TALIFIN NAZARI NA 7
Ku Zama Masu Tawali’u Don Ku Faranta Ran Jehobah
“Ku nemi Yahweh, ya ku masu sauƙin kai na ƙasar . . . ku nemi sauƙin kai.”—ZAF. 2:3.
WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Ubangiji Nagari Ne’
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1-2. (a) Wane irin mutum ne Musa, kuma mene ne ya yi? (b) Me ya sa muke so mu zama masu tawali’u?
LITTAFI MAI TSARKI ya ce Musa mai sauƙin kai ne “fiye da kowane mutum a fuskar duniya.” (L. Ƙid. 12:3) Hakan yana nufin cewa Musa marar kuzari ne matsoraci kuma ba zai iya tsai da shawara ba? Haka wasu suke kwatanta mutum mai tawali’u. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Musa mutum ne mai kuzari, mai yin tsayin daka kuma mai ƙarfin hali. Da taimakon Jehobah ya je gaban sarkin Masar kuma ya ja-goranci Isra’ilawa wajen miliyan uku ta hamada. Ƙari ga haka, ya taimaka wa al’ummar ta yi nasara a kan maƙiyanta.
2 A yau, ba ma fuskantar irin matsalolin da Musa ya fuskanta, amma a kowace rana muna hulɗa da mutane ko kuma muna fuskantar yanayin da zai iya sa ya kasance da wuya mu nuna tawali’u. Duk da haka, muna da dalilai da za su sa mu yi ƙoƙarin zama masu tawali’u. Jehobah ya yi alkawari cewa “masu sauƙin kai za su gāji ƙasar.” (Zab. 37:11) Kana ganin kai mai tawali’u ne? Shin wasu za su iya cewa kai mai tawali’u ne? Kafin mu amsa waɗannan tambayoyin, muna bukatar mu san abin da kasancewa mai tawali’u yake nufi.
MENE NE TAWALI’U?
3-4. (a) Da mene ne za mu iya kwatanta tawali’u? (b) Waɗanne halaye huɗu ne muke bukata idan muna so mu zama masu tawali’u, kuma me ya sa?
3 Tawali’u * yana kamar kayan da aka yi wa zubi mai kyau. Ta yaya? Kamar yadda tela ke yin amfani da kalar zare dabam-dabam don ya yi zubi mai kyau, muna bukatar halaye masu kyau dabam-dabam domin mu zama masu tawali’u. Wasu daga cikin waɗannan halayen su ne sauƙin kai da biyayya da alheri da kuma ƙarfin hali. Me ya sa muke bukatar waɗannan halayen don mu faranta wa Jehobah rai?
4 Mutane masu tawali’u ne kaɗai suke yin nufin Allah. Ɗaya daga cikin nufin Allah shi ne mu zama masu sauƙin kai. (Mat. 5:5; Gal. 5:23) Idan muka yi nufin Allah, hakan yana sa Shaiɗan fushi sosai. Duk da cewa muna da tawali’u da kuma sauƙin kai, mutane da yawa a wannan duniyar sun tsane mu. (Yoh. 15:18, 19) Saboda haka, muna bukatar ƙarfin hali don mu yi tsayayya da Shaiɗan.
5-6. (a) Me ya sa Shaiɗan ya tsani masu tawali’u? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?
5 Mutum marar tawali’u yana da zafin rai, ba ya kame kansa idan ya yi fushi kuma ba ya biyayya ga Jehobah. Haka Shaiɗan yake. Shi ya sa ya tsani masu tawali’u domin suna fallasa halayensa. Ban da haka, suna nuna cewa shi maƙaryaci ne. Me ya sa? Domin duk abin da ya ce ko kuma ya yi, ba zai iya hana masu tawali’u bauta wa Jehobah ba!—Ayu. 2:3-5.
6 A waɗanne lokuta ne nuna tawali’u yake da wuya? Kuma me ya sa muke bukatar mu riƙa nuna tawali’u? Don mu amsa waɗannan tambayoyin, za mu tattauna misalin Musa da na Ibraniyawa uku da aka kai zaman bauta a Babila da kuma na Yesu.
LOKUTAN DA NUNA TAWALI’U YAKE DA WUYA
7-8. Mene ne Musa ya yi sa’ad da wasu ba su daraja shi ba?
7 Sa’ad da muka sami gata: Yana yi wa wasu masu iko wuya su nuna tawali’u, musamman ma sa’ad da wani da bai da iko kamar su ya ƙi daraja su ko kuma ya ce ba su tsai da shawarar da ta dace ba. Hakan ya taɓa faruwa da kai ne? Idan wani a iyalinka ya ƙi daraja ka fa? Mene ne za ka yi? Ka yi la’akari da yadda Musa ya bi da irin wannan yanayin.
8 Jehobah ya naɗa Musa ya ja-goranci al’ummar Isra’ila kuma ya ba shi ikon rubuta dukan dokoki da al’ummar za ta riƙa L. Ƙid. 12:1-13) Me ya sa Musa bai yi fushi ba?
bi. Babu shakka, Musa yana da goyon bayan Jehobah. Duk da haka, Maryamu ’yar’uwar Musa da kuma ɗan’uwansa Haruna sun yi masa ba’a domin matar da ya aura. Da a ce hakan ya faru da wasu da ke da iko kamar Musa, da sun yi fushi kuma sun ɗau fansa. Amma Musa bai yi fushi ba, maimakon haka, ya roƙi Jehobah ya warkar da Maryamu. (9-10. (a) Mene ne Jehobah ya taimaka wa Musa ya fahimta? (b) Mene ne magidanta da kuma dattawa za su iya koya daga misalin Musa?
9 Musa ya bar Jehobah ya horar da shi. Musa ba mai tawali’u ba ne shekaru 40 kafin wannan lokacin sa’ad da yake fadar sarkin Masar. A lokacin yana da zafin rai sosai, har ya kashe wani mutumin da yake ganin yana zaluntar wani. Musa ya ɗauka cewa Jehobah ya amince da abin da ya yi. Amma Jehobah ya ɗau shekaru 40 yana taimaka masa ya fahimci cewa yana bukatar tawali’u fiye da ƙarfin hali don ya ja-goranci Isra’ilawa. Ƙari ga haka, kafin ya zama mai tawali’u yana bukatar sauƙin kai da biyayya da kuma hankali. Ya koyi waɗannan halayen kuma hakan ya taimaka masa ya zama shugaba nagari.—Fit. 2:11, 12; A. M. 7:21-30, 36.
10 A yau, magidanta da kuma dattawa a ikilisiya suna bukatar su yi koyi da misalin Musa. Idan mutane ba su daraja ku ba, kada ku yi saurin fushi, ku nuna sauƙin kai ta wajen amince wa da kuskurenku. (M. Wa. 7:9, 20) Ku yi biyayya ga Jehobah ta wajen bin umurni game da yadda za ku magance matsaloli. Ƙari ga haka, a kowane lokaci ku riƙa ba mutane amsa a cikin sauƙin kai. (K. Mag. 15:1) Magidanta da kuma dattawa da suke bi da matsaloli a wannan hanyar suna faranta wa Jehobah rai. Ƙari ga haka, suna sa a kasance da salama kuma suna kafa misali mai kyau na nuna tawali’u.
11-13. Wane misali ne Ibraniyawa uku suka kafa mana?
11 Sa’ad da ake tsananta mana. Shugabanni sun daɗe suna tsananta wa bayin Jehobah. Suna iya tuhumar mu da “laifofi,” amma asalin dalilin da ya sa suke tuhumar mu shi ne don muna “yi wa Allah biyayya fiye” da mutane. (A. M. 5:29) Hakan yana iya sa mutane sun tsananta mana, su saka mu a kurkuku ko kuma su zalunce mu. Amma da taimakon Jehobah, ba ma ɗaukan fansa, a maimakon haka, muna kasancewa da kamun kai a duk jarrabawar da muke fuskanta.
12 Ka yi la’akari da misalin Ibraniyawa uku da aka kai su zaman bauta a Babila, * Sarkin Babila ya umurce su su bauta wa gunkin zinariya da ya kafa. A cikin sauƙin kai suka bayayya wa sarkin dalilin da ya sa ba za su bauta wa gunkin da ya kafa ba. Sun yi biyayya ga Allah duk da cewa sarkin ya yi barazanar ƙona su a wuta mai zafi sosai. Jehobah ya cece su nan take. Ibraniyawan nan ba su ƙi bauta wa gunkin domin sun san cewa Jehobah zai cece su ba. Maimakon haka, sun yi biyayya ga Jehobah ko da mene ne Jehobah ya ƙyale ya faru da su. (Dan. 3:1, 8-28) Misalinsu ya tabbatar mana da cewa mutane masu tawali’u suna da ƙarfin hali. Hakika, babu wani sarki ko barazana ko hukunci da zai sa mu daina nuna ‘cikakkiyar ƙauna’ ga Jehobah.—Fit. 20:4, 5.
wato Hananiya da Mishayel da Azariya.13 Sa’ad da aka jarraba amincinmu ga Allah, ta yaya za mu bi misalin Ibraniyawan nan? Muna bukatar mu kasance da sauƙin kai kuma mu gaskata cewa Jehobah zai kula da mu. (Zab. 118:6, 7) A cikin sauƙin kai, za mu mayar da martani ga waɗanda suke tuhumar mu da yin laifi. (1 Bit. 3:15) Amma ba za mu taɓa yin abin da zai ɓata dangantakarmu da Ubanmu mai ƙauna ba.
14-15. (a) Mene ne zai iya faruwa idan muna cikin damuwa? (b) Kamar yadda Ishaya 53:7, 10 ya nuna, me ya sa za mu iya cewa Yesu ne ya fi kasancewa da tawali’u sa’ad da yake cikin damuwa?
14 Sa’ad da muke cikin damuwa: Dukanmu muna da abubuwan dabam-dabam da ke sa mu damuwa. Wataƙila muna iya jin hakan kafin mu rubuta jarrabawa ko kuma don wani aiki da aka ba mu. Ƙari ga haka, muna iya damuwa don muna so mu je jinya. Sa’ad da muke cikin wannan yanayin, yana iya yi mana wuya mu nuna tawali’u. Abubuwan da a dā ba sa damun mu suna iya soma ɓata mana rai. Muna iya soma yi wa mutane baƙar magana ko kuma mu soma bi da su yadda bai dace ba. Idan ka taɓa samun kanka a wannan yanayin, ka yi la’akari da misalin Yesu.
15 A cikin watanni na ƙarshe da Yesu ya yi a duniya, ya damu sosai. Ya san cewa zai sha wahala kuma za a kashe shi. (Yoh. 3:14, 15; Gal. 3:13) Wasu watannin kafin ya mutu, ya ce ya damu sosai. (Luk. 12:50) Ban da haka, wasu kwanaki kafin ya mutu, Yesu ya ce: Yana ‘jin nauyi a ransa.’ Kalmomin da ya yi amfani da su sa’ad da yake gaya wa Allah abin da ke zuciyarsa sun nuna cewa yana da tawali’u sosai. Ya ce: “Ya Uba, ka ɗauke mini wannan lokaci? A’a, ai, dā ma na zo musamman domin wannan lokaci ne. Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” (Yoh. 12:27, 28) Sa’ad da lokaci ya yi, Yesu ya miƙa kansa ga maƙiyan Allah da gaba gaɗi, sai aka azabtar da shi, kuma aka kashe shi. Duk da cewa Yesu yana shan azaba kuma ya damu, ya yi nufin Allah cikin tawali’u. Babu shakka, Yesu ne ya fi kafa misalin nuna tawali’u duk da cewa yana cikin damuwa sosai!—Karanta Ishaya 53:7, 10.
16-17. (a) Ta yaya abokan Yesu suka jarabce shi? (b) Ta yaya za mu yi koyi da misalin Yesu?
16 A daren ƙarshe da Yesu ya yi a duniya, abokansa sun yi abin da ya jarraba tawali’unsa. Ka yi tunanin irin damuwar da Yesu yake ciki a daren nan. Zai iya riƙe amincinsa har ƙarshe kuwa? Da a ce bai riƙe amincinsa ba, da babu wanda zai kasance da begen yin rayuwa har abada. (Rom. 5:18, 19) Ban da haka ma, matakin da zai ɗauka yana iya shafan sunan Ubansa. (Ayu. 2:4) A lokacin da ya ci abinci na ƙarshe da manzanninsa, ‘gardama ta taso’ tsakanin mazannin game da “wane ne a cikinsu” ya fi girma. Yesu ya yi wa manzanninsa gyara sau da yawa a kan wannan batun! Amma hakan bai ɓata wa Yesu rai ba. Maimakon haka, ya nuna kamun kai. Yesu ya sake gaya musu irin halin da ya kamata su kasance da shi. Bayan haka, ya yaba musu domin ba su daina bin shi ba.—Luk. 22:24-28; Yoh. 13:1-5, 12-15.
17 Mene ne za ka yi idan ka sami kanka a irin wannan yanayin? Muna iya yin koyi da misalin Yesu, kuma mu kasance da sauƙin kai ko da muna cikin damuwa. Zai dace mu yi biyayya ga Jehobah kuma mu ci gaba da “haƙuri da juna.” (Kol. 3:13) Za mu yi biyayya ga wannan umurni idan mun tuna cewa mu ma mukan yi abubuwan da ke ɓata wa wasu rai. (K. Mag. 12:18; Yaƙ. 3:2, 5) Ban da haka, ka yaba wa mutane domin halayensu masu kyau.—Afis. 4:29.
ME YA SA MUKE BUKATAR MU RIƘA NUNA TAWALI’U?
18. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa masu tawali’u su tsai da shawarwari masu kyau, amma me ya kamata su yi?
18 Za mu tsai da shawarwarin da suka dace. Idan muna bukatar mu tsai da shawarwari masu wuya, Jehobah zai taimaka mana mu tsai da shawarar da ta dace. Amma zai yi hakan idan mu masu tawali’u ne. Jehobah ya yi alkawarin cewa zai “ji kukan marasa ƙarfi.” (Zab. 10:17) Amma ba shi ke nan ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: Jehobah “yakan bi da masu sauƙin kai, yakan bi da su a hanyar da take daidai, ya kuma koya musu hanyarsa.” (Zab. 25:9) Jehobah yana bi da mutanensa ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan * da “bawan nan mai aminci, mai hikima” yake tanadarwa. (Mat. 24:45-47) Wajibi ne mu amince da taimakon Jehobah ta wajen yin amfani da waɗannan abubuwan da kuma yin abin da muka koya da dukan zuciyarmu.
19-21. Wane kuskure ne Musa ya yi a Kadesh, kuma waɗanne darussa ne hakan ya koya mana?
19 Za mu guji yin kurakurai da yawa. Alal misali, Musa ya yi shekaru da yawa yana da tawali’u kuma ya faranta wa Jehobah rai. Amma sa’ad da suka kusan shiga ƙasar alkawari bayan sun yi shekara 40 suna yawo a jeji, sai Musa ya yi kuskure. Hakan ya faru jim kaɗan bayan ’yar’uwarsa, wataƙila wadda ta cece shi a Masar ta mutu kuma aka binne ta a Kadesh. Sai Isra’ilawa suka soma da’awa cewa an yasar L. Ƙid. 20:1-5, 9-11.
da su. A wannan lokacin suna “gunaguni” game da Musa don ba su da ruwa. Mutanen sun yi gunaguni duk da cewa Jehobah ya ba Musa ikon yin mu’ujizai da yawa kuma Musa ya yi musu ja-goranci shekaru da yawa. Ba rashin ruwa kaɗai ba ne ya sa suke gunaguni ba, amma suna gunaguni game da Musa sai ka ce shi ne ya sa suke ƙishirwa.—20 Musa ya yi fushi sosai kuma ya nuna rashin tawali’u. Maimakon ya yi wa dutsen magana yadda Jehobah ya umurce shi, ya yi wa mutanen magana da fushi kuma ya yabi kansa. Sai ya bugi dutsen sau biyu kuma ruwa ya soma zubowa. Fahariya da fushi sun sa Musa ya yi kuskure sosai. (Zab. 106:32, 33) Musa bai shiga Ƙasar Alkawari ba don ya yi rashin tawali’u na ɗan lokaci.—L. Ƙid. 20:12.
21 Misalin nan ya koya mana darasi mai muhimmanci. Na farko, wajibi ne mu riƙa kasancewa da tawali’u a kowane lokaci. Idan muka daina, za mu zama masu fahariya kuma hakan zai sa mu yi abin da bai da dace ba kuma mu yi magana a garaje. Na biyu, zai yi mana wuya mu kasance da tawali’u sa’ad da muke cikin matsi. Saboda haka, ya kamata mu ƙoƙarta mu zama masu tawali’u har a lokacin da muke cikin matsi.
22-23. (a) Me ya sa ya kamata mu ci gaba da zama masu tawali’u? (b) Mene ne ma’anar furucin da ke Zafaniya 2:3?
22 Za mu sami kāriya. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka dukan mugaye a duniya, kuma masu tawali’u ne za su rage. A wannan lokacin, za a yi zaman lafiya sosai a duniya. (Zab. 37:10, 11) Za ka kasance cikin waɗannan masu tawali’u kuwa? Za ka yi hakan idan ka bi umurnin Jehobah da annabi Zafaniya ya rubuta.—Karanta Zafaniya 2:3.
23 Me ya sa littafin Zafaniya 2:3 ya ce: “Wataƙila za a ɓoye ku”? Hakan ba ya nufin cewa Jehobah ba zai iya kāre waɗanda suke faranta masa rai kuma suke ƙaunar sa ba. Maimakon haka, yana nuna cewa muna bukatar mu ɗauki mataki idan muna so a kāre mu. Hakan zai taimaka mana mu tsira wa “ranar fushin” Jehobah. Kuma za mu rayu har abada idan muka ƙoƙarta yanzu don mu kasance da tawali’u kuma muka faranta ran Jehobah.
WAƘA TA 120 Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu
^ sakin layi na 5 Babu wanda aka haifa da tawali’u. Muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu kasance da tawali’u. Nuna tawali’u yana iya kasancewa da sauƙi sa’ad da muke mu’amala da mutanen da suke son salama, amma yana iya yi mana wuya mu yi hakan sa’ad da muke cuɗanya da mutane masu fahariya. A wannan talifin, za mu tattauna wasu matsalolin da muke bukatar mu shawo kansu idan muna so mu zama masu tawali’u.
^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Tawali’u. Mutane masu tawali’u suna da hankali kuma sa’ad da suke hulɗa da wasu suna nuna alheri kuma ba sa saurin fushi. Ƙari ga haka, ba sa fahariya, suna ganin wasu sun fi su daraja. Idan aka ce Jehobah mai tawali’u ne, hakan yana nufin cewa yana nuna ƙauna da kuma jinkai ga mutane da ba su kai shi iko ba.
^ sakin layi na 12 Babiloniyawa sun canja sunayen Ibraniyawa uku nan zuwa Shadrak da Meshak da kuma Abednego.—Dan. 1:7.
^ sakin layi na 18 Alal misali, ka duba talifin nan “Ka Tsai da Shawarwari da Ke Ɗaukaka Allah,” da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2011.
^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya ci gaba da zama mai tawali’u kuma ya yi wa almajiransa gyara a hankali bayan da suka yi mūsu game da wanda ya fi girma a cikinsu.