Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 3

Taro Mai Girma Suna Yabon Allah da Kristi

Taro Mai Girma Suna Yabon Allah da Kristi

“Ceto ya fito daga wurin Allahnmu ne, wannan da yake a zaune a kujerar mulki da kuma daga wurin Ɗan Ragon!”​—R. YAR. 7:10.

WAƘA TA 14 Mu Yabi Sabon Sarkinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya jawabin da aka yi a taron yanki a 1935 ya shafi wani matashi?

AKWAI wasu ma’aurata Shaidun Jehobah da suke da yara biyar kuma sun koya musu su bauta wa Jehobah, su kuma yi koyi da Yesu. Ɗaya daga cikin yaran ya yi baftisma a shekara ta 1926 sa’ad da yake ɗan shekara 18. Kamar yadda dukan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke yi a lokacin, wannan matashin yakan ci gurasa kuma ya sha ruwan inabi a kowace shekara da aka yi taron Tuna da Mutuwar Yesu. Amma, ra’ayinsa ya canja sa’ad da ya ji wani jawabi mai jigo “The Great Multitude” (Taro Mai Girma.) Ɗan’uwa J. F. Rutherford ne ya yi wannan jawabin a taron yanki da aka yi a shekara ta 1935 a Washington, D.C., a Amirka. Mene ne aka bayyana a wannan taron?

2. Wace koyarwa mai ƙayatarwa ce Ɗan’uwa Rutherford ya bayyana a jawabinsa?

2 A jawabin, Ɗan’uwa Rutherford ya bayyana ko su waye ne “babban taro,” wato “taro mai girma” da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:9. Kafin wannan taron, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun gaskata cewa taro mai girma su ne rukuni na biyu da za su je sama amma ba su da aminci kamar shafaffu. Ɗan’uwa Rutherford ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya bayyana cewa ba a zaɓi taro mai girma su yi rayuwa a sama ba, amma su ne waɗansu tumaki * da Yesu ya yi magana cewa za su tsira daga “azabar nan mai zafi,” wato ƙunci mai girma kuma su yi rayuwa har abada a duniya. (R. Yar. 7:14) Yesu ya yi alkawari cewa: “Ina da waɗansu tumaki kuma waɗanda ba na wannan garke ba ne. Su ma dole ne in kawo su. Za su kuwa saurari muryata, za su zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya kuma.” (Yoh. 10:16) Waɗannan tumakin su ne Shaidu masu aminci da suke da begen yin rayuwa har abada a Aljanna a duniya. (Mat. 25:​31-33, 46) Bari mu ga yadda wannan ƙarin hasken ya canja rayuwar mutanen Jehobah da yawa, har da wannan matashi ɗan shekara 18.​—Zab. 97:11; K. Mag. 4:18.

ƘARIN HASKE DA YA CANJA RAYUKAN DUBBAN MUTANE

3-4. A taron yanki da aka yi a 1935, mene ne mutane da yawa suka fahimta game da begensu, kuma me ya sa?

3 Mutane sun yi farin ciki sosai a wannan taron, musamman sa’ad da mai jawabin ya ce: “Don Allah dukan waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a duniya su tashi tsaye.” Wani ɗan’uwa da ke wannan taron ya ce mutane 20,000 ne suka halarci taron kuma fiye da rabi ne suka tashi. Sai Ɗan’uwa Rutherford ya ce: “Ku ga taro mai girma!” Bayan hakan mutane suka yi tafi sosai. Waɗanda suka tashi sun fahimci cewa Jehobah bai zaɓe su su je sama ba. Sun san cewa Allah bai shafe su da ruhunsa ba. Washegari, mutane 840 ne suka yi baftisma kuma yawancinsu suna da begen yin rayuwa a duniya.

4 Bayan wannan jawabin, matashin da aka ambata ɗazu da mutane dubbai sun daina cin gurasa da shan ruwan inabi a taron Tuna da Mutuwar Yesu. Mutane da yawa sun kasance da ra’ayin wani ɗan’uwa da ya ce: “Taron Tuna da Mutuwar Yesu da aka yi a 1935 ne rana ta ƙarshe da na ci gurasar kuma na sha ruwan inabin. Na daina yin hakan domin na fahimci cewa Jehobah bai zaɓe ni da ruhunsa don in yi rayuwa a sama ba. Maimakon haka, ina da begen yin rayuwa a duniya kuma in taimaka wajen mai da ta aljanna.” (Rom. 8:​16, 17; 2 Kor. 1:​21, 22) Tun lokacin, taro mai girma sun ƙaru sosai kuma suna aiki tare da shafaffu da suka rage a duniya. *

5. Yaya Jehobah yake ɗaukan waɗanda suka daina cin gurasar da shan ruwan inabin a taron Tuna da Mutuwar Yesu?

5 Ta yaya Jehobah ya ɗauki waɗanda suka daina cin gurasa da shan ruwan inabi bayan shekara ta 1935? Yaya Jehobah yake ɗaukan Mashaidin da yake cin gurasa da shan ruwan inabi a taron Tuna da Mutuwar Yesu, amma daga baya ya daina ci domin ya fahimci cewa Allah bai zaɓe shi ba? (1 Kor. 11:28) Wasu sun ci gurasar kuma sun sha ruwan inabin domin suna ganin cewa suna da begen zuwa sama. Amma idan sun gane cewa sun yi kuskure, suka daina cin gurasar da shan ruwan inabin kuma suka ci gaba da bauta wa Jehobah, zai amince da su a matsayin waɗansu tumaki. Ko da ba sa cin gurasar da shan ruwan inabin, suna halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu domin suna godiya don abin da Jehobah da Yesu suka yi musu.

BEGE NA MUSAMMAN

6. Mene ne Yesu ya umurci mala’iku su yi?

6 Domin za a yi ƙunci mai girma nan ba da daɗewa ba, zai dace mu tattauna abin da littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 7 ta ce game da Kiristoci shafaffu da kuma taro mai girma. Yohanna ya ga cewa Yesu ya umurci mala’iku su ci gaba da hana iskoki huɗu na duniya hurawa a kan ƙasa. Mala’ikun ba za su yi hakan ba har sai an yi wa dukan Kiristoci shafaffun hatimi, wato sun sami amincewar Jehobah. (R. Yar. 7:​1-4) Shafaffu za su sami ladar zama sarakuna da firistoci a sama domin sun riƙe amincinsu. (R. Yar. 20:6) Jehobah da Yesu da kuma mala’iku za su yi farin ciki sosai sa’ad da suka ga shafaffu 144,000 sun sami ladarsu.

Taro mai girma suna sanye da fararen tufafi, suna riƙe da ganyayen dabino kuma suna tsaye a gaban kursiyin Allah da kuma Ɗan ragon (Ka duba sakin layi na 7)

7. Kamar yadda littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 10 suka nuna, wane ne Yohanna ya gani a wahayi, kuma me suke yi? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

7 Yohanna ya ga wani abu da ya sa shi farin ciki bayan ya yi magana game da waɗannan sarakuna da firistoci guda 144,000. Ya ga “babban taro” da suka tsira daga Armageddon. Wannan rukunin ya fi waɗanda za su je sama yawa domin ba mu san ainihin adadinsu ba. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 10.) “Suna sanye da fararen riguna,” hakan ya nuna cewa ba su bar rayuwar duniyar nan ta ɓata su ba kuma sun kasance da aminci ga Allah da kuma Yesu. (Yaƙ. 1:27) Sun tā da murya suka ce an cece su domin abin da Jehobah da Yesu, Ɗan Ragon suka yi. Kuma suna riƙe da rassan itacen dabino, hakan yana nufin cewa sun amince da Yesu Sarkin da Jehobah ya naɗa.​—Gwada Yohanna 12:​12, 13.

8. Mene ne aka rubuta a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​11, 12 game da waɗanda suke sama?

8 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​11, 12. Mene ne ya faru sa’ad da waɗanda suke sama suka ga taro mai girma? Yohanna ya ga dukan waɗanda suke sama suna farin ciki kuma suna yabon Allah sa’ad da suka ga taro mai girma. Jehobah da Yesu da mala’iku da kuma shafaffu da aka tā da za su yi farin ciki ganin cikar wannan wahayin sa’ad da taro mai girma suka tsira daga ƙunci mai girma.

9. Kamar yadda aka nuna a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​13-15, mene ne taro mai girma suke yi yanzu?

9 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​13-15. Yohanna ya rubuta cewa taro mai girma “sun wanke rigunansu da jinin Ɗan Ragon, suka zama farare.” Hakan yana nufin cewa suna da lamiri mai kyau kuma Jehobah yana farin ciki da su. (Isha. 1:18) Su Kiristoci ne da suka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma sun yi baftisma. Ban da haka, sun ba da gaskiya ga hadayar Yesu kuma sun ƙulla dangantaka da Jehobah. (Yoh. 3:36; 1 Bit. 3:21) Shi ya sa Allah yake farin ciki da su kuma sun cancanci “yi masa hidima dare da rana” a nan duniya. A yanzu, su ne suka fi yin wa’azi game da Mulkin Allah da ƙwazo da kuma almajirtarwa domin abin da ya fi muhimmanci a gare su ke nan.​—Mat. 6:33; 24:14; 28:​19, 20.

Taro mai girma suna farin ciki don sun tsira daga ƙunci mai girma (Ka duba sakin layi na 10)

10. Wane tabbaci ne taro mai girma suke da shi, kuma wane alkawari ne za su ga cikarsa?

10 Taro mai girma da suka tsira daga ƙunci mai girma suna da tabbaci cewa Allah zai ci gaba da kula da su domin “wanda yake zaune a kan kujerar mulkin zai tsare su da tentin kasancewarsa.” Alkawarin da Allah ya yi da waɗansu tumaki suke jira zai cika. Ya ce: “[Allah] zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace.”​—R. Yar. 21:​3, 4.

11-12. (a) Kamar yadda aka nuna a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​16, 17, wace albarka ce taro mai girma za su samu a nan gaba? (b) Mene ne waɗansu tumaki za su iya yi a taron Tuna da Mutuwar Yesu, kuma me ya sa?

11 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​16, 17. A yanzu haka, wasu cikin mutanen Jehobah suna fama da yunwa domin rashin kuɗi ko kuma suna zama a wuraren da ake tashin hankali da yaƙe-yaƙe. An saka wasu a kurkuku domin imaninsu. Amma, taro mai girma suna farin ciki domin sun san cewa idan suka tsira daga halakar wannan duniya, za su sami isashen abinci da kuma koyarwar Jehobah. Sa’ad da Jehobah ya halaka wannan muguwar duniya, zai tabbata cewa ya kāre taro mai girma daga fushinsa da ke “ƙuna.” Bayan ƙunci mai girma, Yesu zai ja-goranci waɗanda suka tsira zuwa “ruwa mai ba da rai” na har abada. Babu shakka, taro mai girma suna da bege mai kyau domin a cikin biliyoyin mutane da suka taɓa rayuwa, wataƙila ba za su taɓa mutuwa ba!​—Yoh. 11:26.

12 Waɗansu tumaki suna godiya ga Jehobah da kuma Yesu don bege mai ban mamaki da suke da shi! Ko da yake Jehobah bai zaɓe su yin rayuwa a sama ba, yana ƙaunar su yadda yake ƙaunar shafaffu. Shafaffu da taro mai girma suna yabon Allah da kuma Kristi. Hanya ɗaya da suke yin hakan ita ce ta halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu.

KA YABI ALLAH DA ZUCIYA ƊAYA A TARON TUNA DA MUTUWAR YESU

Gurasa da ruwan inabi suna tuna mana cewa Yesu ya mutu a madadinmu don mu rayu (Ka duba sakin layi na 13-15)

13-14. Me ya sa ya kamata kowa ya halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu?

13 A kwana-kwanan nan, mutum 1 ne cikin mutane 1,000 da suka halarci taron ne yake cin gurasar da shan ruwan inabin. Hakan yana nufin cewa babu wanda yake cin gurasar da shan ruwan inabin a yawancin ikilisiyoyi a duniya. Yawancin mutanen da suke halartan taron suna da begen zama a duniya. To, me ya sa suke halartan taron? Mutane suna halartan bikin auren abokinsu domin su nuna suna ƙaunar ma’auratan kuma su tallafa musu. Hakazalika, waɗansu tumaki suna halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu domin su nuna cewa suna ƙaunar Kristi da shafaffu kuma su nuna goyon bayansu. Ƙari ga haka, waɗansu tumaki suna halartan taron don su nuna godiya ga hadayar Yesu da za ta sa ya yiwu su yi rayuwa a duniya har abada.

14 Wani dalili kuma da ya sa waɗansu tumaki suke halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu shi ne don su yi biyayya ga umurnin da Yesu ya ba da. A lokaci na farko da Yesu ya yi wannan taro na musamman da manzanninsa masu aminci, ya ce: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.” (1 Kor. 11:​23-26) Waɗansu tumaki za su ci gaba da halartan wannan taron har sai shafaffu da suka rage sun bar duniya. Shi ya sa waɗansu tumaki suke gayyatar mutane su halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu tare da su.

15. Ta yaya kowannenmu zai yabi Allah da kuma Kristi a taron Tuna da Mutuwar Yesu?

15 A taron, muna da damar yabon Allah da Kristi sa’ad da muka yi waƙa da addu’a tare. Jigon jawabin da za a yi wannan shekarar shi ne “Ka Nuna Godiya Don Abin da Allah da Kristi Suka Yi Maka!” Jawabin zai sa mu daɗa nuna godiya ga Jehobah da kuma Kristi. Yayin da ake zagayawa da gurasar da ruwan inabin, hakan zai tuna mana cewa suna wakiltar jini da jikin Yesu. Za mu kuma tuna cewa Jehobah ya ƙyale Ɗansa ya mutu a madadinmu don mu rayu. (Mat. 20:28) Duk wanda yake ƙaunar Ubanmu wanda ke sama da kuma Ɗansa zai so ya halarci wannan taron.

KA GODE WA JEHOBAH DON BEGEN DA YA BA KA

16. Waɗanne alaƙa ne ke tsakanin shafaffu da waɗansu tumaki?

16 Yadda Jehobah yake ƙaunar shafaffu, haka yake ƙaunar waɗansu tumaki. Dalilin da ya sa muka faɗi hakan shi ne, ya yi amfani ne da ran Ɗansa don ya fanshi shafaffu da waɗansu tumaki. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne kawai shafaffu za su je sama, waɗansu tumaki kuma za su rayu a duniya har abada. Dole ne dukansu su kasance da aminci ga Allah da kuma Kristi. (Zab. 31:23) Kuma ka tuna cewa Jehobah yana ba kowannenmu yawan ruhu mai tsarki da muke bukata bisa ga yanayin da muke ciki, ko da mu shafaffu ne ko waɗansu tumaki.

17. Mene ne shafaffun da suka rage a duniya suke ɗokin samu?

17 Ba a haifi Shafaffun Kiristoci da begen zuwa sama ba. Allah ne ke ba su begen. Suna tunani a kan begensu, suna yin addu’a game da shi kuma suna ɗokin samun ladarsu a sama. Ba su san yadda jikinsu zai kasance a sama ba. (Filib. 3:​20, 21; 1 Yoh. 3:2) Duk da haka, suna ɗokin ganin Jehobah da Yesu da mala’iku da sauran shafaffu don su kasance a Mulkin sama.

18. Mene ne waɗansu tumaki suke ɗokin gani?

18 Waɗansu tumaki suna ɗokin yin rayuwa har abada a duniya. Kuma wannan burin ne ’yan Adam suke da shi. (M. Wa. 3:11) Suna ɗokin ganin ranar da za su taimaka wajen mai da dukan duniya zuwa aljanna. Suna marmarin ganin ranar da za su iya gina gidajensu, su shuka gonakinsu kuma su yi renon yaransu a cikin ƙoshin lafiya. (Isha. 65:​21-23) Suna ɗokin ganin lokacin da za su yi tafiya zuwa wurare da yawa a duniya don su ga tuddai da daji da tekuna kuma su yi nazarin dukan abubuwan da Jehobah ya halitta. Amma sun fi farin ciki sanin cewa dangantakarsu da Jehobah za ta yi danƙo sosai.

19. Wace dama ce taron Tuna da Mutuwar Yesu ya ba kowannenmu, kuma a wane lokaci ne za a yi taron a wannan shekarar?

19 Jehobah ya ba kowanne cikin bayinsa bege mai ban mamaki. (Irm. 29:11) Taron Tuna da Mutuwar Yesu yana ba kowannenmu damar yabon Allah da kuma Kristi domin abin da suka yi don mu more rayuwa har abada. Babu shakka, wannan ne taro mafi muhimmanci da Kiristoci suke yi a kowace shekara. Za a yi wannan taron a ranar Asabar, 27 ga Maris, 2021, bayan faɗuwar rana. A wannan shekarar, mutane da yawa za su halarci wannan taro mai muhimmanci ba tare da wani takunkumi ba. Wasu za su halarci taron duk da cewa ana tsananta musu. Wasu kuma za su yi wannan taron duk da cewa suna kurkuku. Yayin da Jehobah da Yesu da mala’iku da kuma shafaffu da aka tā da suke kallo daga sama, bari kowace ikilisiya da rukuni da kuma kowane mutum ya ji daɗin wannan taro na musamman!

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

^ sakin layi na 5 Ranar 27 ga Maris, 2021, rana ce ta musamman ga Shaidun Jehobah. Da yamman nan za mu yi taron Tuna da Mutuwar Yesu. Yawancin waɗanda za su halarci wannan taron suna cikin rukunin da Yesu ya kira “waɗansu tumaki.” Mene ne Shaidun Jehobah suka koya game da wannan rukunin a shekara ta 1935? Mene ne waɗansu tumaki suke ɗokin samu bayan ƙunci mai girma? Ta yaya waɗansu tumaki za su yabi Allah da kuma Kristi sa’ad da suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu?

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Waɗansu tumaki su ne dukan bayin Jehobah har da waɗanda suka zama bayinsa a kwanaki na ƙarshe. Kuma suna da begen yin rayuwa har abada a duniya. Taro mai girma su ne mutanen da suka shaida lokacin da Yesu Kristi yake wa mutane shari’a a lokacin ƙunci mai girma, kuma suka tsira.

^ sakin layi na 4 MA’ANAR WASU KALMOMI: Furucin nan “shafaffu da suka rage” yana nufin mutanen da suke cin gurasa da shan ruwan inabi a taron Tuna da Mutuwar Yesu da suke duniya har yanzu.