Farin Ciki—Hali Ne da Muke Koya Daga Wurin Allah
KOWA a duniyar nan yana so ya riƙa farin ciki. Amma muna ‘shan wuya’ sosai domin muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. (2 Tim. 3:1, Littafi Mai Tsarki) Rashin adalci da rashin lafiya da rashin aiki da baƙin ciki da dai sauransu suna iya sa wasu sanyin gwiwa. Hakan na iya shafan bayin Allah ma. Idan kana fama da waɗannan matsalolin, me za ka yi don ka sake yin farin ciki?
Kafin mu amsa wannan tambayar, zai dace mu fara fahimtar ma’anar yin farin ciki da gaske da kuma yadda wasu suke farin ciki duk da matsalolin da suke fuskanta. Bayan haka, za mu tattauna abubuwan da muke bukatar mu riƙa yi don mu ci gaba da farin ciki kuma mu daɗa yin hakan.
MENE NE FARIN CIKI?
Da akwai bambanci tsakanin farin ciki da kuma fara’a. Alal misali: Wani zai iya shan giya ya bugu sosai. Bayan haka, sai ya soma dariya, amma idan ya dawo hankalinsa, sai ya daina dariya kuma ya ci gaba da fuskantar matsaloli da yake ciki. Murnar da yake yi ba farin ciki na gaske ba ne.—Mis. 14:13.
Akasin haka, farin ciki hali ne da muke nunawa idan muna ɗokin samun wani abu ko kuma mun riga mun same shi. Mutumin da ke farin ciki da gaske zai yi hakan ko da yana fuskantar matsaloli. (1 Tas. 1:6) Ƙari ga haka, mutumin na iya damuwa game da wani abu amma ya kasance da farin ciki. Alal misali, an yi wa manzannin Yesu dūka sosai don suna wa’azi. Duk da haka, sun “fita fa daga gaban majalisa, suna murna da aka maishe su sun isa su sha ƙanƙanci sabili da sunan” Yesu. (A. M. 5:41) Hakika, ba dūkan da aka yi musu ba ne ya sa su farin ciki. Amma sun yi farin ciki domin sun riƙe amincinsu ga Allah.
Ba a haife mu da wannan halin ba, kuma ba ma farin ciki haka kawai. Me ya sa? Domin ruhu mai tsarki ne yake sa mutum ya riƙa farin ciki, shi ne kuma zai iya taimaka mana mu “yafa sabon mutum” wanda ya ƙunshi yin farin ciki. (Afis. 4:24; Gal. 5:22) Idan muna farin ciki, za mu iya jimrewa da dukan matsalolin da muke fuskanta.
MISALAI MASU KYAU
Jehobah yana son abubuwa masu kyau su riƙa faruwa a duniya. Ba munanan abubuwan da suke faruwa a yau ba. Duk da haka, abubuwan da ke faruwa ba ya hana Jehobah farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙarfi da farin ciki suna cikin wurinsa.” (1 Laba. 16:27) Ban da haka, nagargarun ayyukan da bayinsa suke yi a yau suna ‘faranta zuciyarsa.’—Mis. 27:11.
Idan muna zaton samun wani abu kuma hakan bai yiwu ba, ya kamata mu riƙa damuwa ne? Zai dace mu bi misalin Jehobah. Maimakon hakan ya hana mu farin ciki, ya kamata mu mai da hankali ga abubuwan da *
muke da su yanzu, da kuma waɗanda za mu samu a nan gaba.Akwai misalai da yawa a Littafi Mai Tsarki na mutanen da suka yi farin ciki duk da cewa sun fuskanci matsaloli sosai. Ibrahim yana ɗaya daga cikinsu. Ya ci gaba da farin ciki, duk da cewa ya fuskanci matsaloli sosai kuma wasu sun so su wahalar da shi. (Far. 12:10-20; 14:8-16; 16:4, 5; 20:1-18; 21:8, 9) Ta yaya ya yi hakan? Ya mai da hankali ga begen da yake da shi na yin rayuwa a sabuwar duniya sa’ad da Almasihu ya soma sarauta a Mulkin Allah. (Far. 22:15-18; Ibran. 11:10) Yesu ya ce: “Ubanku Ibrahim ya yi murna da ganin ranata.” (Yoh. 8:56) Za mu iya bin misalin Ibrahim, ta yin tunanin albarkar da za mu samu a nan gaba.—Rom. 8:21.
Kamar Ibrahim, Bulus da Sila ma sun mai da hankali ga alkawuran Allah. Sun kasance da bangaskiya sosai kuma sun yi farin ciki ko da yake sun fuskanci matsaloli. Alal misali, duk da cewa sun sha dūka kuma aka saka su a kurkuku, ‘wajen tsakiyar dare Bulus da Sila sun yi addu’a suna rera waƙa ga Allah.’ (A. M. 16:23-25) Sun jimre da wahalar da suka sha domin sun ci gaba da yin tunani a kan alkawuran Allah. Ban da haka ma, sanin cewa an tsananta musu don su mabiyan Yesu ne ya sa su farin ciki sosai. Za mu iya bin misalin Bulus da Sila ta wurin yin tunanin albarkar da za mu samu idan muka bauta wa Allah da aminci.—Filib. 1:12-14.
A yau, akwai ’yan’uwa da yawa da suke farin ciki duk da cewa sun fuskanci matsaloli sosai. Alal misali, a watan Nuwamba na shekara ta 2013, wata mahaukaciyar guguwar Haiyan ta halaka gidajen Shaidun Jehobah guda 1,000 a ƙasar Filifin. Wani ɗan’uwa mai suna George da gidansa ke birnin Tacloban da hakan ya shafa, ya ce: “Duk da abin da ya faru da mu, ’yan’uwa suna farin ciki. Ba zan iya kwatanta irin murnar da muke yi ba.” A duk lokacin da muke fuskantar matsaloli, yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi mana zai taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki. Waɗanne abubuwa ne kuma Jehobah ya yi mana da yake sa mu farin ciki?
ABUBUWAN DA KE SA MU FARIN CIKI
Dangantakarmu da Jehobah ce ta fi sa mu farin ciki. Mun san cewa shi ne Maɗaukakin Sarki. Shi ne Ubanmu da Allahnmu da kuma Abokinmu!—Zab. 71:17, 18.
Ƙari ga haka, muna godiya don rai da Jehobah ya ba mu da kuma yadda muke jin daɗin rayuwa. (M. Wa. 3:12, 13) Da yake Jehobah ya ba mu damar saninsa, hakan ya sa mun san nufinsa ga ’yan Adam da kuma yadda ya kamata mu yi rayuwa. (Kol. 1:9, 10) Amma mutane da yawa ba su san abin da ya sa suke rayuwa ba. Shi ya sa Bulus ya ce: “Ido ba ya gani ba, kunne ba ya ji ba, ba ya shiga zuciyar mutum ba, dukan iyakar abin da Allah ya shirya wa waɗanda ke ƙaunarsa. Amma mu ne Allah ya bayyana mana ta wurin ruhu.” (1 Kor. 2:9, 10) Shin muna farin cikin sanin nufin Jehobah domin ’yan Adam?
Jehobah yana kuma gafarta mana zunubanmu. (1 Yoh. 2:12) Yana sa mu kasance da begen yin rayuwa a sabuwar duniya da ke nan tafe. (Rom. 12:12) Ban da haka, Jehobah ya ba mu abokai da yawa da za mu riƙa bauta masa tare. (Zab. 133:1) Ƙari ga haka, Kalmar Allah ta tabbatar mana da cewa Jehobah yana kāre bayinsa daga Shaiɗan da kuma aljannunsa. (Zab. 91:11) Idan muka ci gaba da yin tunani a kan waɗannan albarka, hakan zai sa mu daɗa yin farin ciki sosai.—Filib. 4:4.
YADDA ZA MU KYAUTATA YIN FARIN CIKI
Zai yiwu ne Kirista da yake farin ciki ya kyautata yadda yake yin hakan? Yesu ya ce: “Waɗannan magana na faɗa muku domin farin cikina ya zauna cikinku, domin kuma farin cikinku ya cika.” (Yoh. 15:11) Babu shakka, hakan ya nuna mana cewa za mu iya kyautata yadda muke farin ciki. Za mu iya kwatanta farin ciki da wuta. Idan muna son wuta ta riƙa ci, wajibi ne mu ci gaba da saka mata itace. Haka ma yake da farin ciki, ruhu mai tsarki ne yake sa mu daɗa farin ciki. Saboda haka, za mu daɗa farin ciki sosai idan muna roƙan Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Ƙari ga haka, muna bukatar mu keɓe lokaci don yin tunani sosai a kan Littafi Mai Tsarki.—Zab. 1:1, 2; Luk. 11:13.
Wani abu kuma da zai sa mu daɗa farin ciki shi ne yin abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai. (Zab. 35:27; 112:1) Me ya sa? Domin an halicce mu ne mu riƙa jin ‘tsoron Allah, mu kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.’ (M. Wa. 12:13) Don haka, idan muna bauta wa Jehobah, za mu yi farin ciki sosai. *
SAKAMAKON YIN FARIN CIKI
Za mu amfana sosai yayin da muke kyautata yadda muke farin ciki. Alal misali, za mu ci gaba da faranta wa Jehobah rai idan muna bauta masa da farin ciki duk da matsalolin da muke fuskanta. (K. Sha. 16:15; 1 Tas. 5:16-18) Ƙari ga haka, idan muna farin ciki, ba za mu riƙa tunanin cewa tara abin da duniya shi ne ya fi muhimmanci a rayuwa ba. A maimakon haka, za mu so yin sadaukarwa a hidimarmu ga Jehobah. (Mat. 13:44) Kuma idan muka ga albarkar da muke samu don yin hakan, za mu yi farin ciki sosai kuma mu sa wasu farin ciki.—A. M. 20:35; Filib. 1:3-5.
Ban da haka ma, idan muna farin ciki za mu sami ƙoshin lafiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya mai-jin daɗi magani ce mai-kyau.” (Mis. 17:22) Wani masanin kiwon lafiya a jami’ar da ke birnin Nebraska a Amirka, ya ce: “Idan kana farin ciki kuma ka gamsu da rayuwarka, babu shakka, za ka sami ƙoshin lafiya a nan gaba.”
Duk da cewa muna rayuwa a duniyar da ke cika da wahala, za mu iya yin farin ciki da gaske. Ta yaya za mu yi hakan? Ta wajen yin addu’a Allah ya taimaka mana da ruhu mai tsarki da yin nazari da kuma yin tunani sosai a kan Kalmar Allah. Ban da haka ma, za mu iya daɗa farin ciki idan muna yin tunanin albarkar da muke morewa a yanzu. Kuma mu bi misalin mutane masu aminci da yin iya ƙoƙarinmu don mu yi nufin Allah. Idan muna yin waɗannan abubuwan, za mu amince da abin da ke littafin Zabura 64:10 da ya ce: “Adali za ya yi murna cikin Ubangiji, ya dogara gare shi kuma.”
^ sakin layi na 10 A nan gaba za mu tattauna game da haƙuri a jerin talifofi game da ’ya’yan ruhu.
^ sakin layi na 20 Don sanin wasu hanyoyin daɗa yin farin ciki, ka duba akwatin nan “ Wasu Hanyoyi da Za Ka Daɗa Farin Ciki.”