Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

Ka Ci Gaba da Nuna Kauna

Ka Ci Gaba da Nuna Kauna

“Ku ba da kanku ga juna da ƙauna irin ta ’yan’uwa.”​—ROM. 12:10.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne ya nuna cewa iyalai da yawa ba sa ƙaunar juna sosai a yau?

LITTAFI MAI TSARKI ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, mutane za su zama “marasa ƙauna.” (2 Tim. 3:​1, 3) Muna ganin cikar wannan annabcin a yau. Alal misali, ma’aurata da yawa suna kashe aurensu don suna fushi da juna kuma yaransu suna ganin cewa ba a ƙaunar su. Har wasu iyalai da suke zama a gida ɗaya ma ba su da dangantaka ta kud da kud. Wani mai ba ma’aurata shawara ya ce: “Iyaye da yaransu ba sa tattaunawa da juna domin a yawancin lokaci, suna amfani da kwamfutarsu ko wayoyinsu ko kuma suna yin wasannin bidiyo. Ko da yake suna zama a gida ɗaya, ba su san juna ba sosai.”

2-3. (a) Kamar yadda Romawa 12:10 ta nuna, su wane ne za mu riƙa nuna wa ƙauna? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ba ma so mu zama marasa ƙauna kamar mutanen duniya. (Rom. 12:2) A maimakon haka, muna bukatar mu daɗa nuna ƙauna ga ’yan iyalinmu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. (Karanta Romawa 12:10.) Wace irin ƙauna ce wannan? Ƙauna ce da ke motsa iyalai su ƙulla dangantaka mai kyau da juna. Irin ƙaunar da muke bukatar mu riƙa nuna wa ’yan’uwa a ikilisiya ke nan. Idan muna nuna irin ƙaunar nan, hakan zai sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai kuma su bauta wa Jehobah da farin ciki.​—Mik. 2:12.

3 Don mu riƙa nuna irin wannan ƙaunar, bari mu ga darussan da za mu iya koya daga misalan da aka ambata a Littafi Mai Tsarki.

JEHOBAH “MAI YAWAN TAUSAYI” NE

4. Mene ne Yaƙub 5:11 ta ambata game da yadda Jehobah yake ƙaunar mu?

4 Littafi Mai Tsarki ya bayyana halaye masu kyau da Jehobah yake da su. Alal misali, ya ce “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Sanin hakan ya sa muna so mu zama abokansa. Amma Littafi Mai Tsarki ya daɗa cewa Jehobah “mai yawan tausayi” ne. (Karanta Yaƙub 5:11.) Wannan ya nuna yawan ƙaunar Jehobah a gare mu!

5. Ta yaya Jehobah yake nuna jinƙai, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

5 Littafin Yaƙub 5:11 ya ce Jehobah mai yawan tausayi ne da kuma jinƙai. (Fit. 34:6) Hanya ɗaya da Jehobah yake nuna mana jinƙai ita ce ta wajen gafarta kurakuranmu. (Zab. 51:1) A Littafi Mai Tsarki, jinƙai ba ya nufin gafarta wa mutumin da ya yi mana laifi kawai. Jinƙai yana nufin yadda mutum yake ji sa’ad da ya ga wani a mawuyacin yanayi kuma ya yi ƙoƙari ya taimaka masa. Jehobah ya ce yana so ya taimaka mana sosai fiye da yadda mahaifiya take so ta taimaka wa jaririnta. (Isha. 49:15) Domin Jehobah mai jinƙai ne, yana taimaka mana sa’ad da muke cikin matsala. (Zab. 37:39; 1 Kor. 10:13) Muna nuna wa ’yan’uwanmu jinƙai sa’ad da muka gafarta musu kuma muka guji riƙe su a zuciya sa’ad da suka yi mana laifi. (Afis. 4:32) Wata hanya mai muhimmanci da za mu nuna wa ’yan’uwanmu jinƙai ita ce ta wajen taimaka musu sa’ad da suke cikin matsala. Muna yin koyi da Jehobah Allah mai ƙauna sa’ad da muka nuna wa ’yan’uwanmu jinƙai.​—Afis. 5:1.

JONATHAN DA DAUDA SUN ƘAUNACI JUNA SOSAI

6. Ta yaya Jonathan da Dauda suka nuna cewa suna ƙaunar juna?

6 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran ’yan Adam ajizai da suke ƙaunar juna sosai. Ka yi la’akari da labarin Jonathan da Dauda. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yonatan  . . . ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar ransa.” (1 Sam. 18:1) Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarki bayan Saul. Hakan ya sa Saul ya tsani Dauda kuma ya yi ƙoƙari ya kashe shi. Amma Jonathan bai goyi bayan mahaifinsa ba. Jonathan da Dauda sun yi wa juna alkawari cewa za su ci gaba da zama aminai kuma su taimaka wa juna.​—1 Sam. 20:42.

Jonathan da Dauda sun zama abokai duk da cewa shekarunsu ya bambanta (Ka duba sakin layi na 6-9)

7. Mene ne zai iya hana Jonathan da Dauda zama abokai?

7 Yadda Jonathan da Dauda suka zama abokai abin mamaki ne, domin akwai abubuwa da yawa da za su iya hana su zama abokai. Alal misali, Jonathan ya girme Dauda da wajen shekara talatin. Jonathan bai yi tunanin cewa babu ruwansa da wannan matashin ba. Jonathan ya daraja Dauda sosai.

8. Mene ne kake gani ya sa Jonathan da Dauda suka zama abokai na ƙwarai?

8 Da Jonathan ya yi kishin Dauda tun da yake shi ne ɗan Sarki Saul, kuma shi ne ya kamata ya gāji mulkin babansa. (1 Sam. 20:31) Amma Jonathan mai sauƙin kai ne kuma yana da aminci ga Jehobah. Don haka, ya amince da zaɓin da Jehobah ya yi na naɗa Dauda ya zama sarki. Kuma ya nuna wa Dauda aminci duk da cewa hakan ya ɓata wa mahaifinsa rai.​—1 Sam. 20:​32-34.

9. Ta yaya muka san cewa Jonathan bai yi kishin Dauda ba?

9 Jonathan yana ƙaunar Dauda, don haka, bai yi kishin sa ba. Jonathan jarumi ne kuma ya iya amfani da kwari da baka. Mutane sun ce Jonathan da mahaifinsa “sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.” (2 Sam. 1:​22, 23) Saboda haka, da Jonathan ya yi burga don abubuwan da ya cim ma. Amma Jonathan bai yi gasa da Dauda ba ko kuma ya riƙe shi a zuciya. A maimakon haka, yadda Dauda ya nuna ƙarfin zuciya kuma ya dogara ga Jehobah ya burge Jonathan. Alal misali, bayan da Dauda ya kashe Goliath ne Jonathan ya soma ƙaunar sa. Ta yaya za mu iya nuna wa ’yan’uwanmu irin wannan ƙaunar?

TA YAYA ZA MU RIƘA NUNA ƘAUNA A YAU?

10. Mene ne ma’anar furucin nan ku yi “ƙaunar juna sosai da zuciya ɗaya”?

10 Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa “ƙaunar juna sosai da zuciya ɗaya.” (1 Bit. 1:​22, New World Translation) Jehobah ya kafa mana misali mai kyau. Yana ƙaunar mu sosai kuma babu abin da zai sa ya daina yin hakan idan mun kasance da aminci. (Rom. 8:​38, 39) Kalmar nan “sosai” a Helenanci tana iya nufin mutum ya yi iya ƙoƙarinsa don ya nuna ƙauna. A wasu lokuta, bai da sauƙi mu ƙaunaci ’yan’uwanmu. Sa’ad da ’yan’uwanmu suka yi abin da ya ɓata mana rai, muna bukatar mu ci gaba da jimrewa “da juna cikin ƙauna.” Kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ‘kiyaye ɗayantuwar nan da ruhu ya ba mu, ta wurin salamar da ta ɗaure mu tare.’ (Afis. 4:​1-3) Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa zaman lafiya da ’yan’uwanmu, ba za mu mai da hankali ga kurakurensu ba. Amma za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ɗauki ’yan’uwanmu kamar yadda Jehobah yake ɗaukan su.​—1 Sam. 16:7; Zab. 130:3.

Bulus ya gaya wa Afodiya da Sintiki su zama abokan juna. A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu zauna lafiya da ’yan’uwanmu (Ka duba sakin layi na 11)

11. Me ya sa nuna ƙauna yake iya yi mana wuya a wasu lokuta?

11 Ba shi da sauƙi mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu, musamman ma sa’ad da muka san kasawarsu. Kiristoci a ƙarni na farko sun fuskanci wannan matsalar. Alal misali, Afodiya da Sintiki sun yi “fama tare da [Bulus] a cikin aikin shelar labari mai daɗi.” Amma Afodiya da Sintiki sun sami saɓani. Don haka, Bulus ya ƙarfafa su cewa “su shirya da juna saboda su na Ubangiji ne.”​—Filib. 4:​2, 3.

Dattawa matasa da kuma tsofaffi suna iya ƙulla abokantaka na kud da kud da juna (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya za mu soma ƙaunar ’yan’uwanmu?

12 Ta yaya za mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu sosai a yau? Idan muka san ’yan’uwanmu sosai, yana iya yi mana sauƙi mu fahimce su kuma mu soma ƙaunar su. Muna iya zama abokansu ko da shekarunmu ba ɗaya ba ne ko kuma al’adarmu ta bambanta. Ka tuna cewa Jonathan ya girme Dauda da wajen shekara 30, amma duk da haka, sun zama aminan juna. Shin akwai wani a ikilisiyarku da ya girme ka ko kuma ka girme shi da za ka so ka zama abokinsa? Ta yin hakan, za ka nuna cewa kana ƙaunar “’yan’uwa masu bin Yesu” a faɗin duniya.​—1 Bit. 2:17.

Ka duba sakin layi na 12 *

13. Me ya sa ba za mu iya kusantar kowa a ikilisiya ba?

13 Nuna ƙauna ga dukan ’yan’uwanmu yana nufin cewa za mu kusaci kowa a cikin ikilisiya? A’a, hakan ba zai yiwu ba. Ba laifi ba ne cewa wasu da ke son abubuwan da muke so za su zama abokanmu. Yesu ya kira dukan manzanninsa “abokai,’ amma yana ƙaunar Yohanna sosai. (Yoh. 13:23; 15:15; 20:2) Duk da haka, Yesu bai kula da shi fiye da sauran almajiran ba. Alal misali, sa’ad da Yohanna da ɗan’uwansa Yaƙub suka ce Yesu ya ba su matsayi mai girma a Mulkinsa, Yesu ya ce musu: “Zama a damana, ko a haguna, ba ni nake da ikon bayarwa ba.” (Mar. 10:​35-40) Ya kamata mu yi koyi da Yesu domin bai kula da abokansa fiye da sauran mutane ba. (Yaƙ. 2:​3, 4) Yin hakan ba zai sa ikilisiya ta kasance da zaman lafiya ba.​—Yahu. 17-19.

14. Kamar yadda Filibiyawa 2:3 ta nuna, mene ne zai taimaka mana mu guji nuna cewa mun fi wasu?

14 Idan muna ƙaunar juna, za mu guji nuna cewa mun fi wasu a ikilisiya. Mu tuna cewa Jonathan bai yi kishin Dauda ba, kuma bai yi ƙoƙarin zama sarki ba. Dukanmu za mu iya yin koyi da Jonathan. Kada mu yi kishin ’yan’uwanmu don baiwar da suke da shi, amma cikin sauƙin kai, mu ‘ɗauki ɗan’uwanmu da muhimmanci fiye da kanmu.’ (Karanta Filibiyawa 2:3.) Ka tuna cewa kowa zai iya yin abin da zai taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Idan muka kasance da sauƙin kai, za mu iya ganin halayen ’yan’uwanmu masu kyau kuma mu amfana daga amincinsu.​—1 Kor. 12:​21-25.

15. Mene ne ka koya daga labarin Tanya da yaranta?

15 Sa’ad da muke fuskantar matsaloli, Jehobah yana ƙarfafa mu ta wajen ƙaunar da ’yan’uwa suke nuna mana da kuma yadda suke taimaka mana. Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata iyali a ranar Asabar bayan sun halarci taron ƙasashe da aka yi a Amirka. Jigon taron shi ne “Ƙauna Ba Ta Ƙarewa!” kuma an yi shi a shekara ta 2019. Mahaifiyar mai suna Tanya da take da yara uku ta ce: “Sa’ad da muke komawa masaukinmu, wata mota ta bugi motarmu. Babu wanda ya ji rauni, amma mun tsorata sosai kuma muka fito daga motarmu muka tsaya a bakin titi. Sai wani ya kira mu mu zo mu shiga motarsu domin kada wani abu ya same mu. Ɗan’uwa ne da yake komawa gida bayan taron. Ba shi kaɗai ba ne ya tsaya don ya taimaka mana ba. ’Yan’uwa biyar daga ƙasar Sweden da suka halarci taron su ma sun tsaya. ’Yan’uwa matan sun rungume ni da ’yata kuma hakan ya kwantar mana da hankali! Na tabbatar musu cewa muna lafiya kuma suna iya tafiya. Amma sun zauna tare da mu har sai da ma’aikatan kiwon lafiya suka zo kuma ’yan’uwan sun tabbatar da cewa mun sami dukan abin da muke bukata. A wannan mawuyacin lokaci, mun ga cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Abin da ya faru da mu ya sa mun daɗa ƙaunar ’yan’uwanmu da Jehobah da kuma nuna masa godiya.” Za ka iya tuna lokacin da kake bukatar taimako kuma wani ɗan’uwa ya nuna maka ƙauna?

16. Waɗanne dalilai ne muke da su na nuna ƙauna ga juna?

16 Ka yi tunanin amfanin nuna wa juna ƙauna. Za mu taimaka wa ’yan’uwanmu su bauta wa Jehobah da farin ciki sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Za mu daɗa sa ’yan’uwanmu a ikilisiya su kasance da haɗin kai. Za mu nuna cewa mu mabiyan Yesu na gaskiya ne kuma hakan zai sa mutane su zo su bauta wa Jehobah. Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa za mu ɗaukaka Jehobah “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya!” (2 Kor. 1:3) Bari dukanmu mu kasance da ƙauna kuma mu ci gaba da nuna ta!

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Yesu ya ce za a san almajiransa domin irin ƙaunar da suke wa juna. Dukanmu muna ƙoƙarin nuna irin wannan ƙaunar. Ya kamata mu nuna wa ’yan’uwa a ikilisiya ƙauna kamar yadda muke ƙaunar ’yan iyalinmu. Wannan talifin zai taimaka mana mu daɗa nuna wa ’yan’uwa a ikilisiya ƙauna.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Wani dattijo da ya tsufa ya marabci wani dattijo matashi zuwa gidansa. Su da matansu suna nuna wa juna karimci.