Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 2

Darussa Daga “Almajirin Nan da Yesu Yake Ƙauna”

Darussa Daga “Almajirin Nan da Yesu Yake Ƙauna”

“Mu ƙaunaci juna, gama ƙauna daga wurin Allah take.”​—1 YOH. 4:7.

WAƘA TA 105 “Allah Ƙauna Ne”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya sanin cewa Allah yana ƙaunar ka yake sa ka ji?

YOHANNA ya rubuta cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Mun san cewa Allah ne ya halicce mu. Amma waɗannan kalmomin sun tuna mana cewa shi ne ya fara nuna mana ƙauna. Jehobah yana ƙaunar mu! Ƙaunarsa tana sa mu kasance da kwanciyar hankali da kuma gamsuwa.

2. Kamar yadda Matiyu 22:​37-40 suka nuna, waɗanne umurnai biyu ne suka fi muhimmanci, kuma me ya sa yake yi mana wuya mu bi na biyun?

2 Yana da muhimmanci Kiristoci su riƙa nuna ƙauna. Wannan umurni ne daga Allah. (Karanta Matiyu 22:​37-40.) Idan muka san Jehobah sosai, zai yi mana sauƙi mu yi biyayya ga umurni na farko da ya ba mu. Domin Jehobah kamiltacce ne, ya damu da mu kuma yana yi mana alheri. Amma yakan yi mana wuya mu bi umurni na biyu. Me ya sa? Domin ’yan’uwa a ikilisiya su ne maƙwabtanmu na kusa kuma su ajizai ne. A wasu lokuta, sukan yi da kuma faɗi wasu abubuwa da za su ɓata mana rai. Jehobah ya san cewa za mu fuskanci wannan matsalar. Don haka, ya sa wasu marubutan Littafi Mai Tsarki su koya mana dalilin da ya sa ya kamata mu ƙaunaci juna da kuma yadda za mu yi hakan. Ɗaya daga cikin marubutan shi ne Yohanna.​—1 Yoh. 3:​11, 12.

3. Mene ne Yohanna ya nanata?

3 A rubuce-rubucensa, Yohanna ya nanata cewa wajibi ne Kiristoci su riƙa nuna ƙauna. A labarin da Yohanna ya rubuta game da Yesu, ya yi amfani da kalmar nan “ƙauna” da “ƙaunaci” fiye da yadda aka yi amfani da ita a littafin Matiyu da Markus da kuma Luka. Yohanna yana wajen shekara ɗari sa’ad da ya rubuta littafin Yohanna da kuma wasiƙunsa uku. Waɗannan littattafan sun koya mana cewa wajibi ne mu riƙa nuna ƙauna a dukan abubuwan da muke yi. (1 Yoh. 4:​10, 11) Amma ya ɗauki lokaci kafin Yohanna ya koyi wannan darasin.

4. A kowane lokaci ne Yohanna ya nuna ƙauna?

4 Sa’ad da Yohanna yake matashi, ba a kowane lokaci ba ne ya nuna ƙauna. Alal misali, akwai lokacin da Yesu da manzanninsa suka bi ta Samariya sa’ad da za su je Urushalima. Mutanen wani ƙaramin ƙauye a Samariya sun ƙi su yi musu karimci. Mene ne Yohanna ya yi? Ya gaya wa Yesu ya ba shi izini ya umurci wuta ta sauko daga sama ta cinye mutanen ƙauyen! (Luk. 9:​52-56) Ban da haka, a wani lokaci kuma, Yohanna bai nuna ƙauna ga sauran manzannin Yesu ba. Shi da ɗan’uwansa Yaƙub sun sa mahaifiyarsu ta gaya wa Yesu cewa ya ba su babban matsayi a Mulkinsa. Sauran manzannin sun yi fushi sa’ad da suka ji abin da Yaƙub da Yohanna suka yi! (Mat. 20:​20, 21, 24) Duk da cewa Yohanna ya yi kurakure da yawa, Yesu ya ƙaunace shi.​—Yoh. 21:7.

5. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

5 A wannan talifin, za mu tattauna misalin Yohanna da kuma wasu abubuwan da ya rubuta game da ƙauna. Yayin da muke hakan, za mu koyi yadda za mu riƙa nuna wa ’yan’uwa ƙauna. Ƙari ga haka, za mu koyi wata hanya mai muhimmanci da magidanci zai nuna yana ƙaunar iyalinsa.

MUNA NUNA ƘAUNA TA AYYUKANMU

Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu ta wajen turo Ɗansa duniya don ya mutu a madadinmu (Ka duba sakin layi na 6-7)

6. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu?

6 Muna iya tunanin cewa nuna ƙauna yana nufin son mutum ko faɗin abubuwa masu kyau game da shi. Amma idan muna so mu nuna wa mutane ƙauna, muna bukatar mu yi hakan ta wajen yi musu alheri. (Gwada Yaƙub 2:​17, 26.) Alal misali, Jehobah yana ƙaunar mu. (1 Yoh. 4:19) Kuma ya nuna hakan ta kalmomi masu daɗi da ke Littafi Mai Tsarki. (Zab. 25:10; Rom. 8:​38, 39) Duk da haka, mun tabbata cewa Allah yana ƙaunar mu ba don abubuwan da ya faɗa ba, amma don ayyukansa. Yohanna ya ce: “Ga yadda Allah ya nuna mana ƙaunarsa. Ya aiko da makaɗaicin ɗansa zuwa cikin duniya domin mu sami rai ta wurinsa.” (1 Yoh. 4:9) Jehobah ya bar Ɗansa da yake ƙauna ya sha wahala kuma ya mutu dominmu. (Yoh. 3:16) Don haka, muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu.

7. Mene ne Yesu ya yi don ya nuna cewa yana ƙaunar mu?

7 Yesu ya tabbatar wa manzanninsa cewa yana ƙaunar su. (Yoh. 13:1; 15:15) Ya nuna cewa yana ƙaunar su da mu kuma ta abubuwan da ya faɗa da kuma ayyukansa. Ya ce: “Ba ƙaunar da ta fi wannan, wato mutum ya ba da ransa saboda abokansa.” (Yoh. 15:13) Idan muka yi tunanin abubuwan da Jehobah da Yesu suka yi mana, me ya kamata mu yi?

8. Mene ne 1 Yohanna 3:18 ta ce mu yi?

8 Za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da Yesu ta wajen yi musu biyayya. (Yoh. 14:15; 1 Yoh. 5:3) Yesu ya umurce mu mu ƙaunaci juna. (Yoh. 13:​34, 35) Ya kamata mu gaya wa ’yan’uwanmu cewa muna ƙaunar su kuma mu nuna hakan ta ayyukanmu. (Karanta 1 Yohanna 3:18.) Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu?

KA RIƘA ƘAUNAR ’YAN’UWANKA

9. Mene ne Yohanna ya yi domin yana ƙaunar mutane?

9 Da Yohanna ya zauna tare da mahaifinsa yana aikin kamun kifi don ya samu kuɗi. Amma maimakon hakan, ya yi amfani da rayuwarsa don ya taimaka wa mutane su koyi gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu. Irin rayuwar da Yohanna ya zaɓa bai da sauƙi. An tsananta masa, kuma a kusan ƙarshen ƙarni na farko, sa’ad da ya tsufa, an saka shi a kurkuku. (A. M. 3:1; 4:​1-3; 5:18; R. Yar. 1:9) Duk da cewa an saka shi a kurkuku domin yana wa’azi game da Yesu, ya nuna cewa yana ƙaunar mutane. Alal misali, sa’ad da Yohanna yake tsibirin Batmusa, ya rubuta littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna kuma ya tura wa ikilisiyoyi domin su san “abin da zai faru ba da daɗewa ba.” (R. Yar. 1:1) Kuma wataƙila bayan an sake shi ne ya rubuta labarin Yesu da kuma hidimarsa. Ban da haka, ya rubuta wasiƙu uku don ya ƙarfafa ’yan’uwa. Ta yaya za ka yi koyi da sadaukarwar da Yohanna ya yi?

10. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar mutane?

10 Abin da ka zaɓa ka yi da rayuwarka zai nuna ko kana ƙaunar mutane. Wannan duniyar za ta so ka riƙa yin tunani game da kanka kaɗai, ka yi amfani da lokacinka don neman kuɗi da yin suna. Maimakon haka, Kiristoci a dukan faɗin duniya suna amfani da lokacinsu don yin wa’azi sosai da kuma taimaka wa mutane su kusaci Jehobah. Wasu ma suna yin hidima na cikakken lokaci.

Muna nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu da iyalinmu ta ayyukanmu (Ka duba sakin layi na 11, 17) *

11. Ta yaya Kiristoci da yawa suke nuna cewa suna ƙaunar Jehobah da kuma ’yan’uwansu?

11 Kiristoci da yawa suna bukatar su yi aiki don su biya bukatunsu da na iyalinsu. Duk da haka, waɗannan Kiristocin suna yin iya ƙoƙarinsu don su tallafa wa ƙungiyar Jehobah. Alal misali, wasu suna taimakawa ta wajen ba da agaji, wasu suna aikin gine-gine, kuma kowa na da damar ba da gudummawa don wa’azin da ake yi a faɗin duniya. Suna yin waɗannan ayyukan ne domin suna ƙaunar Allah da kuma ’yan’uwansu. A kowane mako, muna nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwa ta wajen halartan taro da kuma yin kalami. Ko da mun gaji, muna halartan waɗannan taron. Ko da muna jin tsoro, mukan yi kalami. Kuma duk da cewa dukanmu mana da matsaloli, muna ƙarfafa ’yan’uwa kafin taron ko kuma bayan hakan. (Ibran. 10:​24, 25) Muna godiya domin abubuwan da ’yan’uwanmu Kiristoci suke yi!

12. A wace hanya ce kuma Yohanna ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan’uwansa?

12 Yohanna ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan’uwansa ba ta wajen yaba musu kaɗai ba, amma ta wajen ba su shawara. Alal misali, a wasiƙarsa, ya yaba wa ’yan’uwan domin bangaskiyarsu da kuma ayyukansu masu kyau, kuma ya yi musu gargaɗi sosai game da yin zunubi. (1 Yoh. 1:8–2:​1, 13, 14) Hakazalika, ya kamata mu riƙa yaba wa ’yan’uwa domin ayyuka masu kyau da suke yi. Amma idan wani ya soma nuna halin da bai dace ba ko kuma yin abin da zai iya ɓata dangantakarsa da Jehobah, muna iya nuna masa ƙauna ta wajen yi masa gargaɗi da basira. Muna bukatar ƙarfin zuciya don mu yi wa abokinmu gargaɗi, amma Littafi Mai Tsarki ya ce abokai suna yi wa juna gyara.​—K. Mag. 27:17.

13. Mene ne muke bukatar mu guji yi?

13 A wasu lokuta, muna nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwa ta abubuwan da muka guji yi. Alal misali, ba ma saurin fushi don abin da suka faɗa. Ka yi la’akari da abin da ya faru a kusan ƙarshen rayuwar Yesu a duniya. Ya gaya wa almajiransa cewa idan suna so su sami rai na har abada, dole ne su ci namansa su kuma sha jininsa. (Yoh. 6:​53-57) Abin da Yesu ya faɗa bai yi wa mabiyansa daɗi ba, saboda haka da yawa suka daina binsa, amma aminansa har da Yohanna ba su yi hakan ba. Ba su fahimci abin da Yesu yake nufi ba, kuma wataƙila furucinsa ya ba su mamaki. Duk da haka, aminan Yesu ba su ɗauka cewa abin da ya faɗa bai dace ba kuma ba su yi fushi ba. A maimakon haka, sun amince da shi domin sun san cewa abin da ya faɗa gaskiya ne. (Yoh. 6:​60, 66-69) Yana da muhimmanci mu guji barin abin da abokanmu suka faɗa ya yi saurin ɓata mana rai! A maimakon haka, mu ba su damar bayyana abin da suke nufi.​—K. Mag. 18:13; M. Wa. 7:9.

14. Me ya sa bai dace mu tsani ’yan’uwanmu ba?

14 Yohanna ya gargaɗe mu cewa kada mu tsani ’yan’uwanmu. Idan ba mu bi wannan umurnin ba, Shaiɗan yana iya yaudarar mu. (1 Yoh. 2:11; 3:15) Hakan ya faru da wasu a ƙarshen ƙarni na farko. A lokacin, Shaiɗan ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sa bayin Allah su tsani juna kuma ya sa kada su kasance da haɗin kai. A lokacin da Yohanna ya rubuta wasiƙunsa, mutanen da suke da halayen Shaiɗan sun shigo ikilisiya. Alal misali, Diyotarifis yana ƙoƙarin hana ’yan’uwa su kasance da haɗin kai a ikilisiya. (3 Yoh. 9, 10) Ya rena wakilan hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin. Ya yi ƙoƙarin fitar da waɗanda suke nuna karimci ga mutanen da ba ya so daga ikilisiya. Hakan bai dace ba ko kaɗan! A yau, Shaiɗan yana ƙoƙarin hana bayin Allah tallafa wa juna. Kada mu bari ƙiyayya ta raba mu.

KA ƘAUNACI IYALINKA

Yesu ya ce Yohanna ya kula da Maryamu kuma ya taimaka mata ta ci gaba da bauta wa Jehobah. Magidanta suna bukatar su riƙa biyan bukatun iyalinsu (Ka duba sakin layi na 15-16)

15. Mene ne ya kamata magidanci ya tuna?

15 Hanya ɗaya da magidanci zai nuna cewa yana ƙaunar iyalinsa ita ce ta wajen biyan bukatunsu. (1 Tim. 5:8) Amma yana bukatar ya tuna cewa taimaka wa iyalinsa ta kasance da dangantaka mai kyau da Allah shi ne ya fi muhimmanci. (Mat. 5:3) Ka yi la’akari da misalin da Yesu ya kafa wa magidanta. Littafin Yohanna ya gaya mana cewa, a lokacin da Yesu yake kan gungumen azaba, ya yi tunani game da iyalinsa. Yohanna da Maryamu mahaifiyar Yesu suna tsaye a wurin da aka rataye Yesu. Duk da cewa Yesu yana cikin azaba sosai, ya yi shiri don Yohanna ya riƙa kula da Maryamu. (Yoh. 19:​26, 27) Yesu yana da ’yan’uwa maza da mata da za su iya kula da mahaifiyarsa, amma kamar dai babu mabiyinsa a cikinsu. Don haka, Yesu ya tabbatar cewa akwai wanda zai kula da Maryamu da kuma ƙarfafa ta ta ci gaba da bauta wa Jehobah.

16. Waɗanne ayyuka ne Yohanna yake da su?

16 Yohanna yana da ayyuka da yawa. Shi manzo ne, don haka, wajibi ne ya saka ƙwazo a yin wa’azi. Kuma wataƙila yana da aure, saboda haka, ya bukaci ya biya bukatun iyalinsa da kuma taimaka musu su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (1 Kor. 9:5) Wane darasi ne magidanta za su iya koya a yau?

17. Me ya sa yake da muhimmanci magidanci ya taimaka wa iyalinsa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah?

17 Ɗan’uwa wanda shi magidanci ne yana da ayyuka da yawa masu muhimmanci. Alal misali, yana bukatar ya riƙa aiki tuƙuru a wurin aikinsa don a yabi Jehobah. (Afis. 6:​5, 6; Tit. 2:​9, 10) Kuma wataƙila yana da ayyuka a ikilisiya, kamar su zuwa ziyarar ƙarfafa da kuma yin ja-goranci a wa’azi. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da matarsa da kuma yaransa. Za su nuna godiya domin dukan abubuwan da yake yi don su kasance da ƙoshin lafiya, su riƙa farin ciki kuma su ci gaba da bauta wa Jehobah.​—Afis. 5:​28, 29; 6:4.

“KU ZAUNA A CIKIN ƘAUNAR DA NAKE NUNA MUKU”

18. Wane tabbaci ne Yohanna yake da shi?

18 Yohanna ya yi rayuwa shekaru da yawa kuma ya fuskanci matsaloli da yawa da za su iya sa ya yi sanyin gwiwa. Amma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya bi umurnin Yesu har da umurnin cewa ya ƙaunaci ’yan’uwansa. A sakamakon haka, Yohanna ya kasance da tabbaci cewa Jehobah da Yesu suna ƙaunar shi, kuma za su ba shi ƙarfin jimre matsalolin da ya fuskanta. (Yoh. 14:​15-17; 15:10; 1 Yoh. 4:16) Shaiɗan ko kuma magoya bayansa ba su iya hana Yohanna nuna cewa yana ƙaunar ’yan’uwansa ta kalmominsa da kuma ta ayyukansa ba.

19. Mene ne 1 Yohanna 4:7 ta ƙarfafa mu mu yi, kuma me ya sa?

19 Kamar Yohanna, muna rayuwa a duniyar da Shaiɗan ke mulki kuma ba ya ƙaunar kowa. (1 Yoh. 3:​1, 10) Ko da yake yana so mu daina ƙaunar ’yan’uwanmu, ba zai iya sa mu yin hakan ba sai dai in mun ba shi dama. Bari mu ƙuduri niyyar nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu ta furucinmu da kuma ayyukanmu. Idan muka yi hakan, za mu yi farin ciki sosai domin za mu kasance cikin iyalin Jehobah.​—Karanta 1 Yohanna 4:7.

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

^ sakin layi na 5 Da alama cewa Yohanna ne “almajirin nan da Yesu yake ƙauna.” (Yoh. 21:7) Har a lokacin da Yohanna yake matashi, yana da halaye masu kyau. Shekaru da yawa bayan haka, Jehobah ya yi amfani da shi don ya rubuta abubuwa da yawa game da ƙauna. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da Yohanna ya rubuta da kuma darussan da muka koya daga misalinsa.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Wani magidanci da yake da ayyuka da yawa yana taimaka wa da aikin ba da agaji, yana ba da gudummawa, kuma yana gayyatar wasu don su yi ibada ta iyali tare da shi da matarsa da yaransa.