Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Zama Mai Bangaskiya da Biyayya Kamar Nuhu da Daniyel da Ayuba

Ka Zama Mai Bangaskiya da Biyayya Kamar Nuhu da Daniyel da Ayuba

“Nuhu, Daniel, da Ayuba . . . rayukansu kaɗai za su ceta ta wurin adalcinsu.”​—EZEK. 14:14.

WAƘOƘI: 89, 119

1, 2. (a) Me ya sa misalin Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba zai iya ƙarfafa mu? (b) A wane irin yanayi ne Ezekiyel ya rubuta Ezekiyel 14:14?

KANA fuskantar matsaloli kamar rashin lafiya ko rashin kuɗi ko kuma tsanantawa? Shin yana yi maka wuya a wasu lokuta ka yi farin ciki a hidimarka ga Jehobah? Idan haka ne, misalin Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba zai iya taimaka maka. Me ya sa? Domin sun fuskanci irin matsalolin nan, amma sun kasance da aminci kuma sun yi wa Allah biyayya. Don hakan, za mu iya bin misalinsu.​—Karanta Ezekiyel 14:​12-14.

2 A shekara ta 612 kafin haihuwar Yesu ne Ezekiyel ya rubuta ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin a Babila. * (Ezek. 1:1; 8:1) An annabta cewa za a halaka Urushalima don suna bautar gumaka kuma hakan ya faru a shekara ta 607. A lokacin, mutane ƙalila ne suka tsira don sun bi misalin Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba. (Ezek. 9:​1-5) Irmiya da Baruch da Ebed-melek da kuma Rekabawa suna cikinsu.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Haka ma a yau, mutanen da za su tsira sa’ad da Jehobah ya halaka mugaye su ne masu aminci kamar Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba. (R. Yoh. 7:​9, 14) Don haka, bari mu tattauna dalilin da ya sa Jehobah ya ce waɗannan mutanen amintattu ne. Sa’ad da muke tattauna misalansu, za mu ga (1) matsalolin da kowannensu ya fuskanta (2) da kuma yadda za mu bi misali mai kyau da suka kafa.

NUHU YA KASANCE DA AMINCI HAR SHEKARA ƊARI TARA

4, 5. Waɗanne matsaloli ne Nuhu ya fuskanta, kuma mene ne ya burge ka game da jimirinsa?

4 Matsalolin da Nuhu ya fuskanta. A lokacin da Anuhu yake raye, mutane suna yin abubuwan da Allah ba ya so. Har ma suna “maganganu na ɓatanci” game da Jehobah. (Yahu. 14, 15) Ban da haka, zalunci sai ƙaruwa yake yi. Hakan ya sa ‘duniya ta cika da zalunci.’ Ƙari ga haka, mala’iku sun canja siffarsu zuwa ta ’yan Adam kuma suka auri mata. A sakamako haka, sun haifi ’ya’ya manya-manya masu mugunta. (Far. 6:​2-4, 11, 12) Amma Nuhu ya bambanta da sauran mutanen. “Ya sami tagomashi a gaban Ubangiji. . . . [shi] mutum mai-adalci ne, marar-aibi ne cikin tsararakinsa: Nuhu yana tafiya tare da Allah.”​—Far. 6:​8, 9.

5 Babu shakka, kalaman nan sun nuna mana ko wane irin mutum ne Nuhu. Da farko, ka yi tunanin yawan shekarun da Nuhu ya yi yana bauta wa Allah a zamanin da ke cike da mugunta. Bai yi hakan shekaru 70 ko 80 ba, amma ya yi kusan shekaru 600 yana bauta wa Allah! (Far. 7:11) Na biyu, ka tuna cewa a zamanin, babu ikilisiyar da zai riƙa halartar taro don ya sami ƙarfafa kamar mu a yau. Kuma ’yan’uwansa ma ba bayin Jehobah ba ne. *

6. Ta yaya Nuhu ya nuna gaba gaɗi?

6 Nuhu ba mutumin kirki kawai ba ne. Amma shi “mai-shelan adalci” ne da gaba gaɗi kuma ya nuna cewa ya yi imani da Jehobah. (2 Bit. 2:5) Don haka, manzo Bulus ya ce game da Nuhu: “Ta bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta.” (Ibran. 11:​7, Littafi Mai Tsarki) Babu shakka, Nuhu ya fuskanci zolaya da kuma hamayya, wataƙila har da zalunci ma. Amma duk da haka, bai ji “tsoron mutum” ba. (Mis. 29:25) Maimakon haka, Jehobah ya taimaka masa ya kasance da gaba gaɗi.

7. Waɗanne matsaloli ne Nuhu ya fuskanta sa’ad da yake gina jirgi?

7 Bayan Nuhu ya yi fiye da shekaru 500 yana bauta wa Jehobah, sai Jehobah ya ce masa ya gina jirgi don ya ceci ’yan Adam da kuma dabbobi. (Far. 5:32; 6:14) Yin wannan aikin bai yi wa Nuhu sauƙi ba. Kuma ya san cewa yin aikin zai sa mutane su riƙa yi masa dariya kuma su tsananta masa. Amma duk da haka, “ya yi” duk abin da Allah ya umurce shi kuma ya yi hakan da bangaskiya.​—Far. 6:22.

8. A waɗanne hanyoyi ne Nuhu ya gaskata cewa Jehobah zai yi masa tanadi?

8 Wata matsala kuma da Nuhu ya fuskanta ita ce yi wa iyalinsa tanadi. Kafin ambaliyar, noma tana wahalar da mutane sosai, kuma hakan ya shafi Nuhu ma. (Far. 5:​28, 29) Duk da haka, Nuhu bai fi mai da hankali ga yi wa iyalinsa tanadi ba. Har a lokacin da ya yi shekara 40 ko 50 yana gina jirgi, ya mai da hankali ga ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Kuma ya ci gaba da yin hakan har tsawon shekara 350 bayan ambaliyar. (Far. 9:28) Hakika, Nuhu ya kafa misali mai kyau!

9, 10. (a) Ta yaya za mu bi misalin Nuhu? (b) Yaya Jehobah yake ɗaukan mutanen da suke bin ƙa’idodinsa?

9 Yadda za mu iya bin misalin Nuhu. Za mu iya yin hakan ta ƙin duk abin da Jehobah ya tsana, da kuma ƙin saka hannu a harkokin duniyar Shaiɗan. Maimakon haka, mu sa Mulkin Allah a kan gaba a rayuwarmu. (Mat. 6:33; Yoh. 15:19) Babu shakka, yin hakan zai sa mutane su tsananta mana. Alal misali, mutane suna yin baƙaƙen maganganu game da mu a kafofin yaɗa labarai domin muna bin dokar Allah game da aure da kuma jima’i. (Karanta Malakai 3:​17, 18.) Amma hakan bai dame mu ba don kamar Nuhu, Jehobah ne kaɗai muke bauta wa. Mun san cewa shi kaɗai ne zai iya sa mu yi rayuwa har abada.​—Luk. 12:​4, 5.

10 Kai kuma fa, za ka ci gaba da yin abin da Allah yake so ko da mutane suna maka dariya ko kuma kana fama da rashin kuɗi? Idan ka bi misalin Nuhu, za ka gaskata cewa Jehobah zai kula da kai.​—Filib. 4:​6, 7.

DANIYEL YA NUNA AMINCI DA BIYAYYA A BIRNIN DA BA A TSORON ALLAH

11. Wace babbar matsala ce Daniyel da abokansa suka fuskanta a Babila? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

11 Matsalolin da Daniyel ya fuskanta. Daniyel bawa ne a birnin Babila inda ake bautar gumaka da kuma sihiri sosai. Ban da haka ma, Babiloniyawa sun yi ma Yahudawa kallon reni, sun yi musu ba’a kuma sun yi hakan ma ga Allahnsu Jehobah. (Zab. 137:​1, 3) Hakika, hakan ya ɓata wa Yahudawa masu aminci rai, har da Daniyel ma! Ƙari ga haka, mutanen birnin suna sa wa Daniyel da abokansa Hananiah da Mishael da kuma Azariah ido don za a horar da su su riƙa yi wa sarki hidima. Kuma abincin sarki ake so su riƙa ci, amma wannan matsala ce babba don Daniyel ba ya so ya “ɓāta kansa da abincin sarki.”​—Dan. 1:​5-8, 14-17.

12. (a) Wane irin mutum ne Daniyel? (b) Yaya Jehobah ya ɗauke shi?

12 Akwai wasu ƙalubale kuma masu wuyan ganewa da Daniyel ya fuskanta. Da yake yana da basira sosai, sarkin ya ba shi wasu gata. (Dan. 1:​19, 20) Amma hakan bai sa shi girman kai ko kuma ya ji kamar kome da ya faɗa daidai ne ba. A maimakon haka, ya kasance mai tawali’u kuma ya nuna cewa Jehobah ne ya kamata a yaba wa. (Dan. 2:30) A lokacin da Daniyel yake matashi ne Jehobah ya ce yana cikin mutane masu aminci kamar Nuhu da Ayuba. Ya dace ne da Jehobah ya amince da Daniyel? E. Kuma Daniyel ya kasance da aminci har mutuwa. Wataƙila a lokacin da Daniyel yake kusan shekara 100 ne mala’ika ya ce masa: “Ya Daniel, kai mutum ƙaunatacce ƙwarai.”​—Dan. 10:11.

13. Wane dalili ne ya sa Jehobah ya taimaka wa Daniyel ya sami babban matsayi?

13 Da taimakon Jehobah, Daniyel ya zama ma’aikacin gwamnati a Babila har ma a lokacin da Midiya da Farisa suke riƙe da mulki. (Dan. 1:21; 6:​1, 2) Wataƙila Jehobah ya sa Daniyel ya sami matsayin nan ne don Daniyel ya taimaka wa mutanensa kamar yadda Yusufu ya yi a ƙasar Masar da kuma yadda Esther da Mordekai suka yi a Farisa. * (Dan. 2:48) Hakika, yadda Jehobah ya taimaka musu ya ƙarfafa Yahudawan da ke zaman bauta, har ma da Ezekiyel!

Jehobah yana daraja bayinsa amintattu (Ka duba sakin layi na 14, 15)

14, 15. (a) Ta yaya yanayinmu ya yi kama da na Daniyel? (b) Wane darasi ne iyaye a yau za su iya koya daga iyayen Daniyel?

14 Ta yaya za mu bi misalin Daniyel. A yau, muna rayuwa ne a duniyar da ke cike da lalata da kuma addinan ƙarya. Mutane suna bin tafarkin Babila Babba, wato addinan ƙarya da Littafi Mai Tsarki ya kira “gidan aljanu.” (R. Yoh. 18:2) Da yake mun fita dabam, hakan yana sa mutane su riƙa yi mana dariya kuma su tsananta mana. (Mar. 13:13) Amma, bari mu kusaci Jehobah Allahnmu kamar Daniyel. Idan muka nuna tawali’u kuma muka dogara ga Jehobah, za mu kasance da daraja a gabansa.​—Hag. 2:7.

15 A yau, iyaye za su iya koyan darasi daga iyayen Daniyel. Ta yaya? Daniyel ya yi girma a Yahudiya sa’ad da ake mugunta sosai, amma bai bar hakan ya shafe shi ba, don ya girma yana ƙaunar Allah. Iyayensa ne suka taimaka masa ya yi hakan, don sun rene shi yadda ya dace. (Mis. 22:6) Ƙari ga haka, sunan Daniyel yana nufin “Allah Shi ne Mai Shari’a” kuma sunan ya nuna cewa iyayensa suna ƙaunar Jehobah. Don haka, iyaye kada ku fid da rai amma ku ci gaba da koyar da yaranku cikin haƙuri. (Afis. 6:4) Ban da haka ma, ku riƙa yi musu addu’a kuma ku yi addu’a tare da su. Jehobah zai albarkace ku idan kuka yi iya ƙoƙarinku don ku taimaka musu su san shi.​—Zab. 37:5.

AYUBA YA KASANCE DA AMINCI DA BIYAYYA A KOWANE LOKACI

16, 17. Waɗanne matsaloli ne Ayuba ya fuskanta a rayuwarsa?

16 Matsalolin da Ayuba ya fuskanta. Ayuba ya fuskanci yanayi dabam-dabam a rayuwarsa. Kafin Ayuba ya fuskanci matsala, shi mutum ne da “ya fi dukan ’ya’yan gabas girma.” (Ayu. 1:3) Yana da arziki, ya yi suna kuma ana daraja shi. (Ayu. 29:​7-16) Amma duk da haka, Ayuba bai ji cewa ya fi kowa daraja ba ko kuma ba ya bukatar taimakon Allah. Hakan ya sa Jehobah ya ce Ayuba “kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.”​—Ayu. 1:8.

17 Rayuwar Ayuba ta canja ba zato ba tsammani. Ya yi hasarar dukiyarsa kuma hakan ya sa shi baƙin ciki har ya gwammace ya mutu. Me ya sa hakan ya faru? Shaiɗan ne ya yi ƙarya cewa Ayuba yana bauta wa Allah don albarkar da Allah yake masa. (Karanta Ayuba 1:​9, 10.) Jehobah bai ɗauki zargin da wasa ba. Amma ya ba Ayuba damar nuna cewa yana bauta masa da zuciya ɗaya.

18. (a) Mene ne ya burge ka game da amincin Ayuba? (b) Me muka koya game da Jehobah a yadda ya bi da Ayuba?

18 Shaiɗan ya kai wa Ayuba hari ta hanyoyi dabam-dabam, kuma hakan ya sa Ayuba tunanin cewa Allah ne yake sa shi shan wahala. (Ayu. 1:​13-21) Bayan haka, abokan Ayuba suka zo suna zagin sa cewa Allah yana hukunta shi ne don laifofinsa! (Ayu. 2:11; 22:​1, 5-10) Hakika a wasu lokuta, Ayuba ya yi wasu maganganun da ba su dace ba. Amma ya riƙe amincinsa kuma Jehobah ya fahimci yanayin da yake ciki. (Ayu. 6:​1-3) Jehobah ya ga yadda Ayuba ya riƙe amincinsa duk da irin wahalar da Shaiɗan ya jefa shi ciki. Bayan dukan abubuwan da Ayuba ya fuskanta, Jehobah ya ba shi ninki biyu na dukan hasarar da ya yi, kuma ya daɗa masa shekaru 140. (Yaƙ. 5:11) Ayuba ya ci gaba da bauta wa Allah da dukan zuciyarsa. Ta yaya muka san hakan? Domin bayan Ayuba ya yi shekaru da yawa da mutuwa ne Ezekiyel ya rubuta ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin.

19, 20. (a) Ta yaya za mu bi misalin Ayuba? (b) Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da wasu kamar yadda Jehobah ke yi?

19 Yadda za mu bi misalin Ayuba. Ko da muna cikin mawuyacin hali, muna bukatar mu riƙa dogara ga Jehobah. Mu riƙa yi masa biyayya kuma mu nuna cewa shi muka fi daraja a rayuwarmu. A yau, muna da damar yin hakan fiye da Ayuba. Me ya sa? Domin mun san abubuwa da dama game da Shaiɗan da kuma dabarunsa. (2 Kor. 2:11) Littafi Mai Tsarki da kuma musamman littafin Ayuba, ya sa mu san dalilin da ya sa muke shan wahala. Annabcin Daniyel ya sa mu san cewa Mulkin Allah ainihin gwamnati ne kuma Yesu ne sarkin Mulkin. (Dan. 7:​13, 14) Ban da haka ma, mun san cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin zai kawo ƙarshen wahala.

20 Labarin Ayuba ya nuna mana cewa muna bukatar mu riƙa nuna wa ’yan’uwan da ke fuskantar matsala cewa mun damu da su. Suna iya faɗin abubuwan da ba su dace ba, kamar Ayuba. (M. Wa. 7:7) Amma maimakon yin tunanin da bai dace ba game da su, zai dace mu riƙa tausaya musu. Ta hakan, za mu nuna cewa muna yin koyi da Ubanmu Jehobah, mai jinƙai.​—Zab. 103:8.

JEHOBAH ‘ZAI KAFA KA’

21. Ta yaya 1 Bitrus 5:10 ya tuna mana matsalolin da Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba suka fuskanta?

21 Ko da yake Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba ba su yi rayuwa a lokaci ɗaya ba, dukansu sun jimre matsaloli dabam-dabam. Labarinsu ya tuna mana da abin da manzo Bitrus ya ce: “Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, . . . zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.”​—1 Bit. 5:​10, LMT.

22. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

22 Abin da ke littafin 1 Bitrus 5:10 ya shafi bayin Allah a yau. Jehobah ya tabbatar wa bayinsa cewa zai ƙarfafa su. Babu shakka, dukanmu muna son Jehobah ya ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta masa. Don haka, ya kamata mu riƙa bin misalin Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba! A talifi na gaba, za mu ga cewa sanin Jehobah sosai ne ya taimaka musu su riƙe amincinsu. Ƙari ga haka, sun ‘fahimci’ dukan abin da yake son su yi. (Mis. 28:5) Mu ma za mu iya yin hakan.

^ sakin layi na 2 An kai Ezekiyel Babila a shekara ta 617. Kuma ya rubuta Ezekiyel 8:1–19:14 a “shekara ta shida” da yake Babila, wato a shekara ta 612.

^ sakin layi na 5 Mahaifin Nuhu, wato Lamek mutum ne mai aminci kuma ya mutu shekara biyar kafin Ambaliyar. Idan mahaifiyar Nuhu da ’yan’uwansa suna raye a lokacin Ambaliyar, babu shakka, ba su tsira ba.

^ sakin layi na 13 Wataƙila haka ma yake da abokan Daniyel guda uku da aka ba su babban matsayi.​—Dan. 2:49.