Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

Abin da Halartan Taro Yake Nunawa Game da Mu

Abin da Halartan Taro Yake Nunawa Game da Mu

“Kuna shelar mutuwar Ubangiji ke nan, har ya dawo.”​—1 KOR. 11:26.

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Mene ne Jehobah yake mai da wa hankali sa’ad da miliyoyin mutane suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.) (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

KA LURA da abin da Jehobah yake gani sa’ad da miliyoyin mutane a faɗin duniya suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu. Jehobah yana lura da kowane mutumin da ya halarci taron, ba yawan jama’ar ba. Alal misali, yana ganin waɗanda suke halartan taron kowace shekara. A cikinsu akwai mutanen da ke fuskantar tsanantawa sosai. Wasu ba sa halartan taronmu a kai a kai, amma sun ɗauki halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu da muhimmanci sosai. Bugu da ƙari, Jehobah yana lura da waɗanda suka halarci taron a lokaci na farko, wataƙila domin suna so su ga abin da ake yi a taron.

2 Babu shakka, Jehobah yana farin ciki sosai domin mutane da yawa suna halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu. (Luk. 22:19) Amma Jehobah ba ya mai da hankali ga yawan mutanen da suka halarci taron. Ya fi mai da hankali ga dalilin da ya sa mutanen suka halarci taron. Me ya sa? Domin wannan ne ya fi muhimmanci a gare shi. A wannan talifin, za mu tattauna wata tambaya mai muhimmanci: Me ya sa muke halartan dukan taron da Jehobah ya yi mana tanadin su, ba taron Tuna da Mutuwar Yesu kaɗai ba?

(Ka duba sakin layi na 1-2) *

HALARTAN TARO NA NUNA MU MASU TAWALI’U NE

3-4. (a) Me ya sa muke halartan taro? (b) Mene ne halartan taro yake nunawa game da mu? (c) Me ya sa bai dace mu fasa halartar taron tunawa ba kamar yadda 1 Korintiyawa 11:​23-26 ya nuna?

3 Dalili mafi muhimmanci da ya sa muke halartan taron shi ne don mu bauta wa Jehobah. Allah yana koyar da mu sa’ad da muka halarci taro. Mutane masu fahariya ba sa so a koyar da su. (3 Yoh. 9) Amma muna so Jehobah da kuma ƙungiyarsa su koyar da mu.​—Isha. 30:20; Yoh. 6:45.

4 Idan muka halarci taro, hakan zai nuna cewa muna da tawali’u kuma muna so a riƙa koyar da mu. Muna halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu ba don yana da muhimmanci kaɗai ba, amma domin muna bin umurnin da Yesu ya ba mu cewa: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.” (Karanta 1 Korintiyawa 11:​23-26.) Taron yana ƙarfafa begenmu, kuma yana tuna mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Jehobah ya san cewa muna bukatar ƙarfafa a koyaushe, ba kawai sau ɗaya a shekara ba. Don haka, ya yi mana tanadin taron ikilisiya kuma ya ƙarfafa mu mu riƙa halarta. Tawali’u zai taimaka mana mu yi biyayya. Muna ɗaukan lokaci a kowane mako don mu shirya taro da kuma halartan su.

5. Me ya sa masu tawali’u suke amsa gayyatar Jehobah?

5 A kowace shekara, Jehobah yana gayyatar mutane masu tawali’u, kuma suna amincewa ya koyar da su. (Isha. 50:4) Sun ji daɗin halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu kuma bayan haka sai suka soma halartan taron ikilisiya. (Zak. 8:​20-23) Dukanmu muna murna domin Jehobah yana koyar da mu kuma yana yi mana ja-goranci domin shi ne ‘mai taimakonmu da mai cetonmu.’ (Zab. 40:17) Amincewa da gayyatar da Jehobah da kuma Ɗansa wanda yake ƙauna suka yi mana, ya fi sa mutum farin ciki.​—Mat. 17:5; 18:20; 28:20.

6. Ta yaya tawali’u ya taimaka wa wani mutum ya halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu?

6 A kowace shekara, muna yin iya ƙoƙarinmu domin mu gayyaci mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu. Mutane da yawa sun amfana daga wannan gayyatar. Ka yi la’akari da wannan misalin. Shekaru da yawa da suka shige, an ba wani mutum takardar gayyata zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu, amma ya gaya wa ɗan’uwan da ya gayyace shi cewa ba zai sami damar zuwa ba. A daren da ake taron, ɗan’uwan ya yi mamaki sosai da ya ga mutumin ya shigo Majami’ar Mulkin. Yadda aka marabci mutumin ya burge shi sosai, kuma hakan ya sa ya soma halartan taron ikilisiya. Tun daga lokacin, sau uku ne kawai bai halarci taro ba a shekarar. Mene ne ya taimaka masa ya yanke shawarar halartan taron? Yana da tawali’u kuma hakan ya sa ya canja ra’ayinsa. Ɗan’uwan da ya gayyace shi ya ce, “Mutumin yana da sauƙin kai sosai.” Babu shakka, Jehobah ne ya jawo mutumin nan don ya bauta masa kuma yanzu ya yi baftisma.​—2 Sam. 22:28; Yoh. 6:44.

7. Ta yaya taro da kuma abin da muke karantawa a Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu zama masu tawali’u?

7 Abubuwan da muke koya a taronmu da kuma Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kasance da tawali’u. ’Yan makonni kafin taron Tuna da Mutuwar Yesu, muna mai da hankali ga misalan Yesu da kuma tawali’un da ya nuna sa’ad da ya ba da ransa hadaya. Ban da haka, ’yan kwanaki kafin taron, ana ƙarfafa mu mu karanta abubuwan da suka faru kafin Yesu ya mutu da kuma bayan ya tashi daga mutuwa. Abubuwan da muke koya a wannan taron da kuma waɗanda muke karantawa suna sa mu daɗa godiya don yadda Yesu ya fanshe mu. Ƙari ga haka, suna sa mu bi misalinsa na kasancewa da tawali’u kuma mu yi nufin Jehobah ko da muna fuskantar matsaloli.​—Luk. 22:​41, 42.

ƘARFIN HALI NA TAIMAKA MANA MU HALARCI TARO

8. Ta yaya Yesu ya nuna ƙarfin hali?

8 Muna ƙoƙarin nuna ƙarfin hali kamar Yesu. Ka tuna irin ƙarfin halin da ya nuna ’yan kwanaki kafin ya mutu. Yesu ya san cewa ba da daɗewa ba maƙiyansa za su wulaƙanta shi, su yi masa dūka kuma su kashe shi. (Mat. 20:​17-19) Duk da haka, bai damu ba. Sa’ad da lokaci ya yi, ya gaya wa manzanninsa da suka raka shi zuwa Getsemani cewa: “Ku tashi mu tafi. Ga mai bashe ni nan, ya iso.” (Mat. 26:​36, 46) Sa’ad da taron ’yan iska suka zo su kama Yesu, ya fito ya miƙa kansa kuma ya umurce su su bar manzanninsa su tafi. (Yoh. 18:​3-8) Hakika, Yesu ya nuna ƙarfin hali sosai! A yau, shafaffun Kiristoci da kuma waɗansu tumaki suna yin iya ƙoƙarinsu don su yi koyi da ƙarfin halin Yesu. Ta yaya?

Ƙarfin halin da kake nunawa ta wajen halartan taro yana ƙarfafa wasu (Ka duba sakin layi na 9) *

9. (a) Me ya sa muke bukatar ƙarfin hali don mu riƙa halartan taro a kai a kai? (b) Ta yaya misalinmu zai shafi ’yan’uwan da aka saka a kurkuku don imaninsu?

9 Domin mu riƙa halartan taro a kai a kai, muna bukatar mu nuna ƙarfin hali sa’ad da muke fuskantar matsala. Wasu ’yan’uwanmu suna halartan taro duk da cewa suna makoki ko sanyin gwiwa ko kuma rashin lafiya. Wasu kuma suna halartan taro duk da cewa iyalinsu ko kuma gwamnati tana tsananta musu. Ka yi tunani yadda misalinmu yake ƙarfafa ’yan’uwan da aka saka a kurkuku don imaninsu. (Ibran. 13:3) Idan suka ji cewa muna bauta wa Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarsu, ya sa su kasance da ƙarfin hali kuma ya taimaka musu su riƙe aminci. Manzo Bulus ya fuskanci irin wannan yanayin. Sa’ad da aka saka shi a kurkuku a Roma, ya yi murna sosai a duk lokacin da ya ji cewa ’yan’uwansa suna kan bauta wa Allah da aminci. (Filib. 1:​3-5, 12-14) Jim kaɗan kafin a sake shi ko kuma bayan hakan, Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Ibraniyawa. Ya ƙarfafa Kiristoci a wasiƙar cewa su ci gaba da ‘ƙaunar’ juna kuma kada su fasa halartan taro.​—Ibran. 10:​24, 25; 13:1.

10-11. (a) Waɗanne mutane ne za mu gayyata zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu? (b) Kamar yadda aka ambata a Afisawa 1:​7, me ya sa za mu yi hakan?

10 Muna nuna ƙarfin hali sa’ad da muka gayyaci danginmu da abokan aikinmu da kuma maƙwabtanmu zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu. Me ya sa muke gayyatar su? Domin muna godiya sosai don abin da Jehobah da kuma Yesu suka yi mana. Muna so su san yadda za su amfana daga ‘alherin’ da ya sa Jehobah ya fanshe mu.​—Karanta Afisawa 1:7; R. Yar. 22:17.

11 Idan muka nuna ƙarfin hali kuma muka halarci taro, muna nuna wani hali mai kyau wanda Jehobah da Ɗansa suka nuna a hanya ta musamman.

ƘAUNA CE KE MOTSA MU MU HALARCI TARO

12. (a) Ta yaya halartan taro yake sa mu daɗa ƙaunar Jehobah da kuma Yesu? (b) Mene ne littafin 2 Korintiyawa 5:​14, 15 ya ƙarfafa mu mu yi?

12 Ƙaunarmu ga Jehobah da kuma Yesu za ta motsa mu mu riƙa halartan taro. A sakamakon haka, abin da muka koya zai taimaka mana mu daɗa ƙaunar Jehobah da kuma Ɗansa. A taro, ana yawan tunasar da mu abubuwan da suka yi a madadinmu. (Rom. 5:8) Taron Tuna da Mutuwar Yesu yana tuna mana cewa Jehobah da Yesu suna ƙaunar mu har da mutanen da ba su san muhimmancin fansar ba. Ya kamata mu yi koyi da Yesu ta yadda muke bi da rayuwarmu a kowace rana. Hakan zai nuna cewa muna daraja fansar da ya yi mana. (Karanta 2 Korintiyawa 5:​14, 15.) Ƙari ga haka, zuciyarmu tana motsa mu mu yabi Jehobah domin fansar da ya yi tanadinsa. Wata hanya kuma da za mu iya yabon Jehobah ita ce ta wajen yin kalami a taro.

13. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da Ɗansa sosai? Ka bayyana.

13 Za mu iya nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da kuma Yesu sosai ta wajen kasancewa a shirye mu yi sadaukarwa domin su. A yawancin lokaci, muna sadaukar da abubuwa da yawa don mu halarci taro. ’Yan’uwa a ikilisiyoyi da yawa suna yin taro da yamma a lokacin da wataƙila sun gaji. Ana yin wani taro kuma a ƙarshen mako, a lokacin da wasu mutane ke hutawa. Shin Jehobah yana lura cewa muna halarta taro ko da mun gaji? Ƙwarai kuwa! Jehobah yana daraja mu don ƙoƙarin da muke yi mu nuna cewa muna ƙaunar sa.​—Mar. 12:​41-44.

14. Ta yaya Yesu ya kafa misali a nuna ƙaunar da ba ta son kai?

14 Yesu ya kafa mana misali ta wajen nuna ƙaunar da ba ta son kai. Ya yi hakan ta wajen kasancewa a shirye ya ba da ransa a madadin mabiyansa. Ƙari ga haka, a kowace rana ya nuna cewa bukatunsu ne ya fi muhimmanci a gare shi. Alal misali, ya kasance tare da mabiyansa duk da cewa ya gaji ko kuma akwai wasu abubuwa da ke ci masa rai. (Luk. 22:​39-46) Ban da haka, ya mai da hankali ga abin da zai iya ba wasu, ba abin da zai samu ba. (Mat. 20:28) Idan muna ƙaunar Jehobah da kuma ’yan’uwanmu sosai, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu da kuma taron ikilisiya.

15. Su waye ne musamman muke so mu taimaka musu?

15 Muna cikin ƙungiya ɗaya tak da Jehobah yake amfani da ita, kuma muna farin cikin yin amfani da lokacinmu don mu gayyaci mutane su zo su bauta wa Allah. Amma mun fi son taimaka wa ’yan’uwan da suka daina zuwa taro ko kuma yin wa’azi. (Gal. 6:10) Muna nuna cewa muna ƙaunar su ta wajen ƙarfafa su su halarci taro, musamman ma taron Tuna da Mutuwar Yesu. Kamar Jehobah da Yesu, muna farin ciki sosai sa’ad da mutum da ya daina zuwa taro ko kuma yin wa’azi ya komo ga Ubanmu mai ƙauna Jehobah da Makiyayinmu.​—Mat. 18:14.

16. (a) Ta yaya za mu ƙarfafa juna, kuma ta yaya halartan taro zai amfane mu? (b) Me ya sa ya dace mu yi bimbini a kan furucin Yesu da ke Yohanna 3:16 a wannan lokacin?

16 ’Yan makonni kafin a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu, ku gayyaci mutane da yawa don su halarci taron da za a yi ranar Jumma’a, 19 ga Afrilu, 2019. (Ka duba akwatin nan “ Za Ka Gayyace Su Kuwa?”) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa ƙarfafa juna ta wajen halartan dukan taron da Jehobah ya shirya mana. Yayin da muke kusantar ƙarshen zamanin nan, halartan taro zai taimaka mana mu nuna tawali’u da ƙarfin hali da kuma ƙauna. (1 Tas. 5:​8-11) Bari mu nuna da dukan zuciyarmu yadda muke ji don ƙaunar da Jehobah da kuma Ɗansa suke yi mana!​—Karanta Yohanna 3:16.

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi

^ sakin layi na 5 Taron Tuna da Mutuwar Yesu ne taro mafi muhimmanci da ake yi a kowace shekara, kuma za a yi shi a ranar Jumma’a, 19 ga Afrilu, 2019. Mene ne yake motsa mu mu halarci taron? Muna so mu sa Jehobah farin ciki. A wannan talifin, za mu tattauna abin da halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu da kuma taron ikilisiya suke nunawa game da mu.

^ sakin layi na 50 HOTON DA KE BANGON GABA: Ana marabtar mutanen da suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a faɗin duniya

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa da aka saka a kurkuku don imaninsa ya sami ƙarfafa don wasiƙar da iyalinsa suka turo masa. Sanin cewa iyalinsa ba su manta da shi ba kuma suna kan bauta wa Jehobah duk da cewa ana yaƙi a yankinsu ya sa shi farin ciki sosai.