Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Za Mu Tafi Tare da Ku”

“Za Mu Tafi Tare da Ku”

“Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”—ZAKARIYA 8:⁠23.

WAƘOƘI: 65, 122

1, 2. (a) Mene ne Jehobah ya ce zai faru a zamaninmu? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu sami amsoshinsu a wannan talifin? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)

JEHOBAH ya ce, a zamaninmu “mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zakariya 8:23) Wannan ‘Bayahudin’ yana wakiltar waɗanda Allah ya shafe da ruhu mai tsarki. Ana kuma kiran su “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Mutane goma kuma suna wakiltar waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a duniya. Sun san cewa Jehobah ya albarkaci waɗannan shafaffu kuma suna ganin cewa gata ne su bauta wa Allah tare da shafaffun.

2 Kamar annabi Zakariya, Yesu ya ce mutanen Allah za su kasance da haɗin kai. Ya kwatanta waɗanda suke da begen zuwa sama da “ƙaramin garke” da kuma waɗanda suke da begen yin rayuwa a nan duniya da “waɗansu tumaki.” Amma Yesu ya ce dukan su za su zama “garke ɗaya” kuma su bi shi a matsayinsa na “makiyayi ɗaya.” (Luka 12:32; Yohanna 10:16) Tun da yake rukunin biyu ne, wasu suna iya yin tunani: (1) Shin waɗansu tumakin suna bukatar su san sunayen dukan shafaffu a yau? (2) Yaya ya kamata shafaffu su ɗauki kansu? (3) Idan wani a ikilisiyarmu ya soma cin gurasa da kuma shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu, yaya ya kamata in bi da shi? (4) Shin ya kamata in damu sa’ad da na ga adadin mutanen da ke cin gurasa da kuma shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu yana ƙaruwa? Za a amsa waɗannan tambayoyin a wannan talifin.

SHIN MUNA BUKATA MU SAN SUNAYEN DUKAN SHAFAFFU A YAU NE?

3. Me ya sa ba za mu iya sanin waɗanda za su kasance cikin 144,000 ba?

3 Shin waɗansu tumaki suna bukata su san dukan sunayen shafaffu a yau ne? A’a. Me ya sa? Domin ba wanda zai iya sani ko waɗannan za su sami ladarsu. [1] (Ka duba ƙarin bayani.) Ko da yake, Allah ya riga ya zaɓe su su je sama, za su sami ladarsu ne idan sun kasance da aminci. Shaiɗan ya san da haka, shi ya sa yake amfani da “annabawan ƙarya” don ya “ɓad da” su. (Matta 24:​24, Littafi Mai Tsarki.) Shafaffu ba su da tabbaci cewa za su sami ladansu har sai Jehobah ya bayyana musu cewa sun kasance da aminci. Jehobah ne yake yin hatimi na ƙarshe kuma yana yin haka kafin su mutu ko kuma gab da somawar “babban tsanani.”​—⁠Ru’ya ta Yohanna 2:10; 7:​3, 14.

Yesu ne Shugabanmu, kuma wajibi ne mu bi misalinsa kawai

4. Idan ba zai yiwu ba mu san sunayen dukan shafaffu da ke duniya a yau, ta yaya za mu “tafi tare” da su?

4 Idan ba zai yiwu a san dukan sunayen shafaffu da ke duniya ba, ta yaya waɗansu tumaki za su “tafi tare” da su? Littafi Mai Tsarki ya ce mutum goma za su ‘kama ƙafar wanda shi ke Bayahude, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.’ Wannan ayar Littafi Mai Tsarki ta ambata Bayahude guda ɗaya. Amma sa’ad da ta ce “ku” tana nufin mutane da yawa. Hakan yana nufin cewa Bayahuden ba mutum ɗaya ba ne kawai amma yana wakiltar rukunin shafaffu. Waɗansu tumaki sun san hakan, kuma suna bauta wa Jehobah tare da wannan rukunin. Ba sa bukatar su san sunayen kowa a wannan rukunin kuma su bi kowannen su. Yesu ne Shugabanmu, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne kawai za mu bi misalinsa.​—⁠Matta 23:⁠10.

YAYA YA KAMATA SHAFAFFU SU ƊAUKI KANSU?

5. Wane gargaɗi ne ya kamata shafaffu su yi tunani sosai a kai, kuma me ya sa?

5 Ya kamata shafaffu su yi tunani sosai a kan gargaɗin da ke 1 Korintiyawa 11:​27-29. (Karanta.) Ta yaya wani shafaffe zai ci gurasa kuma ya sha ruwan anab cikin “rashin cancanta” a taron Tuna Mutuwar Yesu? Idan mutumin bai kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah ba kuma saboda haka, ya yi rashin aminci, idan ya ci gurasar kuma ya sha ruwan anab, ba ya daraja Allah. (Ibraniyawa 6:​4-6; 10:​26-29) Wannan gargaɗin yana tuna wa shafaffu cewa wajibi ne su kasance da aminci idan suna so su sami “ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah cikin Kristi Yesu.”​—⁠Filibiyawa 3:​13-16.

6. Wane ra’ayi ne ya kamata Kiristoci shafaffu su kasance da shi game da kansu?

6 Bulus ya gaya Kiristoci shafaffu: “Ni fa, ɗaurarre cikin Ubangiji, ina roƙonku ku yi tafiya irin da ta cancanci kira da aka kiraye ku da ita.” Ta yaya ya kamata su yi hakan? Bulus ya ce: “Da dukan tawali’u da ladabi, da jimrewa, kuna haƙuri da junanku cikin ƙauna; kuna ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar ruhu cikin ɗaurin salama.” (Afisawa 4:​1-3) Ruhu mai tsarki na Jehobah yana taimaka wa bayinsa su zama masu tawali’u ba masu fahariya ba. (Kolosiyawa 3:12) Saboda haka, shafaffu ba sa ganin sun fi sauran mutane. Sun san cewa Jehobah ba ya ba wa shafaffu ruhu mai tsarki fiye da sauran bayinsa. Kuma ba sa ganin za su iya fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai fiye da kowa. Ƙari ga haka, ba za su taɓa gaya wa wani cewa an shafe shi kuma saboda haka ya soma cin gurasa da shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu ba. Maimakon haka, su masu tawali’u ne kuma sun san cewa Jehobah ne kawai zai iya zaɓan mutane su je sama.

7, 8. Mene ne Kiristoci shafaffu ba sa sa rai za a yi musu ba, kuma me ya sa?

7 Ko da yake shafaffu suna ganin gata ne da aka zaɓe su su je sama, ba sa ɗauka cewa mutane za su riƙa girmama su saboda wannan gatan ba. (Afisawa 1:​18, 19; karanta Filibiyawa 2:​2, 3.) Kuma sun san cewa Jehobah bai gaya wa kowa ba sa’ad da ya shafe su da ruhu mai tsarki ba. Saboda haka, shafaffe ba zai yi mamaki ba idan wasu ba su gaskata nan da nan cewa an shafe shi ba. Ya tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana kada mu yi saurin amince da mutum da ya ce Allah ya ba shi wani gata na musamman. (Ru’ya ta Yohanna 2:⁠2) Da yake shafaffe ba ya sa rai cewa mutane za su riƙa daraja shi fiye da sauran mutane, ba zai gaya wa mutanen da ya haɗu da su da farko cewa an shafe shi da ruhu mai tsarki ba. A wani lokaci ma, ba zai so ya gaya wa kowa ba. Kuma ba zai yi burga game da abubuwa masu ban al’ajabi da zai yi idan ya je sama ba.​—⁠1 Korintiyawa 1:​28, 29; karanta 1 Korintiyawa 4:​6-8.

8 Shafaffun Kiristoci ba sa gani cewa ya kamata su riƙa kasancewa tare da sauran shafaffu kawai ba, kamar suna cikin wani rukuni ne. Ba za su nemi wasu shafaffu ba don su tattauna game da matsayinsu na shafaffu ba, ko kuma su haɗu don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki su kaɗai ba. (Galatiyawa 1:​15-17) Ikilisiya ba za ta kasance da haɗin kai ba idan shafaffu suka yi hakan. Ƙari ga haka, yin hakan zai saɓa wa ruhu mai tsarki da ke taimaka wa mutanen Allah su kasance da salama da kuma haɗin kai.​—⁠Karanta Romawa 16:​17, 18.

YAYA YA KAMATA KA BI DA SU?

9. Me ya sa kake bukatar ka mai da hankali game da yadda kake bi da waɗanda suke cin gurasa da kuma sha ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu? (Ka duba akwati mai jigon nan: “ Ƙauna ‘Ba Ta Yin Rashin Hankali.’”)

9 Yaya ya kamata ka bi da ‘yan’uwa shafaffu? Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku duka kuwa ‘yan’uwa ne.” Ya ci gaba da cewa: “Dukan wanda za ya ɗaukaka kansa za ya ƙasƙanta; dukan wanda ya ƙasƙantar da kansa kuwa za ya ɗaukaka.” (Matta 23:​8-12) Saboda haka, ba zai dace ba mu riƙa girmama mutum ainun, ko da shi shafaffe ne. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da dattawa, ya ƙarfafa mu mu yi koyi da bangaskiyarsu, amma bai ce mana mu mai da wani ɗan Adam shugabanmu ba. (Ibraniyawa 13:⁠7) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce wasu “sun isa bangirma ninki biyu.” Amma hakan domin suna aiki tuƙuru wajen yin magana “da koyarwa,” ba domin an shafe su da ruhu mai tsarki ba. (1 Timotawus 5:17) Idan muna yaba wa shafaffu ainun da kuma ɗaukaka su, ba za su ji daɗi ba. Ban da haka, muna iya sa su zama masu girman kai. (Romawa 12:⁠3) Babu wani a cikinmu da zai so ya yi wani abu da zai sa wani shafaffe ya yi irin wannan babban kuskure!​—⁠Luka 17:⁠2.

Yaya ya kamata ka bi da wanda yake cin gurasa da kuma shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu? (Ka duba sakin layi na 9-11)

10. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja Kiristoci shafaffu?

10 Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja waɗanda Jehobah ya shafa da ruhu mai tsarki? Bai kamata mu tambaye su yadda suka zama shafaffu ba. Hakan bai shafe mu ba kuma ba mu da ikon mu sani. (1 Tasalonikawa 4:11; 2 Tasalonikawa 3:11) Ƙari ga haka, bai kamata mu yi tunani cewa mazajensu ko matansu ko kuma danginsu shafaffu ne kamar su ba. Wannan gatan ba gado ba ne. (1 Tasalonikawa 2:12) Muna bukatar mu guji yin tambayoyin da za su ɓata wa mutane rai. Alal misali, bai kamata mu tambayi matar ɗan’uwan da aka shafe shi da ruhu mai tsarki yadda take ji game da yin rayuwa har abada a duniya ba tare da mijinta ba. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa a sabuwar duniya Jehobah zai “biya wa kowane mai-rai muradinsa.”​—⁠Zabura 145:⁠16.

11. Ta yaya muke kāre kanmu idan muka guji yin sha’awar mutane fiye da yadda ya kamata?

11 Za mu kāre kanmu idan muka guji daraja shafaffu fiye sauran ‘yan’uwa. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “munafukan ‘yan’uwan” suna iya kasancewa a cikin ikilisiya kuma su yi da’awa cewa su shafaffu ne. (Galatiyawa 2:​4, 5; 1 Yohanna 2:19) Ƙari ga haka, wataƙila wasu shafaffu ba za su kasance da aminci ba. (Matta 25:​10-12; 2 Bitrus 2:​20, 21) Saboda haka, idan muka guji yin sha’awar mutane fiye da yadda ya kamata, har da waɗanda aka shafe su da ruhu mai tsarki ko sanannu ko kuma waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah, ba za su rinjaye mu sa’ad da suka yi rashin aminci ko kuma suka daina yin tarayya da ikilisiya ba. A maimakon haka, za mu kasance da bangaskiya kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah. ​—⁠Yahuda 16.

SHIN YA KAMATA MU DAMU DA ADADIN SHAFAFFU NE?

12, 13. Me ya sa bai kamata mu damu da adadin mutanen da suke cin gurasa da kuma shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu ba?

12 Shekarun baya, adadin mutanen da suke cin gurasa da kuma shan ruwan anab ya ragu. Amma a kwanan nan, adadin yana ƙaruwa. Ya kamata mu damu da hakan ne? A’a. Bari mu ga abin da ya sa bai kamata mu damu ba.

13 “Ubangiji ya san waɗanda ke nasa.” (2 Timotawus 2:19) Jehobah ya san mutanen da ya shafe da ruhu mai tsarki, amma ‘yan’uwa da suke ƙirga adadin mutanen da ke cin gurasa da kuma shan ruwan anab a taron Tuna Mutuwar Yesu ba su sani ba. Saboda haka, adadin ya ƙunshi mutanen da suke ganin cewa su shafaffu ne amma Jehobah bai shafe su ba. Alal misali, wasu da suke cin gurasa da kuma shan ruwan anab sun daina daga baya. Wasu kuma wataƙila suna da wata matsalar da ta shafi tunaninsu kuma sun ɗauka cewa za su yi sarauta da Kristi a sama. Hakika, ba za mu iya sanin ainihin adadin shafaffu da suka rage a duniya ba.

14. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da adadin shafaffu da za su rage a duniya sa’ad da aka soma ƙunci mai girma?

14 Shafaffu za su kasance a wurare dabam-dabam a faɗin duniya a lokacin da Yesu zai zo ya tafi da su sama. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu zai “aika mala’ikunsa da babbar ƙara ta ƙafo, su kuma za su tattara zaɓaɓunsa daga ƙusurwoyi huɗu, daga wancan iyakar sama zuwa wannan.” (Matta 24:31) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a kwanaki na ƙarshe, shafaffu kaɗan ne za su rage a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Amma bai faɗi adadin shafaffu da za su rage sa’ad da aka soma ƙunci mai girma ba.

15, 16. Mene ne muke bukata mu sani game da shafaffu 144,000 da Jehobah ya zaɓa?

15 Jehobah ne yake yanke shawara a kan lokacin da ya kamata ya zaɓi shafaffu. (Romawa 8:​28-30) Jehobah ya soma zaɓan shafaffu bayan an ta da Yesu daga mutuwa. Kamar dai dukan Kiristoci na ƙarni na farko shafaffu ne. Ɗarurruwan shekaru bayan haka, yawancin mutane da suka yi da’awa cewa su Kiristoci ne ba su bi koyarwar Kristi da gaske ba. Duk da haka, a waɗannan shekarun, Jehobah ya shafe wasu Kiristoci ƙalilan da suka bi koyarwar Kristi. Yesu ya kwatanta waɗannan Kiristocin da alkama da suka girma tare da zawan ko kuma ciyawa. (Matta 13:​24-30) A kwanaki na ƙarshe, Jehobah ya ci gaba da zaɓan mutane da za su kasance cikin shafaffu 144,000. [2] (Ka duba ƙarin bayani.) Saboda haka, idan Allah ya yanke shawara cewa zai zaɓi wasu dab da ƙarshen zamani, mun san cewa yana yin abin da ya dace ne. (Ishaya 45:9; Daniyel 4:35; karanta Romawa 9:​11, 16.) [3] (Ka duba ƙarin bayani.) Wajibi ne mu yi hankali don kada mu zama kamar ma’aikatan da suka yi gunaguni game da yadda Ubangijinsu ya bi da waɗanda suka soma aiki a awa ta ƙarshe.​—⁠Karanta Matta 20:​8-15.

16 Ba dukan waɗanda suke da begen zuwa sama ba ne ke cikin “bawan nan mai-aminci.” (Matta 24:​45-47) Jehobah da Yesu suna amfani da mutane kalilan wajen ciyar da kuma koyar da mutane da yawa a yau kamar yadda suka yi a ƙarni na farko. Shafaffun Kiristoci kaɗan ne a ƙarni na farko suka rubuta littattafan Matta zuwa Ru’ya ta Yohanna. A yau, shafaffu kaɗan ne kawai ke da hakkin tanadar wa mutanen Allah “abincinsu a lotonsa.”

17. Mene ne ka koya daga wannan talifin?

17 Mene ne muka koya a wannan talifin? Jehobah zai ba wa yawancin mutanensa rai na har abada a duniya. Amma waɗanda za su yi sarauta da Yesu za su yi rayuwa a sama. Jehobah zai albarkaci dukan bayinsa, wato ‘Bayahuden’ da kuma “mutum goma.” Ya bukace su duka su bi umurni guda kuma su kasance da aminci. Wajibi ne dukansu su kasance da aminci, su bauta masa tare kuma su kasance da haɗin kai. Ƙari ga haka, dukansu na bukatar su yi aiki tuƙuru don a yi zaman lafiya a cikin ikilisiya. Yayin da ƙarshen yana gabatowa, bari mu ci gaba da bauta wa Jehobah kuma mu riƙa bin Kristi kamar garke ɗaya.

^ [1] (sakin layi na 3) Littafin Zabura 87:​5, 6, ya ce a nan gaba, wataƙila Jehobah zai bayyana sunayen mutanen da za su yi Mulki da Yesu a sama.​—⁠Romawa 8:⁠19.

^ [2] (sakin layi na 15) Ayyukan Manzanni 2:33 ta nuna cewa Yesu yana da hannu a shafe mutum da ruhu mai tsarki, amma Jehobah ne yake zaɓan mutumin.

^ [3] (sakin layi na 15) Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2007, shafaffuka na 30-31 a Turanci don ƙarin bayani.