Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 1

Ka Kwantar da Hankalinka Kuma Ka Dogara ga Jehobah

Ka Kwantar da Hankalinka Kuma Ka Dogara ga Jehobah

JIGON SHEKARA TA 2021: Za ku sami ƙarfi idan kuka kwantar da hankalinku kuma kuka dogara da ni.​—ISHA. 30:15.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar Sarki Dauda, wace tambaya ce wasu cikinmu suke yi?

BABU wani cikinmu da ke son fuskantar matsaloli a rayuwarsa. Ba mai so ya riƙa yawan damuwa, amma a wasu lokuta muna fama da matsaloli. Shi ya sa wasu bayin Jehobah suke masa irin tambayar da Sarki Dauda ya yi masa, cewa: “Har yaushe zan jimre da wahalar nan, in cika da damuwa a raina dukan yini?”​—Zab. 13:2.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ko da yake mukan damu a wasu lokuta, da akwai abubuwan da za mu iya yi don mu rage yin hakan. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwa da za su iya sa mu alhini. Sa’an nan za mu tattauna abubuwa shida da za su taimaka mana mu natsu sa’ad da muke fuskantar matsaloli.

MENE NE ZAI IYA SA MU DAMUWA?

3. Waɗanne matsaloli ne muke fuskanta, kuma za mu iya hana su faruwa kuwa?

3 Abubuwa da yawa suna sa mu damuwa, kuma ba za mu iya hana wasu cikinsu faruwa ba. Alal misali, ba za mu iya hana farashin abinci da tufafi da kuma kuɗin haya ƙaruwa ba. Abokan aikinmu ko abokan makarantarmu za su iya jarraba mu, kuma ba za mu iya hana su yin hakan ba. Ƙari ga haka, ba za mu iya sa mutane su rage yin mugunta a unguwarmu ba. Muna fuskantar waɗannan matsalolin domin muna zama a duniyar da yawancin mutane ba sa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Shaiɗan, wanda ke mulkin wannan duniyar ya san cewa matsalolin da suka cika ko’ina za su hana wasu mutane bauta wa Jehobah. (Mat. 13:22; 1 Yoh. 5:19) Shi ya sa matsalolin da ke sa mutane alhini sun cika duniya!

4. Me zai iya faruwa idan muna yawan damuwa game da matsalolinmu?

4 Waɗannan matsaloli suna iya shawo kanmu. Alal misali, muna iya damuwa cewa ba mu da isashen kuɗin biyan bukatunmu ko za mu yi rashin lafiya ko kuma mu rasa aikinmu. Muna iya damuwa cewa idan an jarraba mu, ba za mu kasance da aminci ga Jehobah ba. Kuma nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan da magoya bayansa za su kai wa mutanen Allah hari. Saboda haka, muna iya damuwa game da abin da za mu yi a lokacin. Muna iya tunanin cewa, ‘Laifi ne in riƙa damuwa game da abubuwan nan?’

5. Me Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Kada ku damu”?

5 Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Kada ku damu.” (Mat. 6:25) Hakan yana nufin cewa Yesu ba ya so mu damu game da kome ne? A’a! Ka tuna cewa a zamanin dā, wasu bayin Jehobah sun damu, amma Jehobah bai yi fushi da su ba. * (1 Sar. 19:4; Zab. 6:3) Yesu yana ƙarfafa mu ne. Ba ya so mu riƙa damuwa ainun game da biyan bukatunmu har hakan ya shafi ibadarmu ga Jehobah. Me ya kamata mu yi sa’ad da wani abu ya dame mu?​—Ka duba akwatin nan “ Yadda Za Ku Yi Hakan.”

ABUBUWA SHIDA DA ZA SU KWANTAR MANA DA HANKALI

Ka duba sakin layi na 6 *

6. Kamar yadda Filibiyawa 4:​6, 7 suka nuna, mene ne zai iya kwantar mana da hankali?

6 (1Ka riƙa addu’a a kai a kai. Ka yi addu’a ga Jehobah idan wani abu yana damunka. (1 Bit. 5:7) Jehobah zai amsa addu’aka ta wajen ba ka “salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.” (Karanta Filibiyawa 4:​6, 7.) Jehobah yana amfani da ruhunsa don ya sa mu kwantar da hankalinmu.​—Gal. 5:22.

7. Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke addu’a?

7 Sa’ad da kake addu’a, ka gaya wa Jehobah abin da ke zuciyarka. Ka gaya masa matsalolinka da kuma yadda kake ji. Idan akwai yadda za a magance matsalar, ka roƙi Jehobah ya ba ka hikimar sanin abin da za ka yi da kuma ƙarfin yin hakan. Idan babu yadda za ka magance matsalar, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka daina damuwa ainun. Idan ka gaya wa Jehobah abin da ke damunka, da shigewar lokaci, za ka ga yadda ya amsa addu’arka. Kada ka daina yin addu’a idan Jehobah bai amsa addu’ar nan da nan ba. Jehobah yana so ka gaya masa dukan matsalolinka kuma ka ci gaba da yin addu’a game da batun.​—Luk. 11:​8-10.

8. Me ya kamata mu ambata a addu’armu?

8 Sa’ad da kake gaya wa Jehobah matsalolinka, ka riƙa gode masa don abubuwan da ya yi maka. Zai dace mu riƙa tuna abubuwa masu kyau da muke da su ko da muna fuskantar matsaloli. Amma, mene ne za ka yi idan ba ka san yadda za ka gaya wa Jehobah yadda kake ji ba? Ka tuna cewa Jehobah zai amsa addu’arka ko da ‘Ya Allah ka taimaka mini’ kawai ka ce.​—2 Tar. 18:31; Rom. 8:26.

Ka duba sakin layi na 9 *

9. Mene ne za mu yi idan muna jin tsoro?

9 (2Ka dogara ga hikimar Jehobah ba ta kanka ba. A zamanin annabi Ishaya, Yahudawa sun ji tsoro cewa Assuriyawa za su kawo musu hari. Saboda haka, sun nemi taimako daga ƙasar Masar. (Isha. 30:​1, 2) Jehobah ya gaya musu cewa zaɓin da suka yi zai jefa su cikin matsala. (Isha. 30:​7, 12, 13) Jehobah ya tura Ishaya ya gaya musu abin da za su yi don su sami kwanciyar hankali. Ya ce: A “cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami ƙarfi.”​—Isha. 30:15b.

10. A waɗanne yanayoyi ne za mu nuna cewa mun dogara ga Jehobah?

10 Ta yaya za mu dogara ga Jehobah? Ga wasu misalai. A ce an ba ka aiki da za a biya ka albashi mai tsoka amma za ka yi aiki na sa’o’i da yawa kuma aikin zai hana ka bauta wa Jehobah yadda ya kamata. Ko a ce wata a wurin aikinku da ba ta bauta wa Jehobah ta soma nuna cewa tana sonka. Ko kuwa wani danginka ya gaya maka cewa: “Babu ruwana da kai idan ba ka daina bauta wa Jehobah ba.” Irin yanayin nan yana da wuya sosai, amma Jehobah zai taimake ka ka san abin da za ka yi. (Mat. 6:33; 10:37; 1 Kor. 7:39) Amma tambayar ita ce, Za ka dogara ga Jehobah kuma ka bi umurninsa kuwa?

Ka duba sakin layi na 11 *

11. Waɗanne labaran Littafi Mai Tsarki ne za su iya sa mu natsu sa’ad da ake tsananta mana?

11 (3Ka koyi darasi daga mutanen kirki da marasa kirki. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da misalan mutane da suka kwantar da hankalinsu kuma suka dogara ga Jehobah. Yayin da kake nazarin labaransu, ka yi tunanin abin da ya taimaka musu su natsu sa’ad da ake tsananta musu. Alal misali, manzannin Yesu ba su ji tsoro ba sa’ad da majalisar Yahudawa suka ce su daina yin wa’azi. Maimakon haka, sun ce da gaba gaɗi: “Dole ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mu yi wa mutum.” (A. M. 5:29) Manzannin ba su ji tsoro a lokacin da aka yi musu bulala ba. Me ya sa? Domin sun san cewa Jehobah yana tare da su, kuma yana farin ciki da su. Saboda haka, sun ci gaba da wa’azi. (A. M. 5:​40-42) Hakazalika, sa’ad da ake so a kashe Istifanus, hankalinsa bai tashi ba kuma Littafi Mai Tsarki ya ce fuskarsa “ta zama kamar ta mala’ika.” (A. M. 6:​12-15) Me ya sa? Domin ya tabbata cewa Jehobah ya amince da shi.

12. Kamar yadda 1 Bitrus 3:14 da 4:14 suka nuna, me zai iya sa mu farin ciki sa’ad da ake tsananta mana?

12 Manzannin Yesu suna da tabbaci cewa Jehobah yana tare da su. Kuma ya ba su ikon yin mu’ujizai. (A. M. 5:​12-16; 6:8) Amma Jehobah bai ba mu wannan ikon ba a yau. Duk da haka, Jehobah ya tabbatar mana cewa yana farin ciki da mu sa’ad da ake tsananta mana don yin nufinsa. (Karanta 1 Bitrus 3:14; 4:14.) Saboda haka, maimakon mu riƙa tunanin abin da za mu yi sa’ad da aka tsananta mana a nan gaba, ya kamata mu mai da hankali a kan yadda za mu ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Jehobah zai taimaka mana, ya kuma cece mu. Ya kamata mu amince da alkawuran Yesu yadda almajiransa suka yi. Yesu ya ce: “Zan ba ku kalmomi da hikima yadda ko ɗaya daga cikin masu gāba da ku ba zai iya juye maganar ko ya yi mūsun abin da kuka ce ba.” Muna da tabbaci cewa: ‘Idan muka jimre, za mu tsira.’ (Luk. 21:​12-19) Kuma ka tuna cewa Jehobah ba zai manta da kome game da bayinsa masu aminci da suka rasu ba kuma zai yi amfani da bayanan nan don ya ta da su.

13. Ta yaya za mu amfana daga yin nazarin labaran waɗanda ba su dogara ga Jehobah ba?

13 Muna iya koyan darasi daga waɗanda ba su natsu ba kuma ba su dogara ga Jehobah ba. Yin nazarin waɗannan misalan zai taimaka mana mu guji yin kurakuren da suka yi. Alal misali, a lokacin da Sarki Asa ya soma mulki kuma sojojin maƙiyansa masu yawa suka kawo masu hari, ya dogara ga Jehobah kuma ya yi nasara. (2 Tar. 14:​9-12) Daga baya, sa’ad da Sarki Baasha na Isra’ila da rundunarsa da ba su kai na dā yawa ba suka kawo wa Asa hari, bai nemi taimakon Jehobah ba. Maimakon haka, ya biya sojojin Suriya su taimaka masa. (2 Tar. 16:​1-3) Ƙari ga haka, sa’ad da Asa yake rashin lafiya mai tsanani kuma ya kusan mutuwa, bai nemi taimakon Jehobah ba.​—2 Tar. 16:12.

14. Mene ne za mu iya koya daga kurakuren Asa?

14 A lokacin da Asa ya fara mulkin, ya dogara ga Jehobah sa’ad da ya fuskanci matsaloli. Amma daga baya, bai nemi taimakon Allah ba. Maimakon haka, ya yi ƙoƙari ya magance matsalolin da kansa. Idan ba mu yi la’akari sosai ba, za mu ga kamar yadda Asa ya nemi taimakon Suriyawa don ya yaƙi Isra’ilawa ya dace. Amma salamarsu ba ta dawwama ba. Jehobah ya tura wani annabi ya gaya masa cewa: “Tun da yake ka dogara a kan Suriya maimakon ka dogara a kan Yahweh Allahnka, to, sojojin Suriya sun kuɓuta daga hannunka.” (2 Tar. 16:7) Ya kamata mu nemi taimakon Jehobah ta wajen bincika Kalmarsa, maimakon mu ɗauka cewa za mu iya magance matsalolinmu da kanmu. Ko a lokacin da muke bukatar yanke shawara ta gaggawa, za mu yi nasara idan mun dogara ga Jehobah.

Ka duba sakin layi na 15 *

15. Mene ne za mu iya yi sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki?

15 (4Ka haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ka karanta ayoyin da suka nuna muhimmancin kwantar da hankalinmu da kuma dogara ga Jehobah, ka yi ƙoƙari ka haddace su. Abin da zai taimaka maka ka haddace su, shi ne karanta su da babbar murya, ko kuma rubuta su don ka riƙa karanta su a kai a kai. An umurci Joshua ya riƙa karanta littafin koyarwar a kai a kai don ya yi nasara. Abin da ya karanta zai taimaka masa don kada ya ji tsoro, amma ya kasance da gaba gaɗin yi wa mutanen Allah ja-goranci. (Josh. 1:​8, 9) Ayoyi da yawa a Kalmar Allah za su taimaka maka ka kwantar da hankalinka a yanayoyi da za su sa ka jin tsoro ko damuwa.​—Zab. 27:​1-3; K. Mag. 3:​25, 26.

Ka duba sakin layi na 16 *

16. Ta yaya Jehobah yake amfani da ’yan’uwa don ya taimaka mana?

16 (5Ka riƙa cuɗanya da mutanen Allah. Jehobah yana yin amfani da ’yan’uwanmu don ya taimaka mana mu kwantar da hankalinmu kuma mu dogara gare shi. Muna amfana daga jawaban da ake yi a taronmu da kalami masu ban ƙarfafa na ’yan’uwanmu da kuma yin cuɗanya da su. (Ibran. 10:​24, 25) Abokanmu a ikilisiya za su ƙarfafa mu sosai idan muka gaya musu abin da ke damunmu. “Kalmar ƙarfafawa” da amininmu ya gaya mana za ta taimaka mana mu daina damuwa ainun.​—K. Mag. 12:25.

Ka duba sakin layi na 17 *

17. Kamar yadda Ibraniyawa 6:19 ta nuna, ta yaya begenmu zai kwantar da hankalinmu sa’ad da muke fuskantar matsaloli?

17 (6Ka ƙarfafa begenka. Begenmu na kamar anka da ke riƙe jirgin ruwa. Yana sa mu kasance da ƙarfi sa’ad da muke fuskantar mawuyacin yanayi ko alhini. (Karanta Ibraniyawa 6:19.) Ka riƙa bimbini a kan alkawuran da Jehobah ya yi cewa za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba. A lokacin, ba za mu riƙa damuwa ba. (Isha. 65:17) Ka yi tunani cewa kana cikin aljanna inda mawuyacin yanayi ba zai sake kasancewa ba. (Mik. 4:4) Ban da haka, za ka ƙarfafa begenka sa’ad da kake wa’azi game da aljanna. Ka yi iya ƙoƙarinka a wa’azi da kuma almajirantarwa. Idan ka yi hakan, za ka ‘sami cikawar abubuwan nan da ka sa zuciya a kansu’ har zuwa ƙarshe.​—Ibran. 6:11.

18. Waɗanne matsaloli ne za mu fuskanta a nan gaba, kuma ta yaya za mu jimre su?

18 Domin mun kusan ƙarshen wannan zamanin, za mu fuskanci matsalolin da za su tayar mana da hankali. Jigon shekararmu na 2021 zai sa mu ga yadda yin dogara ga Jehobah zai taimaka mana mu jimre da matsaloli kuma mu kwantar da hankalinmu. Bari mu nuna ta ayyukanmu a shekara ta 2021, cewa mun gaskata da alkawarin da Jehobah ya yi cewa: Za ku sami ƙarfi idan kuka kwantar da hankalinku kuma kuka dogara da ni.​Isha. 30:15.

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu

^ sakin layi na 5 Jigonmu na shekara 2021 ya nuna muhimmancin dogara ga Jehobah yayin da muke fuskantar mawuyacin yanayi a yanzu da kuma nan gaba. A wannan talifin, za a tattauna hanyoyin da za mu iya bin shawarar da ke jigon wannan shekarar.

^ sakin layi na 5 Wasu ’yan’uwa masu aminci suna fama da yawan alhini ko tsoro. Irin wannan matsalar rashin lafiya ne mai tsanani kuma ba shi Yesu yake magana a kai ba.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: (1) Wata ’yar’uwa tana addu’a sosai game da abubuwan da ke damunta.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: (2) A lokacin hutun rana a wurin aiki, tana karanta Kalmar Allah don ta san matakin da za ta ɗauka.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTO: (3) Tana bimbini a kan misalai masu kyau da marasa kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTO: (4) Tana manna wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da take so ta haddace a jikin firijinta.

^ sakin layi na 71 BAYANI A KAN HOTO: (5) Tana jin daɗin yin cuɗanya da abokanta a wa’azi.

^ sakin layi na 73 BAYANI A KAN HOTO: (6) Tana ƙarfafa begenta ta wajen yin tunani a kan abubuwa masu kyau da za su faru a nan gaba.