Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

Abin da Taron Tunawa Ya Koya Mana Game da Sarkinmu

Abin da Taron Tunawa Ya Koya Mana Game da Sarkinmu

“Wannan jikina ne. . . . Wannan jinina ne na cikar yarjejeniyar.”​—MAT. 26:​26-28.

WAƘA TA 16 Mu Yabi Jehobah Domin Ɗansa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Me ya sa muka san cewa Yesu zai koya mana yadda za mu tuna da mutuwarsa a hanya mai sauƙi? (b) Waɗanne halayen Yesu ne za mu tattauna?

ZA KA iya kwatanta abin da ake yi kowace shekara a taron Tuna da Mutuwar Yesu? Babu shakka, yawancinmu za mu iya tuna da abubuwa masu muhimmanci da ake yi a taron. Me ya sa? Domin yadda ake taron yana da sauƙi. Amma wannan taron yana da muhimmanci sosai. Saboda haka, muna iya yin wannan tambayar, ‘Me ya sa ake yin wannan taron a hanya mai sauƙi?’

2 Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, yakan koyar da abubuwa masu muhimmanci a hanyar da mutane za su fahimta. (Mat. 7:​28, 29) Hakazalika, ya koya mana yadda za mu tuna da mutuwarsa a hanya mai sauƙi. Bari mu yi tunani sosai a kan wannan jibin da wasu abubuwan da Yesu ya faɗa da kuma abin da ya yi. Hakan zai taimaka mana mu fahimci cewa Yesu mai tawali’u ne da ƙarfin hali kuma yana ƙaunar mu sosai. Ƙari ga haka, za mu koyi yadda za mu iya bin misalinsa.

YESU MAI TAWALI’U NE

Gurasar da ruwan inabin suna tuna mana cewa Yesu ya ba da ransa a madadinmu kuma yana sarauta yanzu a sama (Ka duba sakin layi na 3-5)

3. Ta yaya Matta 26:​26-28 ya nuna cewa taron Tuna da Mutuwar Yesu yana da sauƙi, kuma mene ne abubuwa biyu da ya yi amfani da su suke wakilta?

3 Yesu yana tare da manzanninsa guda 11 masu aminci sa’ad da ya kafa wannan taron Tuna da Mutuwarsa. Ya yi amfani da abincin da ya rage a Idin Ƙetarewa don ya yi wannan taron Tunawa. (Karanta Matiyu 26:​26-28.) Ya yi amfani da gurasa marar yisti da ruwan inabi da ya rage a idin. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa waɗannan abubuwa suna wakiltar jikinsa da jininsa da yake gab da bayarwa a madadinsu. Wataƙila manzanninsa ba su yi mamaki ba don yadda wannan taron yake da sauƙi. Me ya sa?

4. Ta yaya shawarar da Yesu ya ba Marta ta taimaka mana mu fahimci abin da ya sa Yesu ya yi taron Tunawa mai sauƙi?

4 Ka yi la’akari da abin da ya faru ’yan watanni kafin wannan jibin, wato a shekara ta uku na hidimar Yesu sa’ad da ya ziyarci abokansa Li’azaru da Marta da kuma Maryamu. Yesu ya koyar da su a wannan lokacin kuma Marta tana wurin, amma ba ta sauraron sa domin ta shagala da yawan dafe-dafe. Da Yesu ya lura da hakan, sai ya yi mata gargaɗi don ya taimaka mata ta san cewa bai kamata tana damuwa da abubuwa masu yawa ba. (Luk. 10:​40-42) ’Yan sa’o’i kafin Yesu ya ba da ransa, ya bi wannan shawarar da ya bayar kuma ya yi taron Tunawa mai sauƙi. Mene ne hakan ya koya mana game da Yesu?

5. Mene ne taron nan mai sauƙi da Yesu ya yi ya koya mana game da shi, kuma ta yaya ya jitu da abin da ke Filibiyawa 2:​5, 7, 8?

5 Yesu ya nuna cewa shi mai tawali’u ne a duk ayyukansa da kuma abin da ya faɗa. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa ya kasance da tawali’u a daren da aka kashe shi ba. (Mat. 11:29) Ya san cewa ya kusan miƙa ransa hadaya, kuma Jehobah zai ta da shi daga mutuwa don ya zama sarki a sama. Duk da haka, bai sa mutane su riƙa girmama shi ta wurin yin babban biki don tuna da mutuwarsa ba. Maimakon haka, ya gaya wa almajiransa cewa su riƙa tunawa da shi ta yin wannan taro mai sauƙi sau ɗaya a shekara. (Yoh. 13:15; 1 Kor. 11:​23-25) Wannan taro mai sauƙi da Yesu ya yi ya nuna cewa shi mai tawali’u ne. Muna farin ciki cewa tawali’u yana cikin halaye masu muhimmanci da Sarkinmu yake da su.​—Karanta Filibiyawa 2:​5, 7, 8.

6. Ta yaya za mu yi koyi da tawali’un Yesu sa’ad da muke fuskantar matsaloli?

6 Ta yaya za mu yi koyi da tawali’un Yesu? Za mu iya yin hakan ta wajen mai da hankali ga bukatun wasu fiye da namu. (Filib. 2:​3, 4) Ka tuna daren ƙarshe da Yesu ya yi a duniya kafin a kashe shi. Ya san cewa ba da daɗewa ba zai sha azaba sosai, amma duk da haka, ya damu da manzanninsa domin za su yi makoki bayan an kashe shi. Saboda haka, Yesu ya yi amfani da daren domin ya koyar da su, ya ƙarfafa su kuma ya taimaka musu. (Yoh. 14:​25-31) Ya nuna cewa ya fi damuwa da bukatun wasu. Hakika, wannan misali ne mai kyau!

YESU YANA DA ƘARFIN HALI

7. Ta yaya Yesu ya nuna ƙarfin hali bayan ya kafa taron Tuna da Mutuwarsa?

7 Jim kaɗan bayan Yesu ya kafa taron Tuna da Mutuwarsa, ya nuna cewa yana da ƙarfin hali sosai. Ta yaya? Yesu ya amince da nufin Ubansa duk da cewa ya san sakamakon yin hakan. Ya san cewa zai sha azaba kuma zai yi mutuwar wulaƙanci a matsayin mai saɓo. (Mat. 26:​65, 66; Luk. 22:​41, 42) Amma ya riƙe aminci domin yana so ya ɗaukaka sunan Jehobah. Ƙari ga haka, ya nuna cewa Jehobah ne ya cancanci ya yi sarauta kuma ya sa ’yan Adam da suka tuba su sami rai na har abada. Bugu da ƙari, Yesu ya shirya almajiransa domin abubuwan da za su fuskanta a nan gaba.

8. (a) Mene ne Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci? (b) Bayan mutuwar Yesu, ta yaya almajiransa suka bi misalinsa na kasancewa da ƙarfin hali?

8 Yesu ya kuma nuna ƙarfin hali ta wajen mai da hankali ga bukatun manzanninsa masu aminci ba ga nasa alhini ba. Taron tunawa da Yesu ya kafa bayan ya sallami Yahuda zai tuna wa mutanen da za su zama shafaffu amfanin hadayarsa da kuma kasancewa cikin sabon alkawarin da ya yi. (1 Kor. 10:​16, 17) Don Yesu ya taimaka musu su kasance da aminci, ya gaya wa mabiyansa abin da shi da Jehobah suke so su riƙa yi. (Yoh. 15:​12-15) Ƙari ga haka, Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa za su fuskanci matsaloli a nan gaba. Sai ya ƙarfafa su su bi misalinsa cewa su “kasance da ƙarfin zuciya!” (Yoh. 16:​1-4, 33) Bayan shekaru da yawa, manzannin Yesu sun ci gaba da bin misalinsa na sadaukar da kansu da kuma kasancewa da ƙarfin hali. Ko da yake za su sha wahala sosai, sun taimaka wa juna a matsaloli dabam-dabam da suka fuskanta.​—Ibran. 10:​33, 34.

9. Ta yaya za mu nuna ƙarfin hali yadda Yesu ya yi?

9 A yau, muna bin misalin Yesu ta wurin nuna ƙarfin hali. Alal misali, muna nuna ƙarfin hali sa’ad da muka taimaka wa ’yan’uwanmu da ake tsananta musu domin imaninsu. A wasu lokuta, an saka su a kurkuku ba tare da yin wani laifi ba. Idan hakan ya faru, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kāre su. (Filib. 1:14; Ibran. 13:19) Wata hanya kuma da za mu nuna ƙarfin hali ita ce ta wajen yin wa’azi “babu tsoro.” (A. M. 14:3) Kamar Yesu, mun ƙuduri niyyar yin wa’azin Mulki ko da mutane za su yi adawa da mu kuma su tsananta mana. Amma a wasu lokuta, muna iya ganin cewa ba mu da ƙarfin hali. Mene ne za mu iya yi?

10. Me ya kamata mu riƙa yi kafin a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu, kuma me ya sa?

10 Za mu iya daɗa kasancewa da ƙarfin hali ta wajen yin tunani game da begen da muke da shi don Kristi ya ba da ransa hadaya. (Yoh. 3:16; Afis. 1:7) Makonni kafin taron Tuna da Mutuwar Yesu, muna da zarafi na musamman na nuna godiya sosai don fansar. Ku riƙa karanta surorin da ake karantawa kafin taron kuma ku yi bimbini a kan abubuwan da suka faru kafin Yesu ya mutu. Idan muka yi hakan sa’ad da muka taru don yin Jibin Maraice na Ubangiji, za mu fahimci ma’anar gurasar da ruwan inabin da kuma fansar da Yesu ya yi. Za mu kasance da bege sosai kuma mu jimre har ƙarshe idan muka nuna godiya don abin da Yesu da Jehobah suka yi mana da yadda mu da ’yan’uwanmu muka amfana.​—Ibran. 12:3.

11-12. Mene ne muka koya daga sakin layi na farko zuwa wannan?

11 Taron yana tuna mana da fansa mai tamani da Yesu ya bayar da kuma yadda ya nuna tawali’u da ƙarfin hali. Muna godiya cewa Yesu, wanda yake roƙo ga Allah a madadinmu ya ci gaba da nuna waɗannan halayen a matsayin Babban Firist a sama! (Ibran. 7:​24, 25) Don mu nuna godiyarmu, wajibi ne mu riƙa yin taron Tuna da Mutuwar Yesu yadda ya umurce mu. (Luk. 22:​19, 20) Muna yin hakan a ranar da ta yi daidai da ranar 14 ga Nisan, kuma wannan kwanan wata ne da ta fi muhimmanci a shekara.

12 Za mu iya koyan wani abu kuma da ya sa Yesu ya mutu a madadinmu daga abubuwan da ya yi a taron. An san shi da wannan halin sa’ad da yake duniya. Wane hali ke nan?

YESU YANA ƘAUNAR MU

13. Ta yaya Yohanna 15:9 da 1 Yohanna 4:​8-10 suka kwatanta ƙaunar da Jehobah da Yesu suka nuna, kuma wane ne yake amfana daga ƙaunar?

13 Kamar yadda Jehobah yake yi, Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar mu sosai a kome da ya yi. (Karanta Yohanna 15:9; 1 Yohanna 4:​8-10.) Ya ba da ransa hadaya a madadinmu da dukan zuciyarsa. Muna amfana daga yadda Jehobah da Ɗansa suka nuna mana ƙauna ta wannan hadaya ko da mu shafaffu ne ko kuma “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16; 1 Yoh. 2:2) Ka yi tunani a kan abubuwan da Yesu ya yi amfani da su sa’ad da ya kafa taron da manzanninsa. Hakan ya nuna cewa Yesu yana ƙaunar almajiransa kuma yana yin la’akari da su. Ta yaya?

Yesu ya kafa taron Tuna da Mutuwarsa a hanya mai sauƙi don mutane su riƙa yin hakan bayan ƙarnuka da yawa da kuma a yanayoyi dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 14-16) *

14. A wace hanya ce Yesu ya nuna yana ƙaunar almajiransa?

14 Yesu ya nuna yana ƙaunar mabiyansa shafaffu ta wajen kafa taron Tuna da Mutuwarsa a hanya mai sauƙi. Da shigewar lokaci, waɗannan shafaffu za su riƙa yin wannan taron a kowace shekara a yanayoyi dabam-dabam, har a cikin kurkuku. (R. Yar. 2:10) Sun yi biyayya ga Yesu kuwa? Ƙwarai kuwa!

15-16. Ta yaya wasu suka yi taron Tuna da Mutuwar Yesu a lokacin da suke cikin mawuyacin yanayi?

15 Tun ƙarni na farko har zuwa yau, Kiristoci na gaske sun yi iya ƙoƙarinsu don su riƙa tunawa da mutuwar Yesu. Sun yi taron yadda ake yi har sa’ad da suke cikin mawuyacin yanayi. Alal misali, sa’ad da Ɗan’uwa Harold King yake cikin kurkuku a ƙasar Caina, ya tuna da mutuwar Yesu. Ya yi amfani da abubuwan da yake da su don ya yi taron a ɓoye. Ƙari ga haka, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ƙirga kwanan watan da za a yi taron daidai. In lokacin yin taron ya kai, sai ya yi hakan shi kaɗai a kurkukun. Yakan rera waƙa, ya yi addu’a kuma ya yi jawabin.

16 Wasu ’yan’uwa mata da aka saka a kurkuku a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu sun sa ransu cikin haɗari don su tuna da mutuwar Yesu. Amma, sun sami zarafin yin wannan taron a ɓoye don taro ne mai sauƙi. Sun ce: “Mun kewaye wani ƙaramin teburi da muka rufe da farin zane da ke ɗauke da gurasar da kuma ruwan inabi. Mun kunna kyandir maimakon wutan lantarki don kada a kama mu. . . . Sai muka maimaita ƙudurinmu na bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinmu kuma mu tsarkaka sunansa.” Hakika, waɗannan ’yan’uwa suna da bangaskiya sosai! Yesu ya nuna yana ƙaunar mu ta wajen sa wannan taron ya kasance da sauƙi domin mu iya yinsa sa’ad da muke cikin mawuyacin yanayi!

17. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

17 Yayin da taron Tuna da Mutuwar Yesu yake kusatowa, ya kamata mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Ta yaya zan riƙa nuna ƙauna sosai kamar Yesu? Na fi tunani game da bukatun ’yan’uwana kuwa? Ina bukatar ’yan’uwana su yi abin da ya fi ƙarfinsu, ko kuma na san kasawarsu?’ Bari mu riƙa yin koyi da Yesu kuma mu riƙa “jin tausayin juna.”​—1 Bit. 3:8.

KU RIƘA TUNA DA WAƊANNAN DARUSSAN

18-19. (a) Wane tabbaci ne muke da shi? (b) Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

18 Ba za mu riƙa yin taron Tuna da Mutuwar Yesu har abada ba. Sa’ad da Yesu zai “dawo” a lokacin ƙunci mai girma, zai tattara waɗanda aka “zaɓa” da suka rage zuwa sama, kuma za a daina yin taron Tuna da Mutuwarsa.​—1 Kor. 11:26; Mat. 24:31.

19 Ko a lokacin da aka daina taron Tuna da Mutuwar Yesu, mutanen Jehobah za su riƙa tuna da wannan taro mai sauƙi da ya nuna cewa Yesu mai tawali’u ne da ƙarfin hali. Ƙari ga haka, ya nuna yana ƙaunar ’yan Adam sosai. A lokacin, waɗanda suka halarci wannan taron za su riƙa gaya wa waɗanda za a ta da daga mutuwa yadda taron ya amfane su. Amma mene za mu yi idan muna so mu amfana daga wannan taron a yau? Wajibi ne mu ƙuduri niyyar yin koyi da Yesu ta wajen zama masu tawali’u da ƙarfin hali kuma mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu sosai. Idan muka yi hakan, muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu.​—2 Bit. 1:​10, 11.

WAƘA TA 13 Yesu, Wanda Muke Bin Misalinsa

^ sakin layi na 5 Ba da daɗewa ba, za mu yi taron Tuna da Mutuwar Yesu Kristi. Wannan taron zai koya mana cewa Yesu mai tawali’u ne da ƙarfin hali, kuma yana ƙaunar mu. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu yi koyi da halayen Yesu.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Kiristoci masu aminci suna taron Tuna da Mutuwar Yesu a wata ikilisiya a ƙarni na farko; a wajen shekara ta 1880; a sansanin Nazi da kuma a zamaninmu a Majami’ar Mulki marar bango a Amirka ta Kudu.