Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A wane lokaci ne mutanen Allah suka zama bayi ko fursunoni na Babila Babba?

Hakan ya soma faruwa wani lokaci bayan shekara ta 100 zuwa shekara ta 1919. Me ya sa wannan sabon fahimta yake da muhimmanci sosai?

Shafaffun Kiristoci sun sami ‘yanci daga Babila Babba, wato addinin ƙarya kuma aka tsara su a cikin ikilisiyar da aka tsarkake. Dukan hujjojin da muke da su sun nuna cewa a shekara ta 1919 ne hakan ya faru. Ka yi tunanin wannan: Ba da daɗewa ba bayan Mulkin Allah ya soma sarauta a sama a shekara ta 1914, an gwada mutanen Allah kuma a hankali aka soma fitar da su daga addinan ƙarya. * (Ka duba ƙarin bayani.) (Malakai 3:​1-4) Bayan hakan, a shekara ta 1919, Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” domin ya ba wa mutanen Allah da aka tsarkake “abincinsu a lotonsa.” (Matta 24:​45-47) Har ila, a wannan shekarar ce mutanen Allah suka sami ‘yanci daga dukan addinan ƙarya wato, Babila Babba. (Ru’ya ta Yohanna 18:⁠4) Shin a wane lokaci ne mutanen Allah suka zama bayi?

A dā, mun bayyana cewa mutanen Allah sun zama bayi na Babila Babba na wani gajeran lokaci, somawa daga shekara ta 1918. A cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga watan Maris, 1992 na Turanci, an bayyana cewa kamar yadda Isra’ilawa suka je bauta a Babila, hakazalika mutanen Jehobah sun zama bayi na Babila babba a shekara ta 1918. Amma binciken da muka yi ya nuna cewa mutanen Allah sun zama bayi ɗarurruwan shekaru kafin shekara ta 1918.

A cikin littafin Ezekiyel 37:​1-14, an yi annabci cewa mutanen Allah za su zama bayi kuma daga baya za su sami ‘yanci. Ezekiyel ya ga wahayin wani kwari da ke cike da ƙasusuwa. Jehobah ya ce masa: “Waɗannan ƙasusuwan jama’ar gidan Isra’ila ne.” (Aya ta 11) Wannan annabcin ya shafi al’ummar Isra’ila kuma daga baya, ya shafi “Isra’ila na Allah” wato shafaffu. (Galatiyawa 6:16; Ayyukan Manzanni 3:21) A cikin wahayin, ƙasusuwan sun yi rai kuma sun zama runduna mai-girma ƙwarai. Hakan ya kwatanta yadda mutanen Allah za su sami ‘yanci daga Babila Babba a shekara ta 1919. Amma ta yaya wannan annabcin ya nuna cewa sun daɗe da zama bayi?

Da farko, Ezekiyel ya lura cewa ƙasusuwan mutanen da suka mutu “busassu ne sosai.” (Ezekiyel 37:2, 11) Hakan yana nufin cewa mutanen sun daɗe da mutuwa. Na biyu, Ezekiyel ya ga cewa waɗannan matattu sun sake rayuwa sannu a hankali, ba nan take ba. Ya ji an yi “cida, ga kuma rawan ƙasa, ƙasusuwa suka harhaɗu, kowane ƙashi ga ɗan’uwansa.” Bayan haka, sai ya ga “jijiyoyi a kansu, nama” ya rufe ƙasusuwan. Daga nan, sai “fata ta rufe su.” Bayan haka, “numfashi kuwa ya zo cikinsu, suka yi rai.” Daga ƙarshe, bayan mutanen suka soma rayuwa, Jehobah ya ba su ƙasar da za su zauna a ciki. Duka waɗannan abubuwan za su ɗauki lokaci.​—⁠Ezekiyel 37:​7-10, 14.

Kamar yadda aka yi annabcin, Isra’ilawa sun yi bauta a wasu ƙasashe dabam-dabam na tsawon lokaci. Sun soma bauta a shekara ta 740 kafin haihuwar Yesu sa’ad da aka tilasta wa ƙabilu goma na Isra’ila wato mulkin arewacin ƙasar su bar ƙasarsu. Daga baya, a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu, Babiloniyawa sun halaka Urushalima kuma aka tilasta wa sauran ƙabilu biyu na Isra’ila wato mulkin kudanci na Yahuda su bar ƙasarsu. Bayan haka, a shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu, an sake su kuma wani ƙaramin rukunin Yahudawa suka koma Urushalima kuma sake gina haikali don su ci gaba da bauta wa Jehobah.

Dukan waɗannan bayanai sun nuna cewa shafaffu Kiristoci sun zama bayin Babila Babba na tsawon lokaci, ba kawai daga shekara ta 1918 zuwa 1919 ba. Sa’ad da Yesu ya ce Kiristoci na ƙarya wato ciyawa za su girma tare da alkama ko kuma “ ’ya’yan Mulki,” ya yi magana game da wannan lokaci mai tsawo. (Matta 13:​36-43) A wannan lokacin, Kiristoci na gaskiya ba su da yawa. Yawancin waɗanda suka ce su Kiristoci ne sun bi koyarwar ƙarya kuma suka zama ‘yan ridda. Shi ya sa muka ce ikilisiyar Kirista sun zama bayin Babila Babba. Wannan bauta ta soma bayan shekara ta 100 kuma ta ci gaba har lokacin da aka tsarkake haikali na Allah a kwanaki na ƙarshe.​—⁠Ayyukan Manzanni 20:​29, 30; 2 Tasalonikawa 2:​3, 6; 1 Yohanna 2:​18, 19.

A waɗannan shekaru, shugabannin coci da shugabannin gwamnatoci suna tilasta wa jama’a su bi ra’ayinsu. Alal misali, ba sa yarda mutane su karanta Littafi Mai Tsarki balle su karanta a yaren da za su iya fahimta. An ƙona wasu mutane da suka karanta Littafi Mai Tsarki a kan gungume. Ƙari ga haka, an hukunta duk waɗanda suka yi adawa da abin da limaman coci suke koyarwa. Hakan ya sa koyan gaskiya game da Allah da kuma sanar da shi ga wasu ya kasance da wuya sosai.

Wani darasi da muka koya daga wahayin Ezekiyel shi ne cewa mutanen Allah sun soma rayuwa kuma an fitar da su daga addinan ƙarya sannu a hankali. Shin a wane lokaci ne hakan ya faru kuma ta yaya? Wannan wahayi ya ambata “rawan ƙasa.” Hakan ya soma faruwa wasu ‘yan ƙarnuka kafin kwanaki na ƙarshe. A lokacin, akwai wasu amintattun mutane da suke so su koyi gaskiya game da Allah kuma su bauta masa duk da cewa koyarwar ƙarya ta zama ruwan dare a lokacin. Sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma sun yi iya ƙoƙarin su su koya wa mutane abin da suke koya. Wasu sun yi aiki sosai don su fassara Littafi Mai Tsarki zuwa yarukan da mutane za su fahimta.

A kusan ƙarshen ƙarni na 19, sai ya zama kamar nama da fata suna rufe ƙasusuwan. Charles Taze Russell da kuma wasu abokansa sun yi iya ƙoƙarin su don su fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma su bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, sun yi amfani da Hasumiyar Tsaro da wasu littatafai don su taimakawa mutane su fahimci gaskiya game da Allah. Bayan haka, a shekara ta 1914 sun fito da fim ɗin nan “Photo-Drama of Creation” kuma suka fitar da littafin nan The Finished Mystery a shekara ta 1917. Waɗannan abubuwan sun taimaka wa mutane Jehobah su ƙarfafa bangaskiyarsu. A shekara ta 1919, kamar dai an ba wa mutanen Allah rai da kuma sabuwar ƙasa da za su zauna a ciki. Tun daga lokacin, waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya har abada suna aiki tare da shafaffu. Yanzu suna bauta wa Jehobah tare kuma sun zama “runduna . . . mai-girma ƙwarai.”​—⁠Ezekiyel 37:10; Zakariya 8:​20-23. *​—⁠Ka duba ƙarin bayani.

A bayyane yake cewa mutanen Allah sun zama bayi na Babila Babba wajen shekara ta 100 bayan haihuwar Yesu. A wannan lokacin ne mutane da yawa suka yi watsi da koyarwar gaskiya game da Allah kuma suka soma bin koyarwar ƙarya. Kari ga haka, sun zama ‘yan ridda. Hakan ya sa ya kasance da wuya a bauta wa Jehobah kamar yadda ya yi wa Isra’ilawa wuya sa’ad da suke bauta a Babila. Amma a yau, ana sanar da dukan mutane gaskiya game da Allah. Muna farin ciki cewa muna rayuwa a wannan lokacin da “waɗanda ke da hikima . . . za su haskaka”! Yanzu, mutane da yawa za su iya “tsarkake kansu” kuma “su tsabtata” don su soma bauta ta gaskiya!​—⁠Daniyel 12:​3, 10.

Shaiɗan ya jarabci Yesu a haikali na zahiri ne, ko kuma a wahayi?

Ba mu san ainihin yadda Shaiɗan ya nuna wa Yesu haikalin ba.

Matta da Luka marubutan Littafi Mai Tsarki sun rubuta abin da ya faru. Matta ya ce ‘Shaiɗan ya ɗauki’ Yesu zuwa Urushalima kuma ya ‘tsayar da shi a kan hasumiya ta haikali’ wato wurin da ya “fi tsayi” a haikalin. (Matta 4:⁠5) Luka ya ce: Iblis ‘ya kai shi Urushalima, ya tsayar da shi a bisa hasumiya ta haikali.’​—⁠Luka 4:⁠9.

A dā, an bayyana a littattafanmu cewa sa’ad da Shaiɗan yake so ya jarabce Yesu, yana iya yiwuwa cewa bai kai Yesu haikali na zahiri ba. A Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 1961, an kwatanta hakan da lokacin da Shaiɗan ya so ya jarabci Yesu ta wajen nuna masa dukan mulkokin duniya daga wani dutse mai tsawo. An bayyana a cikin mujallar cewa babu wani dutse mai tsawo da mutum zai iya tsayawa a kai kuma ya ga dukan mulkokin duniya daga wurin. Ƙari ga haka, Hasumiyar Tsaro ta ce, hakazalika, Shaiɗan bai ɗauki Yesu ya kai shi haikali na zahiri ba. Amma, daga baya an bayyana a wasu talifofin Hasumiyar Tsaro cewa da a ce Yesu ya yi tsalle daga haikalin mai yiwuwa da ya mutu.

Waɗansu sun ce, da yake Yesu ba Balawi ba ne, da ba a yarda ya hau kan haikalin ba. Saboda haka, sun ce Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya jarabci Yesu a cikin wahayi. Shekaru da yawa kafin zamanin Yesu, an kai Ezekiel wani haikali a wahayi.​—⁠Ezekiyel 8:​3, 7-10; 11:​1,24; 37:​1, 2.

Amma idan da gaske ne cewa Shaiɗan ya kai Yesu haikali a cikin wahayi, wasu suna iya yin tunani cewa:

  • Shin da Yesu ya yi tunanin yin tsalle daga haikalin ne?

  • A wani lokaci, Shaiɗan ya umurci Yesu ya mai da duwatsu su zama gurasa, kuma ya yi masa sujjada. Tun da haka ne, yana yiwuwa cewa ya so Yesu ya yi tsalle daga kan haikali na zahiri ne?

Amma idan Shaiɗan bai kai Yesu haikalin ta wahayi ba, wasu za su iya yin tunani cewa:

  • Shin Yesu ya ƙarya doka ne da ya tsaya a kan haikalin?

  • Ta yaya Yesu ya tashi daga daji zuwa haikalin da ke Urushalima?

Bari mu tattauna wani ƙarin bayani da zai taimaka mana mu amsa waɗannan tambayoyi biyu.

Wani farfesa mai suna D. A. Carson ya rubuta cewa kalmar Helenanci da Matta da Luka suka yi amfani da ita wajen kwatanta “haikali” za ta iya nufin harabar haikalin baki ɗaya, ba mazaunin da Lawiyawa kawai ne ke da izinin zuwa ba. Ɓangaren kudu maso gabas na haikalin yana da rufi da za a iya tsayawa a kansa kuma wurin ne ya fi tsawo a haikalin. Wataƙila a kan wannan rufin ne aka saka Yesu. Nisan wajen zuwa ramin Kidron kafa 450 ne. Wani masanin tarihi mai suna Josephus ya ce wannan ɓangaren rufin yana da tsawon kuma idan mutum ya tsaya daga wurin kuma ya dubi ƙasa, zai “yi jiri.” Ko da yake Yesu ba Balawi ba ne, zai iya tsaya a wurin ba wanda zai ce ya yi laifi.

Ta yaya Yesu ya tashi daga daji kuma ya je haikalin da ke Urushalima? Ba mu sani ba. Littafi Mai Tsarki kawai ya ce an kai Yesu Urushalima. Littafi bai ambata nisan wurin da Yesu yake daga Urushalima ko kuma tsawon lokacin da Shaiɗan ya jarabce shi ba. Amma zai iya yiwu cewa Yesu ya taka ne zuwa Urushalima, ko da yake hakan zai iya ɗaukan dogon lokaci.

Wataƙila Shaiɗan ya yi amfani da wahayi ne a lokacin da ya nuna wa Yesu “dukan mulkokin duniya.” Domin ba wani dutse a duniyar nan da mutum zai iya tsayawa ya ga dukan waɗannan mulkokin duniya. Za a iya kwatanta irin wannan yanayin da yin amfani da bidiyo wajen nuna wa mutum waɗansu ɓangarorin duniya. Wataƙila Shaiɗan ya yi amfani da wahayi kuma burinsa shi ne Yesu ya yi masa sujjada. (Matta 4:​8, 9) Saboda haka, lokacin da Shaiɗan ya kai Yesu haikali, yana so Yesu ya sa ransa cikin kasada ta wajen yin tsalle daga kan haikalin. Amma Yesu ya ƙi yin hakan. Da a ce a wahayi ne aka jarabci Yesu, da wuya a ce jaraba ne da gaske!

Saboda haka, zai yiwu cewa Yesu ya je Urushalima kuma ya tsaya a kan wurin da ya fi tsayi a haikalin. Hakika, kamar yadda aka faɗa a farkon talifin nan, ba mu san ainihin yadda Shaiɗan ya nuna wa Yesu haikalin ba. Abin da muka sani shi ne Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya sa Yesu ya yi zunubi amma Yesu ya nace kuma Shaiɗan bai yi nasara ba.

^ sakin layi na 2 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga watan Yuli, 2013, shafuffuka na 11-12, sakin layin na 5-8 da 12.

^ sakin layi na 2 Annabcin da aka rubuta a Ezekiyel 37:​1-14 da kuma Ru’ya ta Yohanna 11:​7-12 sun cika a shekara ta 1919. Annabcin da ke cikin littafin Ezekiyel 37:​1-14 yana nufin yadda dukan mutanen Allah suka soma ibada ta gaskiya bayan zaman bauta da suka yi na tsawon lokaci. Amma annabcin da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna 11:​7-12 yana magana game da wani ƙaramin rukunin ‘yan’uwa shafaffu da suka soma ja-gorar mutanen Allah a shekara ta 1919 kamar yadda yake a ƙarni na farko. Waɗannan ‘yan’uwa ba su samu sun yi aiki da ƙwazo na ɗan wani lokaci ba.