Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yin Aiki Tare da Allah—Abin Fari Ciki Ne

Yin Aiki Tare da Allah—Abin Fari Ciki Ne

“Muna fa aiki tare da shi, muna roƙonku kuwa kada ku karɓi alherin Allah banza.”—2 KORINTIYAWA 6:⁠1.

WAƘOƘI: 75, 74

1. Ko da yake Jehobah ne Maɗaukakin Sarki, wane gata ne ya ba wa ‘yan Adam?

JEHOBAH shi ne Maɗaukakin Sarki kuma shi ya halicci kome. Ƙari ga haka, yana da hikima da iko sosai. Ya taimaka wa Ayuba ya fahimci hakan, shi ya sa Ayuba ya ce: “Na sani kai kake da ikon yin dukan abu, ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.” (Ayuba 42:​2, Littafi Mai Tsarki) Jehobah yana iya yin dukan abin da yake so ba tare da taimakon wani ba. Amma saboda yana ƙaunar mu, ya gayyace mu mu yi aiki tare da shi don ya cim ma nufinsa.

2. Wane aiki mai muhimmanci ne Jehobah ya ba Yesu ya yi?

2 Allah ya halicci Ɗansa, Yesu kafin ya halicci sauran abubuwa har da ‘yan Adam. Jehobah ya ba wa Ɗansa gatan yin aiki tare da shi wajen halittar dukan abubuwa. (Yohanna 1:​1-3, 18) Manzo Bulus ya ce game da Yesu: “Gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da ke sama da abubuwan da ke ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko kursiyai, ko masu mulki, ko masarauta, ko masu iko, wato dukkan abubuwa an halicce su ne ta wurinsa.” (Kolosiyawa 1:​15-17) Jehobah ya ba wa Ɗansa aiki mai muhimmanci kuma ya gaya wa ‘yan Adam game da aikin. Wannan ba ƙaramin gata ba ne!

3. Mene ne Jehobah ya gaya wa Adamu ya yi, kuma me ya sa?

3 Jehobah ya gayyaci ‘yan Adam su yi aiki tare da shi. Alal misali, ya ba Adamu aikin ba wa dabbobi suna. (Farawa 2:​19, 20) Babu shakka, yin wannan aikin ya sa Adamu farin ciki sosai! Ya lura da siffar dabbobin da kuma halayensu sai ya ba kowanne sunan da ya dace da ita. Jehobah ne ya halicci dukan dabbobi, saboda haka yana da ikon ba su suna da kansa, amma ya nuna wa Adamu cewa yana ƙaunarsa ta wajen ba shi wannan gatan. Allah ya kuma ba Adamu aikin sa dukan duniya ta zama aljanna. (Farawa 1:​27, 28) Amma, daga baya Adamu ya yanke shawarar daina yin aiki tare da Allah, kuma hakan ya jawo masa da dukan ‘ya’yansa wahala sosai.​—⁠Farawa 3:​17-19, 23.

4. Ta yaya wasu suka yi aiki tare da Allah don ya cim ma nufinsa?

4 Daga baya, Allah ya gayyaci wasu mutane su yi aiki tare da shi. Nuhu ya gina jirgi da ya cece shi da iyalinsa a lokacin Rigyawa. Musa ya ‘yantar da al’ummar Isra’ila daga Masar. Joshua ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari. Sulemanu ya gina haikali a Urushalima. Maryamu ta zama mahaifiyar Yesu. Dukan waɗannan mutane masu aminci da wasu da yawa sun yi aiki tare da Jehobah don ya cim ma nufinsa.

5. Wane aiki ne Jehobah ya ba mu gatan yi, shin yana bukatar mu taimaka masa a yin wannan aiki ne? (Ka duba hoton da ke shafi na 27.)

5 A yau, Jehobah yana gayyatar mu mu yi iya ƙoƙarinmu don mu goyi bayan Mulkinsa. Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya bauta wa Allah. Ko da yanayinmu ya bambanta, dukanmu za mu iya yin wa’azin bisharar Mulkin. Jehobah zai iya yin wannan aikin da kansa, kuma ya yi wa ‘yan Adam magana kai tsaye daga sama. Ƙari ga haka, Yesu ya ce Jehobah zai iya sa duwatsu su gaya wa mutane game da Sarkin da kuma Mulkinsa. (Luka 19:​37-40) Amma Jehobah ya ba mu gatan zama ‘abokan aikinsa.’ (1 Korintiyawa 3:⁠9) Manzo Bulus ya ce: ‘Muna fa aiki tare da shi, muna roƙonku kuwa kada ku karɓi alherin Allah banza.’ (2 Korintiyawa 6:⁠1) Hakika, yin aiki tare da Allah babban gata ne. Bari mu ga wasu dalilan da suka sa hakan yake sa mu farin ciki.

YIN AIKI TARE DA ALLAH YANA SA MU FARIN CIKI

6. Ta yaya Ɗan Allah na farko ya kwatanta yadda ya ji sa’ad da ya yi aiki tare da Ubansa?

6 Yin aiki tare da Allah yana sa bayin Jehobah farin ciki. Kafin Ɗan Allah, wato Yesu ya zo duniya, ya ce: ‘Ubangiji ya yi ni tun farkon hanyarsa . . . Sa’annan ina nan wurinsa, gwanin mai-aiki ne: kowace rana ni ne abin daularsa, kullum ina farinciki a gabansa.’ (Misalai 8:​22, 30) Sa’ad da Yesu ya yi aiki da Ubansa, ya yi farin ciki domin ya cim ma abubuwa da yawa kuma ya san cewa Jehobah yana ƙaunarsa. Mu kuma fa?

Babu abin da yake sa gamsuwa kamar koya wa mutum gaskiyar Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 7)

7. Me ya sa yin wa’azin bishara yake sa mu farin ciki?

7 Yesu ya ce muna farin ciki sa’ad da muka ba da kyauta da kuma sa’ad da wani ya ba mu kyauta. (Ayyukan Manzanni 20:35) Mun yi farin ciki sa’ad da muka soma bauta wa Allah, amma me ya sa muke farin ciki sa’ad da muka yi wa mutane wa’azin bishara? Domin muna ganin yadda mutane suke farin ciki sa’ad da suka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kuma suka ƙulla dangantaka da Allah. Ƙari ga haka, muna farin ciki sa’ad da muka ga cewa sun canja ra’ayinsu da kuma salon rayuwarsu. Wa’azin bishara ce aiki mafi muhimmanci kuma shi ne aiki mafi gamsarwa da muke yi don hakan yana sa waɗanda suka zama abokan Allah su sami rai madawwami.​—⁠2 Korintiyawa 5:⁠20.

8. Mene ne wasu suka ce da ya nuna cewa suna farin cikin yin aiki tare da Jehobah?

8 Muna faranta wa Jehobah rai sa’ad da muka taimaka wa mutane su san shi, kuma mun san cewa Jehobah yana farin ciki saboda ƙoƙarce-ƙoƙarce da muke yi don mu bauta masa. Hakan yana sa mu ma farin ciki. (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Marco, wanda yake zama a Italiya ya ce: “Ina farin ciki matuƙa da sanin cewa ina iya ƙoƙarina a bautar Jehobah don ba zai manta da aikin da na yi ba.” Hakazalika, Franco, wanda yake hidima a Italiya ya ce: “Ta Kalmarsa da kuma sauran abubuwa da yake mana tanadinsa, Jehobah yana tuna mana kowace rana cewa yana ƙaunarmu kuma dukan abubuwa da muke masa suna da muhimmanci, ko da muna ganin cewa hakan ba shi da muhimmanci. Shi ya sa yin aiki tare da Allah yake sa ni farin ciki kuma ya sa rayuwata ta kasance da ma’ana.”

YIN AIKI TARE DA ALLAH YANA SA MU KUSACE SHI DA KUMA MUTANE

9. Wace dangantaka ce ke tsakanin Jehobah da Yesu, kuma me ya sa?

9 Sa’ad da muka yi aiki tare da waɗanda muke ƙauna, hakan yana sa mu kusace su. Mukan ƙara sanin halayensu. Muna sanin maƙasudai da suka kafa da kuma yadda suke ƙoƙari su cim ma hakan. Yesu ya yi aiki da Jehobah shekaru aru-aru. Hakan ya sa sun ƙaunaci juna sosai kuma ba abin da zai iya ɓata dangantakarsu. Yesu ya bayyana yadda dangantakarsu take sa’ad da ya ce: “Da ni da Ubana ɗaya ne.” (Yohanna 10:30) Hakika, suna da haɗin kai kuma sun yi aiki tare babu matsala.

Yin wa’azi yana ƙarfafa bangaskiyarmu domin yana sa mu tuna da alkawuran da Allah ya yi da kuma ƙa’idodinsa

10. Me ya sa yin wa’azi yake sa mu kusaci Allah da kuma mutane?

10 Yesu ya roƙi Jehobah ya kāre almajiransa. Me ya sa? Ya yi addu’a cewa: “Domin su zama ɗaya kamar mu.” (Yohanna 17:11) Idan muka yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Allah kuma muka yi wa’azin bishara, za mu fahimci halayensa masu ban sha’awa. Za mu koya abin da ya sa ya dace mu dogara ga Jehobah kuma mu bi ƙa’idodinsa. Kuma Allah zai kusace mu idan muka kusace shi. (Karanta Yaƙub 4:⁠8.) Muna kusantar ‘yan’uwanmu domin muna fuskantar irin matsalolin da suke fuskanta kuma abubuwan da suke sa mu farin ciki su ne suke sa ‘yan’uwanmu farin ciki. Ƙari ga haka, maƙasudanmu da nasu iri ɗaya ne. Muna yin aiki da farin ciki da kuma jimre da matsaloli tare. Wata ‘yar’uwa mai suna Octavia da ke Biritaniya ta ce: “Yin aiki tare da Jehobah yana sa in kusaci mutane.” Ta bayyana cewa yanzu abota da take yi da mutane ya dangana da maƙasudinsu da kuma burinsu wadda ya yi daidai da nata. Hakika, mu ma muna da ra’ayi ɗaya da nata. Sa’ad da muka ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ‘yan’uwanmu suke yi don su faranta wa Jehobah rai, hakan yana sa mu kusace su.

11. Me ya sa za mu ƙara kusantar Jehobah da kuma ‘yan’uwanmu a sabuwar duniya?

11 Muna ƙaunar Allah da kuma ‘yan’uwanmu a yanzu, amma za mu fi ƙaunarsu a sabuwar duniya. Ka yi tunanin aiki mai gamsarwa da za mu yi a nan gaba! Za mu marabci waɗanda aka ta da daga mutuwa kuma mu koya musu game da Jehobah. Za mu yi aiki don mu mai da duniya aljanna. Yin aiki tare yayin da muke kamiltattu a ƙarƙashin sarautar Kristi zai sa mu farin ciki sosai. Dukan ‘yan Adam za su kusaci juna da kuma Jehobah, wanda zai “biya wa kowane mai-rai muradinsa.”​—⁠Zabura 145:⁠16.

YIN AIKI TARE DA ALLAH YANA KĀRE MU

12. Ta yaya yin wa’azi yake kāre mu?

12 Muna bukata mu kāre dangantakarmu da Jehobah, domin muna rayuwa a duniyar Shaiɗan kuma mu ajizai ne. Saboda haka, yana da sauƙi mu soma yin tunani kamar mutanen duniya kuma mu soma yin abubuwa kamar su. Hakan yana kama da yin iyo a kogin da ruwan yake gudu kuma yana ƙoƙarin kai mu inda ba ma so. Saboda haka, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi iyo zuwa wani gefe. Hakazalika, muna bukatar mu yi ƙoƙari mu guji tasirin duniyar Shaiɗan. Ta yaya yin wa’azi yake kāre mu? Sa’ad da muke tattaunawa game da Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki, muna mai da hankali ga abubuwa da suke da muhimmanci da kuma nagari, ba abubuwa da za su ɓata dangantakarmu da Allah ba. (Filibbiyawa 4:⁠8) Yin wa’azi yana ƙarfafa bangaskiyarmu domin yana sa mu tuna da alkawuran da Allah ya yi da kuma ƙa’idodinsa. Ƙari ga haka, yana taimaka mana mu kasance da halayen da muke bukata don mu kāre kanmu daga Shaiɗan da kuma duniyarsa.​—⁠Karanta Afisawa 6:​14-17.

Muna kāre kanmu idan muka duƙufa a yin wa’azi da nazari da kuma yi wa ‘yan’uwa alheri, don hakan zai sa mu daina damuwa ainun game da matsalolinmu

13. Ta yaya wani Mashaidi a Ostereliya yake ji game da yin wa’azi?

13 Muna kāre kanmu idan muka duƙufa a yin wa’azi da nazari da kuma yi wa ‘yan’uwa nagarta, don hakan zai sa mu daina damuwa ainun game da matsalolinmu. Wani ɗan’uwa mai suna Joel da ke Ostareliya ya ce: “Yin wa’azi yana taimaka min in san wasu abubuwa da ke faruwa, kamar ƙalubale da mutane suke fuskanta da kuma yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya amfane ni. Yin wa’azi yana taimaka mini in yi ƙoƙari in zama mai tawali’u; hakan yana sa in dogara ga Jehobah da kuma ‘yan’uwanmu.”

14. Me ya sa yadda muke nace yin wa’azi ya nuna cewa ruhun Allah yana tare da mu?

14 Yin wa’azi yana sa mu kasance da tabbaci cewa ruhun Allah yana tare da mu. Alal misali, a ce an ba ka aikin raba wa mutane da ke yankinku burodi. Ba biyanka ake yi ba kuma za ka kashe kuɗin aljihunka don ka kai wa mutane wannan burodi. Ƙari ga haka, yawancin mutane ba sa son burodin, wasu ma sun tsane ka don kana kawo musu wannan burodin. Shin za ka daɗe kana yin wannan aikin? Ba da daɗewa ba za ka soma sanyin gwiwa. Wataƙila ba za ka jima kana wannan aikin ba. Amma, muna ci gaba da yin wa’azi babu fashi, duk da cewa muna amfani da kuɗinmu da lokacinmu kuma mutane suna mana ba’a wasu kuma suna fushi da mu. Hakan ya nuna cewa ruhun Allah yana tare da mu.

YIN AIKI TARE DA ALLAH YANA NUNA CEWA MUNA ƘAUNARSA DA KUMA MUTANE

15. Ta yaya yin wa’azin bishara ya shafi nufin Allah don ‘yan Adam?

15 Ta yaya yin wa’azin bishara ya shafi nufin Jehobah ga ‘yan Adam? Nufin Allah ne ‘yan Adam su yi rayuwa har abada kuma bai canja nufinsa ba sa’ad da ‘yan Adam suka yi zunubi. (Ishaya 55:11) Allah ya yi shirin yadda za a ‘yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Ta yaya? Yesu ya zo duniya kuma ya ba da ransa hadaya. Amma, wajibi ne ‘yan Adam su yi biyayya ga Allah don su amfana daga wannan hadayar. Saboda haka, Yesu ya koya wa mutane abin da Allah yake bukata a gare su, kuma ya ba almajiransa umurni su yi hakan. Idan muka yi wa mutane wa’azi kuma muka taimaka musu su zama abokan Allah a yau, muna aiki ne kai tsaye da Allah a shirin da yake yi don ya ceci ‘yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa.

16. Ta yaya yin wa’azi yake da alaƙa da umurnan Allah mafi muhimmanci?

16 Sa’ad da muka taimaka wa mutane su sami rai madawwami, hakan ya nuna cewa muna ƙaunarsu da kuma Jehobah. Don nufin Allah ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timotawus 2:⁠4) Sa’ad da wani Bafarisi ya tambayi Yesu umurnin da ya fi muhimmanci, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:​37-39) Ta wajen yin wa’azin bishara, muna bin waɗannan umurnan.​—⁠Karanta Ayyukan Manzanni 10:⁠42.

17. Yaya kake ji game da gatan yin wa’azin bishara?

17 Hakika Jehobah ya albarkace mu sosai domin ya ba mu aikin da ke sa mu farin ciki, da ke sa mu kusace shi da ‘yan’uwanmu da kuma kāre dangantakarmu da shi. Ƙari ga haka, wannan aikin yana ba mu zarafin nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma mutane. Jehobah yana da miliyoyin mutane a faɗin duniya, kuma yanayin dukansu ya bambanta. Amma ko da mu yara ne ko manya ko masu arziki ko talakawa ko masu ƙoshin lafiya ko kuma raunanu, muna yin iya ƙoƙarinmu mu yi wa mutane wa’azi. Ra’ayinmu ɗaya ne da wata ‘yar’uwa mai suna Chantel daga Faransa da ta ce: “Allah Maɗaukakin Sarki da kuma Mahaliccin dukan abubuwa, mai farin ciki, ya gaya mini: ‘Ki je, ki yi magana a madadina da zuciya ɗaya. Zan ƙarfafa ki, na ba ki Kalmata Littafi Mai Tsarki, ina tanadar miki taimako daga sama da kuma abokan aiki a duniya. Ƙari ga haka, ina koyar da ke kuma ina ba ki umurni a lokacin da ya dace.’ Hakika, babban gata ne mu yi aikin da Jehobah ya ba mu kuma mu yi aiki tare da Allahnmu!”