Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rubutun da ke dutsen: “Cursed be Hagaf son of Hagav by Yahweh Sabaot”

Ka Sani?

Ka Sani?

Ta yaya rubutun da ke wani allon dutse ya tabbatar da abin da ke Littafi Mai Tsarki?

AKWAI wani allon dutse da aka yi rubutu a kansa a wajen shekara ta 700 zuwa 600 kafin haihuwar Yesu, da ke ma’adanar kayayyakin tarihi da ake kira Bible Lands Museum a Urushalima. An samo dutsen a wani kogo da ake binne mutane kusa da birnin Hebron a Isra’ila. An rubuta a dutsen cewa: “Cursed be Hagaf son of Hagav by Yahweh Sabaot,” wato “Yahweh mai runduna ya tsine wa Hagaf ɗan Hagav.” Ta yaya wannan rubutun ya tabbatar da abin da ke Littafi Mai Tsarki? Hakan ya nuna cewa a zamanin dā, an yi amfani da sunan Allah Jehobah ko Yahweh da haruffan Ibranancin nan YHWH. Wasu rubuce-rubucen da ke kogon sun nuna cewa mutanen da suke amfani da wurin ko kuma suke zuwa wurin don su ɓuya suna yawan rubuta sunan Allah ko kuma su rubuta sunansu da ke ɗauke da sunan Allah a bangon kogon.

Dakta Rachel Nabulsi da ke aiki a jami’ar Georgia ta yi magana game da wannan rubutun da aka yi. Ta ce: “Yadda aka yi amfani da sunan nan YHWH sau da sau yana da muhimmanci. . . . Rubutun ya nuna amfanin sunan Allah a rayuwar Isra’ilawa da kuma Yahudawa.” Hakan ya jitu da sunan Allah da aka rubuta cikin Littafi Mai Tsarki, wato YHWH a Ibrananci kuma ya bayyana sau dubbai. A yawancin lokuta, sunayen mutane a lokacin na ɗauke da sunan Allah.

Kalmomin nan “Yahweh Sabaot,” da aka rubuta a dutsen yana nufin “Jehobah mai runduna.” Hakan ya nuna cewa mutane a zamanin suna yawan amfani da sunan Jehobah da kuma furucin nan “Jehobah mai runduna.” Hakan ya kuma jitu da furucin nan “Jehobah mai runduna” da ya bayyana fiye da sau 250 a Nassosin Ibrananci, kuma a yawancin lokuta ya bayyana a littafin Ishaya da Irmiya da kuma Zakariya.