Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

Ruhun Allah Yana Ba Mu Tabbaci

Ruhun Allah Yana Ba Mu Tabbaci

“Ruhun Allah da kansa tare da ruhunmu yana tabbatar cewa mu ’ya’yan Allah ne.”​—ROM. 8:16.

WAƘA TA 25 Mutane Masu Daraja

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Jehobah ya saukar da ruhunsa a hanya mai ban mamaki a kan Kiristoci 120 a ranar Fentakos (Ka duba sakin layi na 1-2)

1-2. Wane abu mai ban-mamaki ne ya faru a ranar Fentakos ta 33?

AN WAYE gari a birnin Urushalima a ranar Lahadi ta shekara ta 33 kuma ranar Fentakos ce. Almajiran Yesu Kristi 120 sun haɗu a ɗakin da ke saman wani gida. (A. M. 1:​13-15; 2:1) ʼYan kwanaki kafin wannan ranar, Yesu ya umurce su cewa su kasance a Urushalima domin za a aiko musu da kyauta ta musamman. (A. M. 1:​4, 5) Mene ne ya faru bayan haka?

2 “Ba labari sai aka ji wata ƙara daga sama kamar ta babbar iska.” Ƙarar ta cika dukan gidan da suke zaune a ciki. “Sai ga waɗansu abubuwa kamar harsunan wuta” suka sassauko a kan kowane almajiran, kuma “sai duk aka cika su da ruhu mai tsarki.” (A. M. 2:​2-4) Jehobah ya shafe su da ruhunsa a wannan hanya mai ban-mamaki. (A. M. 1:8) Almajiran ne mutane na farko da aka shafe da ruhu mai tsarki * kuma suka kasance da begen yin sarauta da Yesu a sama.

ME KE FARUWA SA’AD DA AKA SHAFE MUTUM?

3. Me ya sa almajiran Yesu a ranar Fentakos ba su yi shakka cewa an shafe su ba?

3 Da a ce kana cikin mutanen da ke wannan ɗakin sa’ad da aka saukar da ruhu mai tsarki, babu shakka, ba za ka taɓa mantawa da aukuwar ba. Wani abu kamar harshen wuta ya sauko a kanka, sai ka soma magana a harsuna dabam-dabam. (A. M. 2:​5-12) Ba za ka yi shakka cewa an shafe ka da ruhu mai tsarki ba. Amma dukan shafaffu ne ake shafewa a wannan hanya ta musamman ko kuma ana shafe dukansu ne a lokaci guda? A’a. Ta yaya muka san da haka?

4. Shin an shafe dukan shafaffu a ƙarni na farko a lokaci ɗaya? Ka bayyana.

4 Bari mu tattauna batun lokaci. Ba waɗannan Kiristoci 120 ne kaɗai aka shafe su da ruhu mai tsarki a ranar Fentakos ta 33 ba. Ƙari ga haka, an saukar da ruhu mai tsarki a kan wasu mutane 3,000 a ranar. An shafe su a lokacin da suka yi baftisma. (A. M. 2:​37, 38, 41) Amma a shekarun da suka biyo baya, ba dukan shafaffun Kiristoci ba ne aka shafe su a lokacin da suka yi baftisma ba. Ba a shafe Samariyawa nan da nan da yin baftisma ba. (A. M. 8:​14-17) Kuma yadda aka shafe Karniliyus da ʼyan gidansa abu ne mai ban-mamaki domin an shafe su kafin ma su yi baftisma.​—A. M. 10:​44-48.

5. Kamar yadda 2 Korintiyawa 1:​21, 22 suka nuna, me ke faruwa sa’ad da aka shafe mutum da ruhu mai tsarki?

5 Bari mu kuma tattauna abin da ke faruwa sa’ad da aka shafe mutum da ruhu mai tsarki. Yana wuya wasu da aka shafe su su yarda cewa Jehobah ya zaɓe su. Suna iya yin mamaki cewa, ‘Me ya sa Jehobah ya zaɓe ni?’ Wasu kuma ba sa jin hakan. Ko da yaya mutum ya ji sa’ad da aka shafe shi, manzo Bulus ya bayyana abin da ke faruwa sa’ad da wani ya zama shafaffe. Ya ce: “A sa’ad da kuka ba da gaskiya ga Almasihu, Allah ya ba ku ruhu mai tsarki kamar yadda aka yi muku alkawari zai yi, ya zama kamar hatimin * shaida cewa ku nasa ne.” (Afis. 1:​13, 14) Jehobah yana yin amfani da ruhunsa don ya sa Kiristocin nan su kasance da tabbaci cewa an zaɓe su. Ta hakan, ruhu mai tsarki ya zama kamar hatimin shaida cewa za su kasance a sama har abada ba a duniya ba.​—Karanta 2 Korintiyawa 1:​21, 22.

6. Mene ne ya wajaba Kirista shafaffe ya yi don ya sami ladarsa ta zuwa sama?

6 Idan an shafe wani Kirista, shin lallai ne cewa sai ya je sama? A’a. Yana da tabbaci cewa an zaɓe shi ya je sama. Amma, dole ya tuna da umurnin nan: ‘Ya ku ’yan’uwa, ku ƙara ƙoƙarinku ku tabbatar da kiranku da zaɓenku wanda Allah ya yi muku. Idan kun yi haka ba za ku taɓa fāɗi ba ko kaɗan.’ (2 Bit. 1:10) Saboda haka, ko da an zaɓi wani ya je sama, zai sami wannan ladar idan ya kasance da aminci har ƙarshe.​—Filib. 3:​12-14; Ibran. 3:1; R. Yar. 2:10.

TA YAYA MUTUM ZAI SAN SHI SHAFAFFE NE?

7. Ta yaya shafaffu suke sani cewa an zaɓe su su je sama?

7 Amma ta yaya mutum yake sani cewa an zaɓe shi ya je sama? Amsar tana furucin da Bulus ya yi ga Romawa da aka ‘kira su zama tsarkakku.’ Ya gaya musu cewa: “Ruhun da aka ba ku ba na bauta ba ne yadda za ku sāke zama cikin tsoro. A’a, Ruhun nan na zaman ’ya’yan Allah ne, kuma ta wurin Ruhun ne muke kira ga Allah, mu ce da shi ‘Abba! Uba!’ Ruhun Allah da kansa tare da ruhunmu yana tabbatar cewa mu ’ya’yan Allah ne.” (Rom. 1:7; 8:​15, 16) Saboda haka, Allah yana yin amfani da ruhunsa don ya tabbatar wa shafaffu da cewa za su je sama.​—1 Tas. 2:12.

8. Ta yaya 1 Yohanna 2:​20, 27 suka nuna cewa shafaffun Kiristoci ba sa bukatar wani ya gaya musu cewa su shafaffu ne ba?

8 Jehobah yana sa mutanen da ya zaɓa su je sama su kasance da tabbaci sarai cewa za su je sama. (Karanta 1 Yohanna 2:​20, 27.) Hakika, shafaffun Kiristoci ma suna bukata a koyar da su a ikilisiya kamar sauran ʼyan’uwa. Amma ba sa bukatar wani ya tabbatar musu da cewa su shafaffu ne. Jehobah ya riga ya yi amfani da iko mafi ƙarfi, wato ruhu mai tsarki wajen tabbatar musu sarai cewa su shafaffu ne!

AN ‘SAKE HAIFAN SU’

9. Kamar yadda aka bayyana a Afisawa 1:​18, mene ne ke canjawa sa’ad da mutum ya zama shafaffe?

9 Yana kasance wa yawancin bayin Allah a yau da wuya su fahimci abin da ke faruwa sa’ad da Allah ya shafe mutum da ruhu mai tsarki. Me ya sa? Domin su ba shafaffu ba ne. Allah ya halicci mutane domin su rayu har abada a duniya ba a sama ba. (Far. 1:28; Zab. 37:29) Amma Jehobah ya zaɓi wasu mutane su rayu a sama. Saboda haka, a lokacin da ya shafe su, yana canja begensu da tunaninsu sosai domin su yi marmarin yin rayuwa a sama.​—Karanta Afisawa 1:18.

10. Mene ne yake nufi a ‘sake haifan’ mutum? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

10 A lokacin da aka shafe Kiristoci da ruhu mai tsarki, ana ‘sake haifan su.’ * Yesu ya kuma ambata cewa ba zai yiwu ba mutumin da aka shafe shi da ruhu mai tsarki ya bayyana wa wani da ba shafaffe ba yadda mutum yake ji sa’ad da aka sake haifan sa ko kuma ‘ruhu ya haife’ shi ba.​—Yoh. 3:​3-8.

11. Ka bayyana yadda tunanin mutum yake canjawa sa’ad da ya zama shafaffe.

11 Ta yaya tunanin mutum yake canjawa a lokacin da aka shafe shi? Kafin Jehobah ya shafe Kiristocin nan, sun yi begen yin rayuwa har abada a duniya. Sun yi ɗokin ganin lokacin da Jehobah zai cire dukan mugaye kuma ya mayar da duniya ta zama aljanna. Wataƙila suna so su marabci wani danginsu ko abokinsu da ya rasu. Amma bayan da suka zama shafaffu, sai tunaninsu ya canja. Jehobah ya yi amfani da ruhunsa wajen canja tunaninsu da kuma begen da suke so sosai a dā. Kafin su zama shafaffu, ba su taɓa yin gunaguni don suna da begen yin rayuwa a duniya ba. Ba domin suna wahala sosai ba ne ya sa suke so su je sama ba. Ƙari ga haka, ba su yi tunani cewa za su gaji da yin rayuwa a duniya a aljanna ba.

12. Kamar yadda 1 Bitrus 1:​3, 4, suka nuna, ta yaya shafaffu suke ji don begensu?

12 Mutumin da aka shafe shi zai iya ji kamar bai cancanci samun begen nan ba. Amma ba ya yin shakka cewa Jehobah ya zaɓe shi. Yana matuƙar farin ciki yayin da yake tunani a kan begen yin rayuwa a sama.​—Karanta 1 Bitrus 1:​3, 4.

13. Ta yaya shafaffu suke ji game da rayuwarsu a duniya?

13 Shin hakan yana nufin cewa shafaffu suna so su mutu ne? Manzo Bulus ya amsa tambayar. Ya ce: ‘Sa’ad da muke zaune cikin jikin nan na duniya, muna nishi saboda matsin da muke sha. Ba wai muna so mu rabu da jikin nan namu na duniya ba, amma muna so a sanya mu da na sama, domin abu mai rai na har abada ya canja abin nan mai mutuwa gaba ɗaya.’ (2 Kor. 5:4) Kiristocin nan ba su gaji da rayuwa a duniyar nan ba. A maimakon haka, suna jin daɗin rayuwa a duniya kuma suna so su yi amfani da rayuwarsu a kowace rana don su bauta wa Jehobah tare da iyalinsu da abokansu. Amma ko da mene ne suke yi, suna tunawa da begen da suke da shi na yin rayuwa a sama.​—1 Kor. 15:53; 2 Bit. 1:4; 1 Yoh. 3:​2, 3; R. Yar. 20:6.

JEHOBAH YA SHAFE KA NE?

14. Waɗanne abubuwa ne ba sa nuna cewa mutum shafaffe ne?

14 Wataƙila kana tunani ko an shafe ka da ruhu mai tsarki. Idan haka ne, ka yi tunanin waɗannan tambayoyi masu muhimmanci: Kana da ƙwazo yin nufin Jehobah sosai? Shin kana ganin kana ƙwazo a yin wa’azi? Kana jin daɗin yin nazarin Kalmar Allah da kuma koyan “abubuwan Allah masu wuyar ganewa”? (1 Kor. 2:10) Kana ganin Jehobah ya taimaka maka ka cim ma abubuwa masu ban mamaki a wa’azi? Kana matuƙar son koya wa mutane game da Jehobah? Ka lura da wasu abubuwa da suka nuna cewa Jehobah ya taimaka maka a hanyoyi da yawa a rayuwarka? Idan amsarka e ce ga dukan tambayoyin nan, shin hakan yana nufin cewa an shafe ka? A’a. Me ya sa? Domin dukan bayin Allah suna jin hakan ko da su shafaffu ne ko babu. Ƙari ga haka, Jehobah yana iya yin amfani da ruhu mai tsarki don ya taimaka ma kowanne cikin bayinsa su yi waɗannan abubuwa ko suna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya. Idan kana shakka ko an shafe ka da ruhu mai tsarki, hakan yana nufin cewa ba a shafe ka ba. Waɗanda Jehobah ya shafe da ruhunsa ba sa shakka ko su shafaffu ne domin suna da tabbaci cewa su shafaffu ne!

Jehobah ya yi amfani da ruhunsa don ya sa Ibrahim da Saratu da Dauda da Yohanna Mai Baftisma su yi abubuwa masu ban mamaki, amma bai yi amfani da ruhun don ya ba su bege yin rayuwa a sama ba (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Ta yaya muka sani cewa ba dukan waɗanda ruhun Allah ya taimaka ba ne za su je sama ba?

15 A cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai misalan mutane da yawa masu bangaskiya da Jehobah ya taimaka musu da ruhu mai tsarki. Duk da haka, ba su da begen zuwa sama. Ruhu mai tsarki ya yi wa Dauda ja-goranci. (1 Sam. 16:13) Ruhu mai tsarki ya taimaka masa ya fahimci abubuwa masu wuyar ganewa game da Jehobah kuma ya rubuta wasu sassan Littafi Mai Tsarki. (Mar. 12:36) Duk da haka, manzo Bitrus ya ce Dauda bai je “sama ba.” (A. M. 2:34) Yohanna mai baftisma yana da “ruhu mai tsarki.” (Luk. 1:​13-16) Yesu ya ce ba mutum da ya fi Yohanna, amma ya ce Yohanna ba zai je sama ba. (Mat. 11:​10, 11) Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya sa waɗannan maza su yi abubuwa masu ban al’ajabi, amma bai yi amfani da wannan ruhu don ya zaɓe su zuwa sama ba. Shin hakan yana nufin cewa waɗanda aka zaɓa zuwa sama sun fi aminci ne? A’a. Jehobah zai ta da su daga mutuwa don su yi rayuwa a Aljanna a duniya.​—Yoh. 5:​28, 29; A. M. 24:15.

16. Wane bege ne yawancin bayin Allah suke da shi a yau?

16 Yawancin bayin Allah a duniya a yau ba su da begen zuwa sama. Kamar Ibrahim da Saratu da Dauda da Yohanna Mai Baftisma da kuma maza da mata da yawa a dā, suna da begen zama a duniya sa’ad da Yesu zai soma sarauta bisa duniya.​—Ibran. 11:10.

17. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a talifi na gaba?

17 A yau, da akwai shafaffu a tsakaninmu, saboda haka muna iya yin wasu tambayoyi. (R. Yar. 12:17) Alal misali, yaya ya kamata shafaffu su ɗauki kansu? Yaya ya kamata mu bi da wani a ikilisiyarmu da ya soma cin gurasa da shan inabi a lokacin Tuna da Mutuwar Yesu? Ya kamata mu riƙa damuwa cewa adadin shafaffu yana ƙaruwa? Za a ba da amsar waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

^ sakin layi na 5 Tun ranar Fentakos ta shekara ta 33, Jehobah ya ba wasu Kiristoci begen zama abokan Mulkin Ɗansa a sama. Amma ta yaya Kiristocin nan suke sani cewa an zaɓe su? Mene ne ke faruwa sa’ad da Allah ya zaɓi mutum ya je sama? An ɗauko wannan talifin daga Hasumiyar Tsaro ta Janairu 2016 kuma za a amsa tambayoyin nan a ciki.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Shafewa da ruhu mai tsarki: Jehobah yana yin amfani da ruhunsa don ya zaɓi mutum ya yi sarauta da Yesu a sama. Yana yin amfani da ruhun don ya sa mutumin ya kasance da “tabbaci” yin rayuwa a sama a nan gaba. (Afis. 1:​13, 14) Kiristocin nan za su iya cewa ruhu mai tsarki ya “tabbatar” musu ko ya sa su sani sarai cewa za su je sama.​—Rom. 8:16.

^ sakin layi na 5 MA’ANAR WASU KALMOMI: Hatimi. Ana hatimce Kirista mai aminci a lokacin da yake gab da mutuwa ko kuma gab da somawar ƙunci mai girma.​—Afis. 4:30; R. Yar. 7:​2-4; ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta Afrilu 2016 na Turanci.

^ sakin layi na 10 Don ƙarin bayani a kan abin da yake nufi a “sake haifar mutum,” ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2009, shafuffuka na 3-12.

WAƘA TA 27 Allah Zai Bayyana ’Ya’yansa

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA Shafi na 24: Ko da an saka mu cikin kurkuku don imaninmu ko kuma muna yin wa’azi a sake, muna da begen yin rayuwa a duniya sa’ad da Yesu zai soma sarauta bisa duniya.