Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Ba Mu Taba Kin Aikin da Jehobah Ya Ba Mu Ba

Ba Mu Taba Kin Aikin da Jehobah Ya Ba Mu Ba

BAYAN an yi ruwan sama da guguwa, sai kogin ya cika da taɓo da manyan duwatsu. Muna so mu haye kogin, amma ruwan ya riga ya rushe gadar. Ni da maigidana Harvey tare da wani ɗan’uwa da ke fassara yaren Amis mun tsorata kuma ba mu san abin da za mu yi ba. Hankalin ’yan’uwa da ke jiranmu a tsallake kogin ya tashi, amma sai muka soma hayewa. Mun saka ƙaramar motarmu a bayan wata babbar mota. Sai babbar motar ta soma haye kogin ba tare da mun ɗaure ƙaramar motarmu da igiya ko sarƙa ba. Kamar ba za mu haye ba, amma muna ta yin addu’a ga Jehobah har muka haye. Wannan abin ya faru ne a shekara ta 1971. A lokacin, muna gabashin teku da ke ƙasar Taiwan, kuma yana da nisa sosai daga ƙasarmu. Bari in ba ku labarinmu.

YADDA MUKA SOMA BAUTA WA JEHOBAH

Harvey ne ɗan fari cikin yara huɗu. Fiye da shekaru 80 da suka shige, iyalinsa sun soma bauta wa Jehobah a garin Midland Junction da ke yammacin Ostareliya a lokacin da ake fama da talauci a ƙasar. Harvey yana ƙaunar Jehobah kuma ya yi baftisma a lokacin da yake ɗan shekara 14. Ba da daɗewa ba, ya koyi yin dukan ayyukan da aka ba shi a ikilisiya. Sa’ad da yake yaro, ya taɓa ƙin karanta Hasumiyar Tsaro a taro don yana ganin bai cancanci yin hakan ba. Amma wani ɗan’uwa da ke tattaunawa da Harvey ya taimaka masa ya canja ra’ayinsa kuma ya ce masa, “Idan wani a ƙungiyar Jehobah ya ba ka wani aiki, yana ganin ka cancanci yin aikin!”​—2 Kor. 3:5.

Na koyi gaskiya a ƙasar Ingila tare da mahaifiyata da yayata. Da farko, mahaifina ba ya son Shaidun Jehobah, amma daga baya shi ma ya zama Mashaidi. Ba ya so in yi baftisma, amma na yi hakan sa’ad da nake ’yar shekara tara. Na kafa maƙasudin soma hidimar majagaba kuma in zama mai yin wa’azi a ƙasar waje. Amma mahaifina bai yarda in soma majagaba ba sai na kai ’yar shekara 21. Ba na so in jira har sai lokacin, amma sa’ad da nake shekara 16, mahaifina ya amince in koma Ostareliya in zauna da yayata. Na soma hidimar majagaba sa’ad da na kai shekara 18.

Ranar aurenmu a shekara ta 1951

Na haɗu da Harvey a Ostareliya kuma muna so mu zama masu wa’azi a ƙasar waje, sai muka yi aure a shekara ta 1951. Mun soma hidimar mai kula da da’ira bayan mun yi hidimar majagaba na shekaru biyu. Da’irarmu a Yammacin Ostareliya tana da girma sosai, saboda haka muna tuƙi zuwa karkara masu nisa a cikin hamada.

BURINMU YA CIKA

Ranar sauke karatu a Makarantar Gilead a Filin Wasan Yankee a 1955

A shekara ta 1954, an gayyace mu mu halarci aji na 25 na Makarantar Gilead. Ba da daɗewa, burinmu na yin wa’azi a ƙasar waje zai cika! Mun isa birnin New York ta jirgin ruwa kuma muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. A makarantar Gilead, muna koyan Sfanisanci, amma hakan ya yi wa Harvey wuya sosai don bai iya furta harafin nan r yadda ya kamata a yaren ba.

A makarantar, malaman sun sanar cewa waɗanda suke so su yi hidima a Jafan su rubuta sunayensu don su soma koyan yaren Jafan. Mun tsai da shawara cewa za mu jira ƙungiyar Jehobah ta tura mu duk inda take so. Ba da daɗewa ba, Albert Schroeder ɗaya cikin malaman ya lura cewa ba mu rubuta sunanmu ba. Sai ya ce mana: “Ku je ku yi tunani game da hakan.” Sa’ad da ba mu rubuta sunanmu ba, Ɗan’uwa Schroeder ya ce: “Ni da sauran malaman mun rubuta sunanku. Ku yi ƙoƙari ku koyi yaren Jafan.” Ya yi wa Harvey sauƙi ya koyi yaren.

Mun isa Jafan a shekara ta 1955 sa’ad da ake da masu shela 500 kawai a ƙasar. Harvey ɗan shekara 26 ne, ni kuma ’yar shekara 24. An tura mu yin hidima a birnin Kobe, inda muka yi wa’azi shekaru huɗu. Amma mun yi farin ciki da aka ce mu soma hidimar kula da da’ira, kuma mun yi hidimar a kusa da birnin Nagoya. Mun ji daɗin hidimarmu sosai, mun ji daɗin cuɗanya da ’yan’uwan, mun ji daɗin abincinsu da kuma ƙasar. Ba da daɗewa ba, mun samu wani damar yin aikin da Jehobah ya ba mu.

MUN FUSKANCI WASU ƘALUBALE A SABUWAR HIDIMARMU

Ni da Harvey da wasu masu wa’azi a ƙasar waje a Kobe Jafan a 1957

Bayan mun yi shekaru uku a hidimar kula da da’ira, ’yan’uwa da ke ofishinmu a Jafan sun tura mu yi wa mutane da ke yaren Amis wa’azi a Taiwan. Wasu cikin ’yan’uwa da ke yaren Amis sun yi ridda, kuma Ofishinmu da ke Taiwan suna bukatar ɗan’uwan da ya iya yaren don ya magance matsalar. * Muna jin daɗin hidimarmu a Jafan, saboda haka wannan canji ya yi mana wuya sosai. Amma Harvey ya koyi yin dukan ayyukan da aka ba shi.

Mun isa Taiwan a watan Nuwamba, 1962. A lokacin, akwai masu shela 2,271 a Taiwan, kuma yawancinsu mutanen Amis ne. Amma mun bukaci mu fara koyan yaren Caina. Muna da littafi guda na koyan yaren Caina kuma malamarmu ba ta iya Turanci ba, amma mun koyi yaren.

Ba da daɗewa ba da muka isa Taiwan, sai aka ba Harvey aikin kula da hidimar da ake a ƙasar. Ofishin ƙarami ne, saboda haka, Harvey ya samu lokacin yin dukan aikinsa a ofishin kuma ya yi aiki da ’yan’uwa da ke yaren Amis makonni uku a wata. Ban da haka, sau da yawa yakan yi hidimar mai kula mai ziyara, wadda ta ƙunshi yin jawabai a babban taro. Ko da Harvey ya yi jawaban a yaren Jafan, ’yan’uwa da ke yaren Amis za su fahimce shi. Amma gwamnati ba ta amince a riƙa taron addini a wani yare ba sai yaren Caina. Duk da cewa Harvey bai iya yaren Caina sosai ba, ya yi jawaban kuma wani ɗan’uwa ya fassara zuwa yaren Amis.

A lokacin, gwamnati ƙasar Taiwan ta kafa wata doka da ta hana mutane yin wasu ayyuka, saboda haka sai ’yan’uwa sun nemi izini kafin su yi babban taro. A lokacin, samun izinin yin babban taro ba shi da sauƙi kuma yakan ɗauki dogon lokaci kafin a ba da izinin. Idan ’yan sanda ba su ba da izinin a makon taron ba, Harvey yakan zauna a ofishin ’yan sanda har sai sun ba shi izini. Wannan dabara ce mai kyau domin ’yan sandan ba sa so su ga wani da ba ɗan ƙasarsu yana jira a ofishinsu.

LOKACI NA FARKO DA NA HAU DUTSE

Muna haye wani ƙaramin kogi a Taiwan don mu je wa’azi

Cikin makonni da muka yi da ’yan’uwan, mukan yi tafiya na awa guda muna hawan dutse da kuma haye koguna. Na tuna lokaci na farko da na hau dutse. Bayan mun ƙarya da safe, sai muka shiga mota da ƙarfe biyar da rabi muka tafi wani ƙauye mai nisa. Muka haye kogi kuma muka hau dutse mai tsayi sosai. Domin dutsen yana da tsayi sosai, ina ganin tafin ƙafar ɗan’uwa da ke gabana sa’ad da na ɗaga kai.

Da safen nan, Harvey ya fita wa’azi da ’yan’uwa da ke yankin, ni kuma na yi wa’azi ni kaɗai a wani ƙaramin ƙauye da mutane da ke yaren Jafan suke zama. Da ƙarfe ɗaya na rana, sai na ji kamar zan sume domin na yi sa’o’i da yawa ban ci abinci ba. Sa’ad da na haɗu da Harvey, duk ’yan’uwan sun tafi, amma ya yi musayar mujallu don ɗanyen ƙwai guda uku. Ya koya mini yadda ake shan ɗanyen ƙwai. Na sha guda ko da yake ban so yin hakan ba. Amma wa zai sha ƙwan da ya rage? Ni ce na sha domin Harvey ba zai iya sauko da ni ba idan na sume.

YIN WANKA A HANYAR DA BAN SABA BA

A wani taron da’ira, na fuskanci wata matsala. Muna zama a gidan wani ɗan’uwa da ke kusa da Majami’ar Mulki. Tun da mutanen Amis sun ɗauki yin wanka da muhimmanci sosai, matar mai kula da da’ira ta shirya abubuwan da muke bukata don yin wanka. Da yake Harvey ya shagala da aiki sosai, sai ya ce in fara yin wanka. Ta kawo mana bokiti uku, ɗaya mai ruwan sanyi, ɗaya da ruwan zafi, ɗayan kuma babu kome. Na yi mamaki da matar mai kula da da’irar ta ajiye kayan a gaban gidan da ke fuskantar Majami’ar Mulki, wajen da ’yan’uwa suke shirye-shirye don taron da za a yi. Sai na gaya mata ta ba ni labule, sai ta ba ni babban farin leda! Na yi tunani in koma bayan gidansu, amma da akwai agwagi da nake ganin za su bi ni idan na je wurin. Sai na yi tunani: ‘ ’Yan’uwa sun shagala da aiki, ba za su lura cewa ina wanka ba. Kuma ba za su yi farin ciki ba idan ban yi wanka ba. Sai na yi wankar!’

Mun saka tufafin mutanen Amis

AN WALLAFA LITTATTAFAI A YAREN AMIS

Harvey ya fahimci cewa yana wa ’yan’uwa masu yaren Amis wuya su ƙarfafa bangaskiyarsu domin ba su iya karatu ba kuma ba littattafai a yarensu. Tun da yake bai daɗe da aka soma rubuta yaren da harufan Romawa ba, yana da kyau a koya wa ’yan’uwan yadda za su karanta yarensu. Wannan aiki ne babba, amma daga baya ’yan’uwan sun koya game da Jehobah a yarensu. An wallafa littattafai a yaren Amis a wajen shekara ta 1966, kuma an soma wallafa Hasumiyar Tsaro a yaren Amis a shekara ta 1968.

Amma gwamnati ba ta son a riƙa rarraba littattafai da ba a wallafa a yaren Caina ba. Don a guji matsala, an rarraba Hasumiyar Tsaro a yaren Amis a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, mun yi watanni 17 muna amfani da Hasumiyar Tsaro da aka rubuta a yaren Mandarin da Amis. Idan wani yana gani kamar an taka doka, sai mu yi kamar muna yin amfani da littafin ne don koyar da yaren Caina. Tun wannan lokacin, ƙungiyar Jehobah ta wallafa littattafai da yawa a yaren Amis don a taimaka wa waɗannan mutanen su koyi game da Jehobah.​—A. M. 10:​34, 35.

LOKACIN TSABTACCEWA

’Yan’uwa da yawa da ke yaren Amis sun yi shekaru da yawa ba sa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Tun da yake ba su fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sosai ba, wasu suna lalata, da yin maye ko shan sigari da kuma tauna betel nut [wata ’ya’yar itace mai bugarwa] Harvey ya ziyarci ikilisiyoyi da yawa don ya taimaka wa ’yan’uwan sun san yadda Jehobah yake ɗaukan waɗannan batutuwa. A ɗaya cikin irin wannan tafiya ne abin da na ambata ɗazu ya faru.

’Yan’uwa masu sauƙin kai suna a shirye su yi canje-canje, amma wasu ba su yi hakan ba kuma wannan ya sa adadin masu shela a Taiwan ya ragu, daga masu shela fiye da 2,450 zuwa 900 cikin shekaru 20. Hakan ya sa mu sanyin gwiwa sosai, amma mun san cewa Jehobah ba zai albarkaci ƙungiyar da ba ta da tsabta ba. (2 Kor. 7:1) Da shigewar lokaci, sai ’yan’uwan suka soma bauta wa Jehobah yadda ya dace, saboda haka a yanzu Taiwan suna da masu shela fiye da 11,000.

Bayan shekara ta 1980, mun lura cewa ’yan’uwa a ikilisiyoyi da ke yaren Amis sun ƙarfafa bangaskiyarsu, kuma Harvey ya mai da hankali wajen taimaka wa masu yaren Caina. Ya yi farin cikin taimaka wa magidantan ’yan’uwa mata da yawa su zama Shaidun Jehobah. Na tuna cewa ya ce ya yi farin ciki sa’ad da ɗaya cikinsu ya yi addu’a ga Jehobah a lokaci na farko. Ni ma na yi farin cikin koya wa mutane da yawa masu son saƙonmu su kusaci Jehobah. Na yi farin cikin yin hidima tare da ɗa da kuma ’yar wata ɗalibata a ofishinmu da ke Taiwan.

RASHIN DA YA SA NI BAƘIN CIKI

Yanzu ba ni da maigida. Bayan mun yi wajen shekaru 59 da aure, Harvey ya rasu a ranar 1 ga Janairu, 2010, bayan ya yi fama da cutar kansa. Ya yi kusan shekaru 60 yana hidima ta cikakken lokaci. Har yanzu ina kewar sa sosai. Na yi farin cikin yin hidima tare da shi a ƙasashe biyu masu ban sha’awa! Mun koyi yin yare biyu masu wuya sosai, amma Harvey ya koyi rubuta su.

Bayan shekaru huɗu, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu sun ce zai fi kyau in koma Ostareliya domin na tsufa kuma ina bukatar taimako. Sai na yi tunani, ‘Ba na son in bar Taiwan.’ Amma Harvey ya koya min kada in ƙi kowane aikin da ƙungiyar Jehobah ta ba ni. Saboda haka, sai na koma Ostareliya. Daga baya, na fahimci cewa ya dace da aka ce in dawo.

Ina jin daɗin yin yaren Jafan da Caina sa’ad da nake kai mutane zagaya a Bethel

A yanzu ina hidima a ofishinmu da ke Ostareliya kuma ina wa’azi da ikilisiya a ƙarshen mako. A Bethel, ina farin cikin kai mutane da ke yaren Jafan da yaren Caina zagaya. Duk da haka, ina ɗokin ranar da za a yi tashin matattu da Jehobah ya yi alkawarinsa, na san cewa zai tuna da Harvey, mutumin da ba ya ƙin kowane aikin da ƙungiyar Jehobah ta ce ya yi.​—Yoh. 5:​28, 29.

^ sakin layi na 14 Ko da yake yaren Caina ne ake yi a Taiwan yanzu, a dā an yi shekaru da yawa ana yaren Jafan a ƙasar. Saboda haka, har ila mutane da yawa suna yaren Jafan a Taiwan.