Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 6

“Miji Kuma Shi Ne Shugaban Matarsa”

“Miji Kuma Shi Ne Shugaban Matarsa”

“Miji kuma shi ne shugaban matarsa.”—1 KOR. 11:3.

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misali Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata ’yar’uwa ta yi wa kanta sa’ad da take son ta zaɓi wanda za ta aura?

DUKAN Kiristoci suna ƙarƙashin shugabancin Yesu Kristi wanda shi kamili ne. Amma, sa’ad da mace ta yi aure tana ƙarƙashin shugabancin mijinta wanda shi ajizi ne. Kuma hakan ba shi da sauƙi. Saboda haka, sa’ad da mace take yanke shawara a kan wanda za ta aura, ya kamata ta yi wa kanta tambayoyin nan: ‘Mene ne ya nuna cewa wannan ɗan’uwan zai zama shugaba nagari? Bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa? Idan ba haka ba, mene ne ya nuna cewa zai taimaka mana mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah?’ Hakika, zai dace ita ma ’yar’uwar ta bincika kanta da tambayoyin nan: ‘Waɗanne halaye ne nake da su da za su ƙarfafa aurenmu? Ni mai haƙuri da kuma karimci ce? Ina da dangantaka mai kyau da Jehobah?’ (M. Wa. 4:9, 12) Shawarwari masu kyau da mace ta yanke kafin ta yi aure ne za su taimaka mata ta ji daɗin aurenta.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 ’Yan’uwa mata da yawa sun kafa misali mai kyau a yi wa mazansu biyayya. Muna yaba musu kuma muna farin cikin bauta wa Jehobah tare da waɗannan mata masu aminci! Za mu tattauna waɗannan tambayoyi uku a wannan talifin: (1) Waɗanne matsaloli ne mata suke fuskanta? (2) Me ya sa mata za ta yi wa mijinta biyayya? (3) Wane darasi ne magidanta da matansu za su iya koya daga Yesu da Abigail da kuma Maryamu mahaifiyar Yesu?

WAƊANNE MATSALOLI NE MATAN AURE SUKE FUSKANTA?

3. Me ya sa dukan ma’aurata suke fuskantar matsaloli?

3 Aure kyauta ne mai kyau daga wurin Allah, amma mutane ajizai ne. (1 Yoh. 1:8) Shi ya sa Kalmar Allah ta ce ma’aurata “za su sha wahala a rayuwar nan.” (1 Kor. 7:28) Za mu tattauna wasu matsaloli da matan aure za su iya fuskanta.

4. Me ya sa mata za ta iya tunani cewa mijinta zai rena ta idan tana yi masa biyayya?

4 Wataƙila domin yadda aka rene mace, tana iya yin tunanin cewa mijinta zai rena ta idan tana yi masa biyayya. Wata ’yar’uwa mai suna Marisol da ke zama a Amirka ta ce: “A inda na yi girma, ana yawan gaya wa mata su riƙa ja da maza. Na san cewa Jehobah ya ba magidanta iko, ya ce mata su riƙa yi musu biyayya, kuma ya dace maza su riƙa daraja matansu. Duk da haka, yana mini wuya in riƙa daraja mijina domin wannan ra’ayin.”

5. Wane ra’ayin da bai dace ba ne wasu maza suke da shi game da mata?

5 Ban da haka, mace tana iya auran mutumin da yake ganin cewa mata ba su da amfani. Wata ’yar’uwa mai suna Ivon da take zama a Amirka ta Kudu ta ce: “A yankinmu, maza ne suke fara cin abinci kafin mata. Yara mata ne suke yin dahuwa da kuma wanke-wanke. Mahaifiyar ce da yara mata suke kai wa ’yan’uwansu maza abinci, domin an koya wa yara maza cewa su ne ‘suka fi iko a gida.’ ” Wata ’yar’uwa mai suna Yingling da ke zama a Asiya ta ce: “Akwai wani karin magana da ake yi a yarenmu da ke nufin cewa mata ba sa bukatar su sami ilimi. Amfaninsu shi ne su yi dukan aikace-aikace gida, kuma bai dace su gaya wa mazansu ra’ayinsu ba.” Mijin da yake da irin wannan ra’ayin da bai dace ba yana sa matarsa baƙin ciki, ba ya yin koyi da Yesu kuma ba ya faranta ran Jehobah.—Afis. 5:28, 29; 1 Bit. 3:7.

6. Mene ne matan aure suke bukatar su yi don su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah?

6 Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, Jehobah yana so magidanta su taimaka wa iyalinsu su bauta masa kuma su biya bukatunsu na zahiri da na motsin rai. (1 Tim. 5:8) Amma, ’yan’uwa mata suna bukatar su riƙa keɓe lokaci kowace rana don karanta Kalmar Allah da yin bimbini da kuma yin addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarsu. Hakan yana iya yi wa matan aure wuya domin sukan shagala da aiki kuma su ji kamar ba su da lokaci ko kuma ƙarfin yin waɗannan abubuwan. Keɓe lokacin yin waɗannan abubuwa yana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin Jehobah yana so kowannenmu ya ƙulla dangantaka mai kyau da shi.—A. M. 17:27.

7. Me zai sa ya yi wa mace sauƙi ta riƙa daraja da kuma yi wa mijinta biyayya?

7 Hakika, mace tana bukatar ta yi ƙoƙari sosai don ta riƙa yi wa mijinta da ajizi ne biyayya. Amma zai yi mata sauƙi ta yi hakan idan ta fahimci da kuma amince da dalilin da ya sa ya kamata ta riƙa daraja mijinta da kuma yi masa biyayya.

ME YA SA YA DACE MACE TA RIƘA YI WA MIJINTA BIYAYYA?

8. Kamar yadda aka nuna a Afisawa 5:22-24, me ya sa ya dace mace ta riƙa yi wa mijinta biyayya?

8 Ya kamata mace ta riƙa yi wa mijinta biyayya domin Jehobah ya ce ta yi hakan. (Karanta Afisawa 5:22-24.) Don ta amince da Ubanta da ke sama, ta san cewa yana ƙaunar ta kuma yana so ta yi abin da zai amfane ta.—M. Sha. 6:24; 1 Yoh. 5:3.

9. Mene ne zai faru sa’ad da ’yar’uwa ta bi umurnin Jehobah kuma ta yi biyayya ga mijinta?

9 Mutanen duniya suna ƙarfafa mata kada su bi ƙa’idodin Jehobah kuma su riƙa ganin cewa yin biyayya ga magidantansu zai jawo reni. Hakika, waɗanda suke ɗaukaka irin wannan ra’ayin ba su san Allah ba. Jehobah ba zai taɓa ba yaransa mata masu tamani umurnin da zai sa a riƙa rena su ba. ’Yar’uwa da take yin ƙoƙari sosai don ta bi umurnin Jehobah, za ta sa iyalinta su yi zaman lafiya. (Zab. 119:165) Kowa a iyalin zai amfana.

10. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga abin da Carol ta ce?

10 Matar da take wa mijinta biyayya tana nuna cewa tana ƙaunar Jehobah kuma tana daraja shi domin shi ne ya ba magidanta iko. Wata mai suna Carol da take zama a Amirka ta Kudu ta ce: “Na san cewa mijina zai yi kuskure, kuma na san cewa yadda na bi da shi sa’ad da ya yi kuskure zai nuna ko ina daraja dangantakata da Jehobah. Saboda haka, ina yin ƙoƙari in riƙa biyayya domin ina so in faranta ran Ubana da ke sama.”

11. Mene ne yake taimaka wa wata ’yar’uwa mai suna Aneese ta riƙa gafarta wa mijinta, mene ne za mu iya koya daga abin da ta ce?

11 Zai yi wuya mace ta riƙa daraja da kuma yi wa mijinta biyayya idan tana ganin bai damu da yadda take ji ba. Amma ga abin da wata ’yar’uwa mai suna Aneese take yi sa’ad da hakan ya faru. Ta ce: “Ina ƙoƙari kada in yi fushi. Nakan tuna cewa dukanmu muna yin kuskure. Burina shi ne in riƙa gafartawa yadda Jehobah yake yi. Sa’ad da na yi hakan, ina kasancewa da kwanciyar hankali.” (Zab. 86:5) Idan mace tana gafarta wa mijinta, zai riƙa mata sauƙi ta yi masa biyayya.

ME ZA MU IYA KOYA DAGA MISALAN DA KE LITTAFI MAI TSARKI?

12. Waɗanne misalai ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

12 Wasu mutane suna iya ganin cewa mai yin biyayya ba shi da ƙarfi. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da misalan mutane masu ƙarfin zuciya da suka yi biyayya. Ka yi la’akari da abin da za mu iya koya daga Yesu da Abigail da kuma Maryamu.

13. Me ya sa Yesu yake wa Jehobah biyayya? Ka bayyana.

13 Yesu yana yin biyayya ga Jehobah ba don ba shi da ilimi ko kuma iyawa ba. Yadda Yesu yake koyarwa a hanya mai sauƙi kuma mutane su gane ya nuna cewa yana da ilimi sosai. (Yoh. 7:45, 46) Jehobah ya san cewa Yesu yana da ilimi sosai. Don haka, ya bar Yesu ya yi aiki tare da shi wajen halittar kome a sama da kuma duniya. (K. Mag. 8:30; Ibran. 1:2-4) Bayan da Jehobah ya ta da Yesu daga matattu, ya ba shi “dukan iko a sama da kuma nan duniya.” (Mat. 28:18) Duk da cewa Yesu yana da ilimi sosai, ya dogara ga Jehobah ya yi masa ja-goranci. Me ya sa? Domin yana ƙaunar Ubansa.—Yoh. 14:31.

14. Mene ne magidanta za su iya koya daga (a) yadda Jehobah yake ɗaukan mata? (b) abin da ke littafin Karin Magana sura ta 31?

14 Abin da magidanta za su iya koya. Jehobah bai umurci mace ta riƙa yi wa mijinta biyayya domin yana ganin mata ba su da muhimmanci ba. Jehobah ya nuna hakan ta wajen zaɓan mata da maza su yi sarauta da Yesu. (Gal. 3:26-29) Jehobah ya nuna cewa ya amince da Ɗansa ta wajen ba shi iko. Hakazalika, miji mai hikima zai ba matarsa ikon yin wasu abubuwa. Kalmar Allah ta ce mace mai kirki za ta iya kula da gida, ta sayi gona ta yi shuki kuma ta riƙa kasuwanci. (Karanta Karin Magana 31:15, 16, 18.) Ita ba baiwa ba ce da ba za ta iya faɗin ra’ayinta ba. Maimakon haka, mijinta yana amincewa da ita kuma ya saurare ta. (Karanta Karin Magana 31:11, 26, 27.) Idan miji yana daraja matarsa, za ta yi farin cikin yi masa biyayya.

Mene ne mata masu kirki za su koya daga yadda Yesu ya yi wa Jehobah biyayya? (Ka duba sakin layi na 15)

15. Ta yaya matan aure za su iya yin koyi da Yesu?

15 Abin da mata za su iya koya. Duk da abubuwan da Yesu ya cim ma, bai yi tunanin ya fi ƙarfin yin biyayya ga Jehobah ba. (1 Kor. 15:28; Yoh. 14:28) Hakazalika, mace mai kirki da take yin koyi da Yesu ba za ta ɗauka cewa mijinta zai rena ta idan tana yi masa biyayya ba. Za ta tallafa wa mijinta ba domin tana ƙaunar shi kaɗai ba amma don tana ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi.

Abigail ta je ta sami Dauda bayan ta aika wa shi da sojojinsa abinci. Sai ta rusuna kuma ta roƙe shi kada ya ɗauki alhakin jini ta wajen rama abin da maigidanta ya yi masa (Ka duba sakin layi na 16)

16. Kamar yadda aka nuna a 1 Sama’ila 25:3, 23-28, waɗanne matsaloli ne Abigail ta fuskanta? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

16 Abigail tana da miji mai suna Nabal. Shi mutumi ne mai son kai da fahariya kuma ba ya nuna godiya. Duk da haka, Abigail ba ta yi ƙoƙarin kashe aurensu ba. Da ta yi shuru kuma ta bar Dauda da sojojinsa su kashe mijinta. Maimakon haka, ta ɗauki mataki don ta kāre Nabal da duk mutanen da ke gidansu. Babu shakka, Abigail ta nuna ƙarfin zuciya sa’ad da ta je wajen maza 400 masu ɗauke da makamai don ta tattauna matsalar da Dauda. Tana shirye ta nemi gafara don abin da mijinta ya yi. (Karanta 1 Sama’ila 25:3, 23-28.) Dauda ya fahimci cewa Jehobah ya yi amfani da wannan mata mai gaba gaɗi don ta ba shi shawara kuma ya hana shi yin kuskure mai tsanani.

17. Mene ne magidanta za su iya koya daga labarin Dauda da Abigail?

17 Abin da magidanta za su iya koya. Abigail mace ce mai hikima, kuma Dauda ya bi shawararta. Hakan ya taimaka masa kada ya kashe mutane marasa laifi. Hakazalika, miji mai hikima zai yi la’akari da ra’ayin matarsa sa’ad da yake so ya tsai da shawarwari masu muhimmanci. Wataƙila abin da ta faɗa zai taimaka masa kada ya yi kuskure.

18. Mene ne mata za su iya koya daga Abigail?

18 Abin da mata za su iya koya. Mace da take ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi za ta sa iyalinta su amfana ko da mijinta ba ya bauta wa Jehobah da kuma bin ƙa’idodinsa. Ba za ta nemi hanyar da ba ta dace ba don kashe aurensu. Maimakon haka, za ta riƙa yi wa mijinta biyayya kuma ta yi ƙoƙari ta sa mijinta ya koya game da Jehobah. (1 Bit. 3:1, 2) Ko da mijinta bai bauta wa Jehobah ba, Jehobah zai yi farin ciki cewa tana wa mijinta biyayya, kuma tana daraja shi.

19. A waɗanne yanayi ne mace ba za ta yi wa mijinta biyayya ba?

19 Mace mai yi wa mijinta biyayya ba za ta goyi bayan mijinta ba idan ya ce ta yi abin da bai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. Alal misali, idan mijin da ba ya bauta wa Jehobah ya gaya wa matarsa ta yi ƙarya ko sata ko kuma ta yi wasu abubuwan da Jehobah ba ya so, ba za ta yi masa biyayya ba. Dukan Kiristoci, har da matan aure za su fi yin biyayya ga Jehobah. Idan aka gaya wa ’yar’uwa ta yi abin da bai dace ba, ya kamata ta ƙi yin hakan, kuma ta bayyana dalilin cikin ladabi.—A. M. 5:29.

Ka duba sakin layi na 20 *

20. Ta yaya muka san cewa Maryamu tana da dangantaka na kud da kud da Jehobah?

20 Maryamu tana da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma ta san Nassosi sosai. Sa’ad da take tattaunawa da Alisabatu mahaifiyar Yohanna mai baftisma, Maryamu ta yi ƙaulin Nassosin Ibrananci fiye da sau 20. (Luk. 1:46-55) Ka yi la’akari da wannan: Duk da cewa Yusufu ya yi wa Maryamu alkawarin aure, mala’ikan Jehobah bai fara zuwa wajensa ba. Amma ya fara yi wa Maryamu magana kuma ya gaya mata cewa za ta haifi Ɗan Allah. (Luk. 1:26-33) Jehobah ya san Maryamu sosai kuma ya san cewa za ta ƙaunaci Ɗansa kuma ta kula da shi. Maryamu ta ci gaba da ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah har bayan mutuwar Yesu da kuma tashinsa zuwa sama.—A. M. 1:14.

21. Mene ne magidanta za su iya koya daga Maryamu?

21 Abin da magidanta za su iya koya. Miji yana farin ciki idan matarsa ta san Nassosi sosai. Ba ya fushi ko kuma ya soma tunani cewa tana so ta zama shugaban iyalin. Ya fahimci cewa idan ’yar’uwa ta san Littafi Mai Tsarki da kuma ƙa’idodin Allah, za ta iya taimaka wa iyalinta sosai. Hakika, ko da mace ta fi mijinta ilimin boko, shi ne yake da hakkin yin ja-goranci a Ibada ta Iyali da kuma sauran ayyukan ibada.—Afis. 6:4.

Waɗanne darussa game da yin nazari da bimbini mata za su iya koya daga Maryamu mahaifiyar Yesu? (Ka duba sakin layi na 22) *

22. Mene ne mata za su iya koya daga Maryamu?

22 Abin da matan aure za su iya koya. Wajibi ne mace ta riƙa yi wa mijinta biyayya, amma ita ce take da hakkin ƙarfafa bangaskiyarta. (Gal. 6:5) Saboda haka, wajibi ne ta keɓe lokacin yin nazari da bimbini. Hakan zai taimaka mata ta riƙa ƙaunar Jehobah da daraja shi kuma ta riƙa farin cikin yi wa mijinta biyayya.

23. Ta yaya matan da suke wa mazansu biyayya suke sa kansu da iyalinsu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya su amfana?

23 Matan da suke wa mazajensu biyayya domin suna ƙaunar Jehobah za su yi farin ciki. Ƙari ga haka, za su samu gamsuwa fiye da waɗanda suka ƙi amincewa da tsarin shugabanci da Jehobah ya kafa. Suna kafa wa matasa maza da mata misali mai kyau. Kuma suna sa a yi zaman lafiya a iyalinsu da kuma ikilisiya. (Tit. 2:3-5) A yau, mata ne suka fi yawa a cikin waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci. (Zab. 68:11) Dukanmu, muna da aiki mai muhimmanci da za mu yi a ikilisiya. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda kowannenmu zai yi wannan aikin.

WAƘA TA 131 ‘Abin da Allah Ya Haɗa’

^ sakin layi na 5 Jehobah yana so matar aure ta riƙa wa mijinta biyayya da kuma daraja shi. Mene ne hakan yake nufi? Mazaje Kiristoci da mata za su iya koyan yin biyayya daga wurin Yesu da kuma matan da aka rubuta labaransu a Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 68 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da Maryamu take tattaunawa da Alisabatu mahaifiyar Yohanna Mai Baftisma, ta yi ƙaulin Nassosin Ibrananci da ta haddace.

^ sakin layi na 70 BAYANI A KAN HOTUNA: Ya kamata matar aure ta keɓe lokacin yin nazarin Littafi Mai Tsarki don ta ƙarfafa bangaskiyarta.