Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Nuna Wace Irin Kauna Ce Ke Sa Mu Farin Ciki?

Nuna Wace Irin Kauna Ce Ke Sa Mu Farin Ciki?

“Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.”​—ZAB. 144:15.

WAƘOƘI: 111, 109

1. Me ya sa zamani da muke ciki ya bambanta da sauran?

MUNA rayuwa a zamani da ya yi dabam sosai. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa, Jehobah yana tara “taro mai girma . . . daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.” Za su zama “al’umma mai-ƙarfi” da ta ƙunshi mutane fiye da miliyan takwas masu farin ciki da suke “yi masa [Allah] bauta kuma dare da rana.” (R. Yoh. 7:​9, 15; Isha. 60:22) Tun da aka halicci ’yan Adam, ba a taɓa yin irin wannan adadin mutane da suke ƙaunar Allah da ’yan’uwansu ba.

2. Wace irin ƙauna ce mutane da suka ware kansu daga Allah suke nunawa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

2 Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya kuma annabta cewa a zamaninmu, mutanen da suka ware kansu daga Allah za su nuna ƙauna don son kai. Kuma manzo Bulus ya ce: A ‘kwanaki na ƙarshe . . .  mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, . . . mafiya son annashuwa da Allah.’ (2 Tim. 3:​1-4) Irin wannan ƙaunar ba ta jitu da ƙaunar da aka ce Kiristoci su riƙa nunawa ba, wato ƙaunar Allah. Mutane da suke son kansu kawai ba sa yin irin farin ciki da suka zato za su yi ba. A maimakon haka, irin wannan ƙaunar ta sa mutane a duniya sun zama masu son kansu kuma hakan ba ya sa su ji daɗin rayuwa.

3. Mene ne za mu bincika a wannan talifin, kuma me ya sa?

3 Bulus ya san cewa irin wannan ƙauna ta-son-kai za ta zama ruwan dare gama gari kuma za ta kasance da lahani ga Kiristoci. Shi ya sa ya gargaɗe mu cewa mu “bijire” daga waɗanda suke nuna ƙauna da ba ta dace ba. (2 Tim. 3:5) Amma ba yadda za mu daina cuɗanya gabaki ɗaya da irin waɗannan mutanen. Saboda haka, ta yaya za mu guji halayen mutanen duniya da ke ko’ina a yau kuma mu yi ƙoƙari mu faranta ran Jehobah, Allah mai ƙauna? Bari mu ga bambanci da ke tsakanin ƙauna da Allah yake nunawa da wadda aka ambata a 2 Timotawus 3:​2-4. Yin hakan zai taimaka mana mu bincika kanmu kuma mu ga yadda za mu nuna irin ƙauna da za ta sa mu samu gamsuwa da kuma farin ciki.

ZA KA RIƘA ƘAUNAR ALLAH KO KANKA NE?

4. Me ya sa ba laifi ba ne mu ƙaunaci kanmu daidai-wa-daida?

4 Manzo Bulus ya ce: “Mutane za su zama masu-son kansu.” Shin hakan yana nufin cewa laifi ne mu riƙa ƙaunar kanmu? A’a, ya dace mu yi ƙaunar kanmu daidai-wa-daida don Jehobah ya halicce mu mu riƙa yin hakan. Yesu ya ce: ‘Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.’ (Mar. 12:31) Idan ba ma ƙaunar kanmu, ba za mu ƙaunaci maƙwabtanmu ba. Littafi Mai Tsarki ya ƙara da cewa: ‘Mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa kansa yake ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma yakan ciyar da shi ya kuma kiyaye shi.’ (Afis. 5:​28, 29) Wannan Nassin ya nuna cewa ya dace mutum ya riƙa ƙaunar kansa daidai-wa-daida.

5. Ta yaya za ka kwatanta waɗanda suke ƙaunar kansu ainun?

5 Irin ƙaunar da aka ambata a 2 Timotawus 3:2 ba ta dace ba. Ƙauna ce da ke nuna son kai. Mutane da suke ƙaunar ƙansu ainun suna ɗaukan kansu fiye da yadda ya kamata. (Karanta Romawa 12:3.) Suna damuwa da kansu fiye da wasu. Idan suka yi kuskure, sukan ɗaura ma wasu laifi maimakon su amince da laifinsu. Irin mutane nan ba sa farin ciki sam.

6. Wane sakamako mai kyau ne muke samu don muna ƙaunar Allah?

6 Wasu masanan Littafi Mai Tsarki sun ce Bulus ya ambata son kai da farko domin son kai ne yake sa mutane su kasance da halayen banza. Amma irin ƙaunar da Allah yake son mu nuna tana sa mu kasance da halaye masu kyau. Irin waɗannan halaye su ne farin ciki da salama da haƙuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamewa. (Gal. 5:​22, 23) Wani marubucin zabura ya ce: “Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.” (Zab. 144:15) Jehobah, Allah ne mai farin ciki kuma mutanensa ma suna farin ciki. Bayin Jehobah suna farin ciki domin su masu bayarwa ne, ba sa kamar mutane masu son kai da suke son a riƙa ba su kyauta amma su ba sa bayarwa.​—A. M. 20:35.

Ta yaya za mu guji zama masu son kanmu? (Ka duba sakin layi na 7)

7. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu san ko muna ƙaunar Allah?

7 Ta yaya za mu san cewa muna son kanmu fiye da Allah? Ka yi tunanin shawara mai kyau da ke Filibiyawa 2:​3, 4: “Kada a yi kome domin tsatsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya mai da wani ya fi kansa; ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na waɗansu kuma.” Muna iya tambayar kanmu: ‘Ina bin wannan shawarar a rayuwata kuwa? Ina ƙoƙarin in yi abin da Allah yake so? Ina son in taimaka wa mutane a ikilisiyarmu da kuma a wa’azi?’ Ba shi da sauƙi mu ba da lokacinmu da kuma kuzarinmu. Hakan na bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu kuma mu sadaukar da kai. Amma za mu yi farin ciki sosai idan muka san cewa abin da muke yi yana faranta wa Jehobah rai.

8. Mene ne wasu suka yi don suna ƙaunar Allah?

8 Domin wasu suna ƙaunar Allah kuma suna so su bauta masa sosai, sun daina sana’ar da suke yi da zai sa su zama masu arziki. Ericka da ke Amirka likita ce amma ta tsai da shawarar yin hidimar majagaba, maimakon yin aikinta na likita. Ƙari ga haka, ita da mijinta sun yi hidima a ƙasashe da yawa. Ta ce: “Abubuwa da yawa da muka shaida sa’ad da muke taimaka wa mutane da ke yin wani yare, da kuma abokai da muka samu suna ƙarfafa mu sosai. Har ila ni likita ce, amma yin amfani da duk lokacina da kuzari wajen taimaka wa mutane a wa’azi da kuma biyan bukatun ikilisiya na sa ni farin ciki da kuma gamsuwa sosai.”

A SAMA ZA KA TARA DUKIYARKA KO A DUNIYA?

9. Me ya sa son kuɗi ba ya sa mutum farin ciki?

9 Bulus ya ce mutane za su zama “masu-son kuɗi.” Wasu shekaru da suka shige, wani majagaba a ƙasar Ireland yana ma wani mutum wa’azi game da Allah. Sai mutumin ya fito da walat, kuma ya ciro kuɗi ya nuna ma ɗan’uwan, ya ce da fahariya, “Ka ga wannan, shi ne allahna!” Ko da yake ba dukan mutane ba ne za su kasance da gaba gaɗin faɗin haka ba, amma duniya tana cike da mutanen da suke son kuɗi da kuma kayan duniya. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi cewa: “Wanda yake ƙaunar azurfa ba za ya ƙoshi da azurfa ba; wanda yake neman yalwa kuma ba za ya ƙoshi da ƙaruwa ba.” (M. Wa. 5:10) Irin waɗannan mutane za su so su riƙa samun ƙarin kuɗi, kuma neman tara kuɗi zai sa su jawo ma kansu “baƙin ciki mai-yawa.”​—1 Tim. 6:​9, 10.

10. Mene ne Agur ya rubuta game da wadata da talauci?

10 Hakika, dukanmu muna bukatar kuɗi don yana kāre mutum a wasu lokuta. (M. Wa. 7:12) Amma, shin mutum zai yi farin ciki idan yana da kuɗin biyan bukatarsa kawai? Ƙwarai kuwa! (Karanta Mai-Wa’azi 5:12.) Agur ɗan Jakeh ya ce: “Kada ka ba ni ko talauci ko wadata. Ka ciyar da ni da abincin da ke daidai bukatata.” Yana da sauƙi mu fahimci dalilin da ya sa wannan mutum ba ya so ya zama talaka tilis. Kamar yadda ya bayyana, ba ya son ya yi sata domin hakan zai ɓata sunan Allah. Amma me ya sa ya yi addu’a cewa ba ya son ya zama mai arziki? Ya ce: “Kada in ƙoshi, in musance ka, in ce, Wanene Ubangiji?” (Mis. 30:​8, 9) Wataƙila ka san wasu da suka dogara da wadatarsu maimakon Allah.

11. Wace shawara ce Yesu ya bayar game da kuɗi?

11 Waɗanda suke son kuɗi ba za su iya faranta wa Allah rai ba. Yesu ya ce: “Ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.” Amma, kafin ya ambata wannan, ya ce: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke fashi da sata: amma ku tara wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su fasawa su yi sata.”​—Mat. 6:​19, 20, 24.

12. Ta yaya sauƙaƙa rayuwarmu zai sa bauta wa Allah ya yi sauƙi? Ka ba da misali.

12 Bayin Jehobah da yawa suna ƙoƙari su sauƙaƙa rayuwarsu. Don sun ga cewa yin hakan yana ba su lokacin bauta wa Jehobah kuma hakan yana sa su farin ciki sosai. Wani ɗan’uwa mai suna Jack da ke Amirka ya sayar da babban gidansa kuma ya daina kasuwancin da yake yi domin shi da matarsa su sami damar yin hidimar majagaba. Ya ce: “Bai kasance mana da sauƙi mu sayar da gidanmu da kuma kayayyakinmu ba. Amma shekaru da yawa, nakan dawo daga aiki ina baƙin ciki don matsaloli da nake fuskanta a wurin aiki. Amma matata da take hidimar majagaba tana farin ciki a kowane lokaci. Takan ce, ‘Ina da shugaba mafi kirki!’ Amma, yanzu da nake hidimar majagaba, mu biyu muna yi wa Jehobah hidima.”

Ta yaya za mu guji zama masu son kuɗi? (Ka duba sakin layi na 13)

13. Mene ne zai taimaka mana mu bincika ra’ayinmu game da kuɗi?

13 Sa’ad da muka bincika ra’ayinmu game da kuɗi, muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Na yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da kuɗi kuma ina rayuwar da ta jitu da shawarar? Neman kuɗi ne ya fi muhimmanci a rayuwata? Na fi damuwa ne da abin duniya fiye da dangantakata da Jehobah da kuma mutane? Na gaskata cewa Jehobah zai biya bukatuna?’ Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehoba ba zai taɓa yasar da waɗanda suke dogara a gare shi ba.​—Mat. 6:33.

KANA ƘAUNAR JEHOBAH KO KANA SON ANNASHUWA?

14. Ta yaya za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da annashuwa?

14 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane da yawa a yau suna “son annashuwa.” Kamar yadda ba laifi ba ne mutum ya riƙa son kansa da kuma kuɗi daidai-wa-daida. Haka nan ma, ba laifi ba ne mutum ya yi annashuwa daidai-wa-daida. Jehobah ba ya so mu hana kanmu jin daɗin rayuwa ko kuma mu ƙi yin ayyuka masu kyau da za su sa mu farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa masu aminci cewa: Ka ‘yi tafiyarka, ka ci abincinka da murna, ka sha ruwan anab naka da farin ciki.’​—M. Wa. 9:7.

15. Wane irin annashuwa ne aka ambata a 2 Timotawus 3:4?

15 Littafin 2 Timotawus 3:4 ya ambata waɗanda suke son annashuwa amma ba sa tunawa da Allah. Ku lura cewa a yare na asali da aka rubuta ayar nan, ba a ce mutane za su so kuɗi fiye da Allah ba, domin hakan zai nuna cewa suna ɗan son Allah. Amma ayar ta ce ‘maimakon Allah.’ Wani marubuci ya ce: “Wannan [ayar] ba ta nufin cewa mutanen suna ɗan son Allah. Amma yana nufin cewa ba sa son Allah ko kaɗan.” Wannan gargaɗi ne ga mutanen da suke mutuwar son annashuwa! Furucin nan “son annashuwa” yana nufin mutanen da suka “shaƙe da . . . annashuwa ta wannan rai.”​—Luk. 8:14.

16, 17. Ta yaya Yesu ya nuna mana yadda za mu yi annashuwa yadda ya dace?

16 Yesu ya nuna mana yadda za mu yi annashuwa a hanyar da ta dace. Ya je bikin “ɗaurin aure” da kuma wani “babban biki.” (Yoh. 2:​1-10; Luk. 5:29) A wurin ɗaurin auren da aka yi ƙarancin ruwan anab, Yesu ya juya ruwa zuwa ruwan anab. Kuma a wani lokaci da masu tsattsauran ra’ayi suka ce bai kamata ya ci da kuma sha da wasu ba, ya ce ra’ayinsu bai dace ba.​—Luk. 7:​33-36.

17 Duk da haka, Yesu bai duƙufa ga rayuwar jin daɗi kawai ba. A maimakon haka, ya saka hidimarsa ga Jehobah a kan gaba kuma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya taimaka wa mutane. Ƙari ga haka, ya sha azaba kuma ya mutu don mutane su sami ceto. Yesu ya gaya ma waɗanda suke so su bi gurbinsa cewa: “Masu-albarka ne ku lokacin da ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farin ciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama: gama haka nan suka tsananta ma annabawan da suka rigaye ku.”​—Mat. 5:​11, 12.

Ta yaya za mu guji zama masu son annashuwa? (Ka duba sakin layi na 18)

18. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu bincika ko mun fi mai da hankali ga yin annashuwa?

18 Mene ne zai taimaka mana mu bincika ko mun fi mai da hankali ga yin annashuwa? Muna iya tambayar kanmu: ‘Shin jin daɗi ya fi halartan taro da kuma fita wa’azi muhimmanci a rayuwata? Ina shirye na yi sadaukarwa domin ina so in bauta wa Allah? Sa’ad da nake zaɓan nishaɗi, ina tunanin yadda Jehobah zai ji?’ Idan muna ƙaunar Allah, za mu guji dukan abubuwan da ba ya so da kuma abubuwan da muke gani cewa za su ɓata masa rai.​—Karanta Matta 22:​37, 38.

ABIN DA ZAI SA KA FARIN CIKI

19. Waɗanne mutane ne ba za su taɓa yin farin ciki da gaske ba?

19 Ya kai shekaru 6,000 da mutane suke shan wahala, amma ƙarshen duniyar Shaiɗan ya kusa. Duniya tana cike da mutane masu son kansu da son kuɗi da kuma son annashuwa. Ƙari ga haka, suna tunanin abin da za su iya samu kaɗai kuma sha’awoyinsu kawai ne suka saka a kan gaba. Irin waɗannan mutanen ba za su taɓa yin farin ciki da gaske ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-farin ciki ne shi wanda yake da Allah na Yakubu mai-taimakonsa, begensa kuwa yana ga Ubangiji Allahnsa.”​—Zab. 146:5.

20. Ta yaya yadda kake ƙaunar Allah yake sa ka farin ciki?

20 Bayin Allah suna daɗa ƙaunarsa, kuma adadinmu yana ƙaruwa a kowace shekara. Hakan ya nuna cewa Yesu yana sarauta a Mulkin Allah kuma nan ba da daɗewa ba, zai sa mu sami albarka sosai. Za mu sa Jehobah farin ciki, kuma mu ma za mu yi farin ciki sosai idan muka yi abin da ya ce mu yi. Waɗanda suke ƙaunar Jehobah za su yi farin ciki har abada! A talifi na gaba, za mu tattauna wasu halayen banza da son kai yake sa mutane su kasance da su. Kuma za mu ga yadda halaye masu kyau na bayin Jehobah ya bambanta da na mutanen duniya.