Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

A zamanin dā, ana amfani da dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa don a sasanta dukan matsaloli?

E, A WASU lokuta. Bari mu yi la’akari da wata doka a littafin Kubawar Shari’a 24:​14, 15. Ayoyin sun ce: Ɗan ƙodago “wanda shi ke matalauci mabukaci ba za ka yi masa zalunci ba, ko ɗan’uwanka ne, ko kuwa na wajen baƙin da ke cikin ƙasarka . . . Kada ya yi ma Ubangiji kuka a kanka, ya zama maka zunubi kuma.”

Tulun da ke ɗauke da roƙon da manomin ya yi

An tono tulun da ke ɗauke da labarin wani mutumin da ya yi roƙo don a taimaka masa. Hakan ya faru ne a ƙarni na bakwai kafin haihuwar Yesu, kuma an tono tulun a kusa da birnin Ashdod. Wataƙila an rubuta wannan roƙon ne don wani manomin da ake zargin sa cewa bai kammala aikin da aka yi yarjejeniya da shi ba. An rubuta cewa: “Kwanakin baya, sa’ad da bawanka [wanda ya kawo ƙara] ya gama kai amfanin gona rumbu, sai Hoshayahu ɗan Shobay ya zo ya ƙwace tufafin bawanka. . . . Duka mutanen da muke aiki tare da su a cikin zafin rana za su ba da shaida cewa . . . abin da na faɗa gaskiya ne. Ni dai ban yi wani laifi ba. . . . Idan gwamna yana ganin ba aikinsa ba ne ya kwato mini tufafina, sai ya ji tausayi na ya yi haka! Don Allah kada ka yi banza da wannan batun don bawanka ba shi da tufafi.”

Wani ɗan tarihi mai suna Simon Schama, ya ce: “Wannan labarin ba kawai roƙon da wani ma’aikaci ya yi don a mayar masa da [tufafinsa] ba ne, amma ya nuna cewa wanda ya kawo ƙarar ya san ƙa’idodin da ke Littafi Mai Tsarki, musamman ma waɗanda suke littafin Levitikus da kuma Kubawar Shari’a game da zaluntar matalauta.”