Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 2

Za Ka Iya “Sanyaya” Zuciyar Mutane

Za Ka Iya “Sanyaya” Zuciyar Mutane

A “cikin abokin aikina ga Mulkin Allah waɗannan su kaɗai ne . . . sun kuwa sanyaya mini zuciya.”​—KOL. 4:​11, Littafi Mai Tsarki.

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne mawuyacin yanayi ne bayin Jehobah da yawa suke ciki?

A FAƊIN duniya, bayin Jehobah da yawa suna cikin yanayi da ke sa su alhini ko kuma baƙin ciki. Ka lura da hakan a cikin ikilisiyarku? Wasu Kiristoci suna ciwo mai tsanani ko kuma suna makoki don an yi musu rasuwa. Wasu suna baƙin ciki sosai domin wani a iyalinsu ko kuma amininsu ya daina bauta wa Jehobah. Har ila wasu suna shan wahala sanaddiyar bala’i. Dukan waɗannan ’yan’uwan suna bukatar ƙarfafawa. Ta yaya za mu iya taimaka musu?

2. Me ya sa manzo Bulus ya bukaci a ƙarfafa shi a wasu lokuta?

2 Manzo Bulus ya fuskanci mawuyacin yanayi sau da yawa. (2 Kor. 11:​23-28) Ya kuma jimre da “ƙaya a jiki” wataƙila wani irin cuta. (2 Kor. 12:7) Ƙari ga haka, ya yi baƙin ciki sa’ad da Demas abokin aikinsa a dā ya yashe shi domin yana “ƙaunar duniyan nan.” (2 Tim. 4:10) Bulus shafaffe ne mai ƙarfin zuciya da ya taimaka wa mutane sosai, amma a wasu lokuta ya yi sanyin gwiwa.​—Rom. 9:​1, 2.

3. Su waye ne suka ƙarfafa Bulus da kuma sanyaya zuciyarsa?

3 Bulus ya sami ƙarfafawa da kuma taimako da yake bukata. Ta yaya? Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya ƙarfafa shi. (2 Kor. 4:7) Jehobah ya kuma yi amfani da wasu Kiristoci don ya ƙarfafa shi. Bulus ya kwatanta wasu cikinsu a matsayin masu ‘sanyaya masa zuciya.’ (Kol. 4:11) Wasu da ya ambata a cikinsu su ne Aristarkus da Tikikus da kuma Markus. Sun ƙarfafa Bulus kuma hakan ya taimaka masa ya jimre. Waɗanne halaye ne suka taimaka ma waɗannan Kiristoci uku su ƙarfafa Bulus sosai? Ta yaya za mu bi misalinsu mai kyau sa’ad da muke ƙarfafa juna?

KA ZAMA MAI AMINCI KAMAR ARISTAKUS

Kamar Aristarkus, za mu iya zama abokan kirki ga ’yan’uwanmu a “kwanakin masifa” (Ka duba sakin layi na 4-5) *

4. Ta yaya Aristarkus ya zama aminin Bulus?

4 Aristarkus wani Kirista ne ɗan Tasalonika da ke Makidoniya kuma ya zama aminin Bulus. Lokaci na farko da aka ambata shi a Littafi Mai Tsarki shi ne sa’ad da Bulus ya ziyarci Afisa a tafiyarsa ta uku a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje. Taron ’yan iska sun kama Aristarkus sa’ad da ya bi Bulus yin wa’azi. (A. M. 19:29) Sa’ad da aka sake shi, bai bar Bulus don ya nemi wurin da zai ɓoye kansa ba. ’Yan watanni bayan haka, Aristarkus yana tare da Bulus a Hellas ko da yake abokan gāban Bulus suna nema su kashe shi. (A. M. 20:​2-4) A misalin shekara ta 58 bayan haihuwar Yesu, an saka Bulus a kurkuku a Roma. Aristarkus ya bi Bulus a wannan doguwar tafiya kuma su biyu sun fuskanci hatsarin jirgin ruwa. (A. M. 27:​1, 2, 41) Wataƙila bayan da suka isa Roma, Aristarkus ya kasance a kurkuku da Bulus na ɗan lokaci. (Kol. 4:10) Babu shakka, irin wannan amini ya ƙarfafa Bulus da kuma sanyaya zuciyarsa!

5. Kamar yadda Karin Magana 17:17 ta nuna, ta yaya za mu zama abokan kirki?

5 Kamar Aristarkus, muna iya zama abokin kirki ta wajen taimaka wa ’yan’uwanmu a lokacin da suke farin ciki da kuma a “kwanakin masifa.” (Karanta Karin Magana 17:17.) Muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa ’yan’uwanmu har bayan sun gama fuskantar jarrabawa. Wata mai suna Farida, * wadda iyayenta suka mutu cikin watanni uku sanadiyyar ciwon kansa ta ce: “Ina ganin cewa jarrabawa mai wuya tana shafanmu na dogon lokaci. Ina farin ciki sa’ad da abokan kirki suka tuna cewa har ila ina baƙin ciki ko da yake ya daɗe da iyayena suka rasu.”

6. Mene ne za mu yi idan muna da aminci?

Abokan kirki suna ba da lokacinsu da ƙarfinsu don su taimaka wa ’yan’uwansu. Alal misali, an binciko cewa wani ɗan’uwa mai suna Peter yana da ciwon ajali. Matarsa Kathryn ta ce: “Wasu ma’aurata a ikilisiyarmu sun kai mu asibiti don a yi wa maigidana gwaji. A wajen ne suka tsai da shawara cewa za su taimaka mana mu jimre da wannan yanayi mai wuya. Kuma sun taimaka mana a duk lokacin da muke bukatar taimako.” Abin ban-ƙarfafa ne mu sami abokan kirki da za su iya taimaka mana mu jimre matsalolinmu!

KA ZAMA MAI RIƘON AMANA KAMAR TIKIKUS

Kamar Tikikus, za mu iya zama mai riƙon amana sa’ad da ’yan’uwanmu suke fama da matsaloli (Ka duba sakin layi na 7-9) *

7-8. Kamar yadda Kolosiyawa 4:​7-9 suka nuna, ta yaya Tikikus ya nuna cewa shi mai riƙon amana ne?

7 Tikikus wani Kirista ɗan Asiya aminin Bulus ne sosai. (A. M. 20:4) A misalin shekara ta 55 bayan haihuwar Yesu, Bulus ya ce a tara kuɗi don a taimaka wa Kiristoci da ke Yahudiya. Wataƙila ya sa Tikikus ya yi wannan aiki mai muhimmanci. (2 Kor. 8:​18-20) Bayan haka, sa’ad da aka sa Bulus a kurkuku a Roma a ƙaro na farko, Tikikus ne ɗan aikan Bulus. Shi ne yake idar da wasiƙu da saƙonni da Bulus yake rubutawa don ya ƙarfafa ikilisiyoyi da ke Asiya.​—Kol. 4:​7-9.

8 Tikikus ya ci gaba da zama aminin Bulus. (Tit. 3:12) Ba dukan Kiristoci a lokacin ba ne suke da riƙon amana kamar Tikikus ba. A misalin shekara ta 65, a lokacin da aka saka Bulus a kurkuku a ƙaro na biyu, ya rubuta cewa Kiristoci da yawa a yankin Asiya sun ƙi yin cuɗanya da shi. Wataƙila sun yi hakan ne domin suna jin tsoron abokan gaba. (2 Tim. 1:15) Amma, Bulus ya tabbata da Tikikus kuma ya ba shi wani aiki. (2 Tim. 4:12) Hakika, Bulus ya yi godiya don yana da abokin kirki kamar Tikikus.

9. Ta yaya za mu iya yin koyi da Tikikus?

9 Muna iya yin koyi da Tikikus ta wurin zama abokan kirki. Alal misali, idan mun yi wa ’yan’uwanmu alkawari cewa za mu taimaka musu, mu tabbata cewa mun cika alkawarinmu. (Mat. 5:37; Luk. 16:10) Waɗanda suke bukatar taimako suna samun ƙarfafa idan sun san za mu taimaka musu da gaske. Wata ’yar’uwa ta faɗi dalilin cewa, “Kana kasancewa da kwanciyar rai domin ka san cewa mutumin da ya ce zai taimaka maka zai zo da wuri kamar yadda ya faɗa.”

10. Kamar yadda aka ambata a Karin Magana 18:​24, su waye ne za su iya ƙarfafa mutanen da ke fama da ɓacin rai ko jarrabawa?

10 Sau da yawa waɗanda suke fuskantar matsala suna samun ƙarfafa sa’ad da suka tattauna matsalarsu da amininsu. (Karanta Karin Magana 18:24.) Wani ɗan’uwa mai suna Bijay ya yi baƙin ciki sosai da aka yi wa ɗansa yankan zumunci. Ya ce: “Na so in gaya wa aminina yadda nake ji.” Wani ɗan’uwa kuma mai suna Carlos ya rasa gatarsa a ikilisiya saboda wani kuskuren da ya yi. Ya ce: “Na so in tattauna yadda nake ji da wani da zai saurare ni sosai. Mutumin da ba zai ɗora mini laifi ba.” Dattawa a ikilisiya sun saurari Carlos sosai kuma sun taimaka masa ya magance matsalolinsa. Ya kuma ya farin cikin sanin cewa dattawa ba su tattauna batun da wani ba.

11. Ta yaya za mu iya zama abokin kirki?

11 Muna bukatar mu zama masu haƙuri idan muna so mu zama abokin kirki. A lokacin da mijin wata mai suna Zhanna ya sake ta, ta sami ƙarfafawa sa’ad da ta tattauna batun da aminanta. Ta ce: “Sun saurare ni sosai, duk da cewa sau da yawa na gaya musu abin da ya faru.” Kai ma kana iya zama abokin kirki ta wajen saurarawa da kyau.

KA RIƘA YI WA MUTANE HIDIMA KAMAR MARKUS

Yadda Markus ya taimaka wa Bulus ya sa ya jimre, mu ma za mu iya taimaka wa ’yan’uwanmu a mawuyacin lokaci (Ka duba sakin layi na 12-14) *

12. Wane ne Markus, ta yaya ya nuna yana son taimaka wa mutane?

12 Markus wani Kirista ne Bayahude ɗan Urushalima. Wani danginsa Barnaba sananne ne mai wa’azi a ƙasar waje. (Kol. 4:10) Kamar dai iyalin Markus masu arziki ne, duk da haka, bai saka abin duniya a kan gaba ba. Taimaka wa mutane ya sa Markus farin ciki. Alal misali, a lokuta dabam-dabam da Bulus da Bitrus suke hidima, Markus ne ya taimaka musu da wasu hidimomi. (A. M. 13:​2-5; 1 Bit. 5:13) Bulus ya kwatanta Markus a matsayin mai “yin aikin Mulkin Allah tare da” shi da kuma mai sanyaya masa zuciya.​—Kol. 4:​10, 11.

13. Ta yaya 2 Timoti 4:11 ta nuna cewa Bulus ya yi godiya don hidimar Markus?

13 Markus ya zama aminin Bulus. Alal misali, a wajen shekara ta 65, Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Timoti sa’ad da aka saka shi a kurkuku a lokaci na ƙarshe a Roma. A cikin wasiƙar, Bulus ya gaya wa Timoti ya zo Roma tare da Markus. (2 Tim. 4:11) Babu shakka cewa Bulus yana godiya don hidimar da Markus ya yi a dā. Saboda haka, Bulus yana so Markus ya kasance da shi a wannan lokaci mai muhimmanci. Markus ya taimaka wa Bulus sosai, wataƙila yana ba shi abinci ko kayan rubutu. Irin wannan ƙarfafawa ya taimaka wa Bulus ya jimre kwanakinsa na ƙarshe kafin a kashe shi.

14-15. Mene ne Matiyu 7:12 ta koya mana game da taimaka wa mutane?

14 Karanta Matiyu 7:12. Sa’ad da muke cikin mawuyacin yanayi, muna godiya ga mutane da suke taimaka mana! Ryan wanda mahaifinsa ya mutu sanadiyyar mugun hatsari ya ce: “Da akwai abubuwa da yawa da kake yi kullum da ba za ka iya yi ba sa’ad da kake cikin mawuyacin yanayi. Yana da ban ƙarfafa sa’ad da wani ya taimaka maka, ko da abin da ya yi ba shi da yawa.”

15 Idan mu masu lura ne sosai, za mu ga hanyoyi da za mu iya taimaka ma wasu. Alal misali, wata ’yar’uwa ta yanke shawara ta taimaka wa Peter da Kathryn da aka ambata ɗazu don su riƙa zuwa wajen likita. Peter da Kathryn ba za su iya yin tuƙi ba don matsalarsu. Saboda haka, ’yar’uwar ta shirya don ’yan’uwa da ke ikilisiyarsu su riƙa kai su asibiti. Wannan shirin ya taimaka musu ne? Kathryn ta ce, “Mun ji kamar an ɗage mana wata kaya mai nauyi.” Zai dace ka riƙa tuna cewa za ka iya ƙarfafa mutane sosai idan ka yi musu abubuwan da ba na a-zo-a-gani ba ne.

16. Wane darasi mai muhimmanci na ƙarfafa mutane ne muka koya daga Markus?

16 Markus wanda ya yi rayuwa a lokacin Yesu ya yi hidimomi sosai. Yana da ayyuka masu muhimmanci a hidimarsa ga Jehobah. Shi ne ya rubuta littafin da ke ɗauke da sunansa. Duk da haka, Markus ya nemi lokaci ya ƙarfafa Bulus, kuma Bulus ya san cewa zai iya gaya wa Markus ya taimaka masa. Alal misali, sa’ad da aka kashe kakar wata ’yar’uwa mai suna Angela, ta yi farin ciki don mutane sun ƙarfafa ta. Ta ce: “Idan abokanka suna a shirye su taimaka maka, zai yi maka sauƙi ka tattauna da su don ka san za su taimaka maka.” Muna iya tambayar kanmu, ‘An san ni da son ƙarfafa ’yan’uwa da kuma taimaka musu?’

KA ƘUDURI NIYYAR SANYAYA ZUCIYAR MUTANE

17. Ta yaya yin bimbini a kan 2 Korintiyawa 1:​3, 4 zai sa mu riƙa ƙarfafa mutane?

17 Yana da sauƙi mu ga ’yan’uwa maza da mata da suke bukatar ƙarfafawa. Muna iya yin amfani da abin da wani ya faɗa sa’ad da ya ƙarfafa mu don mu ƙarfafa wasu. Wata ’yar’uwa mai suna Nino da kakarta ta rasu ta ce: “Jehobah zai iya yin amfani da mu don ya ƙarfafa mutane idan mun ba shi zarafin yin hakan.” (Karanta 2 Korintiyawa 1:​3, 4.) Farida da aka ambata ɗazu ta ce: “Abin da ke 2 Korintiyawa 1:4 gaskiya ne. Idan wani ya ƙarfafa mu, muna iya yin amfani da kalamin da ya gaya mana ko abin da ya yi don mu ƙarfafa wani.”

18. (a) Me ya sa wasu suke jin tsoron ƙarfafa mutane? (b) Ta yaya za mu yi nasara wajen ƙarfafa mutane? Ka ba da misali.

18 Muna bukatar mu nemi hanyoyin taimaka ma mutane ko da muna jin tsoron yin hakan. Alal misali, muna iya jin tsoron cewa ba za mu san abin da za mu faɗa ko abin da za mu yi wa mutumin da ke cikin matsala ba. Wani dattijo mai suna Paul ya tuna ƙoƙarce-ƙoƙarcen da wasu suka yi don su ƙarfafa shi sa’ad da mahaifinsa ya rasu. Ya ce: “Na lura cewa bai yi wa wasu sauƙi su zo wurina don su ƙarfafa ni ba. Ba su san abin da za su faɗa ba. Amma na tuna irin farin ciki da na yi cewa suna so su ƙarfafa ni da kuma taimaka mini.” Hakazalika, bayan da aka yi wata muguwar girgizar ƙasa, wani ɗan’uwa mai suna Tajon da hakan ya shafa ya ce: “Ban tuna kome da mutane suka gaya min bayan girgizar ƙasar ba, amma na tuna cewa sun zo wurina don su tabbatar da cewa ba abin da ya same ni.” Za mu sami sakamako mai kyau wajen ƙarfafa mutane idan muka nuna mun damu da su.

19. Me ya sa ya kamata ka riƙa sanyaya zuciyar mutane?

19 Da yake ƙarshen wannan zamanin ya kusa, abubuwa za su ci gaba da lalacewa kuma za su daɗa wuya. (2 Tim. 3:13) Saboda haka, za mu bukaci ƙarfafawa domin mu ajizai ne kuma muna yin kuskure. Manzo Bulus ya jimre har ƙarshen rayuwarsa don ’yan’uwa sun ƙarfafa shi. Bari mu zama kamar Aristarkus mai aminci da kuma Tikikus mai riƙon amana. Ƙari ga haka, bari mu riƙa yi wa ’yan’uwanmu hidima kamar Markus. Idan muna yin hakan, za mu taimaka wa ’yan’uwanmu su ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci.​—1 Tas. 3:​2, 3.

^ sakin layi na 5 Manzo Bulus ya fuskanci mawuyacin yanayi sosai a rayuwarsa. A waɗannan lokuta, wasu abokan aikinsa sun sanyaya zuciyarsa sosai. Za mu tattauna halaye uku da suka sa waɗannan abokan aikinsa suka kafa misali mai kyau wajen sanyaya zuciyar mutane. Za mu kuma tattauna yadda za mu iya yin koyi da su.

^ sakin layi na 5 An canja wasu sunayen a wannan talifin.

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Aristarkus da Bulus sun jimre sa’ad da jirginsu ya yi hatsari.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: An ba Tikikus aikin idar da wasiƙun Bulus zuwa ga ikilisiyoyi.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Markus ya taimaka wa Bulus sosai.