Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 8

Mu Rika Farin Ciki Sa’ad da Muke Jimre Jarrabawa

Mu Rika Farin Ciki Sa’ad da Muke Jimre Jarrabawa

“’Yan’uwa, ku mai da kowace irin wahalar da ta same ku abin farin ciki.”—YAƘ. 1:2.

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda aka nuna a Matiyu 5:11, yaya ya kamata mu ji sa’ad da muke fuskantar jarrabawa?

YESU ya yi wa mabiyansa alkawari cewa za su yi farin ciki na gaske. Ya kuma ya gaya wa mutanen da ke ƙaunar sa cewa za su fuskanci jarrabawa. (Mat. 10:22, 23; Luk. 6:20-23) Muna farin cikin zama mabiyan Kristi. Amma, yaya muke ji sa’ad da iyalinmu suka hana mu bauta wa Jehobah ko gwamnati suke tsananta mana ko kuma abokan aikinmu da abokan makarantarmu suke ƙoƙarin sa mu yi abin da bai dace ba? Babu shakka, hakan zai iya tayar mana da hankali.

2 Mutane ba sa farin ciki sa’ad da ake tsananta musu. Amma abin da Kalmar Allah ta ce mu yi ke nan. Alal misali, almajiri Yaƙub ya rubuta cewa kada mu bar tsanantawa ta tayar mana da hankali, a maimakon haka, mu riƙa farin ciki. (Yaƙ. 1:2, 12) Yesu ma ya ce mu riƙa farin ciki sa’ad da ake tsananta mana. (Karanta Matiyu 5:11.) Ta yaya za mu ci gaba da farin ciki sa’ad da muke fuskantar jarrabawa? Za mu iya koyan darussa daga wasiƙar da Yaƙub ya rubuta wa Kiristoci a ƙarni na farko. Bari mu fara tattauna ƙalubalen da Kiristocin suka fuskanta.

WAƊANNE JARRABOBI NE KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO SUKA FUSKANTA?

3. Mene ne ya faru bayan da Yaƙub ya zama almajirin Yesu?

3 An soma tsananta wa Kiristoci a Urushalima jim kaɗan bayan da Yaƙub ɗan’uwan Yesu ya zama Kirista. (A. M. 1:14; 5:17, 18) Kuma a lokacin da aka kashe Istifanus, Kiristoci da yawa sun gudu daga birnin kuma suka watse zuwa “yankin Yahudiya da na Samariya” har Kubrus da Antakiya. (A. M. 7:58–8:1; 11:19) Babu shakka, almajiran sun jimre matsaloli sosai. Duk da haka, sun ci gaba da yin wa’azi a wuraren da suka je, kuma sun kafa ikilisiyoyi a dukan yankunan da ke ƙarƙashin Mulkin Roma. (1 Bit. 1:1) Amma bayan haka, sun fuskanci matsaloli da yawa.

4. Waɗanne matsaloli ne Kiristoci na farko suka jimre?

4 Kiristoci a ƙarni na farko sun fuskanci jarrabawa dabam-dabam. Alal misali, a wajen shekara ta 50, Sarkin Roma mai suna Kalaudiyus ya kori dukan Yahudawa daga Roma. Hakan ya sa Yahudawa da suka zama Kiristoci su ƙaura zuwa wasu wurare. (A. M. 18:1-3) A wajen shekara ta 61, manzo Bulus ya rubuta cewa mutane sun wulaƙanta ’yan’uwansa, sun saka su a kurkuku kuma an ƙwace dukiyoyinsu. (Ibran. 10:32-34) Ban da haka, wasu cikin Kiristoci sun yi fama da talauci da rashin lafiya.—Rom. 15:26; Filib. 2:25-27.

5. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa?

5 A shekara ta 62 kafin Yaƙub ya rubuta wasiƙarsa, ya san matsalolin da ’yan’uwansa suke fuskanta. Jehobah ya hure Yaƙub ya rubuta wa waɗannan Kiristoci wasiƙa don ya ba su shawarar da za ta taimaka musu su ci gaba da farin ciki sa’ad da suke fuskantar jarrabawa. Bari mu bincika wasiƙar Yaƙub kuma mu amsa waɗannan tambayoyin: Wane irin farin ciki ne Yaƙub yake maganarsa? Me zai iya sa Kirista ya daina farin ciki? Ta yaya hikima da bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya za su taimaka mana mu ci gaba da farin ciki duk da cewa muna fuskantar jarrabobi?

ME KE SA KIRISTA YA RIƘA FARIN CIKI?

Yadda ƙwan fitila yake kāre wuta daga iska, farin ciki da Jehobah yake ba mu yana ci a zuciyarmu (Ka duba sakin layi na 6)

6. Kamar yadda Luka 6:22, 23 suka nuna, me ya dace Kirista ya riƙa farin ciki sa’ad da yake fuskantar jarrabobi?

6 Mutane suna iya tunani cewa za su iya yin farin ciki idan suna da ƙoshin lafiya da kuɗi kuma iyalinsu suna zaman lafiya. Amma ruhun Allah ne ke sa mu yin irin farin cikin da Yaƙub ya ambata ba yanayinmu a rayuwa ba. (Gal. 5:22) Kirista zai yi farin ciki ko kuma ya samu gamsuwa idan ya san yana faranta ran Jehobah kuma yana yin koyi da Yesu. (Karanta Luka 6:22, 23; Kol. 1:10, 11) Za mu iya kwatanta wannan farin cikin da wutar fitila. Me ya sa? Domin ƙwan fitilar na kāre wutar daga iska. Hakazalika, za mu ci gaba da farin ciki ko da wane irin matsaloli ne muke fuskanta. Rashin kuɗi ko rashin lafiya ba zai hana mu yin farin ciki ba. Za mu ci gaba da farin ciki sa’ad da iyalinmu suke mana ba’a ko kuma tsananta mana. Za mu daɗa farin ciki a duk lokacin da mutane suke so su hana mu yin hakan. Jarrabobin da muke fuskanta don imaninmu sun tabbatar mana cewa mu almajiran Kristi ne. (Mat. 10:22; 24:9; Yoh. 15:20) Shi ya sa Yaƙub ya ce: “Yan’uwa, ku mai da kowace irin wahalar da ta same ku abin farin ciki.”—Yaƙ. 1:2.

Ana iya gwada jarrabobi da wutar da maƙeri yake yin amfani da ita don ya watsa takobi (Ka duba sakin layi na 7) *

7-8. Me ya sa bangaskiyarmu take yin ƙarfi sa’ad da ake jarraba mu?

7 Yaƙub ya ambata wani dalilin da ya sa Kiristoci suke jimre jarrabobi masu tsanani. Ya ce: ‘Wahalar nan [da] take gwada bangaskiyarku takan haifar da jimrewa.’ (Yaƙ. 1:3) Ana iya gwada jarrabobi da wutar da maƙeri yake yin amfani da ita don ya watsa takobi. Takobin yakan yi ƙarfi sosai sa’ad da aka sa shi a wuta kuma ya yi sanyi. Hakazalika, muna ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da muka jimre jarrabobi. Saboda haka, Yaƙub ya ce: “Jimrewarku kuma ya cika aikinsa, ya kai ku ga zaman natsatsu da cikakku.” (Yaƙ. 1:4) Za mu ci gaba da farin ciki idan mun ga cewa jarrabobi na ƙarfafa bangaskiyarmu.

8 A wasiƙar da Yaƙub ya rubuta, ya ambata wasu abubuwa da za su iya hana mu yin farin ciki. Waɗanne ƙalubale ke nan, kuma yaya za mu iya magance su?

ABIN DA ZA MU YI DON MU CI GABA DA FARIN CIKI

9. Me ya sa muke bukatar hikima?

9 Ƙalubale: Idan ba mu san abin da ya kamata mu yi ba. Sa’ad da muke fuskantar matsaloli, ya kamata mu nemi taimakon Jehobah don mu yi zaɓi mai kyau. Yin hakan zai taimaka wa ’yan’uwanmu kuma zai sa mu riƙe aminci. (Irm. 10:23) Muna bukatar hikima don mu san abin da za mu yi da kuma abin da ya kamata mu gaya wa waɗanda suke tsananta mana. Muna iya yin sanyin gwiwa idan ba mu san abin da za mu yi ba, kuma hakan zai iya sa mu baƙin ciki.

10. Mene ne Yaƙub 1:5 ta ce muke bukatar mu yi don mu sami hikima?

10 Abin da za mu yi: Ka roƙi Jehobah ya ba ka hikima. Idan muna so mu riƙa farin ciki sa’ad da muke fuskantar jarrabobi, wajibi ne mu roƙi Jehobah ya ba mu hikima don mu tsai da shawarwari masu kyau. (Karanta Yaƙub 1:5.) Me ya kamata mu yi idan muna ganin cewa Jehobah bai amsa addu’armu nan da nan ba? Yaƙub ya ce mu ci gaba da ‘roƙon’ Allah. Jehobah ba ya fushi idan mun ci gaba da roƙon sa ya ba mu hikima. Idan mun roƙi Ubanmu da ke sama ya ba mu hikima don mu jimre jarrabawa, zai ba mu “hannu sake.” (Zab. 25:12, 13) Yana ganin matsalolinmu, yana jin tausayinmu kuma yana a shirye ya taimaka mana. Babu shakka, hakan na sa mu farin ciki! Ta yaya Jehobah yake ba mu hikima?

11. Mene ne kuma za mu yi don mu sami hikima?

11 Jehobah ya ba mu Kalmarsa don mu kasance da hikima. (K. Mag. 2:6) Don mu sami irin wannan hikimar, muna bukatar mu yi nazarin Kalmar Allah da littattafanmu. Amma ba yin nazari kawai muke bukatar mu yi ba. Wajibi ne mu bi dokokin Jehobah. Yaƙub ya ce: “Ku zama masu aikata kalmar Allah, ba masu ji kawai ba.” (Yaƙ. 1:22) Idan muka bi ƙa’idodin Allah, za mu riƙa zaman lafiya da mutane, mu kasance da sanin yakamata kuma mu zama masu tausayi. (Yaƙ. 3:17) Waɗannan halayen za su taimaka mana mu ci gaba da farin ciki sa’ad da muke fuskantar jarrabawa.

12. Me ya sa ya dace mu san Littafi Mai Tsarki sosai?

12 Kalmar Allah tana kamar madubi don tana taimaka mana mu san gyarar da ya kamata mu yi. (Yaƙ. 1:23-25) Alal misali, bayan mun yi nazarin Kalmar Allah, za mu ga cewa muna bukatar mu rage yin fushi. Idan mutane suka yi abin da ya ɓata mana rai ko kuma muna fuskantar matsaloli, Jehobah zai taimaka mana mu kame kanmu. Za mu fi jimre da matsalolin da muke fuskanta idan muka natsu. Za mu yi tunani da kyau kuma mu tsai da shawarwari masu kyau. (Yaƙ. 3:13) Saboda haka, yana da muhimmanci mu san Littafi Mai Tsarki sosai!

13. Me ya sa ya dace mu yi nazarin mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki?

13 A wasu lokuta, sai mun yi kuskure ne muke sanin cewa bai dace ba mu yi abin da muka yi ba. Hanya mai kyau na samun hikima ita ce ta wajen koyan darasi daga kurakure da kuma nasarar da mutane suka yi. Shi ya sa Yaƙub ya ƙarfafa mu yi koyi da mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki kamar Ibrahim da Rahab da Ayuba da kuma Iliya. (Yaƙ. 2:21-26; 5:10, 11, 17, 18) Waɗannan bayin Jehobah masu aminci sun jimre da jarrabobi da za su iya sa su baƙin ciki. Yadda suka jimre ya nuna cewa Jehobah zai iya taimaka mana mu jimre.

14-15. Me ya sa ya kamata mu ɗauki mataki sa’ad da muka soma shakka?

14 Ƙalubale: Sa’ad da muke shakkar imaninmu. A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu fahimci wani abu da ke Kalmar Allah. A wasu lokuta kuma Jehobah ba ya amsa addu’armu yadda muke so. Hakan yana iya sa mu riƙa shakka. Idan ba mu ɗauki mataki ba, za mu raunana bangaskiyarmu da kuma dangantakarmu da Jehobah. (Yaƙ. 1:7, 8) Hakan zai iya hana mu shiga Aljanna.

15 Manzo Bulus ya kwatanta begenmu da anka. (Ibran. 6:19) Anka tana riƙe jirgin ruwa sa’ad da ake guguwa don kada jirgin ya bugi dutse. Amma ankar tana da amfani idan sarƙar da aka ɗaura a jikin jirgin ba ta tsinke ba. Yadda tsatsa take ɓata sarƙar da ke ankar ne, shakka take raunana bangaskiyarmu. Idan mutum mai shakka ya fuskanci tsanantawa, zai iya soma shakka cewa Jehobah zai cika alkawuransa. Idan mun yi rashin bangaskiya, za mu yi rashin begenmu. Yaƙub ya ce mai shakka “yana kama da raƙuman ruwan teku waɗanda iska take hurawa tana jujjuye su a ta ko’ina.” (Yaƙ. 1:6) Zai yi wuya mutumin da ke irin wannan yanayin ya yi farin ciki!

16. Me ya kamata mu yi idan muna shakka?

16 Abin da za mu yi: Ka daina shakka, ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ka ɗauki mataki nan da nan. A zamanin Iliya, mutanen Jehobah sun soma shakkar imaninsu. Iliya ya ce musu: “Don me kuke raba hankalinku biyu? Idan Yahweh shi ne Allah, ku bi shi. Amma idan Ba’al shi ne Allah, sai ku bi shi.” (1 Sar. 18:21) A yau ma, muna bukatar mu ɗauki mataki da gaggawa. Muna bukatar mu yi bincike don mu tabbatar wa kanmu cewa Jehobah ne Allah na gaskiya, Littafi Mai Tsarki Kalmarsa ce, kuma Shaidun Jehobah mutanensa ne. (1 Tas. 5:21) Yin hakan zai sa mu daina shakka, kuma zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan muna bukatar taimako, za mu iya gaya wa dattawa. Wajibi ne mu ɗauki mataki don mu ci gaba da bauta wa Jehobah!

17. Me zai iya faruwa idan muka yi sanyin gwiwa?

17 Ƙalubale: Idan mun yi sanyin gwiwa. Kalmar Allah ta ce: “In ka nuna jikinka ya mutu a ranar wahala, to, lallai ba ka da ƙarfi ke nan.” (K. Mag. 24:10) A Ibrananci, furucin nan “nuna jikinka ya mutu” yana iya nufin “yin sanyin gwiwa.” Idan ka yi sanyin gwiwa, za ka daina farin ciki.

18. Mene ne yake nufi mu jimre?

18 Abin da za mu yi: Ka dogara ga Jehobah don ya taimaka maka ka jimre. Muna bukatar mu kasance da ƙarfin zuciya don mu iya jimre jarrabobi. (Yaƙ. 5:11) Sa’ad da Yaƙub yake magana game da jimrewa, ya yi amfani da kalmar da ta kwatanta mutumin da ya yi tsayin dāka. Za mu iya yin tunanin sojan da ya yi tsayin dāka a bakin dāga, kuma ya ƙi ya ja-da-baya duk da cewa ana kawo masa hari.

19. Wane darasi ne za mu iya koya daga manzo Bulus?

19 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau a yin ƙarfin zuciya da kuma jimrewa. Akwai lokutan da ya yi sanyin gwiwa. Amma ya iya jimrewa domin ya dogara ga Jehobah ya ba shi ƙarfin da yake bukata. (2 Kor. 12:8-10; Filib. 4:13) Za mu sami ƙarfin zuciya kamar Bulus idan muka amince cewa muna bukatar taimakon Jehobah.—Yaƙ. 4:10.

KA KUSACI ALLAH DON KA CI GABA DA FARIN CIKI

20-21. Wane tabbaci ne muke da shi?

20 Wasu suna ganin cewa sa’ad da muke shan wahala, Allah ne ke mana horo, amma hakan ba gaskiya ba ne. Yaƙub ya tabbatar mana cewa: “Idan jarraba ta sami mutum, kada ya ce Allah ne ya jarrabce shi. Domin Allah ba ya jarrabtar kowa da mugunta, kuma ba ya yiwuwa a jarrabce shi.” (Yaƙ. 1:13) Idan mun tabbata da hakan, za mu riƙa kusantar Ubanmu da ke sama.—Yaƙ. 4:8.

21 Jehobah “ba ya canjawa.” (Yaƙ. 1:17) Ya taimaka wa Kiristoci a ƙarni na farko sa’ad da suke fuskantar jarrabobi, kuma zai taimaka wa kowannenmu a yau. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka samu hikima kuma ka kasance da bangaskiya da ƙarfin zuciya. Zai amsa addu’o’inka. Hakan zai sa ka kasance da tabbaci cewa zai taimaka maka ka ci gaba da farin ciki sa’ad da kake fuskantar jarrabobi!

WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe

^ sakin layi na 5 Littafin Yaƙub na ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana mu jimre sa’ad da muke fuskantar jarrabawa. Za a tattauna wasu cikinsu a wannan talifin. Wannan shawarar za ta taimaka mana mu jimre kuma mu ci gaba da farin ciki sa’ad da muke bauta wa Jehobah.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: ’Yan sanda sun kama wani ɗan’uwa a gidansa. Matarsa da ’yarsu suna kallo yayin da ’yan sandan suka tafi da shi. ’Yan’uwa a ikilisiyarsu sun yi ibada tare da ’yar’uwar da ’yarta sa’ad da ɗan’uwan yake kurkuku. Matar da ’yarta suna addu’a a kai a kai Jehobah ya ƙarfafa su don su jimre jarrabawar da suke fuskanta. Jehobah ya ba su kwanciyar hankali da ƙarfin zuciya. Hakan ya ƙarfafa su sosai kuma ya taimaka musu su ci gaba da farin ciki yayin da suke jimre matsalolinsu.