga ni, baiwar Ubangiji” (Ka duba sakin layi na 13, 14)

14 Mukan yi magana sosai game da wannan babban gatan da aka ba wa Maryamu. Amma akwai wasu abubuwan da suka ba ta tsoro. Alal misali, mala’ika Jibra’ilu ya ce za ta yi juna biyu ba tare da ta sadu da namiji ba. Amma Jibra’ilu bai ce zai bayyana wa danginta da maƙwabtanta yadda za ta yi juna biyu ba. Wane tunani za su yi idan suka gan ta da ciki? Ta yaya za ta bayyana wa Yusufu cewa ba ta ci amanarsa ba? Ƙari ga haka, an ba ta babban gatan yin rainon Ɗan Allah! Ba za mu iya sanin abin da Maryamu take tunanin sa a lokacin ba, amma mun san abin da ta yi bayan Jibra’ilu ya ba ta saƙon. Ta ce: “Ga ni, baiwar Ubangiji; bisa ga faɗinka shi zama mani.”​—⁠Luka 1:​26-38.

15. Me ya sa muka ce Maryamu tana da bangaskiya sosai?

15 Maryamu tana da bangaskiya sosai! Ta shirya zuciyarta ta yi dukan abin da aka umurce ta kamar baiwa. Ta ba da gaskiya cewa Jehobah zai kula da ita kuma ya kāre ta. Ta yaya Maryamu ta kasance da irin wannan bangaskiyar. Ba a haife mu da bangaskiya ba. Amma za mu iya kasancewa da bangaskiya kamar Maryamu kuma mu roƙi Allah ya taimaka mana. (Galatiyawa 5:22; Afisawa 2:⁠8) Maryamu ta yi aiki tuƙuru don ta ƙarfafa bangaskiyarta. Ta yaya muka san hakan? Bari mu yi la’akari da yadda ta kasa kunne da kuma abubuwan da ta faɗa.

16. Mene ne ya nuna cewa Maryamu ta kasa kunne da kyau?

16 Yadda Maryamu ta kasa kunne. Littafi Mai Tsarki ya ce “kowane mutum ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana.” (Yaƙub 1:19) Maryamu ta kasa kunne sosai. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ta saurari abin da aka gaya mata, musamman ma abubuwan da ta koya game da Jehobah. Ta keɓe lokaci don ta yi bimbini a kan waɗannan batutuwa masu muhimmanci. Alal misali, a lokacin da aka haifi Yesu, makiyaya sun gaya wa Maryamu wani saƙon da mala’ika ya ba su. Daga baya, sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, ya yi wani maganar da ya ba Maryamu mamaki. A duk waɗannan lokutan, Maryamu ta kasa kunne, kuma ta yi bimbini a kan abubuwan da ta ji.​—⁠Karanta Luka 2:​16-19, 49, 51.

17. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Maryamu ta yi magana?

17 Abin da Maryamu ta yi magana a kai. Littafi Mai Tsarki bai bayyana mana abubuwan da Maryamu ta yi magana a kai sosai ba. An ambata furuci mafi tsawo da ta yi a Luka 1:​46-55. Wannan furucin ya nuna cewa Maryamu ta san Nassosin Ibrananci sosai. Me ya sa? Furucin Maryamu kusan ɗaya ne da addu’ar da Hannatu, mahaifiyar Sama’ila ta yi. (1 Sama’ila 2:​1-10) Kamar dai Maryamu ta yi ƙaulin nassi wajen sau 20 a furucin da ta yi. A bayyane yake cewa ta ji daɗin yin magana game da abubuwan da ta koya daga wurin babban Amininta Jehobah.

18. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin koyi da bangaskiyar Maryamu?

18 A wani lokaci, Jehobah zai iya ba mu wani aikin da muke gani zai yi mana wuya kamar yadda ya ba wa Maryamu. Bari mu yi koyi da ita, mu karɓi aikin cikin tawali’u kuma mu dogara ga Jehobah ya taimake mu. Ƙari ga haka, za mu iya yin koyi da Maryamu a yadda ta nuna bangaskiya idan muka saurari Jehobah kuma muka yi bimbini a kan abin da muka koya game da shi da kuma nufinsa. Ta yin hakan, za mu yi farin cikin bayyana wa mutane abin da muka koya.​—⁠Zabura 77:​11, 12; Luka 8:18; Romawa 10:⁠15.

19. Yayin da muke yin koyi da amintattun mutane da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?

19 A bayyane yake cewa Ruth da Hezekiya da Maryamu abokan Jehobah ne na kud da kud, kamar Ibrahim. Suna cikin “taron shaidu mai-girma” da suka sami gatan zama abokan Allah. Bari mu ci gaba da bin misalin waɗannan amintattun mutanen. (Ibraniyawa 6:​11, 12) Idan muka yi hakan, za mu sami gatan kasancewa abokan Allah har abada!