Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—A Madagaska
WATA majagaba ’yar shekara 27 mai suna Sylviana ta ce: “Ina yin marmarin zuwa inda ake bukatar masu wa’azi, a duk lokacin da na ji labarin ʼyan’uwan da suka je wurin. Amma ina ganin cewa hakan ya fi ƙarfina.”
Shin kai ma kana ji yadda Sylviana ta ji? Kana son ka yi hidima a wurin da ake bukatar masu wa’azi amma kana ganin ba za ka iya yin hakan ba? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa! ’Yan’uwa da yawa sun shawo kan matsaloli kuma suka ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu wa’azi don su faɗaɗa hidimarsu kuma Jehobah ya taimaka musu. Don mu fahimci yadda Jehobah ya taimaka musu, bari mu ga abin da ke faruwa a Madagaska, wanda shi ne tsibiri na huɗu mafi girma a faɗin duniya.
A cikin sama da shekara goma da suka shige, masu shela da majagaba fiye da 70 sun ƙauro daga ƙasashe 11 * zuwa ƙasar Madagaska a Afirka don su yi wa’azi. Sun yi hakan domin mutanen suna son Littafi Mai Tsarki. Ban da haka ma, wasu masu shela da ke ƙasar sun ƙaura zuwa wuraren nan don su yi bishara. Bari mu ji labarin wasu daga cikinsu.
ME YA TAIMAKA MUSU SU DAINA TSORO DA SANYIN GWIWA?
Louis da Perrine ma’aurata ne da shekarunsu ya fi 30. Waɗannan ma’auratan sun ƙaura daga Faransa zuwa Madagaska don su yi wa’azi. Sun yi shekaru suna tunanin ƙaura zuwa wata ƙasa, amma matar ta yi jinkirin yin hakan. Ta ce: “Ina jin tsoron zuwa wuraren da ban taɓa zuwa ba. Ba na son barin iyalinmu da ikilisiyarmu da gidanmu da wuraren da na sani har da aikin da na saba yi. Wannan ita ce matsala da nake bukata in magance.” Amma a shekara ta 2012, Perrine ta magance matsalarta kuma suka ƙaura. Yaya take ji game da matakin da suka ɗauka? Ta ce: “Jehobah ya ƙarfafa ni sosai kuma hakan ya sa na ƙarfafa bangaskiyata.” Maigidanta ya ce: “Mun yi farin ciki sosai sa’ad da ɗalibanmu
guda goma suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu na farko da muka halarta a Madagaska!”Me ya taimaka musu su ci gaba da hidimarsu sa’ad da suke fuskantar matsaloli? Sun yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka musu su jimre. (Filib. 4:13) Louis ya ce: “Mun ga cewa Jehobah ya amsa addu’armu kuma ya ba mu ‘salama ta Allah.’ Don haka, mun mai da hankali ga yadda hidimarmu take sa mu farin ciki. Ban da haka ma, abokanmu suna tura mana saƙon imel da wasiƙu don su ƙarfafa mu.”—Filib. 4:6, 7; 2 Kor. 4:7.
Jehobah ya albarkaci Louis da Perrine don haƙurin da suka yi. Louis ya ce: “A watan Oktoba na 2014, an gayyace mu zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata * a Faransa. Halartan wannan makarantar gata ne da Jehobah ya ba mu da ba za mu taɓa mantawa da shi ba.” Da suka sauke karatu, sai aka tura su yin hidima a Madagaska wurin da suke kafin su je makarantar.
“ZA MU YI ALFAHARI DA KU!”
Wasu ma’aurata a Faransa masu suna Didier da Nadine, sun ƙaura zuwa Madagaska a shekara ta 2010 kuma a lokacin, shekarunsu sama da 50 ne. Didier ya ce: “Mun yi hidimar majagaba sa’ad da muke matasa. Bayan haka, sai muka haifi yara uku. Amma da suka girma, sai muka soma tunanin ƙaura zuwa wata ƙasa don mu yi wa’azi.” Nadine ta ce: “Ba na son in bar yarana, shi ya sa na yi jinkirin ƙaura. Amma yaranmu sun ƙarfafa mu, suka ce: ‘Idan kuka ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu wa’azi, za mu yi alfahari da ku!’ Abin da suka ce ne ya ƙarfafa mu mu ƙaura. Ko da yake muna nesa da yaranmu, muna farin ciki cewa muna yin hira da su a kai a kai.”
Koyan yaren Malagasy ya yi wa Didier da Nadine wuya. Da fara’a Nadine ta ce: “Mu ba matasa ba ne.” Amma ta yaya suka yi nasara? Da farko, sun je ikilisiyar da ake Faransanci. Bayan wani lokaci, sai suka tsai da shawarar ƙaura zuwa ikilisiyar da ake yaren Malagasy. Nadine ta ce: “Mutane da yawa da muke haɗuwa da su a wa’azi suna son nazarin Littafi Mai Tsarki. A yawancin lokaci, suna gode mana don ziyarar da muke kai musu. Na ga kamar mafarki nake yi. Amma yanzu ina jin daɗin hidimar majagaba da nake yi a wannan yankin. Kowace safiya idan na farka, ina cewa, ‘Kai, yau ma zan ji daɗin wa’azi!’ ”
Didier yana murmushi sa’ad da yake ba da labarin abin da ya faru sa’ad da ya soma koyan yaren Malagasy. “Ina gudanar da taro a ikilisiya, amma ba na fahimtar amsar da ’yan’uwan suke bayarwa. Sai in riƙa gaya musu, ‘Mun gode’ don shi ne abin da na sani a yaren. Akwai wata rana da na gode wa wata ’yar’uwa da ta yi kalami, sai waɗanda suke zaune a bayanta suka yi min alama cewa amsar ba daidai ba. Nan da nan sai na kira wani ɗan’uwa kuma ya faɗi amsar, ko da yake ban san ko amsar da ya bayar daidai ne.”
TA AMINCE DA GAYYATARSU DA FARIN CIKI
Wani ɗan’uwa mai suna Thierry da matarsa Nadia sun halarci wani babban taro a shekara ta 2005, kuma sun ƙalli wasan kwaikwayo mai jigo “Ku Biɗi Maƙasudai Masu Ɗaukaka Allah.” Wasan kwaikwayon game da Timotawus ne kuma ya ƙarfafa su su ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu wa’azi sosai. Thierry ya ce: “Da ake kammala wasan kwaikwayon, sai na tambayi matata a kunne na ce, ‘Mu fa ina za mu je?’ Sai matata ta gaya min cewa ita ma abin da take tunaninsa ke nan.” Nan ba da daɗewa ba, sai suka soma ɗaukan wasu matakai don su cim ma hakan. Nadia ta ce, “A hankali muka soma sayar da kayanmu har ya rage wanda zai shiga jaka huɗu kawai!”
Sun ƙaura zuwa Madagaska a shekara ta 2006 kuma sun ji daɗin hidimarsu tun rana ta farkon da suka je wurin. Nadia ta ce, “Mutanen da muke haɗu da su a wurin suna sa mu murna sosai.”
Amma bayan shekara shida, waɗannan ma’auratan sun fuskanci wata matsala. Mahaifiyar Nadia mai suna Marie-Madeleine da ke zama a Faransa ta faɗi ta karye hannu kuma ta ji ciwo a kanta. Bayan da suka yi magana da likitan mahaifiyar Nadia, sai suka kawo ta Madagaska don ta zauna tare da su. Ko da yake shekarunta 80 ne, ta amince ta zo ta zauna da su. Yaya ta ji game da zuwa wata ƙasa? Ta ce: “A wasu lokuta yana da wuya mutum ya saba da wata ƙasa, amma ko da yake ba ni da ƙoshin lafiya, ina wasu hidimomi a ikilisiyar. Kuma abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne cewa ƙaurar da na yi ya taimaka wa ’yata da mijinta su ci gaba da hidimarsu.”
“NA GA YADDA JEHOBAH YA TAIMAKA MINI”
Riana wani ɗan’uwa ne mai shekara 22. Ya yi girma ne a yankin Alaotra Mangoro a gabashin Madagaska. Da yake shi mai ilimi ne, ya so ya je jami’a. Amma bayan da ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sai ya canja ra’ayinsa. Ya ce: “Na yi ƙoƙari in gama makarantar sakandare da wuri kuma na yi wa Jehobah alkawari cewa idan na ci jarrabawar, zan soma hidimar majagaba.’ ” Bayan da Riana ya gama makarantar, sai ya cika alkawarin da ya yi. Ya ƙaura zuwa gidan wani ɗan’uwa majagaba, ya nemi aiki, sai ya soma hidimar majagaba. Ya ce: “Yin hidimar majagaba shawara ce mafi kyau da na taɓa yanke wa kaina.”
Amma dangin Riana ba su fahimci dalilin da ya sa ya ɗauki wannan matakin ba. Ya ce: “Mahaifina da kawuna da gwaggona sun ƙarfafa ni in je jami’a. Amma ba na son wani abu ya hana ni yin hidimar majagaba.” Bayan wani lokaci, Riana ya so ya ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Me ya sa ya so ɗaukan wannan matakin? Ya ce: “Ɓarayi sun shiga gidanmu kuma suka sace kayana da yawa. Wannan fashin da aka yi min ya sa na tuna da kalaman Yesu game da ajiye ‘dukiya a sama.’ Don haka, sai na soma ƙoƙarin tara dukiyata a sama.” (Mat. 6:19, 20) Sai ya ƙaura zuwa kudancin Madagaska da ake fama da rashin ruwa da yunwa. Yankin yana da nisan mil 800 daga wurin da yake zama. Wurin ne mutanen Antandroy suke zama. Me ya sa ya je wurin?
Wata ɗaya kafin a yi wa Riana sata, ya riga ya soma nazari da mutanen Antandroy guda biyu. Ya koyi wasu abubuwa a yarensu kuma ya soma tunani game da wasu mutanen Antandroy da ba su san Jehobah ba. Ya ce: “Sai na yi addu’a don Jehobah ya taimaka min in ƙaura don in taimaka wa mutanen Antandroy.”
Da Riana ya ƙaura, nan da nan sai ya fuskanci wata matsala. Bai samu aiki ba. Wani mutum ya tambaye shi: “Me ya sa ka ƙauro nan alhalin mutanen da suke nan suna zuwa neman aiki a garinku?” Bayan sati biyu, sai Riana ya tafi don ya halarci babban taro kuma yana ta tunanin abin da zai yi don bai da kuɗi. A rana ta ƙarshe na taron, sai wani ɗan’uwa ya saka ma Riana kuɗi a aljihunsa. Wannan kuɗin zai kai shi garin Antandroy har ma ya soma sana’ar sayar da kindirmo. Riana ya ce: “Jehobah ya taimaka min sosai a lokacin da nake bukatar taimako. Yanzu zan ci gaba da taimaka wa mutanen da ba su san Jehobah ba!” Akwai ayyuka da yawa a ikilisiyar. Riana ya ƙara da cewa: “Ina ba da jawabi ga jama’a kowane mako. Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa
don ya koyar da ni.” Har wa yau, Riana yana taimaka wa mutanen Antandroy da suke son Littafi Mai Tsarki don su koyi gaskiya game da Jehobah.“ALLAH NA GASKIYA” YA ALBARKACE SU
Jehobah ya tabbatar mana da cewa “dukan wanda ke so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka.” (Isha. 65:16, Littafi Mai Tsarki) Idan muka yi ƙoƙari don mu magance matsaloli da za su hana mu faɗaɗa hidimarmu, za mu sami albarka sosai. Ka yi la’akari da labarin Sylviana ’yar Madagaska da aka ambata a farkon wannan talifin. Ka tuna cewa tana ganin ba za ta iya ƙaura wurin da ake bukatar masu shela ba. Me ya sa ta yi wannan tunanin? Ta ce: “Ƙafana ɗaya ya fi ɗayan tsayi, don haka ina ɗingishi sa’ad da nake tafiya kuma nakan gaji sosai.”
A shekara ta 2014, sai Sylviana da wata majagaba mai suna Sylvie Ann suka ƙaura zuwa wani ƙauye mai nisan mil 53 daga wurin da suke. Sylviana ta cim ma maƙasudinta kuma ta sami albarka sosai duk da matsalolin da ta fuskanta. Ta ce: “A cikin shekara ɗaya da na yi ina hidima a wannan wurin, na yi nazari da wata mata mai suna Doratine kuma ta yi baftisma a taron da’ira.”
ZAN “TAIMAKE KA”
Kamar yadda kalaman waɗannan ʼyan’uwa ya nuna, idan muka magance matsaloli kuma muka faɗaɗa hidimarmu, za mu shaida alkawarin nan da Jehobah ya yi wa bayinsa cewa: ‘Zan ƙarfafa ka: in taimake ka.’ (Isha. 41:10) Ban da haka ma, za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Idan muka ba da kai kuma muka ƙaura zuwa wasu wurare a ƙasarmu ko kuma zuwa wata ƙasa, hakan yana sa mu koyi wasu ayyukan da za mu yi a sabuwar duniya. Kamar yadda Didier da aka ambata ɗazu ya ce, “yin hidima a wuraren da ake bukatar masu shela yana horar da mu don abubuwan da za mu fuskanta a nan gaba!” Muna ƙarfafa ’yan’uwa da yawa su yi wannan hidimar don su ma su sami wannan horarwa!
^ sakin layi na 4 Waɗanda suka ƙaura sun fito ne daga Kanada da Jamhuriyar Czech da Faransa da Jamus da Guadeloupe da Luxembourg da New Kaledoniya da Siwiden da Siwizalan da UK da kuma Amirka.
^ sakin layi na 8 Yanzu ana kiranta Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Kuma masu shela da suke hidima ta cikakken lokaci da suke wata ƙasa za su iya zuwa wannan makarantar a ƙasarsu ko kuma a wata ƙasa da ake gudanar da makarantar a yarensu.